Showing 87001 words to 90000 words out of 123632 words

Chapter 30 - SANGARTATTCE complete by Maman Abd Shakur

04 Jul 2024

33735

daura hanunta akan kirjinshi tareda kai kunenta saitin bakinshi tace "meka ce?" ahankali yace "ba wanan madaran ba" zama tayi kan cinyarshi sabida gajiya datayi da tsugunnawa tace "to wani madara? a ina yake na dauko to" tai maganan tana hararan shi, murya chan kasa yace "anan" waigawa tayi tana kalle kalle to ina madaran anan, kaman daga sama taji yaja zip din gefen rigarta yaja rigar kasa, ihu tayi tana neman tashi daga jikinshi ya kara riketa sosai yana sauke ajiyan zuciya, hanunshi har rawa suke yadaura akan kirjinta. "Kai" takirashi da karfi cikin kuka, ta daddage ta fizge hannayen ta daya dike, teddyn ta tadauka ta bugamai akai tana kuka sosai, ture kanshi tayi da duka hannayen ta biyu ta tureshi da karfin ta tatashi tai wurin kofa zata bude tafita ahaka tsabagen yanda ta rude, da sauri ya mike tsaye yazo wajen kofa zai riketa a tsorace ta tsugunna tafashe da kuka tace "don't touch me, wurin sweeth..." da sauri ya dagota yana girgiza mata kai yasa hannu yadaura akan bakinta, da sauri ya sanya ta ajikinshi ya rungume ahankali muryan shi narawa yace "am sorry" tureshi tayi tana kokarin jan rigan ta sama, daukarta yayi yay bedroom da ita, ahankali ya kwantar da ita akan gadon da sauri tai yunkurin mikewa girgiza mata kai yayi ya maida ita yace "please baby".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

76 - 77


Kafin ma tai yunkurin yin wani abu yahada bakinshi da nata yana kokarin zame rigar gabaki daya daga jikinta, wani irin kuka take jikinta duka narawa hanunta tamika ta dauko filo ta bugamai akai tana ture kanshi da filon jikinta nawani irin rawa tana kuka, yamutsa ta yacigaba dayi batare daya saki bakinta ba, jin ana kiran sallan la'asar yasa yasaketa ahankali yatashi ya zauna abakin gado tareda dafe kanshi yana kokarin saita kanshi, filo ta dauka tana bugamai abaya da duka karfin ta tana kuka sosai tama kasa magana, da kyar ya dago kanshi dasukai jajir ya kalleta yanda take kuka na sosamai rai shima ba'a son ranshi bane yake mata wani abuba, filon dake hanunta takara bugamai akai tana ihu kaman mahaukaciya, ahankali yarike filon tareda saka dayan hanunshi yajawota tana tutturjewa saida yahada ta da jikinshi, ya ijiye filon, tana kokarin tashi yaki bata daman yin hakan ya matseta tareda daura kanshi ata wuyanta yana bubbuga bayanta alamun tai shiru dan bazai iya magana ba ayanda yakeji, tun tana mutsu mutsu har bacci yay gaba da ita. Ahankali yaciro ta daga jikinshi tareda manna mata kiss agoshi ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sanan ya mike tsaye idanunshi sun kada sunyi jajir, bayi ya shiga yay wanka yafito ya shirya cikin riga da wando yadau car key da waya yafita daga gidan.

Baiwani dade da fitaba tafarka daga baccin tana kwalla, saikuma kukan ya kankama sosai sosai take kuka tana kiran sweetheart yazo ya dauketa batason gidan nan mutumin nan sai tabata yakeyi. Da kyar ta mike tsaye taje bayi, wanka tayo shima da sabida jikinta daduk yamata tsami ne, sanan tai alwala tafito daure da towel din data gani abayin, wani dan gown data gani white me hanun shimi a wardrobe din tadauko ta saka tana goge kwalla tana harare harare kafin tadau hijabi daya bata dazu tasaka tai sallan la'asar, tana idarwa ta kwanta akan dadduman tana birgima tana kuka. "sweetheart where are you? Katafi kabarni, why?" tafashe da kuka.

Aaman tunda suka koma bauchi rashin lafiya yatasa shi agaba bana wasaba, shi kanshi baisan cewa haka son Ameerah ya shiga ranshi ba, ganin yanda yake yasa Dr Ameenu ya sanya Ummy kiran Maman su, da kanshi ya sanar da ita komi, aiko washe gari saiga Maman da baban su aka tattara aka tafi dashi Abuja gabaki daya. Alhamdulillah yadan samu sauki danhar abinci idan mum tabashi yanaci, yanada wata cousin Usaida datake sonshi nan Abba yahada auren su aka saka rana wata daya kuma baiwani musu ba dan Usaida yarinya ce mai hakuri gata yar gayu.

Ayaan na fitowa daga masallaci hospital dinsu yawuce dan sosai yakejin rashin lpy, office din Dr Ibrahim yawuce bayan yaduba shi ya daga kai yace "dude wai menene matsalar ka, kaifa Dr ne bazaka guji abinda zai batama raiba wai, well I know u already know zuciyar ka na gab da buguwa" awahale yaja gajeren tsaki saikuma yamike tsaye yace "thanks lemme get drugs" fitowa yay daga office din yana tafiyar nan da isa ana gaidashi yana daga kai kawai kaman bashine me babbakama Bilkisu kuka ba.
Magunguna yasiya da drip da wasu allurai a pharmacy sanan yadawo office dinshi, saida yasha maganin da kyar dan ya tsani magani kafin ya kalli alluran tsaki yayi yadau wayarshi yakira Dr Ibrahim, ko minti biyu ba'ayi ba ya shigo office din yace "Boy gani" wani irin mugun kallo Ayaan ya watsa mai, dariya sosai Ibrahim yayi yace "dan nadan dana sunan da Abba ke kiran ka dalla" dauke kai yayi ya bude kwalban alluran ya zugo da sirinji ya mikamai kaman ance yay maganan dole yace "yimin kuma ahankali" karba Ibrahim yayi tareda daukan auduga ya juya yamai, ahankali yace "aaauchh" bugemai kafada Ibrahim yayi yace "ashe da zafi kake parke different patients kullum" dan murmushi yayi yace "thanks Man" kwanciya yayi adogon kujeran office din ya lumshe ido, Ibrahim yabishi da kallo daga ganinshi kasan ciwo na cinshi dakuma tunani dan alluran nan ma na kwantar da sha'awa ne, drip din daya ajiye akan saman table ya dauka yana dubawa wanan na ciwon da heart dinshi keyine dakuma magungunan suma haka, ajiye magungunan yay ya karaso wajen kujeran yana gangaro dogon karfen da ake makala drip ajiki ya kalli fuskarshi yanda ya lumshe ido ahankali yace "nama fixing drip dinne?" gyadamai kai yayi, hakan yasa ya tsugunna yakama hanunshi ya makala mai sanan ya gyara ruwan yana shiga jikinshi, saida yajira na kusan 3mins sanan ya daura hanunshi akan heart dinshi beating din dayake yi yasoma dawowa normal normal hakan yasa yajuya yay hanyar fita yace "zan zo anjima" gyara kwanciya yayi tareda sake lumshe ido yana tunanin Bilkisu, ahankali yaciro wayarshi daga aljihu number Dad Fawaz yakira, Neurologists ne likitan brain, sanan babban Consultant ne akan any matsala na kwakwalwa, yana kiranshi bayan sun gaisa yasanar dashi zaizo hospital dinshi gobe wurin shi da matarshi, nan dai yafada mai matsalanta.


Saida taci kukan ta tana kiran sweetheart tagaji sanan ta tashi daga kan dadduman ta cire hijabin tabude kofa tafito falo, zama tayi akan kujera tadau teddy ta tanama kitso tana kallon Channel din cartoon din da tasa yasaka mata dazu. Gajiya tayi ta mike tsaye tana dirke dirke akan kujera tana dariya gabaki daya ta hargitsa falon dan kanta tagaji tadau ruwa tana sha sanan ta kwanta tana dariya ita kadai, harta fara gyangyadi taji ankira salla da gudu tana tsalle tai bedroom tadauro alwala tafito tahau kan dadduman dawani irin tsalle kafin tafara sallan.


Wuraren magrib Big Mummy ta shigo gidan akatuwar jeep dinta driver ta shikejan motar, parking yayi tafito tana sanye cikin jan ashobin biki mai shegen kyau dayaji uban stones, securities ne sukazo ta nuna musu babbar jakarta tace "awuce dashi shashina" tanunama driver jakar da abubuwa ke ciki wanda aka raba nabikin tace "biyoni da wanan" tafiya takeyi na isa kaman wata boss tana danna waya har zuwa Shashin Mami, murmushi lullube akan fuskarta ta shiga falon Mami na fitowa daga kitchen kenan taga hajiya fadada murmushin kan fuskarta tayi tace "oyoyo hajiya saukar yaushe" dan tabe fuska big Mummy tayi tana huro hanci wanda idan da Sabo Mami tasaba, ta karbi jakan dake hanun dreba shikuma yajuya yafita Mami ta karaso wajen tana mata sannu da zuwa Big Mummy tamika mata jakar tace "gashin nan inji Atine tunda bakizo ba wai" karba Mami tayi tace "sabida jikin Ayaan ne ai da nazo bikin zinatu, Hajiya kinkosan wani abin farin ciki da ikon Allah kuwa daya faru kuwa" "saikin fada" Big Mum tafada agadaran ce, cikin nuna tsananin farin ciki Mami tace "wlh anga Bilkisu, jiya wayansu suka kawota daga bauchi, inata so nakira ki nagaya miki Alhaji ya hanani wai surprise zamu miki, dan wajen ki har ya warke anga Bilkisu haji..." baya da Big Mum tayi zata zube yasa Mami tariko ta da sauri cike da mamaki tace "baki da lafiya ne hajiya?" arude Big Mummy tace "Bilkisu Bilkisun mu dai matar Boy kikace angani?" gyada mata kai Mami tayi tana kokarin zaunar da ita akan kujera ganin tarude sabida good news din, kin zama tayi tarike hanun Mami tace "tayaya aka ganta? Meta ce muku?" "kaman ya metace?" Mami ta tambayeta tana kallon fuskarta, da sauri Big Mum ta kakalo wani irin murmushin dole tama Mami, ahankali Mami tace "yarinyar da bama ta yarda damu, tasami shafewan kwakwalwa ne, duk bata ganemu ba, tana ma dakin Ayaan" da sauri Big Mummy tana share zufan daya keto mata tace "ina boy din nawa nata ya shi murna" tabe baki Mami tayi tace "yaje Clinic wai" zumbur Big Mum tamike jikinta har rawa yake da kyar ta saita kanta ta kakalo hawaye tace "Allah Akbar kabiran! Allah mai girma da daukaka, bari naje nadubo matar Boy dina" Mami tace "gama abincin su chan angama bari nasa Salamatu takai musu tunda tahada a food flask already" da sauri Big Mummy tace "basai kinsa yan aiki ba tunda chan zani, ban in wuce musu dashi" bama tajira Mami tamike ba tai dining tadau food flask da plate da spoon din data gani ta fice daga shashin har tana harde kafa tana maganganu da kanta tace "Bala yace tamutu, Bala yace tamutu, Bala eh yace tamutu" haka tadinga sumbatu kaman tababba hartai shashin nasu.

Tana zaune akan hadadden center carpet din falon tajawo ledan daya kawo dazu da rana chocolate din da tagani na cabry dairy milk tadauka tana fama da budewa takasa, bude kofan da akayi yasa ta mike tsaye da sauri dan tabama koma waye ya shigo yabude mata, ido da ido sukai da big Mummy data shigo rike da food flask da warmer tawani irin kafeta da ido tana kallonta tun daga sama har katsa, itama kafe Big Mummy tayi da ido kanta nadan juyawa, mayar da kofan Big Mummy tayi tarufe sanan ta tako kafa ahankali tana mata wani irin kallo tana takowa, tana shigowa tsakiyar falon ta ijiye food flask din akan kujera, sanan ta dago kai ta kalleta itama har lokacin ita take kallo kanta nadan juyawa fuskar matar nasata jin wani iri iri data rasa name ba, ahankali Big Mum ke takowa tana dumfaro inda take atsaye tana mata wani irin kallo, samun kanta tayi dayin baya, baya, takasa janye idanunta daga kan Big Mum kanta nawani irin juyawa tana ganin fuskar big mum yana kuma bace mata, jinta tayi ajikin bango kafin tayi yunkurin motsawa Big Mum ta tareta da hannayen ta, ta hanyar sakata a tsakiyar hannayen ta data daura akan bango tana wani irin zaro mata ido, wani irin yamutse fuska tayi ta kudundune hancin ta tana zobaro baki kaman Doddannuwa danta tsorata ta, da sauri ta runtse idonta kanta nawani irin zafi kaman ana ta fasa ruwa, dan harwani kara takeji daga kanta zuwa kunenta na shuuuuuu, cikin kakausar murya Big Mum tace "bude idonki shegiya yar matsiyata dake nufina da tsiya, bude nace, bude idonki!" ta dakamata wani irin tsawa tareda buga bangon datake manne ajiki, afirgice ta bude ido tana wani irin nishi, tsabagen tsorata saitaga fuskar Big Mum na rikide mata, gawasu irin maganganun datake ji daga kanta dake mugun vibrating, fincikar hanunta Big Mum tayi kaman zata cire su daga jikinta tsabagen yanda kanta ke juya mata tana ganin flash din fuskar Big Mum yana kuma bacewa yasa tama kasa ihu, murde duka hannayen ta Mum tayi tabaya hakan yasa tasaki wani irin kara tace "was..." finciko ta Mum tayi tana wani irin yimata abu kaman dodo da fuska tace "kalleni da kyau inda ace nasan su Bala bazasu kashemin ke da wlh ninai da kaina, amma listen to me, dudda kinyi losing memory ban yarda ba, inhar kika sake kika tonamin asiri wlh saina" hanunta ta daura akan wuyarta ta zagaye, arude take kallonta jikinta nawani irin rawa, wani irin kallo Big Mum tasake mata tace "nida nake tsananin farin ciki burina yakusa cika, ko bayan tafiyar ku bansamu ankamomin shi yamini signing papers din bane sabida kullum ubanshi da uwar shi natare dashi" janye hannunta tayi daga wuyanta ta fizgo gaban rigarta luuu tataho tana kukkule ido tsabagen yanda kanta ke juyawa, ganin haka yasa Big Mum tawani irin jijjigata ahankali ta ware idon tadaura akan Big Mum, dafe kanta tayi dake wani irin juya mata kaman amadubi saita fara ganin kanta awani bene tana sanye da hijab tana gudu saitai buge da kujera tafadi, saikuma taga fuskar matar nan data riketa, wani irin zubewa tayi akasa wajen asandare ta suma tsabagen yanda kanta kemata wani irin juyi. Tsayawa Big Mum tayi tana kallonta yanda ko numfashin kirki bata fitarwa, da sauri ta juya tabude kofa tafita daga dakin, leka ko ina tayi ganin babu kowa ashashin yasa ta sauke ajiyar zuciya tadawo dakin ta tsaya akanta tana tunane tunane, yanzu idan takashe ta ai koda, dat is idan ma za'a tambayan ta kenan, zata iya cewa tana zuwa ta dubata saita tafi shashin ta sabida taje tahuta itama daga biki take, hakan ma yafi this is the best chance na aikata barzahu datake dashi before tai running plan dinta, duk wanda zai shigo tsakanin ta da dukiyoyin nan da kamfanonin Alhaji wlh bazata mai raiba.

Gama zancen zucinta keda wuya tadau daya daga cikin manya manyan filolin jikin hadaddun kujerun falon tayo kanta, ahankali ta tsugunna ta daura guiwowin ta akasa tadaura filon asaman fuskarta ta danne da karfin bala'in, rashin samin iskan numfashi cikin Suman datake yasa tafara shure shure tana shushure kafa tana dukan filon da hannu, Big Mummy takara danne filon tace "die, die yar matsiyata, ki mutu dan ubanki malam, mayyar yarinya ke kikajama kanki...."

Parking yayi yafito daga motar shi rike da IPhone dinshi, dayan hanun kuma rike da ledan shoprite da abubuwa ke ciki, direct bangaren shi yayi sabida yanda zuciyar shi taki natsuwa sai kawomai Bilkisu take, da dan saurin shi yay ciki as usual yasa hannu ya bude kofar ya shiga, dayake kofar irin wacce bata karan nanne, chak ya tsaya zuciyar shi naneman ta buga gabaki daya..
Big Mum da bama taji alamun bude kofaba dan tabama kofa baya sai kara danne filon Bilkisu na shure shure, tana kara dannawa tana "die, die yar matsiyata" kaman daga sama taji wani irin azababben tsawan da tunda take arayuwanta bata tabajin irinshi ba, jitayi kaman muryoyi mutum ishirin ne suka hadu suka mata tsawan. "B..Big..Big Mum!" awani irin firgice ta mike tsaye idanunta acikin na Ayaan daya rikide yakoma kaman na zaki.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

78 - 79

Da mugun sauri ya shigo dakin ya kasa dauke idanunshi daga kan Big Mum data fashe dawani irin kuka tana shafa fuskarta da kanta kaman mahaukaciya, daidai lokacin Mami ta bude kofar ta shigo rike da bowl din wani farfesun Ganda na magani data hadama Bilkisu, da sauri ya janye katon filon daga kanta, gatanan kaman bata numfashi ya daurata akan kafarshi, bowl din hanunta Mami ne tasaki a kasa tsabagen yanda kirjinta ya buga takaraso cikin dakin da mugun gudu ta tsugunna kusa da Ayaan tana kallon Bilkisu tace "maiya sameta Ayaan naga bata numfashi" hannunshi biyu ya daura akan kirjinta yana dannawa da karfi, cikin tsananin fushi ya kalli Mami da jajayen idanunshi yace "ask her" ya nuna mata big Mum dake kuka sosai, bakinta ya bude ya zubama iska sanan yakara danna kirjinta, mikewa Mami tayi ta kalli Big Mum tace "mekika mata hajiya tadena numfashi?" cikin kuka sosai Big Mum tace "Firdausi kinsan ko dazu adakin ki nakusa faduwa ko kekika taroni, aljanu suka shigeni agidan biki, dazuma agidan biki akace mini na shake wata nakusa kasheta, inaga abinda yasame ni kenan yanzu, oh Allah nagode maka daka turo Ayaan dawuri wlh muryan shi yadawo dani hayyaci na, ko dazu yan gidan biki malami sukace sun kiramin, Firdausi na shiga uku mena dawo haka, ku taimaka mini dan ya rasulllahi, Aljanu ke damuna" wani irin kallo Ayaan ke binta dashi, Mami kam kusan mutuwan tsaye tayi itama kallon hajiyar take, ahankali yace "Mami taimaka mata tatafi shashin ta, Allah sawake" kallonshi Mami tayi ya dauke kai yacigaba da danne heart dinta da haryanzu baya feeling beat dinshi, tashi yayi ya dauketa chak ajikinshi yazo zai wucesu, kafadar shi Mami tarike batare data kirashi ba, dan lumshe ido yayi yabude yana kokarin saita kanshi ahankali batare daya juyoba yace "Mami ki kaita ta chanza kaya tahuta, ku kira malami yamata rukiya" yajuya yafita daga dakin azuciye.
Mami ma saida ta saita fuskarta sanan ta juyo ta kakalo murmushi tace "muje hajiya kidena kuka Allah baki lpy" idanunta kadai ta kalla taji ko kadan bata natsu da itaba, batama yarda bane, koma menene Allah ubangiji ya bayyana gaskiya, ya kuma karesu daga shirin duk mai shairi, cikin wani irin kuka Big Mum ta daga kafa da kyar tace "Firdausi ni fa? Nine yau zan kashe matar Boy dina habadai, nida nake cikin tsananin farin ciki tadawo" ahankali Mami tace "karki damu kidena kukan nan bakida lafiya, muje ki kwanta anjima sai akira limamu yamiki addu'a" ahaka tana kuka sosai suka fita jikinta ko ina rawa yake Allah dai yasa sun yarda, tasha da kyar.


Awajen parking yay parking ya bude bayan motar yakara taba wajen heart dinta, yana beating amma kadan kadan in bama ka natsu ba bazaka jiba, ahankali ya dauketa yay cikin hospital da ita office dinshi ya shiga da ita ya kwantar da ita akan gado kafin yafita da sauri yaje pharmacy wani irin allura ya karbo da sirinji saikuma ruwan alluran baima tsaya biyansu ba yadawo office din da mugun sauri ya fasa kwalban ya debo alluran, hannu yasa ya daga rigarta sama yamata alluran a daidai ta saitin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login