Showing 78001 words to 81000 words out of 123632 words
ya shiga dakin da Mami take yace "anga Bilkisu kije gida kuyi girki dan zamu dawo da bakin da suka kawota, kibar kuka Boy ya warke haha" yay dariya kafin ma Mami ta jefamai wata tambaya haryabi bayan su Abba da gudu duk suka shiga mota sai headquarter.
Tun kafin suyi parking suka hango Cp yana washe musu baki dan kasa hakura yayi ya zauna aciki so kawai yake dashi Alhaji ma zasu fara haduwa, fito da Ayaan sukayi dake bude ido da kyar Cp yakara so wajen yana kallon Ayaan dake kallonshi da idanunshi dasuka kankance yace "ciwo ya kare, muje Alhaji suna office dina" yana gaba suna biye dashi abaya har upstairs Cp ne yabude office din ya shiga suna biye dashi, daidai lokacin Bilkisu ta daura hanunta akan kafadar Aaman tanason ta leka meyake nunama Dr Ameenu awayan shi dayan hanunta kuma rike da pringles takai baki tana gutsura. Dukansu binta sukai da kallo harda Ayaan daya kara bude ido da kyau yana kallonta tundaga yatsar kafarta har zuwa kanta, dago dakai sukayi jin anbude kofa da sauri Aaman ya ture hanunta daga kafadar shi suka mimmike tsaye shida Dr dan daga ganin su sun gane family tane sabida manyan kayan dasuka sa, hannu suka mika ma su Abba daduk Bilkisu suke kallo barinma Ayaan dako kyafta ido bayayi, itakuma tana zaune tanacin pringles dinta batare datama kallesu ba, ga teddy ta agefe, ajiye pringles dinta tayi tadau bottle wata dinta ta mike tsaye ta kusa da Aaman kaman zata shiga jikinshi ta mikamai ruwan kaman zatai kuka tace "sweetheart budemini" wani irin mugun tari da Ayaan yafara yasa ta juyo dakai tana kallonsu barinma mai tarin da manyan mutanen ke kokarin rikeshi ganin yana neman shidewa, da sauri ta boye abayan Aaman tasa hannu ta dafashi ta leko dakai tana kallon mutanen dai dai, hada ido suk sakeyi da me tarin da idanunshi sukai jajir yana tari yana kallonta jijiyoyin kanshi duk sun fito shikuma Aaman sai kokarin tureta yake daga bayan shi amma taki saima kara rirrike mai riga datayi tabaya tana make kafada tana "oh'oh" shikuma yacigaba da tureta, wani irin kallo Ayaan yama Aaman kirjinshi na wani irin zafi kaman an juye garwashin wuta daidai lokacin wani dan Sanda ya shigo dakin hanunshi rike da kulki, fizge jikinshi Ayaan yayi daga hannun Abba da duka karfin dayazo mai, yatako ya fizge kulkin hanun dan sandan daya shigo azuciye yay kan Aaman.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
67 - 68
Da sauri Cp da dan sanan daya fizge Mullin daga hanunshi harda Baba Sulaiman suka rike gam gam, Baba Sulaiman yace "Ayaan are u okay" kokarin watsa dasu yake yana ma Aaman wani irin kallo shima Aaman kallon shi yake irin kallon wanne wanan Kuma, Abba ne ya karbe kulkin daga hanun nashi ya zaunar dashi da kyar ya zauna akan kujeran amma gabaki daya baida natsuwa ahankali Abba ke tofamai addu'a Cp kuma ya kalli su Aaman da har lokacin suke tsaye ga Bilkisu dahar lokacin ke tsaye abayan shi ta rike mai riga yace "ku zauna" Baba dai har lokacin yakasa daina kallon Bilkisu mamakin yanda tarike wani namiji agabanshi ko kunyar shi da tsoron shi ma da bataji ba shiya hanashi magana, he's totally shock, dauko file dinta dake kan table Cp yayi yazo har gaban Abba dake gayama Ayaan da kanshi ke kasa yana wani irin numfarfashi magana a kunne ya mikama Abba file din yace "gashi Alhaji medical record dinta ne, sanadi yar faduwar nan datayi tasami tabin kwakwalwa banda haka tasami memory loss" da sauri Ayaan yadago kai da jajayen idanunshi ya kalli Cp da sauri ya karbi record din ya bude file din yana duddubawa yana karanatawa hanunshi har rawa yake saida yagama karance wa tass sanan yadago kai ya kalleta tana kusa kusa da Aaman kaman zata shige jikinshi tadau teddy tanata jijjigata tana wasa, wani irin zafi dayaji zuciyarshi nayi yasa yaji wasu irin zafafan hawaye naso su xubomai, Abba daya gama karantan dan nashi tsaf ya mike tsaye murmushi kwance akan fuskarshi ya karasa gaban su Aaman ya mika musu hannu yace "mungode, mungode, ubangiji Allah ya biyaku, dan Allah karku cemin a'a kuzo muje gida munsa muku girki dan Allah ya'yana karkuce bazakuba" yay maganan yana kallon su harda Dr, sosai nauyin Abba ya kamasu hakan yasa yace "to Abba" Cp ya mikama police din daya shigo plain sheet da pen ya kalli Aaman yace "zaka iya suffan tamana samari biyar dasuka fito da ita daga bakin motar" dan shiru yayi saikuma yace "yea" nan ya dinga siffanta su police din na zanasu saiko ga sketch din fuskar su Abba ya karba yana kallo babu wanda ya gane cikin su daga nan Abba yace sutafi, mikewa yayi da sauri tamike itama tana kokarin rikoshi Baba ya daka mata wani irin tsawa. "Bilkisu kewai mehaka" dago kai tayi ta kalli Baba saikuma ta murguda baki tana bobboyewa abayan Aaman tace "ni sunana Ameerah ko sweetheart" baya Ayaan yayi zai fadi sabida wani irin jiri dayake dibanshi da sauri Abba ya rikeshi ya kalli Baba yace "kasan bata hayyacin ta karka ga laifin ta" ya kalli Aaman dake faman tureta daga bayanshi yace "kumu tafi yan albarka" murmushi yayi yace "to Abba" su Abba suka rike Ayaan suka fita dashi. Da sauri Aaman ya juyo ranshi ya mugun baci yace "d next time dakika rikeni ko shigewa jikinta saina mareki naughty girl" yay gaba da sauri tsabagen haushi, Dr ya kalleta yanda take goge kwalla ahankali yace "muje" murguda mai baki tayi tana goge kwalla tabi bayan shi suka fita daga office din. Suna kaiwa waje Aaman ya nuna mata motan su Abba yace "jeki shiga motan su Abba" kallon su Abba tayi yanda duk suka tsatsaya suna kallonta barin ma Ayaan kaman zai hadiye ta, ta murguda musu baki tace "oh'oh ni namu zamu shiga" murmushi Abba yayi yace "bakomi kabarta anan muje" da sauri tabude baya ta shiga sukuma suka shiga gaba Abba ya kalli Ayaan yanda yake kallon su ahankali yace "Boy control your heart kar zuciyan ka ta buga haba dan Allah zaka halaka kanka ne jibi yanda kirjinka ke bugu, let's go" bude mota yayi ya saka shi ciki sanan ya shiga shima driver yajasu sukabar wajen motar su Aaman biye da ita har gidansu sukai horn security yabude, sukai parking suka fiffito tana makale kusa da Aaman har suka je part din Mami dayake Big Mummy taje bikin yar kawarta sai Kalle Kallen gidan take tana washe baki tana kallon fuskar Aaman murya chan tace "sweetheart nanne garin namu" ko kallonta baiyiba, babban falon Mami Abba yamusu iso suka zazzauna tana kusa da Aaman, ahankali Mami ke saukowa daga sama cikin shiga ta alfarma idanunta akan Bilkisu dake zaune kusa da wani tana wasa ta teddy Ayaan sai kallonta yake kaman ya hadiye ta, su Abba ma duk ita suke kallo har gabanta Mami tazo zata rungumeta da sauri ta matsa kusa da Aaman tana make kafada hakan yasa Mami tace "Bilkisu" murguda baki tayi tace "Ameerah sunana" tai maganan kaman zatai kuka, kasa magana Mami tayi ta tsaya tana kallonta Abba ne yay jarumtar cewa. "batada lafiya ne Firdausi, je akawo musu abinci" tadade tana kallon Bilkisu gaisuwar dasu Aaman kemata ne yasa ta farka ta amsa musu tana murmushi kafin ta juya tai kitchen nan tasaka yan aiki suka wadata su da abinci da abubuwan sha amma sun kasa ci sabida kunya drinks kawai suka sha shidai Ayaan jingina yay da kujera ya lumshe ido kaman mai bacci amma Bilkisu yake kallo bakaramin daurewa yayiba danji yake kaman ya kashe wanan mutumin datake ta manne mawa, Abba ne yay gyaran murya yace "godiya zan kara muku yarana yanda kuka taimaka mana kuka taimaki yarmu kuka sakamu acikin farin ciki ubangiji Allah ya faran ta muku haka ranan gobe kiyama" ya nuna malam yace "wanan shine mahaifin Bilkisu, ga Sulaimanu shikuma kanina ne, nikuma nine mahaifin mijin Bilkisu" wani irin bugawa kirjin Aaman yayi kafin ya farka daga hakan Abba yanuna Ayaan dake kusa dashi yace "gakuma mijin ta nan" saiya nuna Mami dake zaune gefen Baba Sulaiman yace "ga mahaifiyar shi chan" innalillahi wa innalillahi raji'un kawai Aaman ke ambata aranshi, da hikima batare dawani ya lura ba yakara matsawa daga kusa da ita yanda ta shige mai, wani irin zafi zuciyarshi keyi wasu irin hawaye masu dumi ne suka taru a idonshi ya saci kallon Dr da shiyake kallo shima, ahankali ya girgiza mai kai hakan yasa ya hadiye hawayen da kyar ya kakalo murmushi yadan kalli Ayaan aranshi yace no wonder dazu yayo kanshi baikawo komi dazu ba dan yazaci hala mutumin ya dauka sune suka saceta saisa yay haka ashe shine mijinta, ashe Ameerah matar aure ce, maganar Bilkisu ce yasa yadawo daga dogon zancen zucin dayake ta matso kusa dashi sosai tana nunamai pin din gyalen da Ummy tasaka mata takama rolling gyalen dashi ashagwbe tace "Sweetheart remove it for m..." bata karashe maganan ba sabida wani irin mugun tari daya turnike Ayaan akaro nabiyu da sauri Abba ya dau goran ruwa ya bude yabashi ture ruwan yayi azuciye yanaso ya mike tsaye Abba ya take kafarshi yasan halin danshi koba komi shiya taimaketa kuma Bilkisu bata hayyacin ta. "sweetheart plz cire" takara matso da kanta tanaso tamai kuka da sauri ya mike tsaye ya kalli su Abba yana kakalo murmushin dole yace "zamu koma yanzu karmuyi dare" kafin Abba dasu Baba da Mami dasuka Mike tsaye suma suyi magana Bilkisu tace "yeee zamu tafi, uhnn sweetheart fitsari nakeji jirani nayi" saikuma takara matsowa kusa dashi tace "where is d restroom" da kyar ya tattaro kalaman dake bakinshi dayay nauyi sosai ya nuna mata Mami yace "ga Mum nan je ta kaiki kiyi" kallon fuskarshi tayi jin yanda yay magana saikuma ta washe mai baki tace "okay wait for me" ta sakamai teddy ta ahannu tace "hold my teddy" da sauri tai wurin Mami dake kallonta ta washe mata baki tace "Mum muje" hanunta Mami takama suka hau stairs sai juyowa take tana kallon Aaman tana washe baki har sukai sama da kyar ya kakalo murmushi yace "mutafi Abba kafin tafito" rakasu su Abba sukayi har waje suka karbi number su shidai Ayaan yana zaune falo suna fita ya mike da kyar yay upstairs yay dakin Mami yabude kofa ya shiga Mami ce kadai adakin zaune tana jiranta tana ganinshi ta mike tsaye tai murmushi tace "bari naje nahado mata abinci bataci komiba" tafita daga dakin, kimono ta da gyalen ta dake kan gadon yabi da kallo ahankali ya zauna akan gadon yadau kimono ya rungume sosai yana shakan kamshin dasuke fitarwa, karan bude kofar bathroom dayaji yasa ya zame rigan daya fuskarshi bama ta lura dashi ba tafito tana kokarin jan straight skirt dinta data tattare ta barshi a cinya zuwa kasa, tundaga kai yake kallonta har yatsa, kallon black body hug din da tasa yayi ba karamin kyau yamata ba gashi ya kamata yabi jikinta hakan saiya kara bayyana cikan kirjinta dago dakai tayi bayan tagama jan skirt din yakai kasa ta kalleshi bata damu da ganinshi ba amma ganin rigan ta da gyalen ta a hanunshi yasa ta daure fuska a tsiwace ta rike kugu tana hararan shi, dan lumshe ido yayi yakara budesu ya sauke akan fuskar ta, cike da masifa tayo cikin dakin agaban shi ta tsaya ta murguda mai baki ta mikamai hannu tace "bani rigana aiba naka bane, sweetheart yasaimin" wani irin fizgota dayayi saida tafado jikinshi, gyara mata zama yayi ajikinshi tana mutsu mutsun ta sauka ya sakala hanunshi ta bayanta ya riketa gam yana numfashi da sauri da sauri yana kallon kwayar idonta, murguda mai baki take iya karfin ta tana kokarin kwace kanta ganin takasa yasa tace "leave me" tai maganan tana kokarin kwace kanta, ganin yaki sakinta sai wani irin kallo dayake yasa ta daddage takai bakinta saitin kafadar shi ta daddage ta sakinmai cizo mai shegen zafi da kanta tasaki fatar tashi ta dago kai tana kallon fuskarshi ganin ko gezau baiyiba ita yake kallon har lokacin idanunshi sunyi jajir, ahankali yadaura kanshi akan kirjinta wlh takusa suma ya kankame ta sosai muryan shi nawani irin rawa yace "am sorry wife, am sorry, I've done alot of things to you, please kiyafe min am sorr..." yakasa karashe maganan sai kuka, cusa kanshi yayi a kirjinta sosai yafashe da kuka irin wanda daga shi sai ita zasu dinga jin karan, duk hankalin ta yatashi me haka wanan mutumin yakeyi yawani daura kanshi akan nonon ta yana kuka, jikinta nema yafara rawa tasa hannu tana ture kanshi tace "leave me, let go off me" dago jajayen idanunshi yayi ya kalleta dasu, kara ware ido tayi ta bude baki tana kallonshi cike da mamaki hawayen data gani, ahankali takai karama yatsar ta ta dangwalo hawayen dake gangarawa kuncinshi ta kalla hawaye ne da gaske ware ido tayi tace "laaaa dama babba na kuka, nidai ka sakeni kai, I want to go, mehaka mtsww" tai tsaki tana ballamai harara, wani irin kuka dayaji yasake zuwan mai yasa yasake maida kanshi jikinta ya rungumota sosai kaman zai maidata ciki yace "am sorr..." sosai yafashe da kuka yakasa magana, shi kadai yasan yanda yakeji aranshi. Tureshi ta shiga yi dukta rude tafashe da kuka sosai ta kwala ihu. "wayyo Allah na Sweetheart come" dago rinannun idanunshi yayi yasa hannu ya buge bakinta, kama bakinta tayi tafashe da kuka sosai tana kokarin tashi daga jikinshi, hanunta yakama ya daura akan kirjinshi dudda kukan datake saida yanda taji kirjinshi na wani irin bugu ya bata tsoro, rungume ta yayi sosai yakai bakinshi saitin kunenta da muryan shi da bata fita sosai yace "please wife karki kara kiranshi sweetheart wlh zan iya mutuwa yanda zuciyata ke zafi" tureshi tayi da karfi cikin kuka ta make mai kafada tareda lankwashe kai tana hararan shi tace "saina kirashi din, Sweetheart dinane kuma kabani rigana naje wurin sweetheart mutafi gidan mu" wani irin tari yafara yana dafe kirjinshi yana kallonta, zaro ido tayi atsorace tana kallonshi yanda yake tari, sadaf sadaf ta tako tazo gabanshi zata zari rigarta dake kan jikinshi ya rike mata hannu ya fizgota dawani irin karfi yana tarin yafada kan gado kaman zai mutu yakeji ya matseta sosai ajikinshi bama ya iya bude ido da kyau, sama sama ma yakejin metake cewa da kyar ya daga fuskar ta ya lalubo bakinta da hannu kafin ya dago kai idanunshi a lumshe ya kamo bakin yafara kissing dinta tareda kamata ajikinshi tightly yana shafa bayanta dayan hanunshi kuma yafara yawo agaban rigarta yana neme neme dan baya gani sosai tsabagen yanda yakejin asaba a zuciyar shi.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
69 - 70
Mutsu mutsu tafara tana kokarin fizge kanta amma takasa sabida yanda yarike ta, hanunshi dataji ta cikin gaban rigarta yasa tafara kokarin fincike kanta daga jikinshi hankalin ta dukya tashi sai kuka take babbakawa tana kallon fuskarshi yanda idanunshi suke a lumshe yana fitar da numfashi da sauri da sauri yana abinda yakeyi, hanunta tasa tafara dukanshi a kafada dayan hanunta kuma tadaura akan hanunshi dake cikin rigarta tana kokarin janye hanunta daga kan kirjinta tana wani irin kuka mara kara kaman mahaukaciya haka tadawo. Ta kyar ta daddage ta fizge bakinta daga nashi ta fizge kanta da kyar ta dirko daga kan gadon, da kyar ya tashi ya zauna yana kallon yanda take kuka duktabi ta kankame jikinta tana kuka sosai, juyawa tayi da gudu zata fita daga dakin hakan yasa yay kokarin ya mike tsaye danko rigarta bata gyara ba duk cikinta awaje, riko hanunta yayi da sauri ta juyo ta fasa ihu kafin tasaka hannu ta fallamai Mari da karfi, dafe inda tamare shi yayi yana kallonta asanyaye yanda duk ta tsorace tana kokarin kwace hanunta ta gudu ahankali ya janye hanun daga kan kuncinshi ya daura hanunshi agefen cikinta ya dauketa da karfi yadawo da ita cikin dakin ya zauna akan gado da sauri ta mike tsaye daga jikinshi tafashe da kuka tana murguda mai baki tace "wlh Anty Ummy tacemin babu kyau namiji nama mace haka, niba yar iska bace" shiru yayi yana sauraron maganganun datake natsuwa na shigan shi ganewa da yayi wani bai taba mata hakaba kenan, hannunshi ya daura akan cikinta yana shafawa kafin ya saukar mata da rigan kasa ya rufe mata cikinta sanan ya gyaramata ta wuyan rigan batare daya bata daman guduwa ba, ya gyaramata skirt dinta duk yana kallon fuskar ta da yanda jikinta ke wani irin rawa sanan yajawota tafado kanshi tana hararan shi tana kuka tana murguda mai baki, dan murmushi yay ya kara shigar da ita jikinshi da kyau ta yanda bazata iya guduwa ba, ya kai hanunshi ya daura a daidai ta inda taji ciwo akanta yadanyi shiru yana nazarin abu, shafa wajen yayi sosai hakan yasa tace "wash" ahankali yakai bakinshi saitin kunenta yace "da zafi, ya yake miki?" banza tai dashi tana turo baki tana juya kanta dan murmushi yasake yi yace "gobe zan kaiki hospital na dubaki da kyau if there's any need sai nakira Dr brain" muryan ta har rawa yake tace "please leave me I want to go palour" ahankali yace "kije kiyi mene?" langwabe mai kai tayi ashagwaban ce tace "wurin sw.." saitai shiru ganin wani irin kallo dayake mata tana hararan shi tace "wurin uncle zani mutafi gida" tai maganan tareda daura hannayen ta a kirjinshi tana tureshi danya saketa tafice tana kuka tana kallon kofa gabaki daya ta kosa ta sauka kasa, kama hanunta yayi ya janyo shi ya maidasu ta bayan shi hakan yasa takara kwanto jikinshi sosai tafashe da kuka shikuma yasaka hanunshi ta bayanta ya matso ta sosai har hancin su na gogan juna arude tace "na banu na, ina swe..." kasa karasa wa tayi sabida wani irin kallo daya mata dan murmushi ya mata yana goga hancinshi akan nata murya chan kasan makoshi yace "I miss yhu, I really miss yhu" juyar dakai tayi ta kalli kofa tana kuka ta danna wani uban