Showing 84001 words to 87000 words out of 123632 words

Chapter 29 - SANGARTATTCE complete by Maman Abd Shakur

04 Jul 2024

33740

yay maganan ya kalli dayan dayake kallonta yace "wuce mutafi Musa" da sauri Musan ya tsugunna ya mika hannu zai taba kafar yace "mugan kafar" daidai lokacin Ayaan yashigo part din hanunshi daya rike da babban teddy bear red me gashi dayan hanun kuma white leda ne dake dauke da different snacks, tsayawa yay chak yana kallonsu yanda suke kallon mai mata barinma na tsugunnen. Washe baki Musa yayi yace "haba mana kibari naduba miki ciwon kefa me kyau ce" make mai kafada tayi tana kuka ta matsawa baya tana hararan shi, dayan yace "Allah baka sa'a nidai kaga tafiya ta" yajuya zai koma wajen plant Ayaan daya gani a tsaye yana musu wani irin kallo da idanunshi dayay jajur yasa bakinshi yafara rawa yanason yakira sunan Musa amma yakasa, wani irin watsar da kayan hanunshi dayayi sukai kara shi yasa daga Musa har ita suka dago kai, arude Musa ya mike tsaye ya kalli dayan da shima jikinshi ke rawa yake yace "kai nafasa aikin, nabar aikin, natafi" da sauri yajuya yazo ta gefen Ayaan zai wuce da gudunshi, wani irin fizgo shi da Ayaan yayi saida rigar jikinshi ta yage, bugashi yayi da bango bamm, yawani irin shake shi, dayan na ganin haka da mugun gudu yazo yabi tabayan su yafice, yanda taga Ayaan ya shake shi mutumin na neman mutuwa yasa ta mike tsaye tana zazzaro ido jikinta ko ina na rawa, wani irin duka Ayaan yarufe shi dashi a zuciye yana buga bayan shi da bango. "uban wayace ka kallan min matata? Uban wayace ka kalla min mata ta har kasan ita mai kyau ce ko dan ubanka, yausaina tsiya yar da idon daka kalleta dasu" kamo wuyar shi yayi yana neman kai hanunshi cikin idanunshi, idan kaga Ayaan zaka rantse mahaukaci ne, fashewa tayi da kuka sosai tsabagen yanda ta tsorata tazo wurin ganin kokarin budemai ido da mutumin ya runtse gam yake, tabaya ta rungume shi sosai jikinta na wani irin rawa tafashe da kuka tace "please stop am scared" yanda ta daura hanunta akan kirjinshi yasa wani irin shocking ya shiga jikinshi, da sauri jikinshi ya saki hakan yabama Musa dayaji jiki a hanunshi ya fizge kanshi ya gudu da kyar, yunkurin binshi yayi tai baya zata fadi da sauri ya fizgota azuciye, kankame idanunta tayi a tsorace, ya tsugunna yadau teddy ta da ledan ya fizgo hanunta yabude daki ya shiga da ita.

Wani irin jefata yay akan kujera da idanunshi dasukai kaman banashi ba yace "uban wayace kifita ahaka, kinja wasu maza sun kallan min ke eh, bakisan da aurena akan kiba, u are my wife, my property, am ur husband" make mai kafada tayi tana kallon dan gurjewan datayi tace "ni banda husband, kuma ni sweetheart zan aura dankaji, nasan yau zaizo ya dauke ni mubar muku gidan ku, ni banason nan gidan ma nafison gidan sweetheart dina, farm house dankaji infad..." wani irin tari dataji yanayi yasa ta daga kai ta kalleshi, dafe kirjinshi yayi numfashin shi na neman barin kirjinshi yana kokarin saita kanshi yana tari kaman mai asma, arude ta mike tsaye tana kalle kalle, ruwan data hango kan fridge ta dauka da sauri ta juyo kafin ta karaso ta bashi har ya zube a wurin asume".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

73...


*dake nake, kedai wanan rubabbiyar me hanun tantabara dazata marking ta fitar dashi waje, da idanun kaman na agwagwa, maicin amana dai yay asara, yar air mekama da macen bera, yama sunan macen bera ?? Beratu kawai*


Tsugunnawa tayi ta kwalalo ido waje tana kallonshi ganin ko numfashi bayayi, arude ta daura hannayen ta akan kirjinshi tana dukanshi. "kai, kai, wai bazaka tashi ba, bude idanun ka" girgiza shi take sosai amma ko motsi bayayi, fashewa tayi da kuka ta mike tsaye tana kalle kallen dakin tarasa abinyi, bottle water data dauko ta ijiye kusa dashi ne tagani hakan yasa ta tsugunna da gudu tana kuka tadau ruwan ta bude takai bakinshi cikin kuka tace "dan Allah kasha to katashi kaji, to bazan kara fitan ba, amsa" jijigashi takeyi ruwan akan bakinshi amma baiko motsa, mistakenly garin jijigashi yasa ruwan ya bare mai a fuska daga hanunta, wani irin ajiyan zuciya ya sauke batare daya bude idanunshi ba hakan yasa tafashe da mugun kuka tace "kai kabude ido nace, yakuri to" labban shi dataga yabude yanason yay magana yasa takai kunenta saitin bakinshi da sauri, murya chan chan ciki yace "press my heart" da sauri ta daga kanta ta daura hannuwanta ata saitin zuciyan shi wanda baya bugu da kyau ta daura ta danne da duka karfin ta tana kallon fuskarshi, ganin har lokacin babu wani chanji yasa tasake danne zuciyar, jin still batajin bugun zuciyan sosai yasa ta daddage tai nai uku tana kallonshi, ajiyar zuciya ya sauke sosai tareda bude idanunshi kadan ya kalleta, fadawa tayi kanshi tafashe da kuka tace "kai bazan karaba" saikuma ta dago kanta ta kallai Ita yake kallo asanyaye da idanunshi dasuka kankance tace "u are sick ina maganin ka na dauko ma" shiru yayi yana kallonta, share kwallan daya zubo mata tayi tace "ina maganin ka" shiru yayi yana kallonta da idanun nan dasuka kankance suka chanza kala, matsawa tayi ta jingina da kujeran ta cusa kanta akan guiwowinta tafashe da kuka sosai tace "ni nagaji da gidan nan, anata dukana, anata dambe da mutane har ana kwakule ido ma, tunda nazo tashin hankali nake gani, am tired, Sweetheart kazo ka tafi dani, where are you sweethea..." kasa karashe maganan datake yi tayi sabida yanda Ayaan yataso ya daura kanshi shima akan guiwanta duk yanda yaso ya daure yakasa wani irin nishi yake bakinshi na rawa yace "dan Allah, dan Allah Baby, I know you are not well but pl..." saikuma yay shiru jin yana neman yakara sumewa sabida yanda zuciyarshi ke wani irin gudu, arude ta dafa kanshi tace "kai wai me haka mutuwa zakayi? Na shiga uku Sweet..." fadawa yayi jikinta ya kankame ta sosai yanason yay magana amma yakasa ajiyan zuciya kawai yakeyi, yanda taji zuciyarshi na wani irin beating ba kakkautawa yasa tace "u heart is sick" saikuma tai shiru tana sauraron yanda jikinshi ma yadau rawa kodai ba mutum bane dama gashi fari kaman aljanin zabiya da Anty Ummy tabata labari, ahankali ta shiga tureshi daga jikinta muryan ta narawa tace "sas..sa..sakeni inje induba ko sweetheart yazo mutafi" wani irin matseta yayi ajikinshi yanajan numfashi ya chusa kanshi awuyan ta kirjinshi nawani irin bugu yafashe da kuka sosai yama kasa maganan, itama arude tafashe da kuka so kawai take ta kwaci kanta daga wanan kwakumetan dayayi, cikin kuka tace "sakeni inje in duba swe..." kara fashewa da kukan da yana ganin rabonshi da yin irinshi tun yana yaro, shi karan kanshi baze iya explaining yanda yakeji aranshi inda takira katon nanba, zata sake magana ya daga hanunshi ya kyar ya daura akan bakinta ya shiga rera mata wani irin kuka mai tsinkar da zuciyar mutum, da kyar ya iya controlling yanda zuciyarshi ke bugawa ya bude baki cikin kuka yace "p..pl...lz..stop calling dat name wlh zan iya mutuwa, am begging yhu baby dan Allah ki tausaya min, am suf...fering" shi kanshi baisan meke damun shi ba, yanda yake reramata wani irin kuka irin na sangartattun yaran nan mara kara awuya, hawayenshi har gangarawa suke yi daga wuyanta zuwa kirjinta, da sauri ta hadiye nata kukan taji yawani irin mugun bata tausayi duddu bata gane takamai men meke sakashi kukan ba, amma saitaji tana wani irin jin tausayin shi ahankali tace "to nadena amma nadinga cemai uncle to" runtse idonshi yya da mugun karfi wasu hawayen sharr nazubo wa shi gabaki daya bama yaso yaji tana maganan wani namiji ne aduniyan nan, shiru itama tayi jin yanda hawaye ke gangarawa jikinta, ahankali ta sakala hannayen ta ta daura asaman kanshi ta shafa mai alamun lallashi, wani irin ajiyan zuciya ya sauke yakara kankame ta da kyau ya lumshe ido, tun tana sauraron yanda heart dinshi ke beating da mugun fast har tazo tajishi yasoma komawa dai dai ahaka itama wani wahalallen bacci yay gaba da ita.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

74 - 75


Wuraren sha biyu na rana Baba ya shirya zai tafi Abba sai kiran Ayaan yake amma wayan shi bata shiga dan yakawo ta suyi sallama da mahaifin ta hakan yasa ya kalli Mami yace "jeki kira Ayaan firdausi" tom tace tafita daga dakin sanye da babban lullibin dake jikinta. Akofar dakin tai sallama tai sallama taji shiru hakan yasa ta bude kofan yanda taga Ayaan da Bilkisu ne yasa tai maza ta rufo musu kofa tana girgiza kai, komawa tayi lokacin har Baba da Abba sun fito compound Abba yace "ina suke" dan murmushi tayi tace "inaga kaman yakaita asibiti ne" Baba yace "dama banaso taga tafiya ta dan shirmen zata cigaba da muku ga wanan adinga bata addu'o'i ne nayi a ruwan in sha Allah zata dawo hayyacin ta" karban goran ruwan Mami tayi shikuma Baba ya shiga motan suna mai Allah kiyaye driver yajashi suka fita daga gidan, kamo hanunta Abba yayi yace "come here meyafaru baga motar boy nan ba aparke" dariya kawai tayi tace "wlh bacci suke nashe nashe afalo abinsu" wani irin washe baki Abba yayi yace "masha Allah, Allah sarki my Baby Boy yaushe rabon yay Bacci nashe nashe haka kullum ciwo yake, Allhamdulillah, Allah nagode maka daka dawomai da farin cikinshi, da abu yataba min yaron nan Firdausi wlh gwara ni yataba ni sau dubu" tabe baki Mami tayi tace "oh har yanzu hajiya bari naje na kirata" waya yaciro daga aljihun gaban rigar shi jin ana kiranshi yace "takirani tace koda daddare yau kokuma gobe zata dawo wai sai yau suka kai Amaryan kuma zasu tsaya mata jere, insun gama dawuri zamu ganta" gyadamai qkai Mami tayi, Abba yace "dan Allah je adaura musu abincin rana abinci merai da lafiya, kar wanda yadame su fa, kuma harda ke karki daman min yarana, idan kin gama ki aika musu da abincin su part dinsu" baki Mami tasaki tana kallonshi cikeda mamaki, murmushi yamata yajawo ta suka shiga ciki yana yar dariyan manya.


Wajajen azahar ya farka sabida kiran sallan da akayi yana dafe kanshi sabida yanda kan kemai mugun ciwo, juyo da kanshi yayi ya kalleta yanda take baccinta awahale, dan murmushi yayi ya kalli dan gurjewan datayi akafa, ahankali ya mike tsaye ya dauketa batare daya tada taba ya shigar da ita bedroom akan gado ya kwantar da ita ya ja bargo ya lullube mata kafa sabida sanyi sanan ya shiga bayi wanka yayi dan yadanji dadin jikinshi ya dauro alwala ya fito yasaka soft dark blue yadi simple jumper akamai turare ya fesa yafita daga dakin da sauri dan bayaso yana missing jam'i, saida aka idar yadawo gidan shashin Mami yayi, dining ya tsaya ya dauki apple sabida yunwar daya keji yayi sama, sallama yayi ya shiga dakin Mami bayi take kokarin shiga ganinshi saiya sa ta tsaya murmushi yamata yace "Mami na" "har an tashi daga baccin" da sauri ya kalli Mamin da idanunshi masu kama dana mejin bacci, dan dariya yayi ya gutsiri apple batare dayace komiba, fridge Mami tabude ta dauko wani tsumi a gora dayay sanyi ta bashi ya karba yana kallon goran tace "gashi ka kaimata ta shanye" da sauri yace "meshi Mami?" hararan shi tayi ta dauko goran da Baba yabata na ruwan addu'a tace "wanan kuma kadinga bata kullum ruwan addu'a ne Baba yamata kafin yatafi" karba shima yayi ashagwabe yace "Mami am hungry fa" girgiza kai tayi tace "kadai ajiye iyali yanzu kake abu har yanzu kaman yaro, anyway abincin ku na shashin ku" tashi yayi rike da gorunan yace "bari naje naci inmun gama zamu je hospital" anatse Mami tace "daka bari gobe kuje wat if yanzu kun fita taita cewa ka kaita chan wajen wayanda suka kawota, kabari tadan manta tukun gobe koda da yamma ne basai kujeba" shiru yadanyi saikuma yace "to Mami" fita yay daga dakin yana gutsuran apple din hanunshi, tun daga barrander yakejin dirke dirke da karan kujera, bude kofa yayi ya shiga tana tsaye akan kujera rike da teddy daya siyo mata, wurga teddy tayi sama saitai wani irin ihun dadi ta dirko kasa ta chabe, akan daya daga cikin kujeru falon ya zauna yana kallonta yanda take wasan hankali kwance saibin kafafun ta da kallo yake, juyowa tayi ta kalleshi suka hada ido ya lumshe ido sabida yanda idanunta suka mai wani yarr, da sauri ta dirko daga kan kujeran tayo inda yake tana washe baki tace "kaima zakayi in arama teddy na?" batare daya bude idoba yasa kafanshi ya tadiyota jikinshi dan kara tayi tace "wayyo teddy na, na danneta tana kuka" dan murmushin gefen baki yayi yadan dagata yasa hannu ya zaro teddy din ya ijiye akan kujeran next to him, bin teddy tayi da kallo ta makemai kafada tace "kai kabani teddy na, kakusa sa na kasheta" ware idonshi yayi ya sauke su akan bakin datake turomai wani irin miyau me daci ya hadiye kafin ya mayar da idon ya lumshe su ahankali yace "kinyi salla?" turomai baki tayi ta balla mai harara tace "banai alwala ba natuna hijabi na nachan gidan mu, farm..." da sauri ya mike tsaye ya dauke ta harsaida tadan firgita ta rirrike shi, bedroom yay da ita yaje gaban wardrobe dinshi da ita ya sauketa ya bude, kayane da yawa na mata a kusa da nashi hannu yasa ya zaro hijabi yabata yace "pray kizo muci abinci" turomai baki tayi, ahankali yasa yatsa ya shafa lips din yana mata wani irin kallo da lazy eyes dinshi, da sauri ta tureshi tana hararan shi ta mikamai gogeggen hijabin ashagwabe tace "bude min ni" karba yayi batare daya janye idanunshi daga kan fuskarta ba ya warware yasaka mata ya gyara wuyan, bakaramin kyau hijab din yamata ba, mutuwar tsaye yayi yakasa daina kallonta, juyawa tayi batare data damu da yanda yake kallonta ba tahau kan dadduma tafara salla yafi 2min a tsaye a wurin kafin yaje palour, abincin ya bude a warmer, fried rice dayaji veggies ne da roasted turkey ya deba a plate, ya dauko remote ya kunna TV yadawo ya zauna yana chanza channel zuwa news.
Fitowa tayi sanye da hijabin tazo zata wuce shi ta zauna akan kujera hijabin ta ya jawo harsai da tai yar kara. "wash wai menene kai" tafado kanshi tana turamai baki, matseta yayi ya cire hijabin ya ijiye akan kujera yana kallon fuskarta, murguda mai baki tayi batare datai magana ba tana kallon abincin, cikinta ya shafa ahankali yace "zakici?" gyada mai kai tayi, kwanto da kanta kirjinshi yayi yana shafa soft kumatun ta, da hanun daman shi yasa spoon a abincin ya debo zai kai bakinta, make mai kafada tayi tace "ni baby ne" bakinshi yakai saitin kunenta yadan lasa yirrr dataji yasa tadan zabura zata tashi, rikota yayi yana dan murmushi yace "oya haa" hararan shi tayi sanan ta budemai bakin ya saka mata yana kallon fararen hakoran ta, da sauri ta hadiye tana kallon teddy ta tajuyo ta kalleshi da sauri ta washe mai baki tace "wait, my teddy is hungry too" da sauri ta tashi harda dan gudun ta ta dauko teddy ta dake kan dogon kujera tana tsalle, bin cinyoyin ta daduk intai tsalle rigan ke dagawa yayi, da gudunta tadawo zata zauna akasa yajawota jikinshi tana girgiza mata kai asanyaye, abincin yakara debowa yakai bakinta ta amsa tana jijjiga teddy ta, taci sosai dudda hankalin ta nakan teddy ne kafin ta ballamai harara zata sauka daga jikinshi, girgiza mata kai yayi yakara jawota jikinshi kaman baby ya rungumeta sosai ta yanda ko motsi ta kasa ahankali yace "please stay here, sabida na iyacin abincin" fizge kanta tayi tana turomai baki tana hararan shi zata tashi ahankali yasa hanunshi daya ta bayanta ya riketa da kyau takasa tashi dayan hanun kuma ya debo shinkafar da cokali yafara ci bai wani ci sosai ba ya ture yasha ruwa ya kalleta sai faman yima teddy ta kitso take, ahankali yakai hanunshi kan two kitson dake kanta, shafa kitson yayi kafin ya saukar da hanunshi kan ciwon kannata yana shafawa, dago manyan idanunta tayi ta yatsine fuska tace "stop". Gorunan da Mami tabashi yajawo yamika mata tsumin tafara karba sabida alamun sanyin da tagani ajiki da sauri ta bude takai bakinta lumshe ido tayi tana lashe lebe ta kalleshi tace "dadi" takara kafa sauran abaki ta shanye goran ta mikamai ta mike tsaye daga jikinshi tana kallon TV saikuma tajuyo tafashe da kuka tace "cartoon zan kalla" dan murmushi yayi yace "zoki zauna anan saina kunna miki" da sauri tazo ta zauna kusa dashi, daura kanta yay akan kirjinshi sanan yasa mata Disney junior tana kallon pj mask shikuma ya tattare kwanukan yatura su one side kafin ya kara gyara mata zama ya sanya hanunshi yana wasa da jelar gashin ta.
Batare data kalleshi ba tasaka hannu ta fizge jelar tana murguda mai baki tana kallon cartoon dinta, daganan bai kara tabata ba sai uban kallonta dayake yi kaman yau yafara ganin ta, shikadai yasan yanda yakejin sonta aranshi, to mesa yamata wulakanci da.
Ahankali yadaura kanshi agefen wuyanta yana shakan kamshin fatarta ya kankame ta sosai, zafin dataji daga jikinshi yana gasata yasa ta juyo da kai da sauri ta kalleshi, kallonta yayi kasa kasa saikuma ya lumshe ido, da sauri ta daura hanunta akan goshin shi kafin ahankali tace "sick?" gyada mata kai yayi, da sauri tace "meke ma ciwo" hanunta yakama ya daura akan heart dinshi batare dayace komiba, kaman zatai kuka ta murguda mai baki tace "kasha magani" girgiza mata kai yayi, ashagwabe tace "to wani magani kakesha na dauko ma?" ahankali yace "madara" da sauri ta ijiye teddy akasa ta tashi daga jikinshi tai wurin fridge tunawa da taga madara dazu data bude fridge, hollandia evaporated milk ta dauko mai harda dan gudunta tazo ta tsugunna a kusa dashi tabude ta kaimai bakinshi dan bude ido yayi kadan yasa hannu yature madaran murya chan chan kasa yace "ba wanan ba" dan matsowa kusa dashi tayi dan bataji meyace ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login