Showing 54001 words to 57000 words out of 67868 words

Chapter 19 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15512

da idonsa yana lumshe min su. Suma ne kawai banyi ba a gurin tsigar jikina ta mike sha'awar shi ta yunk'oro min sosai, nima sai naji ina sha'awar abun. Nasihar Umma na tuna hankalina ya tashi sosai nace." Ni ba 'yar iska bace au!! Yanzu nagane nufin ka shiyasa kace dole sai kayi min siyyaya wato badan Allah bane ko? To ko ka bude min mota ko in Tara maka jama'a a gurin nan, nan dai unguwar mu CE,wallahi yanzu zansan ya a fasa maka gilashin mota a raka da dutse." Na k'arashe maganar cikin tsiwa tare da girgiza jiki cikin sigar rashin mutumci.

B'ata fuska yayi had'e da gyara zaman sa sosai cikin motar yace." Duk abunda kika fada zaki iya yi iya zama na dake na fuskanci halayyar ki, tab'e baki yayi yayi k'asa da muryarsa had'e da fadin " nima da wasa nake miki me zan ji a wannan bakin naki me cike da tsiwa da rashin mutumci." Nace." Oho! Dai Dan dai baka samu bane." A d'age yace." Ko na samu bana so a kai kasuwa dama dan naga kamar kina so ne yasa na fadin haka, kanki kika cuta." Yanda ya fad'i maganar yasa na fahimci nade tabar kunya yake da hauka, ganin yak'i yarda mu hada ido dashi nace." Ni dai bude min kofa na futa."! Handbag d'ina ya d'auka dake kan cinya ta ya bude lalube yake min cikin jakar babu ko kwabo sai cingum dina da wayata da kwanata biyu babu chaji saboda matsalar NEPA..... Wayar ya d'auka yana dubawa fuskarsa d'auke da murmushi ko name ye oho!! Yace." Wannan matacciyar wayar meye amfanin ta a gurin ki."? Kaina na sunkuyar kasa cike da kunya da taikaci wannam guy dan tonan asiri ne, ko ina ruwansa da wayata oho!!! Yace." Magana nake mata masu daraja." Ba tare da na kalle shi ba nace." Wayata tana da amfani a gurina tunda ana kirana kuma nima ina kira da ita babu ruwanka da ita..... Kai tsaye yace." Yar da ita zanyi kawai domin bata da amfani gashinan a kashe babu chaji!! K'okarin cillata waje yake ta window motar, cikin azama! Na rike hannunsa ina fadin kar ka jefar mun da waya domin tana yi min rana..." Muje in siya miki wata." Yafad'a bayan ya jefar da wayar waje, cikin tsantsar takaici nace." Kai duk fa inda kasa gaba na sani wallahi duk wayon ka wato kwadayin waya yasa na bika ka kaini gidan ka kayi iskanci dani to na gane."!!! Kallonta yake cike da nazari wato ita tana zargin zai kaita gidansa da wata munufa Wanda shi kuma har ga Allah ba haka bane a zuciyarsa yayi niyyar siya mata wayar. Gyada kansa yayi yace." Ko yanzu ina da damar da zanyi duk abunda nake so dake a cikin motar nan, na k'yaleni ne kawai saboda son raina lukatan baya na samu dama akanki sosai bai sa na keta miki mutumci ba, so ki cire wannan maganar daga ranki duk sanda kika kara zagina da haka ranar zan baki mamaki wallahi, har sai na Kai ki gidana zai yi iskanci da ke, gaki a gabana baki karfina ba, ke kanki nafi ki sanin wacece ke. Kike min wannan maganar bazan. "
Yanda ya kausasa harshe yake magana yasa na soma yin sanyi, zumb'ura bakina nayi had'e da cewa"Ni duk ba wannan nagaji da zaman motar nan ka salla me ni." Ina kallonshi ya bude wani guri a cikin motar ya futo da d'aurin kudi guda uku ya tusa min a handbag jefo min yayi cinya ta tare da fadin " kika kuskura kika watsar min da kudi cikin motar nan sai ranki ya b'aci! Yana gama maganar sa ya bude murfin motar... Futowa nayi ba tare da nace mishi komai ba, wayata na fara k'okarin hadawa batir yayi nasa guri haka ma layi ka na.


Sai da suka futo da kayan tsaf! Suka jibge min su gaba suka shiga motar da sauri suka bar gurin... Yara na fara kira da gudu suka nufo ni na basu umarnin d'aukar min kayan muka tsallaka titi tare dasu.



Aunty Hauwa da Mimi Umma na zaune a tsakar gida sun baza kaya suna dubawa suna hirata ko ina na tsaya oho!! Sai sukaji sallama ta, dukaninsu suka dinga bin yaran dake sauke kaya da kallo cike da mamaki na salami yaran." Aunty Hauwa tace." Wato Dan ubanki nitsa kikayi ciki kika barmu da wahala muna Neman ki." Nace." Aunty Hauwa wace irin nitsa kuma ni da kuka barni a waje,, nayi neman duniya ban gan Ku ba."

Jawo kan ta farayi tana sambato! Cike da mamaki ta d'ago kai tana kallona had'e da fadin "Yana ga ledar Muddansi&Brots kuma." Shiru nayi. Take ta fara zazzage kayan suna dubawa cike da mamaki.


Umma tace." Asma'u duk a gurin kika samu wannan kayan, naga duk sabbi ne babu inda ya b'aci." Nace" A'a Umma me gurin ne ya siya mun su
Da sauri autn Haa tace." Kamar yaya me gurin? Kuna nufin *Amjadu*? D'aga kaina nayi cike da tsarguwa Mimi tayi saurin kallona jin abunda nace. Aunt Tace." Baki da hankali a ina zaki ganshi har ya siya miki wannan kayan.". Nace." Wallahi shine ya siya min, ya ganni a waje cikin rana mutane na turmutsutsu shine yace." Na shiga mota muje a siya min yaga ina bukatar suttura,shine fa mukaje muddanssr&brothers na sharada yace in zab'i duk abunda nake so, ni ko na duba mana anko mu." Kallona suke tunda na fara maganar sun kasa cewa komai. Nace " kunga ma kud'in da ya bani." Zazzage jakar nayi kud'in suka fado kasa, da sauri aunt ta d'auka tana zare ido, lissafawa ta fara yi duk dauri d'aya dubu Hamsin ne, dubu dari kenan. Umma tace." Zan ci ubanki Asma'u ki fada min gaskiya ko budurcin ki kika siyar gama naga take-taken ki kwana biyunan ,ni Sam ban yarda da cewa wannan yaron ne ya baki kudi nan ba, na fi tunanin yawon ki ki ka tafi." Kuka na fashe dashi sosai INA rantse wa da girman Allah, aunt Hauwa tace." Gaskiya nima nayi mamaki Asma'u ta yaya har zaku had'u da mutum irin wannan yayi miki siyayya akwai dai abunda kika b'oye." Kallonta nayi ina goge hawaye nace." Aunt kema abunda zaki ce kenan."? Tace" eh mana nasan halin ki fa da shegiyar k'aryar tsiya dama da akwai inda kikayi niyyar zuwa shine yasa kika ki binmu ciki ko." Ina kuka nace" Allah ne shaidata wallahi ni babu wani Dan iskan namiji da na bawa kaina."


Umma ta kalli aunt ranta a bace tace" kira min Aminu a waya yazo ya fi ubanta ko ta fad'i gaskiya. " aunt ta dauko wayarta da sauri ta fara kiran numbar Aminu, da gudu na tashi na shige dakinmu ina kukan takaici.


Minti goma tsakani sai ga Yaya Aminu ya shigo nan suka Zayyane masa komai, a fusace! Ya shigo dakinmu yana fadin"futo ko na ci ubanki." Sanin muguwar zuciyarsa yasa na mike zaune harara ya watsa min yace." Muje tsakar gida ki fada min uban da ya baki dubu Dari." Ina kuka na futo duk suka zuba min ido, bulala katuwa ya dauko a daki ya tsaya a kaina yana huci, gami da fadin"Dan ubanki gidan uwarwa kike je." Shiru nayi ina kuka ya daga bulalar ya zabga min a jikina, ihu na kurma Mimi tayo kaina had'e da rungume ni tana kuka had'e da rokon Ya Aminu.Bulalar ya daga had'e da zabga mana dani da Mimi din muka rungume juna muna kuka yace." Ni ubanku zan ci munafukai kawai bakinku daya Ashe ? Wato talaucin namu har ya kai kuje gurin samari Ku rokesu kudi ko? Ina ce jiya nace zan baku kud'in Atamapar ko zaki fada min ko sai na karya ki."!!!! Ya k'arashe maganar had'e da sake shimfid'a mana bulalar a fatar jikinmu.......Cikin kuka nace." Ya Isa!! Haka nace ya isa haka ka daina dukanmu alhalin bamu aikata abunda ake zargimu dashi, idan ni baku yarda dani ba to ita Mimi meye laifin ta, da zaka dinga dukanta."!!!!! Hannu ya kawo ya buge min bakina yace." Zagina zakiyi ne Dan ubanki. " da k'arfi nace." Ni ba zagin ka zanyi ba gaskiya ce na fada maka, idan baku yarda ba, Ku tashi muje gidansa tunda dai ba b'oyayye bane sai Ku tambayshiiiii.". Yace" ai ko baki fada sai munje dama ai an ce mane min mata ne, koma dai meye zai fada mana, talauci si ba hauka bane"!! Ya karasa maganar had'e da jefar da bulalar yana kuka. Ni da Mimi muka rungume juna muna kuka.


Umma tace" Maza tattare kayan da ta shigo dasu ki mai dasu ledar su had'e da kud'in bayan sallahr magariba sai kuje har inda yake muji, nifa nafi zarginta ita Asma'un karya kawai take masa domin zuciya tana bani yaron bazai aikata wani aikin assha ba." Cikin zuciyata nace" Umma domin ba ki San waye *Amjadu* bane yanzu da yaya na kwaci kaina daga hannunsa.

Mik'ewa nayi na shige dakinmu Mimi ta biyo ni a baya muka zauna kan katifa muna sauke a jiyar zuciya Minti biyar a tsakani tace." Asma'u wai da gaske kike guy nan ne yayi miki siyyaya"? Nace" Mimi kin San dai ni kaifi daya ce, wallahi duk abunda na fadawa su Umma hakane, babu karya. Tace" kuma babu abunda yayi miki." ? Kallonta nayi nace." Kema zargin da zakiyi min kenan." Girgiza kai tayi nace" To Allah dai guda ne, in kin yarda dashi wallahi babu abunda ya shiga tsakanina dashi." Shiru mukayi ta mike had'e da fadin Bari in dauko miki abunci naga kamar kina jin yunwa."

Mimi da kin barshi kawai ni bakin ciki ma bazai barni inci abunci ba duk akwai yunwa a tattare dani." Wuce wa tayi ba tare da ce komai ba, minti biyu ta shigo dakin hannunta da plate da shinkafa da wake a ciki gami da salak da tumaturi, duk da abuncin da nake mutukar so ne, amma naji ko sha'awar sa ban yi ba, ta aje min ta futa ta d'ebo mun ruwa ta aje min. Nace"Mimi nagode K'warai Allah ya kara zumunci." Shiru tayi kawai ta tsura min ido tace
" ki sako ki ci." Domin kar in watsa mata kasa a ido yasa na sako na fara cin abuncin ba Dan dad'i ba.
[10/29, 9:51 A ********


Kai tsaye ba su wuce ko ina ba sai gidan granny, tunda al'amarin ya faru bai je ba yau kwana biyu kenan, mai gadi ya bude get din yana mik'a gaisuwarsa ga Amjadu ya amsa ta hanyar daga masa hannu. Motar ta shige ciki gami da samun gurin tayi parking, Rambow ya futo da sauri ya bude masa motar ya futo da sauri ya karb'i wayoyinsa hannunsa ya shige ciki suka rufa masa baya. Tsayuwa sukayi bakin kofar palo shi kuma ya shiga bakinsa d'auke da sallama, tana zaune kan kujera hannunta rike da carbi kana ganinta kasan tana cikin damuwa dattiijuwa me sanin ya kamata kenan. Tana ganinsa ta sauke ajiyar zuciya had'e da sakin fuska tace." Ashe kana tafe."? Da sauri ya k'arasa kusa da ita yw zauna had'e da Dora kansa kafadar ta, wani irin tausayi tsohuwar yake ji


Kanshi ta shafa muryar ta na rawa tace." K'ato haka Abu ya faru ko." Girgiza kansa yayi dake kafadar ta yace." Waye k'ato kuma."? Kanshi ta rank'wasa tace" ga kanan a gabana." Gyara zama yayi yana Dan bata fuskarsa yace." Bana son sunan fa." Murmushi tayi tace." Yanzu na fara fada ni kuma." Shiru yayi mata. Minti biyu tsakani tace." Amma mutanan sun cika azzalimai, wallahi tunda nake ban taba ganin mutum maciyin amana ba irin Alhaji Hashimu. Nasan da hadin bakinsa komai ya faru."


Girgiza kanshi yayi cike da b'acin rai yace." Granny ni nafi zargin me girma governor domin dashi mukayi sa'insa a ranar." Tace." Koma dai waye ka barshi da Allah da sannu zai saka maka."


Murmushi me ciwo yayi yace." Dole ne Granny Allah ba abun wasa bane amma zan basu mamaki wallahi nafi su k'ananun shekaru nafi su kuma dabaru sosai governor sai ya gagara futowa wani taro domin sai jama'ar gari sun jefe shi tunda ya nuna kansa a gurin su."


Granny tace." Ai naji a redio sai zaginsa akeyi Allah dai ya kyaua wasu masu mulkin su dauki alk'awari su kasa cikawa su Da Wanda ya hallice su."

Shiru yayi yana girgiza kansa, ta mike a nutse ta nufi kicin da kanta minti biyar tsakani ta dawo hannunta rike da k'aramin tire jere da kayan abunci. Zama tayi tana k'okarin zuba masa, ya bata fuskarsa, tace." Kome zakayi sai kaci abunci ayi mutum yayi ta rayuwa babu cikkaken abunci sai yame-yame." B'ata fuska yayi yace." Si kece komai naki sai kin sanya masa daddawa yayi ta wari."


Hararasa tayi tace" karya kake ba komai nake saka mishi daddawa ba. Kallon plate din yayi yaga wata lafiyayyir wainar shinkafa fara tas da ita, wani kwano me kyau ta bud'e farfesun kayan ciki ne sai kamshi yake yaji kayan kamshi tace." Nasan dai wannan zai yi maka dad'i ko." Murmushi yayi yace." Nagode granny gaskiya kina ji dani sosai, zanci wannan delicious din naki yayi min kyau a ido Allah yasa yayi min dad'i a baki." Duka ta kai masa yasa dariya, hannunsa ya nan nade ya dauki Fork ya fara cin abunci zuciyarsa a sake duk damuwar da yake ciki mutukar yazo gurin kakarshi yana Neman kashi Hamsin ya ras.


Yana cin abuncin tana kara tausar zuciyarsa gami da nasiha na cewar kar ya dauki fansa akan duk Wanda yayi masa haka ya barshi kawai da Allah zai saka masa cikin kan kanin lokaci.

Robar ruwa ya d'auka ya bude ya kafa kanshi Yana sha Sam bai tsaya tsiyayawa a cup ba, sai da ya kusa sanye rabinsa ya aje robar ya aje Fork din had'e da jin gina jikinsa jikin kujera yana lumshe idonsa, shi kadai yasan tunanin da yake. Ta kalle shi had'e da fadin kaga da kana da aure sai kawai ka mik'e matarka tayi maka tausa yanzu ko sai dai ka zare ido." Bude idonshi yayi yana Dan kallonta tace" K'warai kuwa ai gaskiya na fada" zama gyara yana fuskantar ta sosai yace." Kina son inyi aure ne."? Tace" sosai ma kuwa ai ka kai munzali Dan baka da auran ne ma yasa wasu suke samun dama akan ka, kasan shi aure yana karawa mutum Martaba. "


Yace." Nifa ko budurwa bani da ita Granny." Da sauri tace." Ai me sauk'i ne wannan ni idan ka yarda sai in nemo maka matar aure." Murmushi yayi yana Sosa kanshi yace.' A'ina"? Gyara zama tayi cike da murna tace. " ko d'azu mun Dade da Innah ka Suwaiba tazo yi maka jaje shine muka yanke shawarar kaje ka nemi auran Hafsa yarinyar da ka gani ranan a gidan nan."


Bude idonsa yayi sosai yana kallonta Yace." Granny nine zanje in nemi ta ko ita ce zata zo."? Tace." Ka tab'a ganin inda mace tazo Neman aure K'ato." ? Sosa kansa yayi yace." Um!Um kawai ki bar wannan maganar Sam! Yarinyar batai min ba, inan zan kawo miki budurwa ta ki ganta." bata fuska tayi tace"Ai ka saba fad'ar haka, ni dai nace Hafsa nake so ka aura saboda na Yaba da halayen ta."


Kallonta yayi cike da mamaki yace." Granny ni ba tayi min ba in kuma kina so na maida musu da yarinya k'aramar bazawara shikkenan." Jin abunda ya fada ne yasa granny dawo wa nutsuwar ta tace" shikkenan ai yaushe zaka kawo min budurawar taka." Yace." Kar ki damu zan kawo miki ita da ko wane lokaci."



********

Muna idar da sallahr magariba aunty hauwa ta shigo dakin namu tace." Sai Ku futo mu tafi ai naga alama bakin Ku d'aya. " hibaj dina na d'azu na zura fuskata kojale kojale muka futo duk nayi wani zuru-zuru dani. Yaya Aminu na tsaye a bakin kofar futa sai zare ido yake kamar wani dogari , harara ya bimu dashi muka futa simi-simi.... Suka biyo bayanmu bayan sun yiwa Umma sallama.


A dai-dai muka samu muka shiga aunt ta kalli Aminu tare da fadin " yanzu kwatancan gidan zamu nema." Yace." Ai gidansa ba b'oyayye bane a jambolo baza mu sha wahala ba." Su kadai suke hirarsu munyi shiru. Sai da muka zo second get muka sauka muka tsallaka titi da kafa muka fara tafiya, har muka Isa Estate din da muka gani a kulle ga wasu iyayen karnuka a ciki a kwankwance masu tsarin gurin suna zazzaune a gurin zaman su da, ya tsayawa mukayi jikin get din muna shawarwarin yadda za'ayi.












*29/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*




*34*




Yaya Aminu ne yake d'agawa masu dadin hannu. Daya daga cikinsu ya taso da sauri yana zare ido! Hannu Ya Aminu ya mik'a masa yak'i karb'a, fuska a had'e yace." Gurin wa kuka zo."? Shi kansa Aminu a lokacin daburce wa yayi kafin yace." Gurin *Amjadu Young millionaire*" wani irin kallo me gadin yayi masa yace." Bayin Allah yanzu duk irin kyauta da bawan Allah nan yake muku bai muka ba sai kun biyo shi har gidansa." Ya Aminu yace." Ba abunda kake tunani bane ya kawo mu, wata Matsalar CE,idan da hali muna so ka sada mu dashi." Cike da nazari me gadin yake binmu da kallo kafin yace." Bai shigo gida ba." Shiru mukayi dukaninmu. Me gadi ya koma gurin zaman sa yana fadawa 'yan uwa tare da nuno mu da hannunsa suna dariya. Duk sai naji na kaskanta Ashe haka Ya Aminu ya juyo gare ni a zafafe kamar zai kurma min mari yace." Kin kyauta Asma'u kinga wulakacin da kika jawo mana ko." ?
Kasa nayi da kaina cike da tsoro domin kar ya dake ni.aunt tace." Yanzu meye abinyi." Ranshi a bace yace." Tafiya zamuyi domin tsayuwarmu a gurin bata da amfani domin bamu San sanda zai dawo ba."

Hon! Mukaji da k'arfi dukaninmu muka juya da sauri! Gabana ya fad'i ganin motarsa, Aunt tace."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login