Showing 75001 words to 78000 words out of 123632 words
"morning" ya sakai yafice.
Wuraren 8 ya shigo gidan dan yabiya gidan kajin su dubusu, yana shigowa tafito daga dakin nasu da gudu tana sanye da bakin riga abaya mai stones kanta har yanzu kitso biyu ne akanta sabida bandejin da aka sa har yanzu ba'a cireba, jiki asanyaye ta fito tazo ta xauna kusa dashi ba kaman kullum data saba zuwa dazaran yadawo daga masallaci da gudu ba, hakan yasa yadan kalleta yana kokarin ciro wayar shi daga aljihun jallabiya, kaman zatai kuka ta lankwasa kai ta kalleshi tace "good morning uncle" shima kallon fuskarta yayi nayan sakanni kafin ya dauke kai ahankali yace "baki da lafiya ne u look somehow" kaman jira take tafashe da kuka daidai nan Ummy tafito daga kitchen dauke da tray data daura cups din tea akai sakin baki tayi tana kallonta tace "kedai Ameerah kinada kukan banza" hararan ta tayi kaman idanunta zasu fadi kasa ta kalli Aaman da tunda tafara hararan ta yake kallon manyan idanuwanta yanda suke sama da kasa tace "Uncle Ummy is looking for my trouble" dan murmushi yayi yace "bakin riga kin harare taba to" wani irin ihu tayi ta mike tsaye tai dakinsu tana kuka dudda uban kiran da Ummy kemata ko juyowa batayi ba, hannu ya mika yadau coffee da Ummy tahada mai yakai baki saikuma yakasa sha sabida yanda kukan ta ke tabamai rai ya kalli Ummy daketa kallonshi tana murmushi yace "me kika mata take rigima yau?" "wlh Ya Aaman babu abinda na mata" shiru yayi kafin ya ijiye coffee yadau tea dinta da chips yay hanyar dakin nasu ahankali ya bude kofar ya shiga tana kwance ta kifa kanta a pilo tana kuka, ajiye tea da abinci yayi ya zauna a gefen gadon yay dan murmushi yace "Ameerah" make mai kafada tayi tace "oh'oh" tai maganan tana dan juyowa tana lekoshi, folding hanunshi yayi a kirji ya daure fuska yace "why are you crying" lankwashe kai tayi ta nunamai kofa tace "Ummy" ahankali yace "okay to sorry tashi kiyi breakfast" tashi tayi ta zauna tana goge kwalla ya juya zai fita da sauri ta riko hanunshi hararan ta yayi. "bana hanaki tabani ba" turomai baki tayi tace "sit down" ahankali ya zauna abakin gadon dan nesa da ita da sauri ta matso kusa dashi tana leka fuskar shi ta washe baki tace "Uncle daga yau i will be calling you sweetheart" da sauri ya kalleta sake washemai baki tayi tace "kaga ko Ummy na kiran saurayin ta sweetheart" yadade yana kallon fuskar ta kafin yace "to ni saurayin kine dazaki kirani da sweetheart" da sauri ta gyadamai kai tace "eh kai saurayi nane Sweetheart" tai maganan harda wuntsula kafa tana murna sanan tadau chips dinta ta daura akan cinya tasa fork ta debo takai bakinshi tace "haa sweetheart" dan hararan ta yayi kafin ya mike tsaye yafita daga dakin wani irin tsalle tayi tana rawa adakin. "yeeeee uncle is my sweetheart"
Afalo yasami Ummy harta gama chan tea wani irin kallo yamata ya daura kafa daya kan daya yadau coffee shi sanan yace "wato soyayya kike koyama Ameerah ko?" ware ido tayi tace "laaa haka tacema" saikuma tai murmushi ganin shan coffee shi yake hankali kwance, ahankali tace "Ya Aaman nidai wlh inason ka da yarinyar, she's very pretty and lovely, kaga dama Abba nata damunka kafito da mata why don't you go for her" yakai kusan 5min maganar na waka aranshi harta cire rai dazai amsata saikuma yace "I wouldn't risk dat, yarinyar datai loosing memory saina fara soyayya da ita, wat if tanada wanda takeso kafin abinan yasame ta, karma ki kara irin maganan nan" kaman daga sama yaji tace "amma ai kana sonta" da sauri ya kalleta ya nuna kanshi yace "nina cemiki ina sonta" yanayin yanda yake kallonta ne yasa taji wani irin tsoranshi ya shigeta bakinta har rawa yake tace "dama dama naga ka taimake ta ne, kuma yanzun nan datake kuka ka kasa cin abinci saida kaje ka lallaso ta and a whole lot of things danake ta noticing dis past few days" yadade yana kallonta yana karkada kafa idanunshi har sun dan soma chanza kala har yabude baki zaiyi magana Bilkisu tafito da gudun ta tazo ta zauna kusa dashi tana murmushi tace "sweetheart i want teddy" ko kallonta baiyi ba yace "stop calling me sweetheart" make mai kafada tayi tace "ni u are my sweetheart ko Anty Ummy" sumsum Ummy ta mike tabar falon kafin tasata abala'i, Bilkisu tabita da kallo sanan ta juyo ta kalleshi hada ido sukayi dan ita yake kallo yanason yagano me Ummy tagani harta ce yana sonta, washemai baki tayi tace "sweetheart teddy bear" kaman ba zaiyi magana ba saikuma yace "i want to sleep now anjima zamuje musiyo" tashi tayi tana murna tace "yeeeee" tai dakinsu da gudu da sauri ya runtse ido yana dafe kai ahankali yace "please please don't do dis to me, tayaya zanso wacce bansan ko waccece ba, tayaya zanso wacce ita karan kanta batasan kanta ba" ahankali ya ijiye cup din coffee a wurin yatashi ya shiga dakinshi.
Bayan kwana hudu.
Zaune yake acikin mota ya kafesu da ido yanda suke tsalle tsalle su uku ita da zainab da Ummy basu lura dashiba wasan yar gala gala suke yi, tana sanye da doguwar riga ta daura sweetar akai sai tsallake gida gidan take tana dariya daga gani wasan yakai mata, karan wayarshi dayaji shiya fargar dashi daga dogon tunanin dayake yi ganin Dr Ameenu ne yasa ya dauka daga tachan bangaren Dr Ameenu yace "kaga news?" shirun dayayi yasa Dr Ameenu yace "nama san kagani, wat is your plan yanzu kasan dai yakamata ka maidata garin su ko, ka kaita police headquarter da akace duk wanda ya ganta ya kaita, yaushe zaka kaita yanzu" lumshe ido yayi yakara budeso ya daura akanta yanda taketa guje guje su Ummy na binta, ahankali yace "i don't want her to leave Man, tun shekaran jiya nagani a news har a Twitter da Instagram saida naga hoton ta a page din Nigeria police sun saka, i don't know what to do banaso ta bar wajena, i don't want her to leave friend" anatse Dr Ameenu yace "i tot we've talked about this, Aaman tayaya zaka fada tarkon soyayyar wacce bakasan ko wacece itaba, u know nothing about her, bakasan iyayen ta ba, bakasan daga ina takeba, yarinyar daka tsinta rana tsaka kawai sabida ta zauna dakai na watanni saika fada tarkon sonta, tun wuri kama tsamo kanka da kanka, and tomorrow banda office, am off tomorrow bazanje clinic ba inka shirya kaita zan iya binku har kanon" shiru yayi har lokacin yakasa dauke kanshi akan Bilkisu yayyafi ake duksu Zainab sun shige barander suna kiranta tabar ruwa amma taki sai tsalle tsalle abinta take, ahankali Dr Ameenu yakira sunanshi. "Barrister Aaman" ahankali yace "na'am" Dr Ameenu yace "you have to make a decision now" dan lumshe ido yayi yace "wat if muka kaita iyayen ta sukazo suka tafi da ita does that mean bazan kara ganinta ba? Yaya zanyi da raina da zuciyata dake cike da kaunar ta?" "mudai fara kaita tukunna, kayi tunanin wani hali iyayenta ayanzu haka suke ciki, wata nawa basu saka yarsu a idoba wani hali suke ciki just imagine irin farin cikin dazasu shiga gobe idan suka ganta, don't think much abinda kamata kayu kenan ka maidata ladan ka naga Allah" lumshe ido yayi yace "alright Allah kaimu goben" katse wayar yayi ya jinginar da kanshi akan kujera ahankali yake karanto addu'o'i da zasu sakamai natsuwa kafin ya bude motar ya mayar ya rufe ya shigo gidan kaman ance ta daga kai ta ganshi yana tahowa wani irin ihu tayi ta taho da gudu tana murna. "oyoyo sweetheart oyoyo sweetheart dinmu, Anty Ummy sweetheart is back" ganin ya tsaya yaki cigaba da tafiya yasa itama ta tsaya tana washe mai baki tunawa da yahanata fadomai, saikuma ta turomai baki kaman zatai kuka tace "oyoyo fa nake maka sweetheart" ledan snacks din dake hanunshi ya mikamata ta karba tana washe baki tana kokarin budewa yay gaba abinshi hakan yasa ta fasa budewa ta bishi da gudu ganin zata bishi har daki yasa ya tsaya ya juyo ya kalleta ahankali yace "jeki chanza kayan nan bakiga kin jike bane" kara washemai baki tayi tana kallon fuskarshi tace "in chanza" gyada mata kai yayi da sauri ta juya tai dakinsu, cire kayan tayi tasake saka wani doguwar rigar atampa black ta daura dan kwali tabar ledan snacks din adaki tafito harda gudunta, afalo ta sameshi rike da ruwa yana sha ta zauna akusa dashi, cire ruwan yayi daga bakinshi yace "ina Ummy" "sun tafi gidan kaji" gyada mata kai yayi kawai dan bayason magana ya lumshe ido da sauri takara matsowa kusa dashi kaman zata shige jikinshi tace "sick?" yagane tambayan shi take ko baida lpy hakan yasa ya girgiza mata kai ya bude ido tareda sauke ajiyar zuciya hannunshi yasa a aljihu yaciro wayarshi daga pocket yana daddannawa kafin ya bude page din policeng inda aka saka hoton ta ya bata wayar ta karba tana kallonshi ahankali yace "look at d screen wacece wanan?" da sauri ta kalli screen din hoton ta kafe da ido sosai sanan ta kalleshi ta nunamai wayan tace "nine?" ta tambaye shi, wani irin ajiyar zuciya yayi yace "yea kene ance sunanki Bilkisu Abdul..." makemai kafada tayi kaman zatai kuka tace "my name is Ameerah ko sweetheart" shiru yayi yana kallonta daidai lokacin Ummy ta shigo tanamai sannu da zuwa ya amsa sanan yamata magana da yaren french. "ki hada mata kayan ta gobe zan kaita garin su police sun bada sanarwa chan police headquarter zamu kaita nida Dr Ameenu na kano, insha Allah once naga sun kira iyayen ta agabana nagansu dakaina saimu juyo mudawo, zainab ta tayaki kwana zanma Umar magana ya barta" gabaki daya jikinta yay sanyi hakan yasa ta juya kawai ta shiga daki dan wani irin kukane yazo mata, sanan ya kalli Bilkisu data tasashi agaba tana kallo yace "wat? Mesa kike kallona haka" dariya tayi sosai dan har tana buge filon kujera suna faduwa kasa sanan ta kalleshi cikin dariya tace "sweetheart wlh ina sonka ne" tacigaba da dariya tsayawa yayi yana kallonta he's sure awajen su Ummy takejin irin maganganun nan, mikewa tsaye yayi jin ana kiran sallan magrib yace "go and pray zanje masallaci" kaman zatai kuka tabishi da kallo harya fita sanan ta share yar hawayen daya zubo ta wuce dakinsu.
Wuraren nine yadawo lokacin hartai bacci yaci abincin da Ummy takawo mai yawuce daki duk jikinshi yay sanyi.
Wahe gari wuraren goma nasafe yafito daga dakin idanunshi sunyi jajir shima sabida uban knocking kofar shi datake tayi tanamai kuka ne, murmushi yamata bayan ya bude ganin yanda take uban kuka yace "stop crying oya je Ummy ta shiryaki mufita" ya kalli Ummy dake zaune akan kujera yamata alamu dakai hakan yasa ta mike tariko ta sukai dakinsu shikuma yakoma ciki ya shirya cikin manyan fararen kaya dasuka karbe shi sosai yafito da baban trolley dinta da Ummy tahada takawo dakinshi tun jiya da night yafito dashi yasa a boot din mota daidai lokacin motar Dr Ameenu ta danno kai compound din dan murmushi yayi yajira haryay parking yafito shima cikin manyan kaya shada blue yazo yace "guy gaskiya da motar ka zamu bazan kona maina ba kafini kudi" tsaki yay ya wurgamai key motar ya chabe yace "kai xakai driving" ya kwalama Ummy kira sabida tafito da ita shikuma ya bude motar ya shiga Dr Ameenu ma ya zaga ta bangaren driver yabude ya shiga, ita tafara fitowa da gudun ta tana sanye cikin black body hug da black straight skirt sai Ummy ta daura mata maroon kimono me shegen kyau akai ta kulle mata belt din kimono ta gaba sanan tamata rolling black vail akai da keda one one stone ta bakin gyalen tasaka mata takalmi baki maidan tudu daya fito da hasken kafarta, gabaki daya Yay nisa a kallon ta yanda tai kaman balarabiya tsaban kyau maganar ta dayaji akanshi ya fargar dashi. "sweetheart wai zamu fita?" gyada mata kai yayi batare dayace komiba, shidai Dr Ameenu waya yaciro abinshi yakira matarshi suna hira, da sauri tace "ina zamuje park zamu?" girgiza mata kai yayi yace "shiga mota garinku zamu" "inane garin mu?" tafada tana murna, dan murmushi yamata yace "shigo mota muje kigani" tsalle tayi ta bude kofar baya ta shiga tanama Ummy bye bye, kudi yaciro dayawa yabama Ummy yace "I will call u anjima" addua sosai tamusu sosai sanan Dr yaja motar suka bar gidan saida suka danyi nisa yace "ka kosan na dauko file dinta na hospital kasan police da tambayoyin banza kafin suce mumuka saceta na dauko file dinta kai ID card dinama na jikina am not ready to enter any gbese" dariya yadanyi sabida yanda ya karashe maganan yace "kai kayi aure nazaci zuciyar ka zata chanza ta dena wanan tsoro ashe babu abinda ya chanza" hararan shi Dr yayi yacigaba da tuki batare dayace komiba itakuma tana baya saiyima teddy ta mai gashi kitso take tana yar wakarta na yar gala gala yarinya yar gala gala wasan yara ahankali, ta madubi yake ta kallonta har daga baya bacci ya kwashe ta.
Dayake wuraren sha daya sukabar Bauchi sai gurin biyu da rabi suka shigo garin kano kafin sukai police headquarter kuma sai wuraren karfe uku da minti biyar, parking sukayi suka fito ya zagayo tabaya rike da pringles din daya saimata a hanya da bottle water sabida bacci takeyi tuntuni ya bubbuga kujeran hakan yasa ta bude ido da sauri ya dauke kai, waige waige tayi tana kallon wurin tace "sweetheart mun iso garinmu?" dan ita tazaci wani wurine mai suna haka, gyada mata kai yayi hakan yasa tafito tana Kalle Kalle shikuma ya maida kofar ya rufe ya kalleta yanda take kallon polisawan daketa harkan su sun ririke bindigogi yace "muje" girgiza mai kai tayi tana neman yin kuka ta nunamai yan sandan ahankali yace " don't worry babu abunda zasu miki muje" gaba yayi tana binshi abaya har inda Dr Ameenu yake suka shiga ciki saida suka rubuta sunayen su sanan sukace inspector Husaini Ahamad suke nema dan sunanshi aka rubuta a page, kujera aka nuna musu shima dan polisawan sungan su sunyi shigan alfarma ne yasa sanan wani daga cikin su yatafi office din inspector yay kusan 10 min sanan yafito yace "muje" tashi sukayi suka bishi har office din inspector dake zaune yana jiran su sanan yafita, inspector na ganinta ya mike tsaye cike da mamaki kafin ma suyi magana yace "am coming ku zazxauna" fita yayi yay upstairs office din CP, yana shiga ya kame yay saluting CP sanan yafada mishi abinda yagani Cp yabiyo shi suna zuwa office din tsayawa yayi baice komiba yana kallon Bilkisu take fama da bude goran ruwa saikuma yasa hannu a aljihu yaciro wayarshi ya duba yaga ai yarinyar hoton nanne wacce akai kidnapping wani irin shan mur yayi ya kalli su Aaman dake kallonsu yace "su waye ku? And waccece yarinyar nan? A ina kuka samota? Menene hadinku da ita?" kafin ma Aaman yace wani abu Dr ya mike yaciro ID card dinshi yace "am Dr Ameenu and my Friend here is Barrister Aaman, nan ya shiga basu labarin komi tundaga kan yanda Ayaan ya tsinceta da lokacin daya kawota hospital yagama sanan ya bashi file din medical record dinta. Saida Cp yagama dubawa yay wani irin hamdala ya mika musu hannu yana godiya sanan yace sutashi suje office dinshi dan gaskiya wanan good news gwara Alhaji ya gani a office dinshi ba'a office din inspecta ba yau ya tabbata sabuwar mota da kujeran maka zai samu, office suka tafi suka zazzauna sanan yadau waya yakira Abba.
Alhaji dasu Baba da Baba Sulaiman wanda yadawo jiya jiyan nan sabida kiran da Mami tamai dan Alhaji ma ciwo ne yarufe shi, yaudai duk dauriyan da Abba yakeyi kasawa yayi yafashe da kuka sosai, babba dashi amma kuka yake ganin abinda yafi soyuwa agareshi, aduniyar nan gabaki daya ma Ayaan baimasan wake kanshi ba, gashi yaki yarda a kaishi asibiti agida Dr Ibrahim yazo yamai allura yamishi fixing drip, Mami dai fita daga dakin tayi ta shiga nata tana kuka sosai, Baba ne ke kanshi yanamai addu'a aka, shikuma Baba Sulaiman yana calming Abba down, ringing da wayar Abba yayi yasa Baba Sulaiman ya mike ya dauko wayar daga kan gadon da Ayaan yake a kwance ganin Cp ne yasa ya mikama Abba yace "ka dauka Cp ne Allah sa Muji alkairi" goge idanunshi yayi da bakin malummalum din dake jikinshi ya kalli Ayaan da aka sakama oxygen dan baya iya numfashi da kyau ya sake girgiza kai yana kokarin tsayar da hawayen dakeson zubomai, yay picking call din tareda yin sallama ahankali, zumbur yamike tsaye yana neman fadi Baba Sulaiman ya taroshi bakinshi har rawa yake yace "Cp kace anganta, Bilkisu Bilkisun mudai?" kowa na dakin kallonshi yake tsabagen murna ma jefar da wayan yahi ya tsugunna yay sujjada sanan yayo gadon baima bi takan Baba Sulaiman dake tambayan shiba yay cupping fuskar Ayaan da idanunshi ke lumshe yana girgiza shi hawaye na gangarowa daga idanunshi na farin ciki yace "Boy, Boy tashi muje police headquarter anga Bilkisu Boy, anga matar ka" da kyar ya bude idanunshi dasuka kankance ya rike hannun Abba da karfi yana kallon fuskar shi batare daya iya magana ba, gyadamai kai Abba yayi yace "yes, yes my baby Boy, anga matar ka, i love u Boy so so much, oya get up let's go get ur wife" da taimakon Abba da Baba yatashi har lokacin kallon Abba yake dan gani yake kaman zafin zazzabi yasa yakejin Abba nakiran anga Bilkisu, ciremai robar oxygen din Abba yayi sanan yacire mai drip din ya kalli Baba Sulaiman yace "ban rigan shi" clean white t-shirt ya mikomai Abba ya dauramai akan singlet din jikinshi suka mikar dashi yay mugun haske lips dinshi jajir ga rama saidai bai hana kyanshi fitowa ba, takalmin yasaka da kyar Abba da Baba suka fitar dashi shikuma Baba Sulaiman