Showing 18001 words to 21000 words out of 123632 words
mata kai Umma tayi tace "zancen me bayan keda Isyaku kun kasa hakuri har ki gama jarabawa ai wlh malam yamin daidai dayace kawai ranan walimar shi kawai a daura auren". Tashi tai tayo kan Mama tana kuka Mama ta daure fuska tace "kina zuwa nan saina mammake ki" juyawa tai tafita daga dakin tana kuka sosai mara sauti, nan fa aka fara gyara amarya Umma da Mama, ba abar Baaba abaya bama yau abata wanan gobe abata wancan tasha.
****
*kano*
Wani irin mugun kallo yabi yan aikin dake gyara flowers din side din Mami dashi kafin ya bude kofa ya shiga, stairs yahau yawuce dakin Popsy dake nan bangaren ta, da sallama yabude kofar ya shiga dakin yabi kowa nadakin da kallo Daga Pops sai Baba sule da Mami sai big Mummy dake kusa da Mami. gaida su yay Mami tabi tsinannun kayan dake jikinshi da kallo ta nunamai kofa tace "wuce kaje ka chanzo kayan nan" "ke firdausi kibarmin yaro fa yasha iska a gidan nan, shida gidan mahaifin shi ba agida yake yasa ba fita yay dasu kinfa takurawa Ayaan dayawa fa" Big Mummy ta chabe tace "atoh! Duk tabi ta gwanzabi yaro, dududu nawa yake dabazai sa abinda ranshi kesoba bahaka yaran zamani kesa crazy jeans dinan suyi ass down ba is normal suwagan kenan, kifita daga idanunshi gaskiya firdausi" "shekara talatin fa hajiya shine yaro? Sa'anin shi nada yara uku wasu ma fin hakan" Mami ta tai maganan cike dajin haushi, "ahap gorin aure zaki mana? Ai aure nufine na Allah ingaya miki, kuma mata saiya dirja ya dirje ta nunawa duniya wlh, ranan bikin shi dole duniya tasan SANGARTATTCE danmu ke aure" takarashe maganan tana hararan Mami ta gefen ido,
shiru Mami tayi bata sake cewa komiba Abba ya kalleshi yace "shigo kaji dan gata na" shigowa yayi batare daya bari sun sake hada ido da Mami ba yawani shege jikin Abba, Baba Sulaiman dai murmushi kawai yay ya girgiza kai dan agidan nan daga shi sai Mami ne ke kokarin gyara Ayaan tun yana yaro amma Abba da Big Mummy son shi ya rufe musu ido basaji basa ganine akanshi.
Shafa kumatun shi Abba yayi yace "kowani irin kaya kakeso kasaka gidan ubanka kake, idan ban maka abinda kakeso ba inada wani wanda zan mawa ne" ya kalli Mami yace "ki kiyayi fushi na wlh, duk randa kika kara batama Ayaan rai nida kene" yay kwafa yasake juyowa ya maida hankalinshi kan Ayaan yace "son yau kusan sati daya da dawowan ka baka bamu labarin yanda kasamu lpy ba".
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
19 - 20
"Baka bamu labarin yanda kasamu lpy ba dan from video damuka kalla a haukace kabar gidan nan, maiya sameka bayan nan dazaka iya tunawa?" shiru yayi yana kallon fuskar mahaifin nashi kafin ya maida kanshi kan kafadar shi ya yatsine fuska yace "wata yarinya ce haka Popsy a zaria" saikuma yay shiru Abba yace "wace yarinya Boy? Metayi ita yarinyar? Ya sunanta?" shiru yay yana kokarin tuno sunanta dayaji wanan marakunyan yakira amma yakasa tunawa, karamar tsaki yadan ya yace "namanta sunanta Pops buh her brother yace wai itane ta karbo magani wurin Dad dinta tabani ta dinga kula dani na warke?" Abba yace "yanzu shine baka gayamin tuntuni ba, yaudin ma inda ban tambaye kaba haka zakai shiru ko" shiru yay baice komiba. kallon Baba Sulaiman Abba yay wanda shima shi yake kallo bayan gamajin maganan da Ayaan yayi yace "Sulaiman jeka shirya Zaria zamu yanzu kuwa, muje mu godema iyayen ta da ita yarinyar, sanan kome takeso aduniyar nan wlh sainai mata shi inhar baifi karfina ba dan tamin abinda har na mutu bazan iya biyan taba, ta kularmin da Boy" da sauri Ayaan ya kalli mahaifin nashi murya chan kasa dan bai fiye son magana ba yace "Popsy nifa bansan gidan suba" "badai zaria take ba, koma inane koma kwana nawa zai dauke mu saimun nemota dan haka kama debo extra kaya?" "ni fa clinic zani Pops inada patients" yawani daure fuska hakan yasa Abba ya sassauta murya yace "to idan baka bimu munje ba tayaya zamu ganeta kaine ai kataba ganinta" kaman zaiyi kuka sabida bakin ciki danyau akwai party da zaije yace "ni namanta fuskarta i can't recognize her kona ganta" shiru Abba yay saikuma yakamo kafadarshi tareda jan hancin shi da dan karfi hakan yasa yadanyi murmushi, murmushi shima Abban yay yace "to me zaka iya tunawa ranan dai daka gansun?" shiru yadanyi saikuma yace "wanta nada wanan abun da ake xpress dashi?" Abba yace "machine?" girgiza kai yay yace "a'a ni bansan sunan abin ba, but yellow ne kaman car kaman bike" da sauri Baba Suleman yace "keke napep?" shiru yadanyi jin kaman ranan fa yaji yaron yana cewa napep hakan yasa yace "i think so" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Baba Sulaiman yace "ya za'ayi kenan?" Baba Sulaiman yace "yanzu dai idan munje zai fara kaimu inda yatashi yaganshi ne daganan kuma zamu iya tambayan mutanen wajen idan babu wanda yasansu saimu je duk inda yan keke napep ke taruwa ko parking mu binciko wannata aikasan sunanshi ko?" ya jefoma Ayaan dake danna waya yana jinsu tambaya, maida wayar yay aljihu tareda saukowa daga gadon yace "am not sure but i think she called him Muji" Abba yace "shikenan jeka shirya kasa manyan kaya kaji Boy" shiru yay bai amsaba yafita daga dakin duk ranshi adagule, Big Mummy ta mike tace "Alhaji mu shirya mubiku muma?" girgiza kai yay yace "a'a kudai hadamin kaya, muda bamusan gidan suba idan mun gano gidan next zuwa aiduk sai mu shirya mutafi tare". Ranta bai soba haka tai wajen Wardrobe Mami ma tatashi suka hada kayan tare.
Saida Abba yaje part dinshi da kanshi ya ganshi a kwance sai wani cin magani yake, murmushi yay yawuce gaban wardrobe dinshi yaciro mai manyan kaya shadda fara da blue sai kuma yadi mai laushi black daya ijiye mai agefen gado da hula kube agefe dakuma su singlet da boxers, sauran kuma yahada a akwatin shi karami ya dau turarurukan shi yasaka ciki yarufe sanan ya kwalama Mike kira ya shigo dakin da gudu ya bashi jakan yace "yaje yasaka a mota" karba yay yafita, sanan Abba yadawo gadon da kyar ya lallaba shi ya shawo kanshi sanan ya yarda zaisa kayan, kafin yakamo hanunshi yakaishi bayi sanan yabarmai dakin.
Koda suka fito za'a tafi bai fitoba, Abba yakara komawa part dinshi Mami tabishi da kallo tana girgiza kai dan wlh bata data cewa amma abu na Alhaji ya isheta, tare suka fito da Abba yawani sha mur bakaramin kyau manyan kayan sukamai ba bakin soft yard ne da akamai dinkin half jumper daya kama jikinshi yafito da murdaden jikinshi sosai, ga yadin ya haska shi tareda kara bayyana farin fatar shi da pink lips dinshi, harara Mami ta watsamai dasuka hada ido hakan yasa ya dauke kai da sauri, Abba daya kamata lokacin data harare shi ya nunata da yatsa. "kifita daga idona fa Firdausi wlh inkikace xaki takurawa yaron nan zamu zuba dake nefa" gidan gaba ya budemai yashiga dudda akwai body guard dake wajen wanda aikinshi bude kofa ne, Baba suleman ya shiga baya, driver Abba ya shiga mazaunin shikuma Abba yakoma baya ya zauna Mami da Big Mummy suka musu Allah kiyaye hanya suka tafi.
Wuraren azahar suka shigo zaria agaban wani massallaci suka tsaya sukai salla sanan suka kara shiga mota hakadai yadinga nuna musu hanya har gaban bolar nan.
Kin fitowa yay daga mota saidai ya nuna musu ginin suka shiga Abba harsaida yay kwalla babu komi a wajen sai carpet din data sakamai, fitowa sukayi suka shiga motar Abba nata kallon fuskar shi ta madubin kofar mota yana mamakin wakeson halaka mai da, shi baimasan Abba na kallonshi ba dan danna waya yake. Duk wani samari dazasu gani a anguwar saisun tambaye shi koyasan Muji suce basu saniba, hakadai har suka fara zuwa duk inda sukaga yan keke napep sunyi parking suce basusan wani Muji ba, har akai sallan la'asar suka tsaya sukayi suna fitowa yace "Popsy ni am tired fa" "shikenan to muje hotel kahuta gobe macigaba da neman sun" wani hadadden hotel sukai lodging a The Fabs anan suka kwana, washe gari tun wurin 8 Abba ya shigo yatashe shi yace ya shirya su cigaba da nemanta kaman zaiyi ihu haka yatashi ya shirya cikin farar shadda ya dauko black shade yasaka ta sanan yafito sai uban kamshi yake mai shegen dadi fuskar nan daure kaman zai fashe.
Tasha tasha haka suke zuwa har wurin karfe biyu suna abu daya, ata bakin kasuwan tudun wada sukai parking inda masu keke napep ke parking Abba da Baba Sulaiman ne suka fito suka gaggaisa dasu suka tambaye su ko sunsan wani mai keke sunanshi Muji, wani daga cikin su ne yace "Mujin filin mallawa?" shiru Abba yay chan yace "wlh bamu san dan ina bane mundai san sunanshi Muji" mutumin yace "to bari nakira shi kuga ko shine" godiya Abba yamai cike da fara'a aiko yana gama wayan mutumin yace" yace gashi nan zuwa" Kudi Abba yaciro masu yawa yamasu kyauta aiko sai murna suke nan fa suka fara koda yazo inba shi bane koma waye yake nema saisun nemomai shi. Abba yadinga godiya dan shi mutum ne mai fara'a mara girman kai, dason mutane idan yafita baruwan shi baya yanuna shine mai kudin nan da Nigeria keji dashi. Shidai gogan yana mota abinshi iskan Ac na hura shi yana danne danne awaya dan Meram ta isheshi da message.
Cikin minti talatin saiga Muji yazo da keken shi yay parking yafito, ya kalli abokin daya kirashi yace "Maska yane tasamu ne wanan kira dakamin ina masu nemana din?" daidai nan Abba da Baba Sulaiman suka taso daga jikin mota dasuka jingina, dafashi dayaji anyi yajuyo ganin magidanci ne yadafa shi yaci uban babbar riga yasa yay murmushi tareda dan dukar dakai yace "ina yini alaji" murmushi Abba yay yace "Mun wuni lpy, yar tambaya nake dan Allah Kaine Muji" gyada kai yay yace "eh sunana Mujittapa amma Muji ake cemin, kaikasa akirani Alaji dafatan dai lpy?" murmushi Abba yasake mai yace "lpy kalau, dan Allah tambaya nakeson nama kaine kokuma nace kasan wani mahaukaci haka achan wata anguwa haka gaban wani Bola a sabon gari. "wanan mara mutuncin mahaukacin na hanyar dogon bauchi, ai yariga ya warke Alhaji, kanwata data lura dashi tun yana sato buredi ta dinga kawomai abinci yanaci daga bayama ta karbo mai magani wurin baban mu tabashi yasha shine yana warke wa ya zanemu dagani har ita, ya kwada mata mari nikuma ya shakeni yakusa kasheni ai namai Allah ya isa wlh" tunda yake maganan Abba yakasa dauke ido akanshi, saida ya ijiye maganan sanan yace "shine ya shakeku?" da sauri Muji yanuna mai wuyan shi yace "kagani alaji har yanzu wuyana bai dawo daidai ba, har yanzu da shati shatin jan dayayi" dan murmushi Baba Sulaiman yayi dan so kawai yake yaga me Abba zaiyi, ga mamakin shi sai yaga Abba yarike hanun Muji yace "zokaga wani abu" kofar gaban motar ya bude daidai inda Ayaan dake chatting yake, bakin glass din fuskarshi Abba ya cire hakan yasa Ayaan dago kai ya kalli Abba, Abba ya nuna Ayaan da hannu ya kalli Muji yace "wanan ne ya shake kan?" shiru Muji yay yako kafeshi da ido shima Ayaan Mujin ya kalla rass ya ganeshi amma yawani basar ya cigaba da danna wayar dayake yi, ta kwayar idonshi masu kama dana mage muji ya gane shi dan har gobe bazai manta da idanun mahaukacin daya shake shiba aiko ya ballamai harara ganin ya dauke kai ya kalli Abba yace "shine alaji" Abba ya daure fuska tamau yace "Boy dama abinda kama wayanda suka taimake ka kenan dan iskanci, oya bashi hakuri right dis minute" tsaki Baba Sulaiman yaja aranshi dan yazaci Abba zaidan zubama Ayaan mari ne ya ramama yaron amma ina bazai iyaba, tashi ma yay daga wurin yakoma bayan mota ya bude ya shiga abinshi ya xauna. Ayaan dako dago kai baiyiba Abba yace "badakai nake ba bashi hakuri" dago kai yay ya zubama Muji ido batare dayace komiba, bakaramin kwarjini yama Muji ba, dauke kai Muji yayi ya kalli Abba yay murmushi yace "haba alaji basai yabani hakuri ba, mu dan Allah muka yi kumama wlh inda nasan dan kane daban fadama ba saiyanzu naga kaman ku wlh kaman kai kaki" murmushi Abba yay kaman bashine ya daure fuska ba yanzun nan yace "nagode dan albarkan yanzu kaimu gida mu godema mahaifin naka da ita yarinyar ko" rasa yanda Muji zaiyi yasa yakoma keken shi dan kunyan tsohon yake ya kunna keken shikuma Abba yashiga mota sukabi keken nashi abaya har kofar gidan su Bilkisu dake cike da almajirai anata karatu.
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
21 - 22
Parking Muji yafara yi kafin babbar jeep dinsu kirar range rover tai parking, Muji ne yafara fitowa kafin Abba da Baba Sulaiman, gaban motar Abba yabude ganin baida niyyar fitowa ya kalleshi yace "fito mah boy" fitowa yay sai wani cin magani yake, Abba yasa hannu yacire shegen bakin gilashin dake idonshi tareda turawa a aljihu, Muji ya kalli Abba yace "bari nagaya mai" shiga zauren yayi almajiran dai sunata karatu sai kallon su Abba suke, karasa wa zauren Muji yayi ya tsugunna agefen malam dake biyama wani karatu saida yagama sanan ya dago kai yace "Mujittapa ba'aje sana'a bane yau" dariya yay yace "Baba baki nakawo ma, kai ake nema suna kofar gida" Baba ya mike tsaye yace "muje" fita sukayi daga xauren shida Muji, Abba na ganinshi ya washe baki dudda zai girmi Baba bai hanashi dukawa ba lokacin daya mikomai hannu, shima Baba kunya yaji ya duka ya karbi hanun nashi suka gaisa, sanan ya mikama Baba Suleman hannu suka gaisa, bugeshi Abba yay tabayan shi hakan yasa yamikama Baba hannu yanadan murmushin dabaikai ciki ba yace "barka da warhaka" karba Baba yay cike da fara'a dudda dai bai sansuba amma yaga kaman daga gani dan tsohon nanne, ya kalli Muji yace "shiga gida kace su gyara zan shigo da baki" da sauri Muji yajuya yay cikin gidan yayinda Malam yajuya aka cigaba da gaishe gaishe kaman ansan juna, Muji yafito yace "Baba zaku iya shiga" Malam ya kallesu yace "to Bismillan ku" Muji ne yafara gaba Baba biye dashi abaya sai Abba daya fizgo hannun Ayaan da baida niyyar zuwa sai kallon almajiran yake kaman baitaba ganiba, daure fuska yay yabi Abba suka shiga zaure ya nunama Abba allo yana wani yatsine fuska yace "wats dat Pops" gaba Abba yay abinshi ya barshi tsaye yanata kallon bangon da yaran daketa kallonshi suna washemai wani harda lashe majinan daya fito daga hancin shi da sauri yajuya ya tabe baki kafin yabi bayan Abban nashi dayaga ya bude kofa suka shiga cikin gidan dake a gyare tsaf dashi, simintin sai kyalli yake, babu kowa a tsakar gidan sai kamshin turaren wuta mai dadin kamshi dake tashi, iso Malam yamusu afaddadden falonshi dake gyare tsaf an shimfida babbar tabarma a tsakiya duk suka zazzauna sai bin dakin yake da kallo yanda yaga littatafai kala kala sun cika bangon dakin an jerasu kaman mesuim, Baba ya kalli Muji tareda ciro kudi a aljihu yace "jeka sawo ruwan gora" ganin yanayin su na yan gayu ne, da sauri Abba yace "ina ga randa nan ina gani kawani ce ruwan gora malam, ban yarda ba gaskiya" yay maganan yana nuna randar dakin yana dariya, tashi Muji yay yadebo ruwa ya cika babbar jug din malam mai tsafta yadaura akan tray dinshi sanan ya sanya kopuna biyun a kai yakawo musu Abba ya karba yana washe baki diba yay yasha Baba Sulaiman ma yasha ruwan dadi ga sanyi, tsiyayawa Abba yay ya mikama Ayaan dake gefenshi duk atakure, murmushin dole yay yace "ina azumi kamanta ne Popsy" shanye ruwan Abba yay sanan ya ijiye cup din, Baba yay murmushi yace "Masha Allah sassannun ku da zuwa saidai ban ganekuba wlh" Muji ne yadawo kusa da Baba yace "Baba uhm dama" saikuma yakasa magana Baba yace "ina jinka" ahankali Muji yace "Baba dan Allah kayakuri daga ni har Bilkisu bamu fada muku komi akaiba, dama akwai wani.. ...." nan Muji yafadi ma Baba komi, Abba ya chabe da. "Malam babu abinda zamu iya ce muku sai ubangiji Allah ya saka da alheri yakuma biya bukata yakara daukaka ka, ai da Ayaan yafada mini shine muka shirya tundaga kano mukazo neman ku, munsha wuya kafin mu gano nan, Allah ubangiji ya biya muku bukatun ku duniya da lahira, yanda kuka taimaki dana kuka sani farin ciki ubangiji Allah yasaku ku farin ciki ranan gobe kiyama, watana daya da kwana goma sha biyu banga Ayaan ba rana daya kawai yadawo ta sanadin ku, nagode nagode malam" murmushi Malam yay yace "Ameen Alaji mugode ma Allah, a'aa ikon Allah kaji magana fa, shine kuma yaran nan sukamin karya, inda ace Bilkisu tafadamin ai danasa ma har gida anje an dauko shi namai addu'a nabashi magun guna anan, to ubangiji Allah ya kara mana katanga da makiyan mu, ko lokacin dana bata addu'an nace mata inhar sihiri ne dazaran yasha zai karya ashe kam sihirin ne" Abba ya girgiza kai cike da damuwa yace "bamusan waye ke neman shi da shairi hakaba, amma muna kan rokon Allah daya bayyana mana gaskiya" Baba yace "ai wanan ba matsala bace zan bashi addu'o'i dazai dingayi kullum safe da maraice in sha Allah babu abinda zasuyi dazai kara kamashi da izinin Allah kuwa dan kariya ce" Abba da kaman yazuba ruwa akasa yasha yace "mun gode, mun gode akaramakallahu, Allah ya biya bukata" sukadan yi shiru shidai Ayaan kanshi akasa Allah Allah kawai yake Pops yagama surutun shi sutafi, gashi yakasa daddana waya hakanan yaji malam ya cikamai ido, maganan Abba ne yadawo dashi daga zancen zucin dayake yi. "Malam ina diyar naka Bilkisu zanzo mu ganta mu kara yimata godiya idan ba damuwa" murmushi Baba yay yace "tana makaranta chan dogon bauchi, dayake na rana takeyi sai biyar da rabi zata dawo" Abba