Showing 6001 words to 9000 words out of 123632 words

Chapter 3 - SANGARTATTCE complete by Maman Abd Shakur

04 Jul 2024

33718

kibata kice nace kudin zubi na nayau" da sauri tafita saida takara gaida Baba da wasu alamajiran data gani taredashi sanan ta wuce ta tafi, akofar gidan ta hango Muji yana kokarin tada keke da sauri ta karasa wajen ta daure fuska tace "biyani dari biyuna yaya Muji" saurayin wanda da kadan yafita tsawo da jiki ya dago kai tareda daure fuska har zaiyi magana saiya ga wayar hanunta da sauri yasa hannu yakar ba yana jujjuyawa yace "iyye waya saimiki waya dan aramin?" make kafada tayu tace "bindi salon kaje kabata min, jiya jiyan nan fa Ishak dina yabani" tsaki yayi yace "yarinya anjima nan nima zan dawo da tawa sabuwar wayar yau xan bada karamar tawa na siyo mai camera ma, soft touch, tunda hakane bazan baki daniba, kuma bazakimin hoto dawayar ba" tabe baki tayi tace "kai Yaya Muji Karya kasa, a ina kasami kudin siyar irin wayar nan daka kira wurin dubu ashirin fa ake sayar da irin wayoyin nan?" dariya yayi yace "kinga tafiya ta nidai, kuma bazan biya daribiyun ba" yana fadin haka yaja keken shi yay gaba, fashewa tai da kuka ta shiga gidan tafada jikin Baaba daduk ta rude tana tambayan ta lpy cikin kuka tace "ba yaya Muji bane yaki biyana kudina ba" share mata hawayen Baaba tayi tace "bari yadawo saiya baki dan gidansu, tashi kitayani wanan wankin dama dukna kosa kizo" karban wankin kayan tayi tama Baaba tsaf tana gamawa Baaba ta zubo mata shinkafa da miya zama tayi ta cinye harda kari kai Bilkisu badai ciba wolla.

Wuraren shadaya da rabi tabaro gidan ta dawo gida wanka tasake yi sanan tafara shirye shiryen school Mama tamika mata dubu biyu tace "idan zaki dawo daga makaranta ki sauka a tudun wada ki kaima balaraba dillaliya kudin samiran ta dana siya, ki tabbatar ita kika bama kudin ba yayanta ba, karki manta fa kinga ta dameni nakawo mata saiyau babanku yaban kudin" karban kudin tayi ta cusa chan kasan jaka tace "bazan manta ba Mama" sanan tafita daga dakin tareda mata sallama tana karban kudin mota, wurin Baba ta tafi bayan tabiya gidan Baaba ta karbi wainarta a kula.
Tana shiga aji tasami su Walawa na wasan nonon su as usual, tsaki tayi takoma ta zauna hakan yasa suka dinga ihu Fa'iza tace "yar malam haba mana ki bari muji naki manyan nan" ko kallonta batayi ba saima bude jakarta datake yi tana kokarin ciro littafin biology dan sake karanta wa danyau sunada test, Aisha Shehu tabude jakarta cingum taciro guda shida ta mika mata tace "kinji share Fa'iza Billy, ga cingum din bikin Fateema" dan zaro ido tayi ta kalli Fateema daketa sussune kai tace "dama aure zakiyi koki fadan mana" Walawa tace "toke kin fadan mana nakine da Ishak dinki?" raurau da ido tayi tace "to ai ni sai mun zana waec tukunna za' ayifa ba yanzu bane kuma ainafada muku" hanunta Aisha Shehu ta chapke ta sakamata cingum din aciki tana kallon tafin hanun nata yanda yay zufa sosai sabida taushi tace "kedai kin more Billy jikinki taushi kaman na jaririya wai wani mai kike shafawa ne, jibidai fatar hanunki taushi kaman auduga" yatsine fuska Bilkisu tayi tareda zuba cingum din cikin jaka tace "yaushe ne bikin" "ran Saturday, amma fa 4 cingum ne naki, biyu na Raiyana biyu na Layla muna gayyatar su" murmushi tayi tace "aiko zamuzo in sha Allah" zasuyi maganan wani malamin dake musu physics ya shigo hakan yasa duk sukai shiru suna sauraron karatun, koda aka tashi break goruba tasaima su Raiyana guda hudu da topi duk ta zuba ajaka, sanan tawuce wajen su Walawa tare sukaci wainar nata sanan suka koma aji. Wuraren biyar da rabi aka tashe su, tareda su Walawa suka jero suna dandarawa zuwa bakin junction inda zasu sami mota, daidai wajen wani mai shayi sukaga wani mahaukaci yazo da gudu yadau biredin kan table ya gudu gefe kan wani dakali ya bude yawani yago kato yakai baki yanaci yana sosai kai, dariya su Aisha Shehu sukayi sukace "Allah sarki yunwa mahaukacin yakeji, amma nasan idan mai shagon nan yafito yakama shi wlh bazaiji dadadi ba, innine shi yanda Allah ya ciyar dashi dinan yagudu kawai" gani sukayi ya yayyago biredin ya tura baki rabi yazube akasa sanan yakara tashi ya koma shagon da gudu ya kara dauko biredi har biyu yana yayyaga ledan jikinsu yana kokarin yago buredin daidai lokacin mai shagon yafito daga cikin dakin shagon yana ganin mahaukacin yafito daga shagon tareda daukan katon iche daya riga yakama da wuta yayo kan mahaukacin daya zauna akan dakalin yanata cin biredi zai kwalamai da gudu Bilkisu tai wurin hakan yasa Fa'iza tace "ke Bilkisu maizakije kiyi a wurin Allah sa mai shagon yahada dake, mudai mu wuce mutafi ba ruwan mu" juyawa duk sukayi sukai tafiyan su suna maganganu, fizgo mahaukacin mai shayin yayi azuciye ya chakumo rigarshi yana jijjigashi yace "dan uwarka kasan buredin nawa kaci yanzu nan dari shida fa, kowani daya naira dari biyu ake saidawa, dan kaga jiya kazo ka dauka na barka sabida tausayi" shidai mahaukaci ko kallon fuskarshi baiyiba saima cin buredin yake kaman an aikoshi hakan yasa wani zuciya ya dauki mai shayin ya daga itchen zai bugamai Bilkisu da isowarta wurin kenan tace "dan Allah malam ka yakuri karka dakai zan biyaka nawane biredin?" ture mahaukacin mai shayin yayi ya kalleta yace "dari shida" jakarta taciro ta kwaso duka yan kudinta ta kirge su tass harda na motan ta dari uku gareta nakanta ta mikamai kaman zatai kuka tace "dan Allah ka yakuri karbi dari uku ga makarantar muchan karka dakai kaga baida lpy baimasan mekake cewaba gobe idan nazo zan kawo ma ragowar kudin" tana maganan ne tana rataya jakar tata ahannu akan saman hijab, karban kudin mahaukacin yayi yace "wlh kin taimakai dayau wlh namai lilis hakanan zaijamin asara ba gyara ba dalil..." kasa karasa maganan yayi sabida fisge jakar Bilkisu dayaga mahaukacin yayi ya ruga aguje yay kasan layi arude Bilkisu tace "na shiga uku jakata Malam" tabe baki mai shayin yayi yajuya yace "aisai ki bishi awani gida da ba'a gama ginewa ba naga mahaukacin yake kwana anan kasan layi, kije tun kafin ya salwantar miki da jakan school" shigewa shagon shi yayi yacigaba da aikin gabanshi, sosai jikinta ke rawa tabishi da kallo yanda yake gudu yana tsalle yana wulla jakar nata sama, arude ta dafa kirjinta ta kwalalo ido tace "na banu kudin Mama" da gudu tabishi gashi yay mata nisa, hangoshi tayi ya shiga wani gida da ba'a gama ginewaba, karasawa wajen ginin tayi jikinta na rawa tana kuka arude tana bin ginin da kallo ganin anma maida wajen wurin bola, ahankali ta tsallake bolar da bismillah tadan leka cikin ginin dakai tana goge hawayen dake zuba, hangoshi tayi ya zauna akasa ya zazxage jakan nata ya barbazar da komi naciki yadau cingum yana cusawa abaki batare daya bare bawon ba, ga kudin Mama agefe akasa suma iska sai kadasu yake, kasa shiga ciki tayi jikinta sai kakkarwa yake tana goge fuska, shiko baima lura da itaba cingum dinshi yakeci yadau goruba yanata jujjuyawa yana kallonshi yana kaiwa baki ya yatsine fuska ya jefar, ya dau kulan wainar ta yanata jujuyawa yakasa budewa, jijjigawa yahauyi yana karawa a kunne yanajin karan dayake yi hakan yasa yafara bubbuga kulan abango yana dariya kaman an aikoshi, babu inda baya rawa ajikinta ita bama ta damu da littafan ba note ne xata iya kwafewa kudin Mama ne kawai takeso hakan yasa takara fashewa da kuka mara sauti tana share fuskar jikinta na bari, gani tayi ya tsaya chak da dena buga kular a bango yadena dariyar haukan dayake yi, lokaci daya kawai taga yajuyo dakai ya kalleta hada ido sukayi, wani irin faduwa gabanta yayi dasuka hada idon gashi yaki dena kallonta, ahankali tafara komawa baya tana daddafa bango jikinta na rawa, turgude kafa tayi, tai mugun faduwa kanta ya bugu da karfe dake kan bolan hakan yasa ta buga ihu daganan bata sake sanin inda kanta yakeba.
[7/15, 12:17 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦



Maman Abd Shakur

6 & 7

Keken suka shiga yatada sukabar wajen saida yadanyi nisa da tafiya sanan yace "tayaya jakanki yazo nan Bilkisu?" maida kanta kan titi tayi tana kallon yanda motoci ke gudu abunsu tace "jiya nefa damuka taso daga school na hango wani mai shago zai dakeshi sabida ya daukomai beredi yaci, wlh ba karamin tausayi yabani ba kana ganinshi kasan yunwa yakeji kato dashifa shine mai shagon dakokaika baiyiba yawani chakumo shi zai daka, wlh inda ace lpy shi lau ai daga ganin mahaukacin nan bazai dakun maiba, mutane basuda kirki da tausayi, shine nikuma nabashi 300 nace zan cikamai 300 yau danwai bread din 600 yaci, shine shikuma mahaukacin ya fizge jakana ya gudu" shiru tayi kafin ta share hawayen daya dan zubo ta kalli Muji da shima ita yake kallo ta madubin keken tace "wlh ko, da'ace ni wata mai kudi ce dana kaishi asibitin mahaukata da wanan gararin dayake tayi agari ba abinci, aita dukan shi dan sunga shi baya dukan mutane" saikuma tafashe da kuka tana goge fuska da hijabi, wani dogon tsaki Muji yaja yace "wlh bantaba ganin banziya wawiyar mutum irin kiba, aisai ki kaishi tunda kanin ubankine, irin kune kesa kanku a bala'i da sunan taimako, nidai inane gidan balaraban kafin haushin ki yasa na wuce ban bansaniba" nunamai gidan tayi yay parking tafito tabarshi akeken ta shiga ciki, yabita da kallo yana girgiza kai.
Yanada shekara uku aka haifi Bilkisu kusan tare suka taso, Bilkisu akwai tausayi ko minti yaganta dashi lokacin suna yara idan ya tambaye ta hanshi to karyan rashin lpy zaimata yafashe da kuka, hakan zaisa cike da tausayi tabashi tace yama shanye duka taitamai sannu.
Wuraren shadaya da rabi suka koma gida hakan yasa ta shiga wanka tafara shirye shirye shabiyu da rabi nayi tawuce tatafi.
Wuraren biyar da rabi ta shigo gidansu tana yin salla ta dauko wayar da Isyaka ya bata ta kunna "Balkisu" Mama takirata dake uwar daka ajiye wayar tayi ta tashi ta shiga dakin akan gado taga Mama a zaune rike da kofi karasawa wajen tayi tace "gani Mama" kofin ta mikamata tace "Malam ne yamiki wani sabon addu'a sha saiki rage na shafa miki akan ciwon" karba tayi ta sha da bismilla sanan ta mikama Mama kofin, kaman zatai kuka dan batason abinda zai taba ciwon nan nata danko ta tashi wanka bata ma zuwa wajen balle ta wanke, hararan ta Mama tayi tace "dagamin rigarki" ahankali ta daga rigar tana kallon fuskarta ganin yanda ta daure yasa ta natsu, debo ruwan addu'an Mama tayi takai hannu zata shafa akan ciwon da sauri ta dafe hannun Mama tareda zaro ido atsorace tafashe da kuka tace "Mama wlh kina tabawa zai faramin zafi ne, kinga tun ranan nan baisake min zafi ba yawarke dan Allah kiyakuri" hannun nata Mama ta kabar ta shafa mata ruwan ahankali sanin mugun rakin ta, ihu tayi wanda saida yasa su Layla da Raiyana dake falo suna home work suka shigo dakin da gudu, tsaki Mama tayi bayan tagama shafawa tarufe cup din ta ijiye agefe ta kalli yanda ta zube awajen tana kuka tace "wlh Balkisu kibi asannu fa inba hakaba zan cimiki mutunci dama kinsan taraki nake ko, yarinya sai iskancin banzan dako kanninki basayi zan mugun saba miki, tashi ki fitanmin daga daki" tashi tayi ahankali da taimakon Raiyana suka fita daga dakin tana kuka, yanda ta tsani mutuwa haka ta tsani abinda saisa ataba mata ciwon nan, suna kowama falon ko kallon wayar bata karaba tacigaba da kuka ahaka taci kukanta bacci yay gaba da ita, koda Isyaka yazo saidai Layla taje dakin Baba tacemai tariga da tai bacci.



******************

Banko kofar dakin da akayi bako sallama yasa duka mataye biyun dake bedroom din zaune kan katafaren gadon dakin dago kai, wata matace tashigo tadan mayyanta dan akalla zatai 55, ta kalli daya daga cikin matayen afusace tace "haba Firdausi daga tafiyata biki yau duka duka kwanana biyar bana gidan nan shine zan dawo na tarar da wanan mummunan labari Ayaan ya bata ba'a ganshi ba, sabida nimai kula dashi baninan, ke wace irin uwa cewai? Kin haifi yaro kin kasa janshi jiki, kullum tsakanin ki dashi kyara ce da fada, ba so ba lallami, halama bayan tafiya na fada kikamai shine yabar gidan" tafashe da kuka saikuma ta nunata da yatsa tace "wlh inhar ba'a ganoshi ba wlh saina mugun saba miki nidake zamusa kafar wando dai ne, kuma bari Alaji ya warke za'asan nayine, muguwar mata mai bakin hali kawai" tafashe da kuka tafita ta bugo mata kofa, tagumi wacce aka kira da Firdausi tayi hakan yasa matar dake kusa da ita wacce kawarta ce tazo mata jajen abinda yafaru ne taja tsaki ta kalleta tace "keda danki dakika haifa da cikin ki har wata step mum ta isa tazo tana gayamiki magana haka? , Ita tasan yanda kikeji ne shine kekuma kika mata shiru iya hakuri" wani handky mai kyau dake gefenta ta dauka ta goge kwallar daya zubomata ta ijiye sanan tai murmushi ta dafa kan hanun kawartata tace "Ummu Haneef bahaka bane ai abin dadine wanda ba ita tahaifi yaronka ba hartazo tana fada dakai akan danka, wanan alamune na soyayya yanzu kinga ko bayan raina nasan Hajiya Ashferh nason dana hankalina ya kwanta" tabe baki Ummu Haneef tayi tace "lallai ni bansan irin zuciyar kiba Firdausi, anfa kiraki muguwar uwa da sauran su shine kike wani yabonta haka ai yayi kyau kicigaba" murmushi tamata tace "bahaka bane kokema kinsan halin Ayaan da Hajiya da Alhaji sun mugun bata yaron, ya lalace, sabida ina yawan mai fada da kokarin gyrashi shine suke ganin ina takura mai" handky takara dauka tasake goge wasu hawayen kafin ta kalli hadadden agogon dake bangon dakinta tace "lokacin maganin alhaji yayi bari naje nabashi ina zuwa" tashi tayi tafita daga dakin Ummu Haneef ta bita da kallo cike da tausayin yanda dukta lalace.
Tana dawowa bayi ta shiga ta dauro alwala tafito Ummu Haneef tace "sallan mezakiyi warhaka?" Ahankali tace "addu'a zanyi dukma inda Ayaan yake Allah ya tsaremin shi, ya bayyanar dashi, ya kulamin dashi, yakuma dawo dashi lpy" tashi itama Ummu Haneef tayi ta daura wayarta akan gado tace "bari nima nayo natayaki".


*********

Wuraren 12 tafita daga gidan Baaba bayan ta karbi wainar ta data saka mata akula, mota tahau zuwa school dinsu sai tunane tunane take har aka kawo ta sauka tafara dandarawa, kallon layin da mahaukacin nan yake tayi taji takasa cigaba da tafiya ta tsaya chak, kulan wainar da Baaba tabata ta kalla saikuma ta kalli layin jitayi takasa wucewa ta tafi makarantar hakan yasa tai layin tana tafiya ahankali danji take kaman wani abu na fizgarta zuwa kaimai abincin nan, ahaka har takai ginin da mahaukacin yake tsayawa tayi chak tanabin bakin kofar wajen da kallo ganin dige digen jini da sauri ta shiga cikin ginin tanabin trace din dige digen jinin, hango shi tayi a tsakar wajen ya zauna yanata hura iska akafar shi dataga yana jini sosai kaman wani abune ya yankeshi, yanata yarfe hannu, yana cije baki, yana jijjiga kafar da dayan hanunshi alamun abun namai ciwo sosai, dena jijjiga kafar yayi yadebo kasan dake wajen ya kwarara akan ciwon yana huhhurawa da baki dan har miyau yake fita yana yarfe hannu yana runtse ido kaman xaiyi kuka, da sauri ta karaso gabanshi kaman tafashe da kuka dan mantawa ma tai da tsoron datake ji tayi ta tsugunna tana kallon kafar tace "yanama zafi?" dago kai yayi ya kalleta suka hada ido da sauri ta dauke kai jin gabanta yakara faduwa ta kalli kafar yanda kasa kebin jinin dake fita tace "kadena saka kasa to zaikarama zafine" jakarta tabude taciro dan ruwan data zuba a goran fanta dan dashi take alwala a school taciro da sauri tabude saikuka take ta kalleshi gani tayi ita yake kallo hakan yasa ta karanto addu'o'i aranta, kaman yana gane abinda take cewa tace "bari na wanke ma ciwon" tsiyaya ruwan tayi akan ciwon hakan yasa yaja kafar arude danhar yana buge mata hannu, ahankali tace "sannu da zafi?" tai maganan tana share kwallan dataji yazubo mata, kara dan matasawa kusa dashi tai kadan tace "kawo nakara sa wanke ma kasar saina shafama rob inada rob ajaka" ko kallonta baiyiba saima juyamata baya dayayi yanata pipita duka hanunshi akan kafar dakuma hurawa da baki, kana ganinshi kasan yanajin azabane, hawaye takara shareware dasuka kasa tsayawa sabida tausayi da sauri taciro kular wainar da Baaba tabata tunawa dayana son abinci ta bude ta zagayo ta gabanshi ta mikamai tana murmushi aiko ya fizge kulan da sauri yafaraci yana sosa kunne, hakan yasa ta dauko rob ajakan nata da ruwan tadawo ta gaban shi ta tsugunna ta tsiyaya ruwan kan ciwon tsayawa yay dacin wainar yana kallonta atsorace tadan koma baya tace "yakuri" ganin yacigaba dacin wainar yasa ta karasa wankewa tass ta ijiye ragowan ruwan agefe sanan ta lakato rob ta shafama ciwon tai tagumi tana kallonshi dan jira take yagama tadau kulan ta tafi, cinyewa yay tass kafin ya wurgar da kulan yana dariyan mahaukata saikuma yay shiru yanata kallon ruwan data ijiye gefenta kallon gefen nata tayi ganin abinda yake kallo yasa tadau ruwan ta mikamai da sauri ya fizge danhar saida ruwan yakusa zubewa ya kafa abaki yana sha yanagama sha ya wurgar yana dariya saikuma taga ya buga kanshi akasa ya baje awurin yay wani katon hamma kafin ya lumshe ido sai bacci, tagumi takarayi ta bishi da kallon tausayi tana share hawayen dataji yazubo da bayan hannu "to baida iyayene dasuka barshi shi kadai sai wahala yake? Ashe ciwo yaji saisa Allah ya turota ta kula dashi? In sha Allah daga yanzu kullum saina kawoma abinci kaci, Allah yabaka lpy". daukar kulan da goran tayi tarufe ta saka ajaka sanan tabar wajen tana waigenshi.
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦


Maman Abd Shakur

8 - 10

Tafito tawuce school, tun daga gate tahango Sargent na dukan latti. "innalillahi wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login