Showing 39001 words to 42000 words out of 123632 words
kuka gyangyadi gyangyadi dan yanzu hakama bama taji shigowan shiba, juyowa yay yace "sannu Baaba" ya ijiye ruwa da takeaway din abincin agaban ta ahankali yace "Baaba ga abinci kici, nakira su Mami zasuzo sutafi dake gida kihuta dan theater zamu shiga yanzu, nariga naduba hoton da aka mata dole aiki za'ayi acire" tagumi Baaba tayi tace "oh ni Salamatu shikenan anjama yar karaman yarinya operation, duka duka sha takwas take fa, inda tunda cikin yafara ciwo Malam ya kaita asibiti ai da abu baikai hakaba, amma shi ina saida addu'a da magungunan hausa yarinya sai wahala take" dan murmushi yayi ya mike ya bude wani kofa ya shiga wani hadadden dakine ya bayyana, bathroom ya shiga yayo wanka sanan yafito ya shirya cikin wani green riga ta likitoci wacce ta tsayamai a cinya an rubuta Dr Ayaan ata wurin kan aljihun dakuma doguwar wando yasa hular kayan blue yadau wayarshi yafito yana kamshi daidai lokacin nurse din tai knocking office din afirgice ta farka tana kokarin bude idanunta duka, dan kallonta yayi kafin ya dauke kai ya kalli kofar yace "yes come in" shigowa nurse din tayi tana gunguro wani hadadden gado tace "sir everything is set" gyada mata kai yayi tareda nuna mata Bilkisu dake kuka wanan karan mara sauti dantai bala'in gajiya, ahankali nurse din tadafa Bilkisu tai murmushi tace "my shagwaba friend yama sunanki" cikin kuka ta turo baki tace "Bilkisu kuma niba shagwababbiya bace, ciwo yakemin saisa nake kuka ai" kama baki nurse din tayi dan tasan aikin ta ta iya lallaba patients tace "ai yama rage ciwon tunda gashi baki ya bude, dazu ko uppan baki cewa sai uban ihu dakike mana kunenmu duk ciwo suke yanzu" kara matso wasu sababin hawayen tayi batare datace komiba, hanunta nurse din takama tana dariya Baaba ma dariya tai tace "Bilkisu uwar raki" nurse din tanuna Baaba tace "nuna mata keba mai raki bane taso kihau gadon da kanki" baki Baaba ta rike jin dariya na neman fitomata Bilkisu dai data sani inbadai tadane jin zafin gabaki daya bane shine zata mike da kanta amma inhar tanaji ko kankanu ne wlh bata mikewa, kallon Baaba tayi idanun nan sai shining suke sabida hawayen daya cikasu da sauri Baaba ta mike tsaye tana lullube fuskarta da hijabin ta tace "ke nifa ba dariya nake ba haba mai gadon zinare yar wajena guda" karaf suka hada ido da Ayaan da tuntuni yake tsaye yana daddana waya kaman da gaske nanko kallon su yake kawad dakai tayi kafin ahankali tai yunkurin mikewa tsaye ihu sosai tayi. "wayyo Allah na Mama" komawa tayi zata zauna da sauri nurse din tarike ta daurata akan gadon ta kwantar, fashewa tayi da kuka sosai danji tayi gabaki daya wurin yafara wani sabon ciwon dan dan baccin datayi yasa ya lafa amma yanzu yafara, gungura ta nurse din tayi suka fita daga dakin, dan murmushi yayi yatura wayar aljihun wando ya kalli Baaba yace "ki zauna anan, zaki iya shiga ciki kiyo alwala idan zakiyi salla su Abba nanan zuwa saiku tafi tare dan bansan lokacin dazamu fito daga operation dinba" kaman Baaba zatai kuka tace "to dannan ubangiji Allah yasa ayi a sa'a, Allah yabata lpy Allah kuma yabaku nasara" Ameen ya amsa ciki ciki sanan yabude kofa yafita.
Hadadden theater ta gungurata suka shiga duk tana kuka, ko ina haske wajen, dagota tayi ta zauna da kyar sanan tacire mata hijabin jikin nata tana murmushi ta linke ta ijiye, sanan ta wuce wajen wani hadadden wardrobe din bango ta bude taciro sabuwan rigar nan da ake bama Wayan da za'a musu aiki su saka, tadawo tace "kinga rigar nan zaki saka, dole ki cire na jikinki" ta bayanta ta koma ta zuge zip din doguwar rigan dake jikinta tana kokarin saukar da kafadun rigar ta rike mata hannu tana kuka ahankali tace "zan iya" ahankali nurse din tace "are you sure zaki iya" gyada mata kai tayi da kyar, nurse din tace "okay to bari na taimaka miki ki mike tsaye, komifa na jikinki zaki cire, wanan rigar kawai ake bukata kisa" aranta cewa take to uban me za'a matane daga dan ciwon cikin nan dahar ake cewa tacire komi najikin ta, tsaki taja aranta, nurse din tarike hannunta ta mike tsaye da kyar tareda dafa gado tana hawaye, nurse din tace "sannu kinji kinama kokari" hannu takai ta zame rigar daga sama yay kasa yarage daga ita sai bra da dogon sket daya tsaya a gwuiwa kasa tai dakai duk kunya ta isheta, dan murmushi nurse din tayi tace "bari nabaki wuri to kicire sauran nan ki ijiye agefe, bari naje nadauko file dinki idan nadawo zan tattare kayan nasaka miki a wardrobe kafin Dr yazo" tana fadin haka tafita daga dakin tareda rufo mata kofa.
Hawaye ta goge kafin ahankali tadanyi bendi kadan ta tube sket din batare data cire white pant din dake jikinta dayabi fatarta yay wani irin kyau kaman jikin wata celebrity, hannu tasa tabaya da kyar ta balle maballin clean white bra dake jikinta, kirjin masha Allah luhu luhu dasu a tsaye, hannu ta mika tadau rigar tabude tana kallo tana kuka mara sauti, tama rasa ta yanda zata saka dan igiyoyi ne ajikin rigar takasa gane inane wuya inane hannu, karan bude kofa dataji yasa ta dago kai atsorace suka hada ido wani irin ihu tayi ta daura rigar agaban kirjinta ta danne da hannu dayan hannun kuma ta daura ta danne ta wajen cinyarta tana wani irin kuka, mayadda kofan yay ya yarufe ya shigo dakin, wani irin firgicewa tayi tana waige waige inda zata gudu tsabagen yanda jikinta da hannayen ta ke rawa yasa rigar fadi akasa, wani irin ihu tayi zata tsugunna tadau rigar amma saitai baya zata fadi sabida yanda cikin yamata wani irin azababben zafi da sauri yataro ta tafado jikinshi yamata iso a fadadden kirjinshi, ihu takeyi amma baya fita tsabagen uban ihun datayi yau muryanta ya taushe tana kokarin kwace kanta amma takasa daidai lokacin akai knocking kofar. "Sir is Dr Ibrahim ur assistant permission to come inside sir" da kyar ya iya bude bakinshi dayamai nauyi yace "she's not ready Ibrahim go, will call u later" okay yafadi yajuya batare daya bude kofar ba, kokarin cirota yake daga jikinshi amma taki sakinshi saima sake rukunkume shi datayi dan wlh bazai gane mata jikiba, dan gajeren tsaki yay awahale kafin yajata ahaka tana jikinshi ya daurata akan gado, still taki rabuwa dashi saima uban kukan datake yi mara sauti, hannun shi yakai bayanshi ya bambare hanunta data kulla abayan shi ya fisge kanshi yana tsaki yana hararan ta, da sauri ta dauki rigarta dake kan gadon ta rufe kirjinta dashi tana kuka, tsaki yasake yi ya tsugunna yadau rigar ya gyara mata ta yanda zata sa sanan ya saka mata akai ya barshi anan wuyan ta, ganin yadan tarufe kirjinta da kaya ya koma baya yana kallonta yanda take sauke ajiyar zuciyar kuka tana share hawayen da sunki dena zuba yace "ke saka rigar nan da kyau an kicire wanan abun na jikinki" yanuna farin pant din dake jikinta, ko kallonshi batayi ba saima kara jajjan rigar take tana rufe cinyarta dashi daidai lokacin akai knocking juyawa yayi kaman ance dole yay maganan yace "who" daga waje akace "nurse Sameera" tsaki yasake yi yakoma kan kujeran dake wurin desk din dake dauke da computer a theater din ya zauna sanan yace "come in" shigowa nurse din tayi tana kallon Bilkisu tace "laa bakisa sakaba har yanzu, ki cire pant din mana" ko kallonta batayi ba, ganin haka yasa ta saukar mata da labulen daya zagaye gadon ta lallabata tacire ta dubata taga tai shaving dan dole idan za'ayi operation ayi shaving sanan ta taimaka mata tasaka rigar sanan ta kwantar da ita akan gadon duk tana kuka ta tattare labulen sama, sanan ta tattare kayan data cire ta linke taje ta ijiye a wardrobe sanan ta dauko roban fitsari tazo gaban desk din dayake tace "Dr nasaka mata robar fitsarin ne incase of fitsari" shiru yadanyi kafin agadaran ce yace "no intanajin fitsari a kaita tayi" komawa tayi ta ijiye tana mamakin shi wanan itace first patient din dayake hana kar asamata kome yahana oho. Bayan ta ijiye ya kalleta yace "go and call Dr Ibrahim lets start, and the anesthesiologist"
Fita tayi daga dakin shikuma ya mike yaje wardrobe ya ciro rigar operation ya saka ya kulle igayan ta baya yadan juyo ya kalleta yaga tana kwance ta lankwashe kafa tana hawaye, dan tabe baki yayi yaje gaban washhand basin ya wanke hanunshi har zuwa elbow yadawo jikin gadon ya kukkuna wasu mashina yanadan satan kallon fuskar ta idanunta alumshe ya kunna wani wuta dake saman gadon aiko ya haskota bau da sauri ta bude ido tana kakkare fuskarta tana hawaye, hada ido sukayi da sauri yawani dauke kai yakoma yasake wanke hannu sabida abubuwan daya taba sanan yazo ya saka hand glove yadauko dan kwanon dake dauke da different surgical blades daga sterilizing machine yadawo gaban gado ya ijiyesu akan table din dake kusa da kanta da karfi kwanon yay kara hakan yasa tasake bude idon data lumshe tayi ahankali dan bacci bacci tafara ji ta mugun gajiya, wasu Sharpe surgical blades ya dauko kusan guda uku ya nunamata ya daure fuska tamau yace "kingan su, kinga wayan nan wukaken" ya ijiyesu ya sake dauko wasu ya nuna mata yana wani shafa wukan da hand glove din hanunshi amma blunt side din yake shafawa yace "kinsan yanda ake fede akuya?" yay maganan yana kallon fuskar ta yanda ta zaro ido tana kallon wukaken ya kara daure fuska yana kallonta yace "haka zan fideki kaman yanda ake fede akuya yau" wani irin nishi take kaman kirjinta zai fashe, kafeta yay da ido yanda take breathing heavily tana zazzaro ido tana kallonshi, ahankali yasake ijiyesu ya dauko biggest surgical blade din cikinsu ya nuna mata yace "kinga wannan dashi zan fede duka fatocin ki uku na ciki, ur 3 layers duka zan barke" wani irin nishi takeyi hawaye na bulbulowa daga idonta ganin kaman zata sume yasa yace "fedeki zanyi namiki operation da wayan nan wukaken duka" azabure ta mike ta diro daga kan gado kaman mahaukaciya tama manta da ciwon datake fadawa jikinshi tayi ta kankame shi sosai da sauri ya ijiye wukar karya je ya yanka su, wani irin kuka tafashe dashi sosai kafin ta dago kanta dayake akirjinshi danya fita tsawo sosai, kanta ta daura hannayenta takama rigar theater dake jikinshi asaitin kirjinshi ta kalleshi da idanunta dasuka kumburu suna tsiyayar da hawaye tace "mene maka daka tsaneni haka eh?" fashewa tai da kuka sosai ta tace "kome menama ka, dan Allah kayakuri kayafemin, dan Allah karka sakamin wayanan wukaken ajikina, dan girman Allah, dan Allah kayakuri Ya Ayaan" tai maganan tana wani irin kuka tana kallon kwayar idonshi gashi dukta rukunkume shi yanda kirjinta ke bugawa kaman zai fashe tsabagen tsoratatar dayayi, ta maida kanta kan kirjinshi tana wani irin kuka mai tsuma rai tana furta "kayakuri kayakuri" agalabaice, ahankali yadan lumshe ido tareda sakin gajeruwan ajiyar zuciya.
[7/20, 12:30 PM] +234 803 238 4602: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
39 - 40
Ahankali yadaura hannayen shi akanta yana shafa manyan da kananun kitson dake kanta batare daya bude idanun daya lumshe ba, knocking kofar da akayi yasa yadan bude ido ahankali yace "common in" yay maganar yana saukar da hannayen shi daga kanta tareda gyara bayan rigarta. Dr Ibrahim, Nurse Sameera da Anesthesiologist mai suna Moses ne suka shigo dukansu atare, da ido yama Moses alamu ya shirya alluran, hannu yasa zai cirota daga jikinshi amma taki sakinshi sai kuka take kasa kasa, daukar ta yay batare data sakeshin ba ya kwantar da ita akan gadon zai tashi takara rirrikeshi tanamai kukan dabaya fita sosai tana kallon fuskar shi, jin yanda kirjinta ke bugawa yasa yadan hadiye haushin kanshin dayake ji namata wani laushi ahankali yace "relax nafasa miki to, calm down" sake kama rigarshi tai gam gam kaman mai rada tace "dagaske" yana kallon yanda lips dinta sukai jajir tsakiyar ya gyada mata kai yakai hanunshi bayan rigar yadan bude daidai inda za'ayi allurar da Moses yagama hadawa batare data masan yayiba dan duk hankalin ta atashe yake da wukaken dayace zai fedeta, da ido yamai alamu yayi, sanan yadan kalli fuskarta yanda take kallonshi da idanunta dasuka kankance tsabagen kuka ga dogayen gashin idon duk sun jike sun mammanne da juna kaman tasa gum, iskan bakinshi ya hura mata akan idon hakan yasa ta lumshe idon da sauri, wani irin azaba dataji tabayan ta yasa ta bude ido tareda kara damke shi da karfi tana kuka sosai saikuma luuu ta komar da kanta kan gadon wani irin bacci yay gaba da ita batare data sakeshi ba, dan murmushin gefen baki yayi sanan yasa hanunshi yacire hannayenta dake kan rigarshi ya maidasu kan gadon ya ijiye tareda sake gyara mata kwanciya ya dauko wani zani yarufe tundaga kafarta har cikinta sanan ya bude daidai wajen ciwon yadau abun rufe hanci da baki yasaka tareda kunna wutar operation, samira data rike kwanon surgical blades din da tagama kirgasu tace "Sir daga gani wanan patient din is very special sai kappa kappa kake da it..." wani irin kallo daya mata yasa tai shiru bata karasa ba, wani abu kaman marker Dr Ibrahim ya mikamai nan yay layin daidai saitin inda zasu yi aikin, sanan yakara mika hannu aka sakamai wani surgical blade akai, ahankali yadan kalli fuskarta kafin yasaukar dawani labule daya raba tsakanin su, sanan yama Moses magana yakara sakko da wutar kasa sosai yanda zasuga cikin da kyau, wukar ya dauka ya yanka fatar wajen Dr Ibrahim na share jinin dake zuba.... Nan dai operation ya kankama.
Akan kujera dake hanyar wurin theater din duk suka zauna Mami, big Mummy da Baaba dasuke ta bata baki dan kuka take ganin yanzu kusan awa uku kenan ba'a gamaba balle a fito, Abba da Baba Sulaiman suna tsaye suma addu'an samun lpy ta suke.
Anyi anyi Baaba tazo atafi gida taki tafiya wai ita sai taga anfito da Bilkisu tukunna zata tafi.
Sai wuraren 12:50 nadare suka gama operation din tatas, sai kallon appendix din daya cire mata suka saka awani kwalba yake yanda yay girma sosai dan gab yake daya fashe, inda kuma yafashe da mutuwa zatayi wlh. Da kanshi ya gungurota daga gadon dan kaita dakin hutu yana fitowa kam yaga su Abba dasu Baaba sun tatashi suna kallonta, Baaba ta fashe da kuka tana tattaba fuskarta ganin bata motsi, dan murmushi yay yace "lpy ta lau bacci take zata farka, operation din was successful" Alhamdulillah duk suka ce, yace "bari nakaita dakin hutu" wani daki ya bude kofa ya shiga da ita dakin mutum dayane ga gado ga tv harda fridge sanan akwai bayi aciki, ahankali ya dauketa sabida dinkin ya daurata akan gado yadan sake kallon fuskarta kafin yajuya yafita dan zuwa dauko wani rigan asibiti danna jikinta duk yabaci da jini, tsayawa chak yayi yay folding hanunshi akirji jin yanda Abban shi ke tonamai asiri a hospital.
Dariya Nurse Sameera da Dr Ibrahim harma da Moses sukayi, Nurse Sameera tace "habawa no wonder naga Dr was extra careful sai lallabata yake kaman Kwai shida baya wani lallaba patients, ashe matar shi ce" Abba yawani kara washe baki yace "biki ma har yana neman wata biyu" Dr Ibrahim yace "lallai nema shine koya fadama" daure fuska yay yazo zai wuce wajen ya shiga theater Abba ya fizgo shi, kaman zaiyi kuka yace "Pops kaga kadena badani a wajen aiki, ni kuma zo kutafi please" ya karashe maganan kaman zai mutu sabida haushi, Big Mummy tace "dont mind them boy kuzo mutafi" ta kalli Abba tace "mu barshi yay aikin shi da kyau gaskiya Alhaji". Kaman zaiyi kuka ahankali yace "stop calling me Boy in front of them big Mum" rufe baki big Mummy tai da sauri tanaso tai dariya aiko duka wajen aka kwashe da dariya, shigewa yay theater abinshi Abba ya kalli Baaba da Mami dake zaune suna yar dariya suma yace "mutafi gida ki huta ga mijin tanan ai xai kwana da ita" hakanan suka tashi sukaje driver yajasu sai gida
Sabon kayan asibiti ya dauka ya koma dakin ya ijiye kayan akan gadon yana kallonta yanda fuskar ta yay fayau tsabagen wahala da kuka gakuma santala santalan cinyoyin ta dasuka bayyana, dan gajeren tsaki yaja yay gaban gadon yadan zauna ta baki bakin kafin yasa hannu ya dagota ahankali, dan igiyan bayan rigan ya warware yana wani ciccije lebe, sakin igiyan yayi kafin yakai hanunshi ta gaban rigar yawani ja rigar kasa da sauri ya saketa tafada gadon bam dudda cikin bacci take saida tadan yatsine, runtse idonshi yayi da karfi kafin yadan mikar da hannu yana kokarin ya maida mata rigar inyaso yafita yakira Sameera tasamata, neman rigar yake wacce ya zameta takai kan cikinta, hanunshi dayaji ya sauka akan kirjinta yasa ya matsa baya da sauri har yana bigewa da kujera yace "f*ck!" fita yay daga dakin da sauri kaman ana ingiza shi, yay hanyar office dinshi daidai lokacin Nurse Sameera tafito daga dakin wata patent daure fuska yayi yace "kije ki chanza mata riga" ahankali tace "to Ango" wani mugun kallo dayamata yasa tabar wajen da sauri tana gimtse dariya, office dinshi yakoma ya shiga ya rufe kafin ya wuce bedroom din ciki, bayi ya shiga yay wanka abinshi yafito daure da towel fridge din dakin yabude yadau Vita milk mai sanyi ya bude yakoma kan gado yana sha, agogo ya kalla yaga har daya nadare yawuce ma tsaki yayi dan bazai iya kiran Meram ba is too risky hakan yasa ya ijiye bottle din yakoma ya kwanta sai bacci ba zancen salla.
Wuraren 8:30 yatashi da kyar, ya shiga bayi yayo brush yay wanka yay alwala, yadau mai ya shafa sanan ya shirya cikin dogon black jeans da soft cotton t-shirt maroon bakaramin kyau yamai ba color, ya shafa man gashin shi dake karasa gashin kanshi kyalli sanan yadau turaren shi mai kama jiki ya fesa kafin yahau dadduma yay sallan asuban yana idarwa ya mike