Showing 30001 words to 33000 words out of 123632 words

Chapter 11 - SANGARTATTCE complete by Maman Abd Shakur

04 Jul 2024

33711

ya kwanta rashin lpy, ka kashe mu duka ka huta and leave ur life d way u want,babu mai takura ma, kabi mata kasa matsiyatan kaya, kaje party and d rest, do as u pleases duniya ce ta isheka riga da wando harda malum malum ma" ta mike tsaye zata fita da sauri ya rike mata hannu ya mike tsaye idanunshi sun kada sunyi jajir kaman zaiyi kuka dan tunda yake Mami tasha fushi dashi amma bata tabamai maganganu hakaba irin nayau, nayau fa kaman ma baki tamai, hannunta yarike gam ya rungume yama kasa magana hakan yasa tamai wani irin mugun kallo tace "sakin mini hannu" girgiza kai yayi da muryan shi datai bala'in rauni yace "Mami please am sorry, naji wlh na yarda zan aureta din, please don't be mad at me sweet Mum" fizge hanunta tayi ta wuce part dinsu dan dama tazo kiranshi ya duba Abba ne dan zazzabi yake jikinshi yay zafi, tana shiga ta rufo kofa tai sama yafi 5 minute tsaye a wurin sanan yawuce part dinshi.

Wuraren 9 na safe yay sallama a bedroom din Abban wanda dagashi sai Baba Suleman dake gefenshi, fuskar Abban ya kalla aiko yaga yaramemai sosai, ahankali ya karasa shiga dakin ya gaida Baba Suleman kafin ya kalli Abba dayama ki kallonshi saima magana daya cigaba dama Baba Suleman yace "good morning Pops" ko kallonshi Abba baiyiba, first time indis life da Abba yay fushi dashi, Baba Suleman kam gimtse dariyar dake cinshi yake dan zaiso yaga yanda yayan shi zaiyi fushin nan yakai, zama kusa da Abba yayi ya daura kanshi akan kafadar Abba ahankali yace "Pops am sorry" ko kallonshi Abba baiyiba hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya ya runtse ido sabida yanda maganan dazai fada ke mugun yimai daci a zuci da baki ahankali yace "ok na amince na yarda zan aureta" da sauri Abba ya juyo farin ciki yawani lullube shi yace "banason iskanci kafa Boy, are u serious" gyadamai kai yayi da dan murmushi ganin for d first time tunda ya shigo dakin Abba yay murmushi, da sauri Abba ya kalli Baba Suleman yace "Alhamdulillah yau juma'a ko Sulemanu?" cikin jin dadi Sulaiman yace "eh yaya""in Allah ya kaimu gobe zaria zamu da sassafe kuwa muje mu nemo mai auren ta, boy harda kai za'a sabida ku sasanta da yarinya, bari na kira Alaji Hashimu (abokin shi) ya shirya" tsayawa yay yana kallon fuskar baban nashi wanan farin ciki haka f*ck.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

27 - 28

*This book is for sale in baki biyaba don't read inba hakaba u and god*

Karfe goma shadaya tamusu a kofar gidansu Bilkisu ne, duk suka fiffito daga mota sunci mayan kaya suka aika amusu sallama da Malam, cikin mintuna da basu wuce uku ba yafito aka gaggaisa sanan ya jagoran cesu zuwa cikin gida.
Falon shi yakaisu inda baban wanshi daya zo daga Sokoto yake zaune yana duba wani littafi nan fa aka fara gaishe gaishe wani sabon hira ya kashame tsakanin su, jiyake kaman ya mutu dan bakin ciki, sai bayan hiran yadan lafa ne shine Abba ya gyara zama ya kalli Yayan Baba mai suna Malam Isma'il dakuma Baba dake zaune gefenshi yace "Malam zuwan mu dinan mai dalili ce, dan da kokon baran mu muka dawo fa" dan dariya yay irin tasu ta manya ya dafa kafadar Ayaan dake sanye cikin white shadda kanshi akasa yace "dana fa yace yana ciki tunda yaga Bilkisu, shine muka zo nema mai auren ta idan za'a bamu" ya karashe maganar dawata irin murmushi akan fuskar shi, tunda yake maganar jikin Baba da Malam Isma'il yay sanyi, gyra zama yay yace "ai mutuncin kadai ya isa yasa nabaka koma me kake so, dan sanin ka danai na wanan karamin lokacin nagane kai mutum ne mai mutunci mai son jama'a ga sanin hakin musulmi, saidai wani hanzari ba gudu ba" yadanyi shiru sanan yay murmushi yace "ita yar wajen tawa Bilkisu dayake so, nariga nabada ita tun tana yar kankanuwa, namaba wani yaro na tun yana dan karami aka kawoshi karatu awajena, yanzu hakama ranan juma'a mai zuwa ne bikin su" wani irin dadi da farin ciki daya rufeshi yasa yadan murmusa kafin yadan saci kallon fuskar Abban shi, yanayin yanda yaga fuskar Abban nashi ne yasa yaji wani irin mugun tausayin tsohon yakama shi, daidai nan wayarshi yay ringing abinda ya ratsa shirun da dakin yay kenan, duba wayar yayi sanan yadan kalli Abba anatse yace "daga asibiti ne bari na amsa" excusing kanshi yayi yafita daga dakin yay hanyar zaure.

Tun safe tana gidan Baaba ana mata gyaran jiki sai yanzu aka gama fatarta har wani sheki take, maroon dogon hijabi ne ajikinta me hula sai kallon motoci biyun data gani akofar gidan su take ganin babu ko almajiri daya balle ta tambaya su waye suka zo dan antashe su sun tafi bara yasa tawuce ta shiga zaure, Isyaka data gani tsaye yana kokarin maida tawada cikin wani jaka dake makale jikin bango yasa tai murmushi zata wuce dan Baaba tace sudena zance tunda bikin yakusa, yace "bamagana amaryan alaramma" dan juyowa tai ta kalleshi saikuma tai kaman zatai kuka tace "me wai, ba kace min zaka fitaba mekakeyi da har yanzu baka tafi ba" ajiye tawadar yayi yadan matso kadan dan da gap sosai a tsakanin su ya gyara tsayuwa da kyau sanan yace "zanje na siyo fentin da za'ama dakin mune, kinga gidan mu na chan kauye badai kyau ba, akwai bishiyar mangwaro, kashu, da gwaiba a tsakar gidan mu harda na agwaluma ma" zaro manyan dara daran idonta tayi tace "da gaske" gyada mata kai yayi hakan yasa tai murmushi tana dan kare fuskar ta da hijabi ahankali yakira sunanta "Bilkisu" dago kai tayi tace "na'am" "kauyen mu akwai dadi saima bayan auren mu munje chan zaki gani kinaso na kaiki rafi?" murmushi tayi tadaga mai kai cike da kunya yay yar dariya yace "shikenan gimbiyar mata ni natafi sabon gari siyo fentin" murmushi tamai tace "adawo lpy" "insiyo miki ice cream?" a kunyace ta daga kai dariya yasake yi yace "wanan dan bakin naki ya iya shan ice cream ko gimbiyar mata" da dan gudunta ta juya zata zata bude kofa ta tsaya chak numfashin ta na barazanar barin kirjinta ganinshi tsaye rike da waya yana mata wani irin kallo, Allah kadai yasan tun yaushe ya shigo zauren dan daga ita har Isyaka babu wanda ya lura dashi, wani irin kallo yamata kafin yama Isyakan dashima ya tsaya turus yana kallon bakon Malam, wani irin dogon tsaki yaja musu yace "bunch of villagers" yafita daga zauren ya jingina da mota yana tattaba waya, bude kofa tayi jiki asanyaye ta shiga cikin gidan nasu batare da tama sake waigawa bayaba, dakin Umma ta shiga ta zauna agefen Raiyana dake tsince shinkafa tana maida numfashi ganin zuciyarta nata bugawa.

Yakai kusan 20mins awaje yaga su Malam sun rako su Baba, idanunshi ya sauke akan Pops ganin yanda duk jikinshi yay sanyi yakoma kaman mara lpy lpy yasa yaji duk wani iri, lallai wanan abu ya shiga ran Popsy sosai, sallama su Malam suka musu shikuma ya kalli Abba dayay wani iri ahankali yace "Pops kutafi ni anjima zan dawo sabida anyi inviting dina zuwa wani induction ceremony anan shika" asanyaya Abba yace "to saika dawo" yabude mota ya shiga su Baba Suleman man ma suka shiga driver yajasu suka bar wajen bin motar yay da kallo kafin ya bude dayar motar ya shiga yabar anguwan.

Wuraren la'asar Isyaka yadawo bayan ya sauka daga bus yafara dandarowa layinsu, tunda yake tafiya yaketa kallon wata bakar van dake pake agaban wani gida anan anguwan tasu, gadaishi gilashin motan bakake dan haka baya ganin naciki, tafiya yaciga ba dayi anatse kaman daga sama yaga wasu samari uku sun sha gabanshi, kafin yay tunani ko yama kawo wani abu aranshi yaga sun fesamai wani abu kaman turare a fuska daga nan kuma bai sake sanin inda kanshi yakeba.

Da sassafe wanan bakar Van dinan tai parking abakin layinsu aka bude yafito, yana fitowa Van din yatafi, ahankali yadinga tafiya harya karaso gidansu su da Malam yaci karo akofar gida yace "ina ka kwana Isyaka?" murmushi ya kakalo yace "Allah taimaki malam naje nai fentin gidan ne" kallo malam ya bishi dashi kafin chan yace "maiya faru to duk na ganka wani iri?" murmushi yay yace "Allah taimaki malam bansami bacci bane, gabaki daya aiki na dinga yima gidan jiya" Malam yay murmushi yace "ayyo to jeka huta Allah maka albarka" da Ameen ya amsa kafin yawuce ciki.

Wasa wasa fa biki ya kankama Amarya gyra take sha ba kadan ba, Mama nayi Umma nayi Baaba nayi, tai wani irin fresh tai bulbul fatarta dakeda mugun taushi yakara wani extra taushin, Walawa ma datagan ta tace abubuwa sun kara manya Isyaka yasamu na sakawa abaki yay bacci aiko tabuga mata dundu.


*kano*
Cikin bacci yaji Abba na bugamai kafa bude ido yayi yaga Abba ya shirya cikin hadaddiyar gizna shadda ga uban malum malum yace "jekai wanka harda kai zamu zaria bikin Bilkisu, kawani kwanta kana bacci kasan karfe nawa?" turo baki yayi Abba ya tallabemai keya ahankali yamike ya shiga bathroom.
Fridge harda su washing machine Abba yasai ma Bilkisu zai bada as gift su Mami dakuma big Mummy dasuma zasu zaria suka hada mata atampopin da lace harda turarurruka duk sunci gayu sunyi kyau. kusan 20 minute sanan yafito fuskar nan adaure, ya sanya sky blue shadda dake kyalli tsabagen kyau ya kafa wata hadaddiyar hula aka yana tafiya daidai sai uban kamshi yake. gaban mota ya shiga driver yajasu sai zaria, matayen suka fara kaiwa gida Malam ya kira Mama tamusu jagora ciki sanan Malam yama mazan jagora zuwa massallacin jumma'an dake anguwan su, bayan anyi sallan jummu'a duk aka natsu a massallaci wanda malamai da dama abokanen malam sun halarta, saikuma Isyakan dayay kyau yasha yar farar shaddar shi ta daidai kudi da mutanen shi danhar baban shi yazo daga sokoto, gakuma daliban malam gasu Abba agefe kusa da malam sai murmushi yake dudda har cikin ranshi yaso ace Bilkisu rabon danshine. 🎤 limami ya rike ya kalli Baba yace "ina angon da iyayen shi ku matso sabida adaura" tashi Isyaka dake sahu nabiyu yayi yazo gaba shidai Ayaan sai binshi yake da kallo yana wani irin tabe baki, microphone din Isyaka ya karba daga hannun limamin yay murmushi yace "inada wata yar sanarwa ne" mikamai limamu yayi ya e bismilla, karba Isyaka yayi sanan ya gyara tsayuwa ya kalli Malam da yayan shi dama duka mutanen dasuka cika masallacin makil, yay gyaran murya sanan yasake kallon malam da murmushi kekan fuskar shi yace "Allah gafarta malam gaskiya nidai nafasa auren, banison yarka Bilkisu, kayakuri bawai cin mutunci bane amma bani sonta ko kadan nafasa auren, na fasa" ya ijiye microphone din yafita daga masallacin ta kofar inda liman kejan sahu, nan fa masallaci ya kacame da surutu baban isyaka yatashi yabi yaron da sauri amma harya hau mashin yabar wajen.
Wani irin matsiyacin murmushi Ayaan yayi ya kalli fuskar malam dahar wani zufa ke ketomai, dawowa yay kaman mara lpy ma su Abba se baki suke bashi, hanun Baba Suleman yaja hakan yasa Baba Suleman dake magana dago kai ya kallai, kara janshi yayi hakan yasa yamike ya bishi abaya suka fita waje Baba Suleman yace "wai wani irin iskanci ne wanan kana ganin babanta baida lpy ne kake jawoni waje, ba yanzu zamu tafi ba leave me" Baba Suleman yay maganan cikin fushi, kaman zai mutu dan bakin ciki yadai saita kanshi yace "Baffa nizan aureta kafada ma Pops adaura auren dani dama saisa nakira ka waje nafada ma" da mugun mamaki Baba sule ke kallonshi yace "kace me?" murmushin yake yay yace "adaura dani" da gudu Baba sule ya juya yay cikin masallacin shikuma ya dunkule hannu ya daki iska. "f*ck wlh zakici ubanki ne ahannuna" azuciye ya shiga masallacin ya hango Baba sule nama Abba magana akunne tashi Abba yay tsaye yazo inda yake tsaye yace "son are u serious?" murmushi yama Abban ya gyada kai, kamashi Abba yayi yamai peck a goshi tsabagen farin ciki, kafin yajuya da sauri yakoma gaban masallacin yadau mike ya tsaya yace "asaurara jama'a, asaurara" shiru akayi duk aka maida hankali kan Abba, yay murmushi ya kalli Baba yace "dama muntaba zuwa neman ma dana auren Bilkisu amma munyi latti lokacin, to gashi dannawa har yanzu yace yana ciki fa, alfarma muke nema ataimaka mana abamu malam" "Allahu Akbar" kawai aketayi a masallacin malamai nata kabbara suna cema malam "Allah ya fitar dakai kunya" wan Baba ya kalli Malam dayay shiru yace "kabasu Bilkisu tunda danshi na sonta kaga munfita kunya" murmushi Baba yay ka kalli Abba yace "na amince kuma nabaku ubangiji Allah ya sanya albarka" zokaga murna wajen Abba da Baba Suleman kamoshi Abba yayi ya zaunar dashi kusa dashi nan fa aka gyara zama liman ya daura aure tsakanin AYAAN ABDULRASHEED DA BILKISU ABDULBASY akan sadaki dubu dari da hamsin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

29 - 30

Bayan Mama ta kaisu dakin Umma dan nanne ba jama'a sosai sai gaishe gaishe suke sanan Umma ta kwalama Layla kira yarinyar ta shigo da gudunta ta sanya yar atampa ta mai kyau ja ta anko, Umma tace "yi maza jeki kira Bilkisu tazo ta gaishe da baki ai kinsan inda take paty ko?" yarinyar ta gyada kai tana washe baki tana kallon su Mami dasukai shigan alfarma sunyi kyau da sauri ta juya tafita daga dakin, wani gida dake nan kusa da gidansu ta shiga gidan Mrs Alkaleey matar amarya ce badai kirki ba tanason Bilkisu saisa ma tace "tazo itada kawayen ta suyi party anan" da gudu ta shiga babban falon inda kawayen Bilkisu yan dogon Bauchi suka cika ko ina su Fa'iza, Fateema, Walawa, Aisha Shehu, Maryam Umar, Fadila, Bass, Maymuna, Hajjaju, Zainab, Reemar, Hajaea gasunan rututu dai ancika falon Mrs Alkaleey sai hira ake anacin shinkafa da salad ana hiran samari da first night, ganin bata falo yasa tai hanyar bedroom din Mrs Alkaleey kwankwasa kofar tayi akace ta shiga, turawa tayi ta shiga ciki, baki tabude tana kallon Yayar tata da Dr Binta ke kokarin zage mata zip din jan lace dakeda ratsin baki din jikinta, ga Maryam Gafai agefe tana kokarin nada dankwalin da za'a daura mata, takowa tayi tazagayo ta gaban ta ta tsaya tsabagen mamaki hannu tasa ta kama bakinta, Mrs Alkaleey tace "rufe mana bakin ke" washe gibi tayi tace "wlh Anty Baby kinyi mugun kyau" murmushi Bilkisu tayi daya lobar da dimple dinta takara kallon fuskarta ajikin madubi dudda kayan data saka na daidai karfi ne, dan wanan lace din ma Baba ya saimata bai hana kyawunta yafito ba, Maryam Gafai ta rangada mata ubansun dauri, an mata riga na sket da ja da bakin lace din da akama aiki awuyan rigan, tasaka bakin takalmi hill da kuma bakin jakarta mai kyau, an saka mata wani hadadden sarka barawon zinare da dan kunen shi da warwaro harda ma zobe, gashi Dr Binta ta chanchara mata makeup da tunda take bata tabayi ba, anyi parking gashinta anmata donut a tsakiya sanan akai daurin dan kwali mai step aka fito da gashin ta tsakiyan daurin. Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayay wanan hallitar! abinda su Reemar keta fadi kenan lokacin data fito falo, Walawa tace "gaskiya Isyaka yau zai sha dadi, anya xai sarara miki kuwa yau idan ankaiki? Kinyi romo romo da yawa yar malam" tai maganan tana wani irin shu'umin murmushi, Fadila tace "koma kakide kakide ne tayi mudai gobe da sassafe zamu faso gidan muzo mu ga yanda take tafiya" dukansu suka fashe da dariya, zama tai akan kujera hawaye ya taru a idanunta sosai zatai kuka dan haka nan taji wani irin kuka takeji duk hankalin ta atashe yake, dafata Mrs Alkaleey tayi tace "karki biye musu kinji ki bata kwalliyar ki, inhar kikai musu kuka haka zasuyi ta zolayar ki" Laylah data kasa dena kallon yar tata tace "Anty Baby Mama ce tace nazo nakira ki wai kinyi baki" ihu dakin ya dauka Bass tace "an daura, an daura su Isyaka ne, tashi kije yar malam amuku wa'azi tare" kaman bazata tashi ba saikuma ta mike tsaye, Raiyana ta dauko bakin gyale mai kyau ta daura mata akai share dan kwallan dataji ya zubo mata tayi ta kalli Reema tace "muje ki rakani" tashi Reema tayi tadau gyalen ta saba akafada suka fita bayan ta kara jan gyalen ta tarufe fuskar ta.

Tunda suka fito daga gidan kanta ke kasa sabida yanda taga maza sun cika layin alamun andaura auren kenen, ahaka har suka shiga cikin gidansu aiko ana ganin ta matan dasuka cika tsakar gidan suka hau guda ayyiririri ga amarya ga amarya, kara lullube fuskar ta tayi har suka shiga dakin Umma da Layla ta nuna musu, Umma ce dake daga bakin kofa ta yaye mata gyalen data rufe fuska dashi tace "ai sai abude fuskar ko tunda kin shigo amarya, ga baki kinyi daga kano iyayen Ayaan ne" dukda bata gane waye Ayaan din da Umma ke fadi ba hakan bai hanata dago kai ta kalli manyan mata biyu dake zaune akan doguwar kujeran ran Umma da aka wadata su da abincin biki agaban suba suma ita suke kallo a kunyace ta dukar dakai ta tsugunna tana wasa da hannayenta dasuka sha lallin amare ahankali tace "ina yinin ku Mumy kunzo lpy" atare Big Mummy da Mami suka amsa mata da lpy lau tareda yima ta godiya akan abinda tama Ayaan, sai a lokacin ma tagane ashe iyayen mara mutuncin mahaukacin nanne, suka mata fatan alheri tareda addu'a zama lpy duk kanta nakasa dan bata yarda sun sake hada ido ba dan kunyan su takeji sosai, Mami ma takasa daina kallonta har kasan ranta takeji kam inama ace Ayaan ya sameta din ya aura da tai farin ciki sosai yarinya mai natsuwa haka da kunya. Ganin takasa tashi yasa Umma tace "to tashi kuje ku koma wajen kawayen ku" ahankali ta mike tsaye tadan kallesu kafin tasake dukar dakai tace "mungode Mummy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login