Showing 21001 words to 24000 words out of 67868 words
 da cewar shi kadai suke jira ganin lokacin da ya shigo suna gyara zama masu hararsa nayi da masu yi masa tsaki.
 Kafin ya zauna sai da ya gaishe su jam'i kasancewar shine me k'ananun shekaru a cikinsu wasu suka amsa wasu suka yi masa shiru, cike da jarumta ya mik'a wa me girma governor hannu suka gaisa a muntuce sannan aka bude taro da addu'a.
Shugaba taro ya mike ya fara fadin "Dalilin da ya tarasu anan domin a zauna a samu maslaha da fahimtar juna a matsayin su na 'yan kasuwa da suke kawowa kasa cigaba saboda haka an bawa kowa dama ya tashi ya fad'i ra'ayin sa a kan abunda yake faruwa.
Dukaninsu kusan bakinsu yazo daya na cewar *Amjadu* yana so ya rusa su ya dakatar musu da harkokin kasuwancinsu bayan bude company da yayi ya sauke farashin kaya sunyi kasa kuma yana da ma'aikata sosai suna tsaye a company ko suna kawo cigaba kayayyakin da suke yi wane na kasar waje da wata Dubai ma saboda haka bakinsu ya had'u gurin cewar gomnati ta rusa wannan company domin yana dak'ile harkokin kasuwanci su."
Yana hakimce cikin kujera yana kallon bakin kowa Alhaji Hashimu me citta shi yafi kowa zak'ewa a gurin  Akwai Alhaji Sunasi me leshi mutum da ko sati ba'ayi ba yaje masa da maganar cewa yana so su hada hannu dashi, domin faranta ran talaka da k'ananun 'yan kasuwa Ashe duk k'arya ne lallai dam Adam mugun ice ne gashi harda shi cikin masu hada masa taro.
Bayan me girma governor duk ya gama jin k'orafe-k'orafen su sai ya kalli *Amjad* cikin nutsuwa yace." *Young millionaire* kaji abunda suka fada, wannan metting din muna yin sa ne domin Samar da zaman lafiya gami da maslaha ga gomnati da kuma Ku 'yan kasuwa. 
Cikin nutsuwa ya dago kansa yana kallon me girma governor yace." Ranka ya Dade duk naji abunda suke k'orafi akai, farko dai ina so su gaya min cikin su wa na tab'a shigarwa harka ko kuma na tab'a zuwa ran can kudi gurunshi, bayan nan kud'in waye company nin waye? Ko yau nace a daina futar da kaya da zumar siyarwa a daina karb'ar kud'in duk Wanda ya shigo sari a bashi kyauta ko dila nawa yake so ina ganin babu damuwar kowa a cikinsu tunda babu kwabon kowa a ciki so ina ganin wannan taron da aka hada shi an hada sh domin a bata maka lokaci Yallab'ai kai da kake aiki a gabanka."Ya k'arashe maganar sa yana zakud'a kafad'a kamar ba a gaban governor yake ba. Zufa ce kawai take karyo wa daga jikinsu dukaninsu sunyi mutukar mamakin jin abunda ya futo daga bakin k'aramin yaro Wanda wasu daga cikinsu ma sun haife shi, wani dattijo me suna Alhaji d'an Akushi ya mik'e tsaye a zafafe! Ya daki tebur ya kalli Ajamd tare da nuna shi da ya tsa yace." Baka isa ba Wallahi domin tunda ka bude wannan company naka shikkenan kasuwancinmu  ya rushe ko mun futa waje mun d'auko kaya to babu wani k'aramin Dan kasuwa da zai zo ya Sara sai dai ya barmu da abun mu saboda haka baka isa ba, muna kiranka da babbar murya ka je ka rushe wancan mutsiyacin company naka domin tun baka San kanka ba muka san meye kasuwanci babu abunda zaka nuna mana." Alhaji Dan Akushi ya kare maganar sa kumfa na futa daga bakinsa .  
Me girma governor ya kalli Amjad yace." Kaji kan maganar Young suna tuhumar ka da dakushe musu harkar kasuwancin su, da kayi wannan shine maganar maslaha muke nema."
Amjad ya dago ransa ya soma b'aci ya kalli governor ido da ido yace." Yallab'ai INA ce kaji abunda nace ko ina nan kan bakana gurin ganin na taimakawa na kasa dani."
Cike da b'acin rai Alhaji Hashimu me citta ya mike tsaye baki na kumfa yace." To kuwa ka kwana da sanin zamu sa a kone company domin bashi da wani amfani a gurin mu." Wani malalacin kallo yake masa yana miskilin murmushi cike da son cusa haushi yace." So what don kunsa an kone company *Amjadu Abul Abbas* nasan dai ni baku Isa Ku kona ni ba, kuma ko yau Ku ka kone company na to ina me tabbatar mu da cewar ko kwana baza'ayi ba zan fara aikin bude wani sanin kanku ne ni kudi ba matsalata bace."
Sai ince kusan a tare suka mike suna caccakar sa gami da nunashi da Dan ya tsa har da masu son su tsune masa ido zaginsa kawai suke gami fa cin alwashi a kansa.
 Governor da yaga abun yana so ya shige gona da iri sai ya tsawatar amma duk da waha wasu basu bari ba sai da suka gama fad'ar abunda yake bakinsu sannan suka koma suka zauna suna huci!! Yana zaune yana kallonsu fuskarsa d'auke da kwantaccan murmushi, da alama abunda sukayi din bai dame shi ba, shiyasa dukaninsu yake musu kallon mahaukata wadanda basu San me suke ba kuma masu son Kansu da iyalinsu. Hakan da yayi musu ya mutukar tun zura zucuyarsu sun so ya tanka musu su ci masa mutum ci sosai sai yayi aiki da iliminsa ya kyalesu a matsayinsa na me k'ananun shekaru akan su sai ya dauki girman kawai, shi kanshi governor yasan shi yake da gaskiya, tun farko da suka kai masa maganar to amma don kar suce ya goyi bayansa yasa ya amunce da zuwa taron gashi sun zo suna hauka.
Yace."Young ina ganin abu d'aya zamuyi Wanda zai kawo maslaha a tsakaninmu." Duk sukayi shiru suna sauraron sa me girma governor ya cigaba da cewa." Zaka k'ara farashin kayanka akan yanda ka sauke a da sukayi raga-raga Wanda hakan yasa sauran 'yan kasuwa kasuwar su ta tsaya saboda duk wani me Neman sauk'i sai ya gudu company ka domin ya d'auko kaya ina Neman wannan alfarmar a gurin ka ka d'aga 'yan ?uwanka kafa suma su samu nasu kason." A lalace *Amjad* yake kallon me girma governor ranshi in yayi dubu ya b'aci a matsayinsa na shugaban aluma talaka da me kudi har wani da bashi da mukami a gomnati ya iya sadaukar da kudunshi duk dan a kan talaka yaji dad'i amma shi yana maganar ya tsawwala farashin kayansa domun a kuntatawa talaka abunda bazai yi wu bane. Da karsashi yace." Yallab'ai wannan magana da kake fada Sam baza ta samu ba ka sanja wata domin ni nan daka ganni dukiya ta ta talakawa ce so ina ganin babu Wanda zai nuna min ga yanda zanyi da ita." Sosai sukayi mamakin abunda ya fadawa governor shi kansa yayi mamaki lallai yaron yana da tsaurin ido a matsayinsa na shugaba yace ga abunda za'ayi amma yace bazai yi ba ran governor ya mutukar b'aci sosai da sosai. Alhaji Hashimu me citta yace." Ranka ya Dade kaga kaima ya nuna maka halinsa ko ai da ni na tun yau ba nasan yaron nan DOMIN tun ubanshi na yawon haya da bin kasuwanni karb'o kaya nasan bashi da mutumci ubanshi Abbas mugun Dan taurin bashi ne a wancan lokacin kafin 6a mutu da k'yar na samu ya biya ni kud'ina duk da haka da wasu a kansa ya tafi kuma baya fe masa zanyi ba, Alhaji Sunasi me leshi yace." Gashi ya mutu ya bar baya da kura  zakuwa mu dauki mataki." Kafin ya k'arasa *Amjad* ya mike tsaye a zafafe! Ya daki k'aton tebur din dake tsakiyar su robobin ruwa da Lemo suka dinga tsalle suna fadowa kasa, muryarsa a sama! Alhaji Hashime kake kome ? To ka kiyaye ni wallahi bani da kyau, na fuskanci kai baka san ka girma ba idan baka sani ba ina so in sanar da Kai ku in kara tuna maka kana magana ne da *Amjadu d'an Asali Amjadu Dan Abul Abbas* ko a wannacan lokacin da muka gwabza da kai ba samu riba ballanta na yanzu saboda haka ina kasanar daku dukkaninku Ku rike girmanku kar Wanda ya shigo gonata zamu sanya k'afar wando guda dashi.!!! Yana gama maganar shi ya d'ibi wayoyinsa ya fuce, da zafin zuciya tafiyar da yake tamkar zai dasa tayal din gurin.
Tsit!!!!!! Gurin yayi kowa yana mamaki abunda Amjadu ya aikata tabbas yaron ya cika tak'adiri kuma mara tsoro. Me girma governor ya sauke ajiyar zuciya ransa a bace yace." Yaron nan bashi da kunya ko kad'an kuma dole gomnati ta dauki mataki a kansa za mu nuna masa mulki da izzarsa zai da k'arfin mulki zamu nuna masa shi ba kowa bane tun fmda har yak'i ya bamu hadin kai mun zauna domin a samu sulotion mu samu mafita ya karya doka ya nuna ma bashi da lokacin mu to duk Ku kwantar da hankalin Ku zaku ga abunda gomnati zata aiwatar akansa." Dukaninsu fara mik'a godiyarsu ga governor, ya rufe taro da addu'a kowa ya watse zuciyoyi babu dad'i!!
*****
Yana kwance ya bayan mota da karan sigari a hannunsa ya kusa shanye kwali guda kana kallonsa kasan ransa ya bace yake saboda yadda jijiyar kansa tayi rad'ad'a busa sigari kawai yake yana shawarwari a zuciyarsa ta yanda zai bulluwa magautansa, Ciki da ladabi Doh-doh yace." Sir ina muka nufa."? Shuru yayi masa sai da ya kara maimaitawa sannan yace." Gyad'igyad'i gidan Granny". Rambow yace" Sir yau ka tuna da ita kenan."? Shiru yayi masa kawai ya lumshe idonsa.
Suna shiga get din gidan masu gadi gami da masu aiki suka dinga zuwa suna kawo gaisuwarsu ya futo daga mota a tsanake ya na amsa musu ya wuce ciki gidan cikin kakkarfan takunsa.
Wata lafiyayyir dattijuwa na gani zaune a wani kayattacan falo da ya gaji da haduwa komai na more rayuwa akwai kwata-kwata farlon baiyi kama dana tsohuwa ba tana zaune cikin kujera me cin mutum guda sanye take da Riga da zani na atamfa ammata dinki irin na tsoffafi  idanunta sakaye da farin glashi na kara k'arfin gani carbi na gani a hannunta tana ja ta zubawa tv ido tana kallon tashar sunnah tv malam jafar mahamud Adam na tambihi *Allah ya jaddada rahama a gareka malam*
Granny kenan kakar *Amjad* ta gurin ubah sunanta na asali Saratu bafulatana ce usul duk da ta tsufa amma har yanzu da hasken ta tamkar tsada k'afar nan kamar ka matsa jini yayi sartuwa, sai ince muku duk kamaninta *Amjad* ya kwaso sosai suke da kyau kamar ka sace ka gudu.
 Tana zaune ta dinga n k'amshin turaransa da sauri ta kalli kofar shigowa aikuwa shi ta gani sunkuye yana k'okarin cire takalman sa, d'auke kanta tayi da sauri ta dauki goranta ta b'antara k'asa-k'asa tace." Bazan kula ka nima tunda sai ka ga dama zaka zo gareni kallonta ta cigaba da yi kamar bata San ya shigo farlo ba, abun mamaki sai taga ya nufi inda wasu tangama-tangama hutuna suke jingine yana zuwa gurin ya tsunguna tare da sanya hannunsa yana shafa jikin hotan, gabanta ya fad'i tace." Yau a n tab'o zuciyarsa kenan." Mik'ewa tayi ta biyo bayansa shi kuma ya rungume hotonan  a k'irjinsa yana kukan zuciya wasu zafafan hawaye suka biyo kucinsa. Granny ta dafa kafadarta muryarta a tausashe tace." Tashi muje ka fada min wanene ya tab'oka dama tunda na ganka nasan akwai dalili ka aje hotan an Wanda ya mutu ya Riga ya mutu addu'a ce kawai tsakanin mu dasu." Da k'yar granny ta shawo kansa ya aje hoton a inda ya mike ta kama hannunsa suka bar gurin ni kuma da sauri na kalli hoton wasu mutane nagani mace da namiji jikin hotan da alama mata da miji ne namiji yana tsananin kama da granny macan kuwa kana ganinta kaga a salin bahaushiya domin bak'a ce amma kuma me kyau hanci har baka. Tausayi *Amjad* ya bani sosai ganin yana tsiyayar da hawaye da alama yana da alak'a da mutanan dake jikin hotan. Farlo na bisu domin  jiyo muku me suke tattaunawa.
*Wanene Amjadu?*
Zamu had'u daku a pege na gaba.
*18/October/2009*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA. 
*21*
 Abul Abbas mutumin Chadi ne inda nema ya kawo shi garin Kano bayan rasuwar mahaifinsa sai ya d'auko mahaifiyar sa, Saratu sukayi kaura daga mahaifarsu suka dawo Kano gaba d'aya. Suka bar 'yan uwansu da abokanan arziki a can sai dai suna zuwa duk shekara su duba su, tunda Abbas ya dura a garin na Kano bai zauna ba duk wata kasuwa da ta shahara a garin yana shigarta ya nemi kudi a cikinta yayi Hulda da mutane sosai da sosai hakanan kuma ya karb'i kayayyakin mutane ya juya har Allah ya sa ya samu nasa jarin inda ya kafa tebur a bakin titi kafin kashiga ai nihin kasuwar. Babu laifi yana samun kudi sosai saboda duk Wanda ya kwana ya tashi cikin garin Kano ya San da zaman kasuwar k'wari yara da manya kasuwa CE me albarka da d'umbun tarihi cikin ikon Allah ya siyi gida maidaidaci can rijiyar zaki sai suka tashi daga hayar da ya kama musu. Nan mahaifiyar sa ta matsanta masa da dole yayi aure, lokacin Neman kudinsa ne kawai a gabansa yace kawai ta nema masa mata,aikuwa batayi sanya ba ta nema masa  Aishatu 'yar kusa da d'akinta dake gidan da suke hayar basu kadai bane, Aisha yarinya kntsatsaya me hankali gami da ilimin addini, nan take iyayenta suka yadda, to shima Abbas da mahaifiyar sa ta fada masa bai musa ba domin dama yana yaba kamala da nutsuwar yarinyar, lokaci guda aka sanya rana Abbas ya hada lefe abunka da Dan kasuwa komai yayi na bajinta lokacin buki yayi akayi cikin aminci da yardar juna amarya ta tare gidan mijinta dake rijiyar zaki. Daki da rumfa manya sai k'aton tsakar gida,dakin Inna na gefe guda can wajan kofar futa.rayuwa suke ta fahimtar juna dake Inna bata da sa' ido kan suruki  shiyasa suke zaune lafiya cikin ikon Allah Aisha ta samu ciki, to tundga samuwar cikin nan arziki yayi musu sallama Abbas ya bude k'aton shago can cikin kasuwa ya fara harkokinsa da manyan yan kasuwa,  makotansa na kasuwa cikinsu akwai Alhaji Hashimu mai citta sai Alhaji d'an Akushi, sai suka Dora masa ido sosai da sosai kyashi gami da haddasa duk suka dame su gashi dai suma suna ciniki suna samun rabonsu amma sun d'ora ido kan abunda Abbas yake samu a cewar su shi na Dan gari ba yazo yana cin albarkar gari.nan suka farayi yi masa bita da k'ulli,hakan da suke sai ya zame masa alkairi domin kofofin samun sa ne suka kara budewa, *Dama Annabi ya fada cewa a yayin da kake wa mutum hassada to a lokacin Ubangiji zai cigaba da d'aga shi a duniya idan kun faya kun ta sauka a kan bawa to babu wani mahalukin da ya Isa yace ba haka ba Allah ta tsare mu da ciwon hassada domin babban bala'ine*
 Lokacin da Aisha ta haifi *Amjadu* sai da talakawa sukayi farin ciki dama lokacin cikin azimi ne dab da sallah Abbas ya sauke farashin kaya ko na ko wane shagunan shi a lokacin sun kai bakwai cikin kasuwar k'wari uku na takalma ne uku na kayan sawa daya na mayafai ne, haka ya dinga bonanza mutane suka dinga zuwa suna siyarwa iyalinsu kaya DOMIN suyi bukin sallah, sosai WANNAN abu da Abbas yayi ya dugun zuma rayukan 'yan kasuwa bari ma su Alhaji. Hashimu take suka fara shirya masa sharri Wanda suke so ya tattara ya bar k'asar gaba daya ya koma tasu k'asar.
*Amjad* yaro kyakyawa bafulatani usual tun yana yaro yake da miskilanci gami da rashin son magana, kakar shi tayi ta tsokanar shi da suna k'ato uban 'yan muskilanci lokacin yayi ta jin haushinta ko d'akinta baya shiga ita kuwa ba ta fasa kiransa da k'ato uban 'yan musklaci dake *Amjad* irin masu GAF!GAF din jiki ne yayi mutukar saurin girma sosai shekararsa shida sai kace shekara goma saboda girma ga Abu yanayi irin na manya a lokacin Alhaji Abbas ya gina gida k'aton gaske cikin *Jambulo* suka koma da iyalinsa lokacin arzkinsa ya kai ya kawo duk sati biyu suka zuwa umara shi da iyalinsa aikin hajji kuwa baya wuce su KUMA duk shekara yana d'iban mutane goma cikin 'yan uwa da abokan arziki ya biya musu su sauke farali. *Amjad* tun yana yaro yake da zuciya kwata-kwata ba ayi masa Abu ya k'yale sai ya rama babu ruwan shi da shiga sabgar da bata shi ba, in ya ga dama ko Maman shi baya yiwa magana sai ya ga dama hakama a skull ba kowa yake kulawa ba Sam bai yarda da abokai ba, yawanci ma abokan shi mata ne Wanda sune suke nace masa gami da zuwa inda yake wai ya duba musu jarrabawa dake akwai brain sosai nan zai karb'a ya nuna musu inda basu gane ba.
 *****
Alhaji Hashimu me citta sai da ya san yadda yayi ya jone harkar kasuwanci sa dana Alhaji Abbas domin ya cimma wata manufa tashi, Sam Alhaji Abbas be san da wani kudiri a zuciyar mai citta ba kacokan ya mik'a masa yardarsa tare da amuncewar sa suka cigaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci, kamar babu wani k'ulli a zuciyar me citta.
*Amjad* na kammala scondry skull ya wuce London ya fara karatu kan harkokin kasuwanci ra'ayin sa ne haka kuma ra'ayin mahaifinsa yana mutukar so yaga ya gaji mahaifinsa kan sanar shi to shima Alhaji Abbas din nashi b'angaran haka yake. Lokacin *Amjadu* na da shekara ashirin da  hudu inda yayi wani irin girma tsayi da fadin k'irji gami da kuzari sai kace wani Dan shekara talatin tunda ya fara zama saurayi yake da akidar turawa dakin shi duk dics din mawak'a ne na kallo dana ji ko da yaushe kunnen shi mak'ale da airphone yana jin music *Amjad* yana sauraren wak'okin tsohowan mawak'in nan bom marly da macaal Jackson 2pac Sisqo Joy BIG da sauransu. Cikin mawak'a mata kuma yana sauraron wakokin Cilen dion Janeepar Burandi Tony  da dai sauransu, gashi dai bai zo a zamaninsu ba amma yana bala'in