Showing 66001 words to 69000 words out of 123632 words
yanzu na chanza plan gabaki daya saisa ma nace ki shiryo kizo" dan dariya Munari tayi takara gyara zama akan katafaren kujeran datake kai, Big Mum tace "zan tura su Bala sumini kidnapping dinshi nariga nasa lawyer na yamini pepopin kuma na sato wasu documents din ownership of the company daga dakin Alaji, yanzu abinda nakeso su Bala zansa sumin kidnapping dinshi jibi, kekuma zaki tafi chan gidan dazasu kaishi, abu daya kawai nake bukata daga wurin shi shine signature, inhar yamini to duka dukiyar ta dawo tawa daga nan zansa su Bala su kashe min shi shikuma Alaj..." kasa karashe maganan tayi sabida karan fashewan abu dasuka ji arude duk suka mike tsyae big Mummy da gudu tabude kofa mace tagani da hijabi tana sauka daga stairs da gudu hakan yasa itama tabi bayanta, bigewa Bilkisu tayi da kujera hakan yasa tafadi da sauri ta mike sai a lokacin big Mummy taga fuskarta tace "Bilkisu" kafin takarashe maganan Bilkisu tamike tafita daga dakin da gudun ta tana fita tai mota ta bude binta yay da kallo yana waya ganin yanda take nishi ta zazzaro ido, kunna mota yay da hannu daya yay horn aka bude musu suka fita atsorace ta rike hanunshi da kyar tace "Ya Ayaan" hannu yanuna mata alamun yana zuwa yacigaba da magana daga hospital ne wata patient tasami complications a surgery da ake mata shine yake fadinma Dr Ibrahim abinda zaiyi.
Da gudu Munari tafito ta tara da Big Mummy turus agaban kofa ta dafe kai tace "waye ya jimu?" cikeda bacin rai Big Mum tace "mayyar matar shice, ban wayana da sauri kafin ta batamin plan" da sauri Munari ta koma sama Big Mum kuma takoma cikin falon tasaka hannu tadau glass bowl din decoration dake kan center table ta buga shi akasa ya tarwatse, runtse ido tayi da karfi ta sanya kafar haggun ta akai ta taka wani karami aiko ya yanketa saiga jini da sauri ta zauna akan kujera tana runtse idon azaba, daidai lokacin Munari ta sauko daga kan bene tana ganin jini tace "saratu kinada hankali kuwa" murmushi mai ciwo tamata tace "trust me i know wat am doing" karban wayan tayi tai dailing number Ayaan har lokacin busy yake yana driving yana magana da Dr Ibrahim sunma kusa gida, Bilkisu dukta damu yagama wayar sai kallonshi take, saida suka shigo anguwan su sanan ya katse wayar ya ajiye akan cinyarshi yadan kalleta suka hada ido kafin ya maida hankalinshi kan hanya yay murmushin gefen baki yace "ke kallon fa" kaman zatai kuka tace "dazu danaj..." wayarshi tai ringing big Mummy daya gani a screen yasa yace "1min" daukar wayar yayi daga tacan bangaren big Mummy tai wani irin murya tace "Boy kana ina?" dan murmushi yayi yace "gani nan a anguwan mu bama mukarasa gidaba, missing me already" yanda yay maganan yasa ta gane bai riga yasan komiba wani irin nishi tayi da sauri yace "menene are u okay" Munari ta kanne ma ido hakan yasa Munari ta fizge Wayan cike da tashin hankali Munari tace "Ayaan hawan jininta yatashi jiri ya dibeta ta fadi afalo yanzu hakama kafarta jini yake ta taka katoton kwalba, she's seriously bleeding, ka ajiye matarka agida kazo da wuri dan Allah" arude yace "okay okya, ki danne wajen try and stop d bleeding kafin nazo" katse wayar yayi daidai yakawo kofar gida yay horn mai gadi ya bude ya shiga ciki adan rude ta kallai tace "ina zaka i want to talk to you" fuskarta ya kalla saikuma ya matso yama lips dinta kiss murya chan kasa yace "ina zuwa, sauka ki shiga gida big Mum bata da lpy" da sauri ta girgiza mai kai, tsayawa yayi yana kallonta ganin zatamai kuka yasa yace "ke" a tsorace ta sauka yatada motar yafita daga gidan, yana fita wayarshi takara ringing ya dauka Munari tace "kataho kuwa yafaki tsayawa jinin" ahankali yace "nariga nataho inama hanya yanzu, idan akwai ice a fridge ki dauko kisa" da sauri ta katse wayar ta kalli Big Mummy tace "yariga yabar gida yafara zuwa" hannu Big Mummy tamika ta karbi wayar batare datama damu da kafarta da ke jini ba, wani number mai suna Bala naga tai dailing ringing daya ya dauka, anatse tace "ka kwashi boys dinka yanzu yariga yabar gidan kuje ku dauko yarinyar koma tayaya ne ku kaimin ita warehouse, tariga tasan secret dina baniso ta tonamin asiri, idan kun daukotan karka kirani kamini text" shiru tayi tana sauraron meyake cewa kafin ta katse wayar.
Tafi minti goma a wurin kafin tai cikin gida ahankali tana goge hawayen idonta, yanzu dama big Mummy dake sonshi haka dama bason tsakani ga Allah bane, dama itace ta haukatar dashi lallai duniya abin tsoro, dama anacewa makashinka yana tare dakai, kuma ma sabida dukiya take son kashe shi dukiyar banza, to yanzu idan tafadamai ma zai yarda da ita, da tunane tunanen nan takai dakinta ta shiga bayi tai wanka tafito ta shirya cikin rigan baccinta na doguwar riga mai kauri tai addu'an bacci ta kwanta tanata tunane tunane toko tamai text? Tunanin hakan yasa ta tashi zaune tsaki taja tunawa da jakarta dake dauke da wayarta na cikin motar shi.
Da sauri ya shiga part din big Mummy rike da first aid box tana ganinshi tawani baje a kujera tana nishi ga kafarta na didduga da jini kadan kadan Munari na fifitata. "subhanallah sorry Big mum" kafarta ya dauka yay treating kafin ya mike tsaye yadan duko saitin kan big Mum din yace "ina zuwa bari naje side dina na dauko abin auna BP" yana fadin haka yafita.
Har bacci yafara daukarta taji karan bude kofa sake shigewa tai cikin bargo tai lamo sosai kaman tana bacci dan karya mata komi ko yazo, taku dataji daban daban sanan anata bude kofofi yasa tadan bude ido dan wanan ba tafiyan mutum daya bane toko dai dawani yazo ne, wani irin bugo kofar dakinta da akayi yasa takara bude ido atsorace, Maza ne guda biyar sanye da bakaken kaya da bakake mask sun rurrufe fuskar su. "hasbunallahu wa ni'imal wakil" kawai take maimaitawa ta runtse idonta da karfi dan gani take kaman mafarki take yanda suka tsatsaya sun zagaye gadon suna kallonta da idanunsu tacikin mask, Babban cikinsu ne yawani irin fizgo hanunta hakan yasa ta fasa wani irin uban ihu wani irin mari ya sakin mata abaki batare dayace mata ko kala ba, aiko baki sai jini fashewa tayi da kuka tana tirjewa tace "dan Allah ku sakeni wlh ni banda kudin baku amma kudau kome kukeso" wani irin finciko hanunta dayayi saida hanunta yay kara yajata tana tirjewa yafita da ita daga dakin sauran hudun suka rufa musu baya, ihu take sosai. "na shiga uku Ya Ayaan, Wayyo Allah Babana" tutturjewa take yanajanta akasa hanunta yaja plate din dake kan center table din falon saman daidai sunkai wurin stairs zai sauka yana janta ta daddage ta mike ta kifamai kwanon akan hanun daya riketa dashi hakan yasa tai wuf zata koma daki daya daga cikin hudun da suke bayansu yasa kafa yawani irin tokareta aciki da baya tayi luuuuu tawani irin mugun faduwa a stairs wani irin wahalallen kara tayi kafin tafara tumble tumble tumble har takusa kai kasa sai kuma kanta yay wani irin landing da buguwa a karfen stair case din, ko kara bude idonta batayi ba tasume warwas sai jini dakebin kanta yana zuba a stairs din.
Daidai lokacin ya shigo part din big Mum rike da abin auna Bp dan yadade yana nema baisan inda ya ijiye ba, wani irin faduwa gabanshi yayi da baisan lokacin daya saki abin auna BP hanunshi ba yafadi akasa, daura hanunshi yay akan kirjinshi yay shiru, Big Mummy tadan dago dakai ta kalleshi kaman mara lafiyan gaske tai magana ahankali tace "Boy lafiya zoka dubani man" sake danne zuciyar shi dake bugawa sosai sanan ya kalli Big Mum, abu yaji yana gangaro wa daga hancin shi ahankali ya kai hannu yataba yaga jini, da sauri big Mummy tace "ur nose is bleeding boy" kirjinshi yakara tabawa dake bugawa sosai yace "Big Mum she's not fine, i can sense it, my heart is telling me" da sauri ya juya yace "am coming" da saurin shi yafita daga dakin Big mum na kiranshi ya shiga mota yay horn yafita daga gidan dawani irin azababben gudu hancinshi na jini.
Dayan daya rikota ne tun farko ya fizgo wanda ya tokaretan sai a lokacin yay magana yace "dan uwarka ance mutaba tane?" tureshi yay da karfi ya sauka suna biye dashi abaya, daukarta yayi ya sabata akafada gatanan kaman mara rai kanta na diddiga da jini suka fita daga dakin ya wurgata acikin bakar van din dasuka shigo da ita compound din, daya daga cikin su yay gudu yaje yabude musu gate yana kallon mai gadin da har yanzu yake asume suna fita ya bisu ya shiga motar sukabar anguwan da mugun gudu gate din gidan abude.
[7/25, 9:18 PM] 0mmer Farouk: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
61 - 62
Ko parking bai gama yi da kyau ba awaje yafito yana kallon gate din gidansu dako rufewa ba'ayi da kyau ba, runtse idonshi yay da mugun karfi kirjinshi na wani irin bugawa kaman ba gobe, da kyar ya iya daga kafan shi daya mugun yimai nauyi ya shiga ciki, da mai gadi yafara cin karo azube kaman baya numfashi ga fuskarshi dukta kumbura sabida naushi, wani irin bugawa kirjinshi yayi ya karasa ya tsugunna ya sauri yana duba pulse dinshi ganin he's still alive suma ne kawai yasa yay reviving dinshi sanan da gudu yay cikin gida, jinin daya gani a stairs yasa heart dinshi ke wani irin mugun racing da mugun gudu, yay sama yana kallon plate dake kasa sanan ga dakunan su duk abude, dakinta ya shiga da gudu babu kowa, wani irin mugun bugawa kirjinshi yayi kaman zai fashe da sauri yabude bayi ya shiga nan ma ba kowa, da gudu yasake fita kaman mahaukaci ya shiga dakin shi da bayin shi bakowa yasake fitowa da gudu ya shiga dayan dakin bakowa, yafito yay kitchen ba kowa ya shiga store bakowa, yafita yay garden bakowa, dawowa falo yayi yana jujjuya wa yana kallon ko'ina amma bakowa, kanshi yawani irin rike da hannu biyu kafin da bude baki da karfin bala'i yace "Bilkisssssss" yawani irin zube akasa ya rirrike jikinshi dake wani irin mugun rawa kaman mai farfadiya, da gudu yafita yay inda mai gadi yake arude ya dauko ruwa ya yayyafa mai hakan yasa yabude ido gabaki daya da sauri ya dagoshi da idanunshi dasukai jarababen ja muryan shi har bata fita da kyau tsabagen bala'i yace "me..me..meya...meya faru?" Mai gadin da biyu biyu yake gani da kyar yace "wasu mutane su biyar sukazo amota sun rufe fuskokin su, suka dakeni sukai cikin gida daga nan bankara saning meya faruba daga nan ba" Gabaki daya jikinshi rawa yake kokarin ma saita yanda zuciyar shi ke bugawa yake sabida karya samu heart attack, da kyar ya mike tsaye yana dafe zuciyar shi yana runtse ido kanshi na juyawa da kyar ya iya ya lalubo waya bama yagani da kyau ya lalubo number Abba yakira ringing biyu Abba dake kan dadduma yagama shafa'i da wuturi ya dauka yace "Boy" da kyar ya iya bude baki yace "p...pops kazo" zumbur Abba yamike daga kan dadduma jin yanda muryar shi ke fita da kyar tana breaking, Mami dake kwance ta bishi da kallon mamaki, arude yace "Boy are u okay, menene, talk to me Boy, u don't sound like u, menene?" da kyar yace "Pops Bilkis, an, ban..ban ganta ba..an dauke..." tsabagen yanda jikinshi ke rawa ma wayar tazame tafadi akasa ta tarwatse, Abba yace "boy, boy" kallon wayar yay yaga ta yanke, Mami tace "menene ba yanzu nan yabar nan ba bayan yay treating kafar hajiya baima tsaya ya auna BP taba fa haka Munari takece min" girgiza kai Abba yayi yace "sako hijabi ki sameni akasa, Boy doesn't sound gud something is wrong" yana maganan yana fita Mami tadau babbar hijabin ta saka ta bishi abaya, Big Mum suka gani tana dingisawa tana zuwa sanye da hijabi hanunta rike da plate tana ganin Mami da Alhaji tace "ina zaku haka nida nazo na debi fruits a fridge nawa ya kare" Mami tace "ga Alhaji nan shinake bi wai Ayaan ba lpy" arude big mumy ta kalli Abba tace "meya sami Boy Alhaji? Mutafi mutafi mugano danmu" gaba Abba yayi suna biye dashi Big Mum ta kalli Mami tace "kedai wlh Allah wadaran halinki Ayaan baida lpy ne shine wai Ayaan" direba Abba yakira ya shiga duk suka shiga aka jasu sai gidan Ayaan.
Yanayin parking motar Ayaan dasuka gani awajen yasa Abba yacema driver yay parking duk suka sassauko Abba ne yafara shiga tsakar gidan ko lura damai gadi ma baiyi ba sai Ayaan daya hango a tsugunne jikinshi nawani irin rawa uncontrollably, da sauri Abba yay kanshi yana "Boy, Boy" dago shi Abba yay yay cupping fuskarshi, hanun Abba yakama gam gam yarike da kyar ya bude baki yace "Pops where is mah wife?" hanunshi Abba yakama ganin kaman ma baya hayyacin shi yay cikin gida dashi yana binshi luuu su Mami suka bisu abaya hankali tashi, shikuma direba ya taimaka ma mai gadi ya shigar dashi dakinshi ya kwantar dashi yanamai sannu.
Zaunar dashi Abba yayi yana kallon jinin daya ga a stairs bakinshi na furta "innalillahi wa innalillahi raji'un" Big Mum tafashe da kuka sosai ya kalli Mami datai shiru tana kallon Ayaan da jikinshi ke wani irin rawa hancinshi jini na zuba yace "ban ruwa Firdausi, mara sanyi" da sauri Mami tai kitchen ta dauko goran ever mara sanyi ta bude ta mikamai Abba ya karba da hannu daya dayan hanun nakan kafadar Ayaan yakai goran bakinshi yana tofamai addu'o'i, Kukan da big Mum keyi yasa Abba ya dakama ta tsawa akule yace "ke kokimana addu'a kokiyi shiru" yasama Ayaan goran abaki ya tsiyaya mai ruwan da kyar yasha sanan yadawo kusa dashi ya zauna ya kwanto dashi yadaura kanshi akan cinyarshi yana kara tofamai addu'an ko jikinshi zai dena rawan, kafin yaciro wayarshi daga aljihu number governor kano yakira gabaki daya, ringing biyu gwamna da kanshi da dauka, Abba yamai explaning abinda ke faruwa.
Within 15 good minutes karan motocin police kakeji suna shigowa anguwa, ansace matar da tilo ga Abdulrasheed Gwanaye ai dole gwamna dakanshi ya turo polisawan, tundaga waje CP yafara saka team dinshi bincike wasu na interrogating mai gadi daya farfado kafin yazo da kanshi har bakin kofa yay sallama Mami tabashi izinin shigowa shida wasu manya police guda uku suka shigo ya tura biyu dake tareda shi sama bincike sanan ya zauna kusa da Abba dake ma Ayaan dahar lokacin bai dawo daidaiba addu'a, saida Abba ya idar sanan ya nisa yace "Alhaji naga akwai CCTV camera a compound din" sai a lokacin ma Abba yatuna yace "harda ma falon nan akwai" IG yace "ina computer to zanzo mu kalla dan musan meya faru" da kyar ya mike tsaye Abba ya rike shi yace "Boy" gyada ma Abba kai yayi da kyar alamun zai iya, Abba yarike shi sukai sama IG nabiye dasu abaya, Mami da big Mummy ma suka bisu, wani daki sukaje nan suka tariyo computer har zuwa daidai inda goons din sukazo sukai horn mai gadi yafita waje dubawa sai gashi daya daga cikin su sanye da mask ya shigo da mai gadi yana dukanshi kafin ya sumar dashi ya bude musu gate bakin van din ya shigo, pursing video IG yayi ya rubuta plate number motar down sanan ya danna play suka cigaba da kallo gashi sun shigo sun fiffito daga motar sunyi cikin gidan sun bude kofa sun shiga falo sukai upstairs, dayake babu CCTV a sama basu ga maiya faru ba saidai ihunta dasuke ji da lokacin datake kiran Ya Ayaan, runtse idonshi yay da karfi wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomai da sauri ya share, saikuma inda daya daga cikin su yasa kafa yatokare mata ciki tafado ta fasa kai wani irin dunkule hannu yayi zai daki computer da sauri IG ya rike shi calmly yace "be strong Man, i know how u feeling, zamu kamasu idan ma kidnappers ne dan basuyi kama da yan fashi ba, inda yan fashi ne da sata xasuyi, indai har kidnappers ne zasuyi contacting dinku, so u people should stay alert zasu iya kiranku kowani lokaci, yanzu dai one good thing is zamu nemo motar nan tasu ta hanyar plate number nan koma ina motar take a fadin kanon nan, sanan Alhaji" ya kalli Abba yace "yakama ta yanzu akwai body guard dazasu dinga yawo da family ka most especially ur son, yanzu dai zan koma office zan zuba team dina akowani hanya da express way na barin garin kano zamu kamasu da izinin Allah, one last thing is i need hoton ta, dan nan CCTV footage fuskar ta is not clear sosai dan musa a media incase idan wani yagan ta" Da sauri Abba ya kalleshi yace "kanada hoton ta Boy kabamu?" saida yarike hanun Abba sanan ya iya magana da kyar yace "yafashe" Abba ya kalli Cp yace "wayarshi tafashe dazu amma zasu samo hoto bari yadawo daidai tukun" ajiyar zuciya cp ya sauke yace "shikenan we will use dis for now, please take care of him he doesn't look good" yanuna ma Abba Ayaan sanan yawuce yafita daga dakin, da taimakon Abba suka fito sabida jirin dayake ji sosai suka zauna afalon sama ya daura kanshi akan kafadar Abba shi kadai yasan yanda yakeji, Abba sai addu'a yakemai jin yanda zuciyar shi kewani irin rawa, tashi Big Mum tayi ta kalli Mami datai wani irin tagumi daurewa kawai take danji take kaman tai ihu tace "bare na shiga bayan gida" gyda mata kai kawai Mami ta iyayi tai shiru tana tunani abu kaman mafarki Bilkisu da dazu dazun nan tana tare da ita, da dingishi Big Mummy ta shiga dakin dake kusa dana Bilkisu ta maida kofar ta rufe, bayi ta shiga ta rufe sanan tafito da