Showing 66001 words to 67868 words out of 67868 words
 haka  ni baka da iko dani da duk wani abunda ya shafe ni."
Murmushi yayi hade da shafa fuskarsa as'usuel yace." Karya kike ko yanzu na gada zanyi iko da abunki kuma babu yanda zakiyi dani, wallahi kuma na kara ganin kina rigima a kan titi sai ranki yayi mugun b'aci sai na miki horo me tsanani, kullum kina kiran kanki mace me daraja amma kin kasa hankali kina shashanci, rigima da 'yan iska  ki kiyaye wallahi."!!! Yafad'a. Da murya a kausashe.
Mamaki yaba ni sosai nace "To kai meye damuwar ka meyasa da ka ganmu bakayi tafiyarka ba, duk abunda nayi rayuwa ta ce."!!! Na fada haka cikin tsiwa da sigar bada haushi.
 A zafafe! Ya juyo dani muna fuskantar juna, fuskar sa a hade yace." Ina magana kina girgiza jiki don baki da kunya, wa ya fad'a miki saboda ke na tsaya a gurin? K'ifk'ifta ido nake tsoro ya fara shiga ta ganin yanda yake wani muzurai duk wannan fara'ar babu ita a fuskarsa.
Ya cigaba da cewa"Saboda Mimi na tsaya na lura yarinyar kamila ce ita yafi kamata ta kira kanta mace me daraja bake ba, tunda duk ganin da zanyi muku bata tab'a aikata mummunan abu ba, ke kuwa fa.? Yafad'a yana zare min ido! Kasa nayi da nawa cike da tsoro! Girgiza kafad'a ta yayi da k'arfi yace." Ki bani amsa mana".? Shuru babu magana. Yace." Mimi tafi kirki tafi ki kyau ta fiki hankali da sanin ya kamata,   Ko ba haka bane."? Shiru nayi masa bakina na rawa, tsaki! Yaja had'e da fad'in." Ko kwana uku ba ayi na 'yan uwanki suka zo nan suna tuhumar ki, kan rashin yarda saboda sun San halin ki, hakane koba haka ba ne."?
Wasu zafafan hawaye ne suka soma zubo min a fuska na fara kifta idona domin in mai dasu Sam bana son yaga gazawata. 
Sakina yayi yace." Wannan ya zama na farko da k'arshe a gurin ki, wallahi wallahi kar in kara kama ki da aikata Abu makamcin haka, zan tsaurara bunkice a kanki domun nima ban yarda dake b........... Hannu na d'aga masa murya ta na rawa na mik'e tsaye cikin tsananin b'acin rai nace." Duk abunda zaka fad'a ka fad'a akaina dai-dai ne a gurin ka, ka fad'e shi son ranka, Idan iyayena sunyi zargina kai meye alak'arka dani da zaka tasa ni a gaba kana zagina had'e da fad'amin bak'ar magana, idan iskancin nakeyi Kaine ka koya min, tunda nake a rayuwata babu namijin da ya tab'a kusanta ta sai kai, me yasa na rufa maka asiri a don duniya? Meyasa na rufa maka asiri a gidanmu?! Ka sani ina da damar da zan shiga ko ina ne in b'ata maka suna me yasa ban yi ba?!! Sai kai ne zaka turke ni kana tuhumata kan abunda ban aikata shi ba. To wai ma meya shafeka dani idan a *Ibedi*  nake ina karuwanci! Babu abunda ya shafeka dani, zan dauki hakan daga makusanta na, wato iyaye na, amma bazan dauki raini da k'azafi ba daga gurin wani gardi."!!!!!! Ganin ya mik'e a zafafe! Ne yasa na ruga da gudu bakin kofar futa ina k'okarin bude wa, kulle gam!! Finciko ni yayi da hannu guda ya jefar kan kujerar a zafafe ya Fidda hannu ya gaura min mari, Wanda sai da naga wasu taurari, yana haki! Yake cewa." Ni kike fad'awa wannan maganganu ko."
Hannu na nasa na dafe kuncina zuciyata nayi min suya, tsura min ido yayi fuskarsa kamar Wanda aka aikowa da mala'ikan mutuwa yace." Ana fad'a miki meye rayuwa kina k'okarin zagin mutane, Dan kinga na damu ke shine kike wannan iskancin!? Kije ki tambayi waye. *Amjadu* a gari zasu fad'a miki, ko kuma kije ki tambayi 'yan mata irin ki, wad'anda suke da kyau da wayewa ilimi kud'i ba irin ki ba bagidajiya da ko kwalliya baki iya ba, idan kika tambaye su zasu fad'a miki wanene ni,  idan mace bata yi min ba, ko kallo ba ta ishe ni ba, duk kyawun ta da waye warta don ke kin samu wannan damar shine kike mun iskancin har da su zagi,."!!!! Hannuna na sanya ina dukan k'irjinsa da yayi min rufa dashi INA kuka nake fadin" Babu ruwana dasu tunda ba Kai ne a gabana ba, da kake maganar Mimi tafi kyau tafi ni kirki da komai, to sai me? Idan sonta kakeyi to Bari kaji wani Abu, itama sonka take sai me? Ni babu abunda zai dame ni, daku  kuma daga yau ka futa daga rayuwata in huta da jaraba! Idan haka gaskiya take to bana bukatar ta a gurin ka, duk halin da na fad'a kai ne sila."!!!!!!!! Na k'arashe maganar ina kuka wiwi! Bakin ciki kamar ya kasheni, wai ni suke zargi!! Lallai na yarda da maganar hausawa da suke cewa namiji sai yayi Abu ya zama ado a gare shi, mace ko da tayi sai duniya ta  ji ta. Yanzu dubi babu sata babu zina babu mayyata amma suna zarginta.
Kuka nake ina dukansa a k'irji hade da ya kushin sa, so nake kawai ya d'aga ni. Yak'i sai kace wani maye ya zuba min idonsa da suka yi jazur dasu. Minfi minti goma a haka sannan ya sauka daga kaina, na mik'e da sauri! Had'e da d'aukan k'ananun pillows ina jifansa dasu hade da fad'in"I hit you! I hit it."!  Kayansa ya ke sanyawa ranshi a mugun b'ace ya zama dole ya cire yarinyar nan daga ranshi domin ya lura tana da mugun taurin kan tsiya ga rashin kunya dole yayi nesa da ita da rayuwarta dama tausayin maraicin su yake ita kuma bata duba wannan. Dole ya aje ta gefe guda ya fuskanci abunda yake gabansa bata tab'a b'ata masa rai ba irin yau. Yana jinta har ilayau tana jifansa hade da surutai share ta kawai yayi ya dauki turaransa ya fesa jikinsa, dashu. Juyo wa yayi muka hada ido, gani fuskar sa nayi kamar ta zaki! Da sauri na jefar da pillow hannuna hade da zubewa kan kujarar ina shashshekar kuka.
Ba tare da yace min komai ba ya bude kofa ya futa, zumbur na mik'e nima na bi bayansa, Mimi ta mike da sauri hade da mikomin mayafina na yafa muka sauka k'asa.
Ina kallonshi shida rambow suna magana sai kuma naga Rambow ya nufi parking spece da sauri ya bude wata lafiyyayr mota yana buge ta shiga yayi ciki ya futo da ita kana ya fito daga ciki hade da bude murfin motar.
Cikin yanayin tafiyar sa ta jarumai ya k'araso gurin hade da karb'ar key din motar hannun Rambo ya shiga ya zauna mazaunin dravar, rbow ya k'araso kusa damu tare da fadin" kuje Ku shiga motar.
A zuciyata nace"Yau shi zaiyi dravin din kenan Mtssss. Baki na tab'e kawai INA d'auke kaina muka Isa gurin motar
 Mimi ta kama murfin kofar baya zata shiga yace.'"Mimi dawo nan kusa dani." A hankali ta saki murfin ta bude na gaba ta shiga ta zauna tana sink'e kai. Tsaki nayi a fili na bude na shiga. Kunna motar yayi had'e da kallonta da murmushi a fuskarsa yace." Ko kina so in zama dravar ki ne." Mimi ta sunkuyar da kanta cike da kunya tana mamakin yanda yake mata magana, cikin nutsuwa motar gidan, ta hau kan kwalta. Music na tashi kad'an-kad'an.. Sam naki dago kaina in kalle shi balle in San wane irin kaya ne a jikinsa, shiru motar kusan minti goma yace." Mimi naji wata magana gurin 'yar uwarki hakane."?  Mimi gabanta ya fad'i kaddai Asma'u ta fad'a masa, sai ta sanya mayafin ta ta rufe fuskar ta, naji kamar ina mangarta, saboda haushi tsaki naja me k'arfin gaske Wanda nasam duk sunji ni,amma abun mamaki ita dashi babu Wanda ya kulani.
K'asa-k'asa naji yace." Kinyi shiru my Mimi  hummm! Wai ya sunan ki ne na gaskiya ne."? A hankali Mimi tace." Sunana Aisha." Cike da kulawa ya kalleta yace." Mommah na ce ashe  haba shiyasa naji ina kaunar ki, kin San duk me wannan sunan tana da daraja irin sune ya kamata su kira kansu da mata masu daraja."!!! Gabana ya yanke ya fad'i. ! Babu shiri na dago kaina ina kallonsu, ni YAKE fad'awa magana kenan. Zuciya tayi min bak'ik'ikirin, haushi ya turnike ni, ganin yanda yake sakin wani murmushi yana kashe muryarsa Wanda sai na kasa kunne sosai nake jin abunda yake fad'awa Mimi.
Yace." Yaushe ne party naku."? A hankali tace." Asabar ta jibi." Gyad'a kansa yayi fuskar da a sake yace." Wane guri za'ayi."? Tace" cikin makaranta ne."  "Hakan yayi wane irin tanadi kuka yi." Mimi tace"mun gama komai ma." 
"A'a ki fadamin ko akwai taimakon da zan miki kinji ko." Mimi ta dago kanta muka had'a ido da ita ta mirror wani banza kallo na watsa mata gami da d'auke kaina, cike da mamaki ta d'auke kanta tana mamakin kallon da nayi mata. Ni kaina sai bayan nayi mata shi na dawo ina da nasa ni.
Yace." In kuna son a futa sai a ka ma muku guri ko."? Girgiza kanta tayi tare da fad'in" gidanmu baza'a bar mu ba." Murmushi yayi kawai, minti uku yace." Tom ya maganar mu dake." Mimi duk ta diririce tana kauda kanta. Dariya yasa har sai da hak'oran sa suka bayyana. Yace." Ko dai k'arya take miki ne? Ita ce ta aiko kanta. " Mimi ta girgiza kanta alamun A'a. Ji nake kamar in shako wuyan Mimi in ta dukanta ko na huce takaicina a zuciyata nace "Banza wacce ta rako mata kawai.!!!
Hira suke dashi sosai duk k'arfin hirarar shine yake yi ita dai sai Umm da umum kawai take yi, ni zaune a baya sun bawa banza a jiya ta, Allah-Allah nake mu sauka daga motar ko na samu in samu sassaucin rad'adin da zuciyata take min a game dashi.
Dai kwanar gidanmu yayi parking din motar, da sauri na bude na futo, babu Wanda ya kula ni a cikinsu, shiru-shiru Mimi bata futo ba, ga glass din motar duhu balle inga me ya tsare ta a ciki, kawai sai na tsinci kaina da k'urawa motar ido ina jin wata irin hajijiya na k'okarin ta yar dani a gurin
Duk abunda take yana kallonta, yaji mutukar dad'i ganin yanda ta tada hankalinta,sai ya nuna mata batada wayo wallahi tunda bata da kunya ita. Rike Mimi yayi da hira, Mimi kuwa ta saki jikinta suna ta hira abunka da zuciyar da ta narke a kan so. Idona ne ya fara kawo ruwa ganin kusan mintina goma Mimi bata futo ba yasa na fara k'okarin tsallaka titi nai tafiya ta duk sanda ta gama soyayyar ta tawo.
Wayarsa guda ya dauko hade da sanya mata wani sabon sim card Mimi taga ya mik'o mata dalleliyar waya k'arar Infinx yace." Ungo wannan ki sanya chaji na sanya miki sabon sim card zan dinga kiran ki muna gaisawa." Mimi taki karb'a tana sink'e kanta yace." Ashe ba so na kike ba ko."? Girgiza kanta tayi ta sanya hannu biyu ta karb'a tana godiya yace." Yawwa ko kefa." Bude mata kofar yayi da kanshi suka yi sallama.
Motar ya ja da sauri ya bar gurin.Mimi kuma ta fara Neman inda Asma'u take bata ganta ba, zuciyarta ta ayyana tabbas tayi tafiyar ta, sai ta tsallake titi cikin sauri ta nufi gida itama............
*Yanzu aka fara*