Showing 57001 words to 60000 words out of 67868 words

Chapter 20 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15504

Allah yasa shine." A hankali nace "shine ma" duk suka kalle ni cike da mamaki.

Gefe muka matsa me gadi ya bude get din motar ta silala ta shiga ciki, karninkan da suke kwance a gurin suka mike da gudu suka nufi motar, dake akwai haske ko ina a gurin muna kallon abunda yake faruwa daga waje. Ya Aminu ya kaskantar da murya yana rarrashin me gadi kan yaje ya sanar da shi tunda ya dawo.


Yace.' Da kunyi hakuri gobe Ku dawo domin nasan a gajiye ya dawo ko baku San abunda ya faru dashi bane."? Ya Aminu yace." Mun sani shiyasa ma muka zo muyi masa jaje." Me gadi ya kalli Aminu cike da mamaki minti biyu yace." Bari in fada masa." Ya Aminu yayi masa godiya ya wuce ya barmu tsaye bakin get muna hangosa ya isa gurin shi yana daf da shiga part din shi. Tsayuwa naga yayi yana kallomu, minti biyu ya nufo inda mike wannan dog din nasa da nagani farkon fara gani na dashi ya biyo bayansa, tare dasu rambow. Tun kafin ya k'araso na sunkuyar da kaina kasa.

Shi ko *Amjadu* tun kafin ya isa gurinsu ya gane ta, ko cikin mata dubu yarinyar zata shiga yana iya gane ta, ballanta guri da haske futulo dal-dal tamkar rana, mamaki yake me ya kawo ta gidan shi, kuma? Ya karasa fuskarsa babu yabo babu fallasa. Da sauri Ya Aminu ya mik'a masa hannu alamun su gaisa, ba tare da girman kai ba ya mik'a masa NASA sukayi musabaha, kamar bai sanmu ba nida Mimi haka ya nuna ya kalli aunt da Aminu a nutse yace." Ina fatan lafiya ko." Ya Aminu ya diririrce domin guy yayi masa mugun kwarjini ashe jinsa kawai yake a baki wannan shine jinka yafi ganin ka, duk taurin kai gami da dakiya irin na Aminu sai da ya risina. Ya sunkuyar da kai tare da fadin" Yallab'ai magana ce take tafe damu ina fatan babu damuwa." Ni ya kalla ina kallonsa a fakaice ya d'auke idonsa daga kaina yace." Babu matsala amma ku shigo ciki ko." Aminu yace." Godiya muke." Wuce wa yayi ciki muka bi bayansa tuni dog d'insa ya fara wani irin ihu! Yana tsalle zai cafke ni! Da gudu na matsa ina zare ido!! Wan!wan!wan!wan! Dog din kawai yake yayo kaina tare da kama bakin hijabina da yake Jan k'asa!! Ihu!! Na kurma ina k'ank'ame jikina guri guda." Cikin tsawa naji yace." Tegar"!! Stop."! Daina haushin yayi ya tsaya yana kallona. A hankali ya ja siririn tsaki ya kalli Ya Aminu tare da fad'in "wannan black din abun da ya gani a jikinta ne yasa yake tunanin ko Anjalina ce." Wato matar shi, cikin dizgi! Ya Aminu yace." Dama ya cije ta ai da mun huta da halin taurin kai. Ita b'aka ta kama ta sanya b'akin abu ba dole karnuka su biki ba." Babu abunda yace yayi gaba muka bishi a baya gabana sai bugawa yake yi na tsinewa dog din nan yafi sauri dari, shima Ya Aminu yanzu wani mugun haushin sa nake ji

Rambow ya bude masa kofa ya shiga muma muka shiga, ina kallon aunt Hauwa sai kalle-kalle take a parlor ni da Mimi dama gidan ba bakonmu bane, shi kanshi Ya Aminu zare ido kawai yake yi sai kallon parlor yake yi
Bedroom dinsa naga ya nufa, na kauda kaina zuciyata na tuna min abunda ya faru dani da shi kwana biyu da suka wuce.

Muna zaune kimanin mintuna ashirin babu Wanda yacewa da Dan uwansa uffan! Dukaninnu jiran futawar sa muke. K'amshin tura ransa ne ya tabbatar mana da ya iso, tunda na daga kaina sau daya ban sake kallonsa ba, saboda nasan na tsananta to Zan iya tonawa kaina asiri.. Yana sanye da wasu had'addun kayan shan iska black and White rigar sharara k'irjinsa a bude shi kuma wandon iya kacin sa gwiwa da alama Wanka yayi ganin yanda fuskarsa take shek'i gashin girar shi da danshin ruwa, zama yayi kan kujerar dake fuskanta ta, ya kalli Aminu a nutse yace. " na barku ko kuyi hakuri nayi Wanka ne." Ya Aminu yace." Babu komai yallaby." Yace." Ok ina jinka." Cikin daburcewa Ya Aminu ya fara magana kamar haka.

"Yallab'ai waccan yarinyar dake zaune kujerarar dake kallon ka, k'anwar mu, ce d'azu misalin k'arfe hudu bayan an idar da sallahr la'asar kenan ta shigo mana gida da kudi da kaya wai Kaine ka bata, shine hankalin mahaifiyar mu ya tashi tace bata yarda da ita ba, Dole tace azo a tambaye ka."

Sunkuyar da kaina nayi zuciyata kamar tayi bundiga wai ni ake wa wannan tozarcin humm! Lallai ya Aminu.

Ta kasan idona nake kallonshi yana Dan satar kallona, ya kalli Aminu tare da fadin" Abunda nake so na fahimta anan shine dama can yarinyar tana bin maza ne ? Ko ko kuna zargina da ita ne."? Yadda ya fad'i maganar zaka san ranshi a bace yake. Ya Aminu yayi saurin cewa"Ko daya Yallab'ai ita yarinyar muke zargi ba kai ba.". Shiru parlor yayi mintuna biyar sannan yace." Duk abunda tazo ta fada muku a gida hakane nine na siya mata kaya kuma nine na bata KUDI don ra'ayina ba don wani abu ba, saboda haka Ku daina tuhumar ta, a kan aikata alfasha, naji dad'i da samun ku iyayen jajurtattu gaskiya na yaba k'okarin Ku." Ya Aminu yayi murmushi had'e da godiya, aunty Hauwa ma sai washe baki take..Mik'ewa yayi yace." Ni zan shiga ciki Ku sauka lafiya kai idan kun futa doh-doh na tsaye a waje kace injini ya kai Ku har gida." Ya Aminu yace" godiya mukeyi" hannu kurum ya daga masa ya shige bedroom dinsa.


Jiki a sanyaye na mik'e tsaye sosai nake mamakin halin ko in kula da guy nan yake nuna mini in ya ganni cikin mutane sai ya nuna sam bai sanni ba, yanzu ma dubi yanda yake wani shan kamshi ba, tab'e bakina nayi na futa daga parlor cike da taikacin wulakamcin da yayi mana, gaba nayi kawai ina jin ya Aminu ya tsaya yana fadawa doh-doh sak'on da oganshi yace..

Aunt hauwa ta kwala mib kira nayi nisa ma ina daf da fita tace." Kizo mu shiga mota mana ko baki ji abunda aka ce ba." Ba tare da nace komai ba na dawo da baya, sai da suka gama shiga tsaf! Sannan na shiga doh-doh ya ja motar muka futa daga gidan.



*****

Tsaf Ya Aminu ya zayyanawa Umma komai tayi hamdala gami da godewa Allah, ta kalle ni tare da fadin"Allah ya cece ki wallahi." Ni dai shiru kawai nayi ina mamakin halin Ya Aminu, aunty hauwa tace." Mara mutunci gurin siyar kayan ko ki tuna dani ko Isilam baki tuna ba balle ki siya mata ko pant ne." Shan kunu nayi domi itama aunt hausshin ta nake ji.Mik'ewa nayi ba Tare da nace mata komai ba. Hararata tayi tace." Sai kije kiyi tayi ai gaskiya ce dole a fada miki..

Dakinmu na shiga na kwanta kan katifa gami da rintse idona suffar sa kawai nake tunawa lokacin da ya futo daga bed d'insa, a d'azu tsigar jina ta tashi da idona ya hasko min k'irjinsa na cije leb'ena gabana na fad'uwa da na tuno abunda yace da Ya Aminu wai yayi min siyayya ne ba don wani dalili ba kawai ra'ayin sa ne. Wannan kalma da ya fada sam ba tayi min dad'i ba.. Mimi ta shigo dakin tana buge gurin kwanciya tare da fadin "bakiyi sallah ba kinzo kin kwanta." Mik'ewa zaune nayi nace." Mimi Wanka ma nake so nayi hummm! Ai ni yau 'yan gidan nan sun bani mamaki ." Mimi tace." Wane mamaki kuma"? Cike da takaici nace" baki ga irin zargin da suke min ba Mimi."?

Murmushi tayi kawai ta cigaba da gyara shimfid'a na mike zuciyata babu dad'i na futa, ina kallon aunt Hauwa zata tafi suna sallama da Umma Ya Aminu na tsaye yana jiranta DOMIN ya raka ta hanya saboda dare ya fara yi, ko kallonsu banyi ba na dauki bokiti na cika da ruwa na shiga band'aki abuna.


Wanka nayi na futo na tsuguna bakin rijiyar na d'aura alwala, lokacin da na shiga dakinmu Mimi ta kwanta tana lumshe idonta dama ita sarkin bacci, duguwar Riga na zura na sanya sabon hijabina na tada sallah duk sai da na rama sallolina nayi addu'a sannan na mike had'e da ninke daddumar na aje ta, ba tare da na cire hijab dina ba na nufi kicin Fula's din da ake zuba mana abunci na dauko na dauko dugon jug na Debi ruwa a randa na wuce dakinmu ba tare da na kalli kofar dakin Ummamu ba.


A hankali nake cin abunci kamar me cin magani ko rabi ban ci ba na rufe Fula's din, ruwa na d'auka nasha. Jin gina kaina nayi jikin katifa INA addu'a Allah yasa nannauyan bacci ya d'auke ni domin bana so tunanin guy nan ya dame ni.. Haka kurum daga na tuna shi a ko wane hali sai gabana ya yanke ya fad'i!


Allah ya amshi addu'a ta bacci naji a idona nayi saurin hayewa katifar had'e da runtse idona kafin minti biyar bacci ya kwashe ni, me nauyin gaske!



*****

Shi kuwa Amjadu bayan tafiyar su, mamaki yake sosai yanda iyayen ta suke da kula da tsantse ni gaskiya sun burge shi sosai kuma yarinyar ta kara samun girma a cikin zuciyar sa,, kashe wayonyinsa yayi duka ya kwanta shima domin wani irin bacci yake, abunda da Wanda ya kwana ya yini a tsaye.

*Asubah ta gari Young millionaire*



******
Me girma governor hankalinsa ya kai kololuwa tashi sosai yanda jama'ar gari suke zaginsa kuma suna zargin sa, dole ne ya zauna da manya 'yan kasuwa kamar su Mai citta, hankalinsa bai kara tashi ba sai da ya saurin Maganar *Amjadu* ta yau inda 'yan jarida suke masa tambayar shin yana sha'awar shiyasa, hankalinsa ya tashi sosai da yaga jama'ar gari suna ihu tare da fadin"Muna sonka zamu Mara ka baya duk inda kake." : Lokaci kankani yaji wata irin muguwar tsanar yaro ta kara shiga zuciyarsa yana ganin da alama yaron yana da farin jinin jama'a, kuma alumma zasu yi sauya masa ra'ayin sa ya fara sha'awar siyasa Wanda yake ganin haka kamar karshen mulkinsa ne yazo gashi yana so yayi tazarce, dole nema ya sake tsaurara matai kuma zai k'irk'iri abubuwa Wanda zasu jawo hankalin allumma su dawo kansa. Da wannan shawarar ya kira Alhaji Hashimu ya fada masa cewar gobe k'arfe goma na safe ya zo gidan gwamnati zasu tattauna magana me muhimamci.



******
Ko da na tashi da safe babu Wanda na kula ita kanta Umma gaisuwa ce kawai ta shiga tsakanina da ita, na koma dakinmu na kwanta zuciyata duk babu dad'i. Mimi ta shigo dakin hannunta d'auke da jug cike da koko d'ayan hannun kuma takardar k'osai CE,ta aje tare da fadin " ki tashi mu karya duk wannan nukufurcin babu inda zai kai ki." Ganin yanda ta damu dani ne yasa na mike zaune muka fara karya wa.

Bayan mun gama tace." Ya Aminu yace." Mu dauki kud'in atampar a cikin kud'in jiya." Nace" kudina ne babu Wanda ya Isa ya tab'a min bayan sun gama ce min 'yar iska kuma zasu ci kud'in iskan ci kenan." Na karasa maganar raina w bace.!! Mimi tace" duk abunki dai ba a canzawa towo suna dole kiyi hakuri dasu,kuma ni banga laifin su." Nace" ai baza ki gani ba Mimi tunda ba ke aka yi wa ba." Mimi dai shiru tayi min ganin yanda na hayayyak'o mata da masifa.

Muryar Umma naji tana kwala min kira, amsa wa nayi na mike da sauri. Daga bakin kofa na tsaya nace" Umma gani" Sam naki kallon Ya Aminu dake tsaye yayi shirin makaranta.

Tace." Idan anjima aunt Ku zata zo sai kuje Ku siyo shaddar da atamfar ga dubu ashirin a cikin kud'in dole a fada miki tunda hakkin ki ne."
"To" kawai nace na kama hanya zan koma daki. Ya Aminu yace." Dawo Dan ubanki ba,a gama magana ba zaki tafi." Rai abace nace" nifa na tsani wannan abunda kake min haka kawai sai ka dinga yi min tsawa kana hantara haka jiya a gaban mutane ka tsinkani ni gaskiya ka daina min irin haka bana so."Hannu ya kawo zai dake ni na kauce da sauri ina zumb'ura baki! Yace." Idan na kara me zaki min? kaji min Mara kunyar yarinya ko." Umma tace"kai tsiyata da kai saurin duka ka daina don Allah." Yace" Umma wannan yarinyar ai duka ne maganin ta." Nace"wallahi Umma baga yanda jiya ya dinga min masifa ba a gaban mutumin nan. " Umma tace." To ke meye damuwar ki.? Shiru nayi kawai. Ya Aminu ya wuce Yana mata sallama ita kuma sai fatan alkairi take masa, kallona tayi tace" kuyi sauri Ku gama aikin Ku kafin tazo domin kun santa da azazzala." Nace" toum Umma" Mimi na kwalawa kira ta futo muka fara aikin gida.

********

Yana zaune a gefen bed jikinsa daure da wani faffad'an towol da alama daga Wanka ya futo Loptop dinsa ce a cinyar sa, suna magana da babban abokin shi Anthony dake can Chana. Dama duk yana da labarin abunda ya faru da abokin nasa shine suke shawarwarin abunda za'ayi.Anthony yace." Company uku ya kamata a bude Wanda zai dinga kawo ko wane irin kaya daga na hausawa har na turawa, daya a Chana d'aya a America d'aya a nan kano din, saboda haka k'wararraun ma'akata zai zo dasu cikin wannan satin a fara aikin gurin." *Amjad* yaji dadin wannan shawara da abokisa ya bashi gashi dai arne ne amma yafi wani musulimin kishin musulunci, nan ya amunce da shawarar abokin nasa.sun tsaida rana Monday Anthony zai shigo najeria tare da ma'aikata domin a fara gudanan da aikin sabon company me zaman kansa.



******

Me girma governor ya kalli Mai citta murya a cunkushe yace." Ina fatan jiya ka saurarin maganar wannan yaron ko."? Mai citta yayi kamar bai fahimci wa yake nufi ba.
Yace." Ranka shi Dade wane yaro ne."? Me girma governor ya daki! Tebur din da yake gabansa ransa a bace yace." *Young millionaire* ne zaka ce baka fahimta ba, ko wace kafar sadarwa tana watsa muryarsa jama'ar gari suna ihu! A kansa tare da bashi goyon baya ko ta Ina, wannan nasarar da ya samu ina me tattabar maka da cewa, ni asara ce a gare ni, domin mutukar mutanan gari sukayi mubayi'a dashi to babu shakka kashina ya bushe 4+4 din da nake so nayi bazan samu ba."
[10/30, 10:50 AM] Binta U Abbale👄: Mai citta hau inda-inda! Cike da takaici da jin haushi governor ya kunna wayarshi had'e da bude rocouding na muryar Amjadu ya mika masa.

Shima sai da jikinsa yayi sanyi, jin hayaniyar jama'ar gari da ihu duk a kam Amjad. Gyad'a kai yayi yace." Yanzu meye abinyi."? Governor yace." Dole ne ku ne mi maslaha dashi, ko kuma Ku zauna kuyi shawarwari a tsakanin ku, Ku manyan yan kasuwa abunda zai fishhe Ku, saboda duk abunda nasa aka yi wannan yaron DOMIN in faranta muku ne, nima sai kuyi kokari kuga na zauna kan kujerarar mulki shekara takwas." Share gumi! Me citta yayi cikin zuciyarsa yake cewa" lallai ubangiji me kyauta a kan bawan sa wani lokacin akan yi wa mutum mugun Abu sai ya zama alkairi a gareshi, mutukar ubangiji ya so bawa da rahamarsa ta babu shakka babu wani d'an Adam d'in da ya isa ya hana faruwar haka.... Yace." Ranka ya dad'e ina ganin zamu fara bin malamai da 'yan tsubbu kan yaron nan domin naga kansa da tauri! Ina ganin idan aka nakasa masa wani b'angare na jikinsa tou sai ya nemi guri ya zauna, kaga kenan babu shi babu wani mulki."


Governor yace." Ni dai babu ruwana duk abunda zakuyi kuje kuyi kujera ta kawai na sani idan ba haka ba, kafin na sauka daga kan mulki wallahi duk sai na ruguza Ku." Mai citta yace." Duk baza'ayi haka ba ranka ya Dade zamu San abun yi, insha Allahu.".
Sallama sukayi ko wanne ransa babu dad'i.

********

Yau bai yi niyyar futa don haka da towol din a jikinsa ya kwanta kan bed ringingine yana lumshe idonsa, jiya yaso ya tsosi yarinyar nan, bai samu dama ba, abun ya tsaya masa a rai duk da halin damuwar da yake ciki hakan bai hana shi sakin murmushi lokaci zuwa lokaci ba, Zumbur! Ya mike jikin wardrobe dinsa ya nufa ya bude ya fara lalube can ya Ciro pant din ta, ya rike a hannu yana sakin wani miskilin murmushi. Bed din ya nufa hannunsa rike da pant din ya zauna had'e da tsira masa ido kawai yana kallonsa....yanayin jikinsa ya fara sauyawa tsigar jikinsa ta mike tunda yake mu'amula da mata iri-iri bai tab'a samun yarinyar da ta shiga zuciyarsa ba irin ta ya rasa meye dalili?? Kawai dai ya San yana mutukar son bakinta mussaman in tana tsiwa yanda take da zafi-zafi haka bakinta yake da tes miyau ta yayi masa sosai uwa uba albarka tun k'irjinta masu taushi gami da girma Wanda yake kasa ritsa su da hannunsa,, yarinyar tayi ta ko wace siga, d'an ya tsansa ya dago yana kalla, murmushi yayi had'e da Dan Sosa kanshi a fili yace." *Asma'u!!!!* zan San yanda nayi kika dawo gidanan domin kin d'an d'ana min zumar ki, mai wahalar mantawa.... Wayarsa ce tayi k'ara alamun ana kira. Yana dubawa yaga sabuwar numbar, Kamar kar ya d'auka sai kuma ya mik'a hannunsa ya dauki wayar tana daf da k'arshe yace." Salam"" Hibbah ta saki ajiyar zuciya jin muryar gwarzon zuciyar ta. Tace." My Apple gani nazo gidan ka masu gadi sun hana ni shigowa wai sai na nuna shaida." Mik'ewa zaune yayi sosai jin muryar kamar ya San me ita, kai tsaye yace." Wacece ke."? Wata irin shashshekar kuka tayi tace." Ka manta da kankanaty ka ko.? Nice Hibbah!!!" Take ya tuno yarinyar 'yar gidan me citta CE." Cikin basarwa yace." Oh! Hibbah ya kike? Ya gida."? " lafiya Lou Nazo yi maka jaje banzayen masu gadi sun hani shigowa kamar basu San wacece ni ba a gurin ka." Murmushi yayi yace." Akan aikin su suke so ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login