Showing 99001 words to 102000 words out of 123632 words

Chapter 34 - SANGARTATTCE complete by Maman Abd Shakur

04 Jul 2024

33722

irin murmushi dasuke iyajin sautin shi tace "inhar kanaso ka kara saka mahaifiyar ka a ido abu nafarko danake so kayi shine duka kamfanin Alhaji da dukiyoyin shi daya maida sunanka kamaida su sunanan wato su zama mallaki na, nabiyu inaso yarana dakuka kama dan nasan yanzu haka police natare dakai asake min su, na uku wanda yake na karshe inhar kana son ka kara saka mahaifiyar ka da mahaifin ka wanda yanzu haka yakusa isowa hannuna a id...." da sauri ya katse ta ta hanyar cewa "Pops" yafada yana dafe kirji, murmushi tayi tace "kwarai kuwa Pops, pilot din Alhaji hmmm" tai wani irin murmushi dazan kirashi dana keta, tace "pilot din Alhaji yanda kasan tip da taya haka muke, shikemini komi dan baban ka karfi yakare kuma gani nikuma da kuzari ta" wani irin runtse ido Ayaan yayi jijiyoyin kanshi na fitowa tace "mahaifin ka nakiranshi yace yazo suzo sutafi nigeria akwai matsala yakirani, kafin yakirani Bala yariga yafada min halin da ake ciki, yanzu haka ubanka na cikin jirgi baisan inda kanshi yakeba anmai wata alluran bacci" kara danne kirji Ayaan yayi zaiyi magana CP ya girgiza mai kai, Big Mum tace "abu na uku inhar kanaso ka kara ganin mahaifin ka da mahaifiyar ka shine zaka bani Bilkisu amadadin su" "wat!" Ayaan yay wani irin ihu tareda dukan computer dake kan desk jikake kakakakak sun tarwatse, da sauri CP ya girgiza mai kai, Big Mum tai wani irin dariya tace "daka natsu dayafi shinema abu mafi alkairi, Bilkisu wato matar ka itace silar komi ya bacin mini haka har asirina yatonu, dan haka dolene na kasheta ita tafara jiyo asiri na aranan na kiraka itakuma natura aka dauketa akaje Bauchi aka yarda ita, saikawai gata tadawo saisa naso na kasheta ranan kafin tafadi komi amma ka kamani, Ayaan ka ganni nan akan dukiya zan iya komi wlh, bazan iya hakura bane uban dukiyar mahaifinka ka gaje komi ba, my initial plan was nakamo ka kamin signing komi yadawo nawa saina kasheka kai kadai, bayan ka mutu kaga ai bakin cikin rashin ka shizai halaka tsohon mahaifinka, uwarka kuma nabarta da ranta dan babu abinda zata iyamin, shine fa makirar matar ka tabata mini komi, Ayaan!" ta kirashi dawani irin kakausar murya tace "inhar kanason ka kara ganin Pops da Mami kamaida dukiya komi yadawo nawa, kasa asaki yaran aikina, sanan ka bani matar ka Bilkisu itace dan silar komi, kasan mezan yi inhar baka bani Bilkisu ba" tai wani irin murmushi mai kara kafin tai shiru tace "kadaisan nasan gidan su Bilkisu ko, saina sa ankashemin kowa nagidan su, fara daga kan Malam, Mamar ta, kishiyar mamar ta, kaninta mata biyu Raiyana da Layla, Baaba wacce tazo gidan mu da danta Muji, Ayaan! Rai daya tal dinan danake nema wato Balkisu inhar baka bani ita ba saina kashe rai bakwai hada da iyayen ka yakama rai Tara kenan, nabaka awa ashirin da hudu I lokacin ya cika zakaga kira" ta katse wayar kit.

Jama'a yaya kenan?
In nine Ayaan hakanan zanbada Bilkisu akashe ta gaskiya koya kukace?
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

85...

Dafe zuciya Ayaan yayi yana wani irin nishi, kirjinshi na zafi sosai yama rasa ina zaisaka kanshi yaji dadi, kanshi kaman anzubai wuta, da sauri Mike yafita ya dauko mai cold water, CP ne ya karba ya bude ya samai abaki da kyar ya kurbi kadan ya saukar dawasu tagwayen ajiyar zuciya kafin ahankali ya dago jajayen idanunshi ya kalli inspector yace "inaso kayi contacting headquarter police din zaria azuba jami'an tsaro a anguwar su Bilkisu gabaki daya right now please" yanda yakara she maganan yasa CP yace "calm down" ya kalli babban inspector dake tareda shi yace "kira officer saminu na zaria ka sanar dashi, Ayaan bamu address din gidan" ahankali Ayaan yabasu address din shikuma CP yadau waya yakira headquarter dan atura police suje Amina kano international Airport tayanda bazasuci sa'an ficewa da Abba daga airport dinba bayan sun iso, sanan ya kalli Ayaan dake dafe da zuciyar shi yace "tashi muje masallaci daganan muwuce headquarter dan ayi tracking phone number ta" da kyar ya tashi suka fita daga dakin yana ganin jiri jiri.
Saida sukai salla sanan suka wuce police headquarter number wani police yazo ya karba ana kokarin tracking shikuma yabi bayan CP zuwa dakin da ake interrogating yaran Big mum din, CP ya shiga dakin shikuma ya tsaya ta gaban glass din waje yana kallon yanda ake questioning dinsu, Sosai suke kuka tsabagen azaba daya daga cikin su yace "wlh, wlh, mu bamusan hajiyar ba ogan mune yasan hajiyan, ogan mu Bala" da sauri Ayaan yakara gyara tsayuwa yana kallonsu yana maimaita sunan Bala aranshi, "Bala, Bala a ina ma yataba jin ko ganin sunan nan?" hanunshi ya goya abaya yafara zagaye wajen chak ya tsaya yace "yes! Wanan letter, awanan letter naga sunan Bala dama number shi" daidai lokacin CP yafito yana gyara hanun rigarshi daya tattare kafin ma yay magana Ayaan yace "inada number Ogan nasu Bala ta hanyar wani sako da aka turamata dana karba naga number shi da sunan shi akasa" gyadakai CP yayi yace "good good" daidai nan suka bude kofar wani daki da ake tracking number Big Mum, tashi mai tracking number dake gaban wasu computers yayi yasarama CP yace "sir bamu iya samun location dinta ba is as if ta karya sim dinne" da sauri Ayaan yace "bari naje na dauko wasikar saina turo muku number ayi tracking Ogan dan duk inda Bala yake nasan yana tareda Big mum, CP ya wayan da sukaje airport by now yakamata ace Pops sunyi landing" asanyaye CP ya dafe kafadar shi yana girgiza mai kai yace "team dina sunce har yanzu babu any jet daya sauka banda haka ma basuga any suspicious person ba, yanzu dai abinda nakeso dakai Ayaan shine kaje ka boye Bilkisu inda matar nan bazata taba ganota ba, zakuma muhadata da police da zasu tsare ta, hospital dinka is not safe tanada men dazata iya saka wa suje su daukota, kaje idan kaje yanzu ka turamin number Bala koma yaya ake ciki zandinga sanar dakai" gyada mai kai kawai yayi ahankali yajuya yafita daga office din yana kiran sunan Allah aranshi shi kadai yasan yanda yakeji aranshi ya shiga mota yatada tunani kawai yake ina zai iya boye Bilkisu dan duk wani gidajen Abba da nashi babu wanda bata saniba, wani zubin sai big mum tasan wani abu nashi Mami ma bata saniba, lumshe ido yayi wasu irin hawaye masu zafi suka zubomai ahankali yace "Ya Allah please take care of my Pops and Mami" baida matsala gidan su Bilkisu dan yasan babu ta yanda zasu iya wuce jami'an tsaron da aka zuba suje dauko wani, saidai in Big Mum takashe shi dan wlh bazai taba bada matar shi da batada lpy ba, bazai taba badata bane, yanzu a ina zai iya boyeta, ya killace ta, dan ko kadan brain dinta bayason damuwa yanda take last stage of recovery dinan Aaman! Zuciyar shi takira, da sauri ya rage saurin gudun dayake amota gudun karyay hatsari, to wama zai kira dole shine, yakula da ita bayan ya tsinceta batare dayaci amanar taba gashi ko godiya baimai ba lokacin ashe yanada rana, to yanzu ina zaima sami number shi? Da sauri yace "Pops log book" kwana yay da sauri akan titi yadau hanyar dazai kaishi gidansu, ko parking din kirki baiyiba yafito polisawan dake gadin gidan na gaishe shi baimabi ta kansu ba yay cikin gidan da mugun gudu, dakin Abba yayi bayan ya bude drawer shi yaje yana fiffito da takardar du da kyar yaga littafin, zama yay anan kasa yana duddubawa page by page arude, tsaki yayi ya jefar da book din akasa yace "sh*t" jingina yay da drawer ya dafe kanshi dake wani irin bugawa da karfi ahankali yace "Allahumma ajirni fi musibati" haka yadinga maimaita wa kusan sau biyar kafin ya dago kanshi ahankali ya kafe littafin da pages din keta buduwa sabida iska ido, da sauri ya rarrafa ya dauko book din yadawo ya zauna yana bi page by page yana dubawa yana wani irin nishi tunda yake arayuwan shi baitaba sanin tashin hankali haka yakeba saiyau, lokacin Bilkisu shi wanan bamaya hayyacin shine, harzai ijiye littafin idanunshi suka sauka akan sunan Aaman, da sauri yaciro wayar shi ya kwashi number yay dailing ya kafa a kunne har yagama ringing ba'a dauka ba yasake dailing akaro nabiyu harya cirerai saiya ga anyi picking da sauri yace "A...Aaman, Barister Aaman" daga ta dayan bangaren anatse Aaman dake kwance kan doguwar kujeran mom dinshi yatashi zaune yace "yes nine, waye ke magana" ahankali yace "Dr Ayaan, amm mijin mijin wacce ka taimaka, mijin wacce ka dawo mana da ita kano u and ur friend" shiru Aaman yayi baisake cewa komiba dan yagane shi daga explanation din dayayi, shiru shima Ayaan yayi zuciyar shi nawani irin mai zafi, ya lumshe ido saikuma ya budesu ahankali muryan shi nadan rawa yace "am sorry Man" dan murmushi Aaman yayi yace "bakomi, why is ur voice like dat is everything okay?" girgiza kai yayi wasu irin hawaye sun taru a idonshi muryan shi narawa yace "please taimakon ka nake nema wayanda suka taba kiddaping wife sunyi kiddaping Pops dina da Mami and my step Mum ce" zumbur Aaman ya mike tsaye yace "subhanallahi" "and tace abasu Wife in exchange inba hakaba bazata saki su Pops ba and.." kasa magana yayi sabida kukan da tun dazu yake dannewa yazomai, runtse ido Aaman yayi sabida radadin da zuciyar shi tahau yi, ahankali ya budesu ya kalli agogo 8:40 nasafe ne yanzu ahankali yace "Dr be strong man, ina Abj ne, amma yanzu nan zanbi flight nazo kano before 10 I will be there, text me address din inda kake, be strong Man babu abinda zai sami Dad da Mom da izinin Allah" gyadamai kai Ayaan yayi yama kasa magana ya katse wayar yamai text din address din hospital sanan ya mike tsaye bayin Pops ya shiga ya wanko fuskarshi ya share da towel sanan yawuce yafita ya shiga mota yadau hanyar hospital.

Parking yayi a parking space sanan yafito daga motar jiki asanyaye idanunshi sunyi jajir, dark shade dinshi ya dauka yasaka sanan ya kulle motar yay cikin asibitin, tun daga bakin office dinshi yakejin kukan Bilkisu da sauri yabude kofar ya shiga ya mayar ya rufe yay cikin bedroom din bayan ya cire glasses din ya ijiye akan table ya bude kofa ya shiga, ajikin kofa ya tsaya ya kafeta da ido yanda take zaune akasa ga abinci a gabanta na Mrs Biggs sai uban kuka take Nurse Sameera da tsabar karfin kukan ta baima barta taji alamun shigowan mutum ba sai faman lallashin ta take.

Yafi minti biyu kallonta yake wani irin sonta na ratsa kowani jijiya na jikinshi, dan gyaran murya yayi da sauri daga Nurse Sameera har ita suka dago kai suka kallai da gudu ta mike tana kuka tafada jikinshi ta kankame shi tsam tsam tana kuka sosai da sauri Nurse Sameera ta mike kanta akasa tana murmushi tace "tundazu ta tashi takicin abinci nazaci na dakin ne bata so na aika aka siyo mata a Mr biggs shima takici sai kuka takeyi taki cemin komi kuma, tunda kadawo bari natafi" dan murmushi yayi yace "thank you so much nurse Sameera" murmushi tayi tace "bakomi Dr" tabude kofa tafita daga dakin ta rufo musu, sai alokacin yay hugging dinta back tightly kafin yafara tapping bayanta alamun tai shiru, dago kanta tayi daga jininshi ta kafeshi da jajayen idonta dake tsiyayar da hawaye, ahankali ya bude ido shima ya kalleta, dukan kirjinshi tahauyi tana kuka sosai, da kyar ya daga hannu yakama hanunnata yahada da nashi yana girgiza mata kai yama kasa magana, shigewa jikinshi takara yi sunkai 2min ahaka sanan yaciro ta daga jikinshi yaja hanunta sukai cikin dakin akan gado ya zauna ya zaunar da ita a gefenshi, hanun yasa ya share mata hawayen dake zubowa ya girgiza mata kai ahankali yace "am sorry nabarki nafita ko, stop crying zokici abincin ki" abincin ya dauko ya daura akan jikinshi yadau spoon ya debo yakai bakinta budemai tayi tana kallon idonshi tanaci haka yadinga bata fuskarta kadai nasa shi kwanciyar hankali, saida ta koshi ta karbi spoon din daga hanunshi da sauri ta debo itama ta kaimai baki tana washe mai baki, bude mata yayi ahankali yana kallon fuskar ya karba yaci dan yasata farin ciki amma ko kadan bayajin dadin abincin abakin shi, da sauri tasake debowa tana wani irin washe baki tsabagen murna takaimai bakinshi tana kallonshi, wani irin zuciyar shi keyi, kasa bude baki yayi hakan yasa tasake matsowa tana budemai bakinta alamun yabude baki tasaka mai, wani irin rawa zuciyar shi tafara na kuka sake tunamai da Pops datayi dan dayana yaro haka yakemai in yana rashin lafiya yakicin abinci, da sauri ya ture spoon din ya jawo ta yasaka ta ajikinshi ya fashe da wani irin kuka, da sauri tafara kokarin fizge jikinta daga nashi jin yana kuka hakan yasa yasaketa ahankali, kallon fuskarshi tayi ganin yanda yake kuka yasa ta kwaye fuska zatai kuka itama cike da damuwa, da sauri ya girgiza mata kai yana goge hawayen dayake, da sauri ta zauna akan cinyarshi tasa hannu kaman yanda yamata dazu ta share mai hawayen duktai wani irin da fuska rungume fuskarshi tayi hawaye nataru wa a idonta tana shafa kanshi nakusan 1min saikuma tasake shi ta dago kanta ta kalleshi dan tabbatar daya dena kukan, murmushi yamata asanyaye, sake washe mai baki tayi tasake rungume shi saikuma tasake shi ta sauka daga kan jikinshi ta mike atsaye agabanshi tana kallon fuskarshi shima ita yake kallo a sanyaye, hannayen ta ta daura akan kafadar shi tana washemai baki ta dugo da kanta ahankali tana kallon kwayar idonshi shima ita yake kallo kaman yau yafara ganinta, daura lips dinta tayi akan nashi da sauri ya chapke tareda rungumota jikinshi sosai yana wani irin sauke ajiyar zuciya, daukar ta yayi chak ya kifata a gado yasa hannu ya zuge mata zip din doguwar rigan ya cire doguwar rigar ya yar shima cire kayan jikinshi yayi yahayo gadon, da sauri tafada jikinshi ta kankame shi sake hada bakinsu yayi yana wasanni da ita kafin ya shige ta yana yanda yaga dama da ita.

Wuraren goma ya shigo garin kano, taxi ya dauka ya bashi address din hospital din da Ayaan yatura mai, goma da kusan 15 minutes taxi yay parking a hospital din, ya shiga yana kalle kalle ahankali yaciro wayarshi yay dailing number Ayaan amma ba'a dagaba akaro na uku ya dauka murya chan kasa yace "please kabani 10min am coming" bai kawo komiba Aaman yace "okay ina reception" , dagata yayi yakaita bayi wanka yamata agurgurje yafito yana tsane gashin kanta da towel sai kallonshi take, dan murmushi yamata, yamata kiss a kumatu yace "thank you, Allah miki albarka kin sa nasami natsuwa" hanunta ya daura akan towel din ya dauko mata wani bakin doguwar rigan Abaya ya shiryata tsaf yasaka mata dogon hijabi daya kai mata guiwa pink, yasaka mata loafers sai kallonshi take sanan shikuma ya shirya cikin Jean da riga white yasaka takalmi yadau jakarta da magungunan ta yadawo yarike mata hannu yace "let's go" fita sukai daga dakin, a reception yaga Aaman zaune yana danna waya, kaman ance ya dago kai ya gansu suna tahowa hanunta cikin nashi da sauri ya kori abinda kemai yawo a ranshi ya mike tsaye yana dan murmushi.

Hannu Ayaan yamika mai suka gaisa da ido yamai alamu suje waje, wajen motar shi sukaje, ahankali Ayaan yace "duk duniyar nan a yanzu kai kadai nai trusting, koda yau na mutu nasan tana good hand, please ga wife inaso kabar garin nan da ita harsai naci nasaran kubutar da iyayena bazan tsaya jiran police ba" bai jira mezaice ba yajuyo ya kalli Bilkisu da shi taketa kallo, cupping face dinta yayi ahankali yace "Baby follow him he's going to take care of you for me kinji, be a good gurl, I love you so so much wife" lumshe ido yayi da sauri, patting kafadar shi Aaman yayi ahankali yace "I can stay with you lemme help you Bro, inada wata sister dake aure a garin nan zamu iya boyeta a gidanta" girgiza kai Ayaan yayi yace "kai nakeso ka kulanmin da ita, I want her out of kano, I don't want to risk her life in anyway tana last stage na recovery ne, please please take care of her for me" da sauri yay wurin motar shi baya ya bude yasaka jakarta ya rufe yadawo yana mata murmushi yakaita gaban mota yace "kibishi zanzo na daukeki don't cry okay" washe mai baki tayi, ahankali ya sumbaci gaban goshin ta yasaka ta aciki ya kullo yadawo inda Aaman yake a tsaye sai binshi da kallo yake hanunshi Ayaan ya kama ya saka key mota da magungunan ta yace "once kakai kabata magungunan nan twice a day ne bacci yake sata, ga key kayi parking motar a Airport leave d key with security, I will never forget dis favor" da sauri ya juya zai wuce Aaman ya kama hanunshi, ahankali ya tsaya chak batare daya juyoba zagayowa ta gabanshi Aaman yayi yay hugging nashi yana buga kafadar shi yace "all d best, I promise to take care of her, Allah yabaka sa'a, ya kubutar dasu" Ameen Ayaan yace yana kokarin hana kanshi kallon motar, ahankali Aaman ya sakeshi yajuya ya bude motar ya shiga, da sauri ya juya baya bayason ya kalleta dan kuka zaiyi, Aaman yaja motar sukabar asibitin.
♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦




Maman Abd Shakur

86 - 87

Har suka shiga titi waige waigen shi take hartazo tadena ganinshi, kuka tafara mara kara ahaka har sukakai airport yay parking motar yaciro jakanta ya zagayo ta inda take kukan ta ya bude mata kofar yana kallon ta, ahankali yace "fito" fitowa tayi tana kallen wajen tana kuka saikuma ta kalleshi tafashe da kuka sosai, girgiza mata kai yayi cikin muryan lallashi yace "stop crying gashinan zuwa, zomuje, goge hawayen" share hawayen tai da sauri, yabama security key suka shiga cikin airport

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login