Showing 30001 words to 33000 words out of 67868 words

Chapter 11 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15515

ido tare da fad'in" in zakije kawai ki shiga mota mu tafi." Baki na rawa tace " INA tsoron fadan Umma kina ji fa tace." Kar mu Kai magariba ba ko." Ko sauronta banyi ba naja hannun Munnu muka shiga Mimi ta shigo duk jikinta a sanyaye mai a dai-dai ta yaja motar muka tafi.



*Tofa*
My fans ko me zai faru a haduwar Asma'u da Amjad a karo na biyu


Ku muje zuwa dai








*21/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.



*24*




Dai-dai jaction muka sauka nace "Mimi bashi kudinsa" nan take ta ciro Dari biyar ta bashi ya dauki Dari uku ya bamu canjin Dari biyu, muka tsalla a nutse. Estate din shiru kamar babu wani mahalukin da take rayuwa a cike sai dai haske dal-dal a ko ina duk da cewar gidaje uku ne kawai a ciki,muna shiga karnukan da suke ciki suka fa ihu!! Tare da yowa kanmu duk suka tsorata ni ko na dake yare da cewa"idan kuna nuna razanar Ku a fili sai su zata b'arayi ne." Munnu tace." Wallahi asma'u na fara da na sanin zuwa fa" gaba nayi ban saurare ta ba, suka biyo ni a baya. Daga can nesa na hango shi ya futo daga massalacin dake jikin gidansa, zai shiga gida yana sanye da doguwar jallabiya fara tas!! Irin ta Larabawa kwata-kwata su Mimi basu ganshi ba nice na ganshi, nima kuma da suffar shi na gane shine. Muna zuwa bakin get din me gadi ya bimu da kallo irin na tuhuma nayi saurin cewa" munzo gurin me gidan ne." Kallonmu yake cikin nazari yace." Kunyi b'atan kai 'yan mata banan bane" nace" kaga malam wai ba nan bane gidan *Amjad* ba" yace" nan ne 'yan mata" cike da bada umarni nace" to sai ka bude mana malam" yace." Me gidan bai bada izini ba domin da yasan da zuwan Ku zai fada min a bude muku get Ku shiga" haushin sa ya kamani na masa wani banzan kallo tare da cewa" kai malam kalle mu da kyau ka gani ba tsiyace ta kawo mu nan ba arziki ne, kuma mu 'yan uwan me gidan ne idan kana tamtama kaje ka tambayo shi kaji" kallona yayi naga yayi saurin risinar da kansa, dama ni haka nake da mugun kwarjinin tsiya in na zuba ma mutum idona baya iya ketare hukuncina to haka ce ta faru da me gadi bakinsa na rawa yace" bazan barku Ku shiga ba domun bansan da me kuke tafe ba, amma bari inje in Sanar da masu tsaron kofar shi halin da ake ciki." Ya ya bud'e karamar kofar ya shiga yana k'okarin kullewa babu zato yaji an buge hannunsa yayi saurin cirewa na fada cikin gidan INA kiran su Mimi suka shiga da sauri, nace" tunda mun shigo si munyi me wuyar kuma.

Duk abunda yake faruwa yana kallonsu ta CCTV Camara d'inshi ya cire rigar jikinsa daga shi sai shout nickar da kwalin Lemo a hannunsa yana sha, murmushi ne kwance a fuskarsa yana mutukar mamakin taurin kai irin na yarinyar mamaki yake sosai yanda akai har suka samu nasarar shigowa bayan sun baza karnuka a gurin saboda tsabar kokari da k'arfin hali har tana buge get man d'insa tana shigowa ko ubanta ta aje masa a gida ihu! A fili yace." Kome ta zo tayi min a gida oho cike da mamaki yake kallonsu ita dasu rambow tana fada suna fad'a kamar zata tsokane musu ido Wayarshi ya d'auka dake aje a gefansa ya nemo numbar Rambow yana d'auka yace." Barsu su shigo" ya kashe wayar ba tare da ya tsaya yaji me rembow zai ce ba.

Rambow yace." Kun fi sa'a Boss yace" Ku shiga amma da badan haka ba wallahi ba zaku shiga ba" hararsa nayi nace" shima ogon naku nakusa karya alkadarinsa" cike da mamaki Rambow ya bita da kallo jin abunda take cewa, hannun munnu naja muka shige DOMIN naga Mimi sai wani ja baya take.

Muna wucewa Doh-doh yace"wallahi ina jin tausayin yarinyar nan duk ranar da zata shiga hannun Oga sai ta gane shayi ruwa ne" Rambow yayi k'wafa tare da fadin" k'aryar rashin kunya ta dama.

A hankali muka tura kofar parlor muka shiga, sanyi kamshi ne ya buge mu mu dukan mu sai muka fara zare ido sosai nake karewa parlor kallo DOMIN zuwana na farko ban kalle shi ba, wow gaskiya na yaba da tsarin parlor gami da k'yatuwar sa, komai na parlor orange color ne ina mutukar son Abu orange Munnu tace."Asama mun banu kizo mu koma kawai na fasa" nace ke dallah can tsorone daku wallahi Ku zauna ni inje dakin shi si na sani mybe ma baya ciki.


Mimi ta rik'o hannuna tana girigiza mun kai wai kar inje fuzge hannuna nayi nai gaba ba tare da na wai wayo su ba."


Ganin tana nufo kofar shigowa ne yasa ya mike da sauri haske dakin ya kashe ya tsaya jikin bango yana sauraron shi gowarta. Ina bude kofa naga duhu d'un d'um!! Na gane inda makkuni yake aikuwa nafara lalube zab kunna". Wani abu naji ina tab'awa shi ba gashi ba shi ba fatar jikin mutum ba gashi dai yafi yawa a jiki, gabana ya fara fad'uwa jin kamar hucin nuffashin mutum, hannuna na daga da niyyar in kunna futular domin na fara tsorata, da k'arfi! *Amjad* ya jawo ta kirjinta ya daki nasa ya zura hannunsa kasanta ya rik'o kwankwanso ta sosai inda baza ta iya guduwa ba, sannan ya mik'a d'aya hannunsa sama ya kunna futula, haske ya gauraye dakin.

Cike da tsoro na kura masa ido fuskarsa a murtuke shima nasa idon ya samun kamar zai cinye ni danya, munfi minti uku muna kallon_ kallo kafin nace." Sake ni inyi abunda ya kawo in tafi." Shiru yayi min bai CE komai kuma har yanzu idonsa na kaina yana kare min kallo inda naga ya fi kalla a jikina na kalla ina dubawa, sai naga kwaurina da ya futo waje dalilin yanayin dinki bayin saurin Jan mayafi na rufe ina hararsa, hannunsa yasa ya janye gyalen ya jefar kasa ya cigaba da bin jikina da kallo kamar tsohon Maya. Cikin ikon Allah kuma time din banji wannan azabban fleengs din Dana ke ji ba in ya kusance ni.


Karfina nasa da gaske nake k'okarin ture shi. Ko motsi kirki ya kiyi . muryar shi a harhad'e yace." Me kika dawo kimin a gida"? Ko nuffasawa ban bari yayi ba nace." Bana munafurci na dawo d'aukar handbag dina ne."
[10/22, 8:58 AM] BintaUmarAbbale👄: Kallo yake min kamar Wanda be tab'a ganina ba, gashi ya wani had'e fuskarsa tamau!! Yace." Karya kike da akwai dai abunda ya kawo ki,babu wata handbag da kika manta." Fuzge jikina nayi ina galla masa harara gefe na matsa ina bin dakin da kalo ko a ina zan ga handbag din oho min... Cikin tafiyar shi ta jarumai ya nufi bed d'insa ya zauna tare da Dora kafa daya kan d'aya yace." Zo ki duba kayan ki inda kika aje ki fuce min daga d'aki". Kai tsaye.. Na nufi bed d'in na fara duba bayan shi da lukunanshi,aikuwa sai na hango ta, da sauri na zura hannuna na d'auko abata. Bayansa na kalla naga ki juyo bai yi sai danna waya yake. Rike da ita a hannuna na tsaya a kanshi nace." Sai sak'on da aka bani na bak'a" ya dago kanshi tare da cewa." Ina jin fad'a min ki fuce ki bani waje" cike da taikacin yanda yake kyarata wai in fuce!!! Sai kace wata tinkiya nace." Kai kaga bafa komai ne yasa nazo gidan ka ba da har kake k'okarin gaya min magana dama ko baka ce na fuce ba zan fuce in bar maka d'akin ka..... Ya katse ni ta hanyar fadin " naji ki fad'i sak'on ki, ki futa min a d'aki fitinanniya kawai wa zakiyi wa preetanding ni nasan abunda ya k'ara kawo ki gurina kuma baza ki samu ba" ya k'arashe maganar cikin sigar rashin mutumci" zuciya ta kamar ta tsage saboda zafi nace." Ni ba shashashar mace bace kuma ni ba irin 'yan Matan ka bane wallahi ni nafi k'arfin ka bare in kawo kaina gurin ka ko abunda kayi min baya ma Allah ya isa."

Murmushin gefan baki yayi ya d'an sosa sumar shi kad'an da Jan ido ya kalle ni still da murmushi a fuskarsa yace." Ok naji ba abunda ya kawo bane kin tsaya kina Jan magana fad'a min sak'on ko in sa yanzu ayi waje dake domin bana bukatar ganin wannan mummunar fuskar ta ki bak'akirin!!!!!!!!!! Asamau da tsani ace mata mummuna lokaci guda hankalin ta ya tashi taji wani irin hawaye me zafi na k'okarin zubo mata da sauri! Ta aro jarumta da dauriya ta aza a ranta, wani kallon Tara saura kwata ta mai tace." Wa kake da suna *Amjad* ko me?? Kai dai ka sani, bari kaji wani Abu da baka sani ba, kyau ba shi bane kyawun hali da nasaba me kyau da shi a ke tunk'aho Allah Ubangiji ya raba mu da kyau irin naku babu kyawun hali da nasaba me kyau Wanda nasan ni nafi ka nasaba da tarbiyya me kyau duk wannan iskancin da kake rashin tarbiya ne da rashin samun iyaye jajirtattu saboda haka tun wuri gwara ka koma islamiyya ka samo ilimin addini domin kasan meye banbanci kyau da muni." Ina karasa maganar na nufi kofar futa ina da na sanin zuwa gidan. Kofar nake k'okarin budewa taki nayi-nayi na juyo a fusace! tare da kaurara murya ta nace" zo ka bude min kofa in futa daga wannan annobar" ina kallonsa ya mik'e ya nufo inda nake, fuskarsa na tsurawa ido kamar mala'ikan mutuwa take naji tsoro ya shiga raina na kauce daga bakin kofar, cike da k'arfin hali na dinga watsa masa kallo ko kallona bai ba ya bude kofar zai futa na biyo bayansa, da sauri hannunsa guda ya sanya ya ingiza ni ciki dakin na fad'i kasa, ko juyo wa bai ba ya rufe kofar tare da murza key! Na mike a zafafe! Na daki! Kofar dak'afata ina janta tun karfina ko motsi tak'iyi ihu!!!!! Na kurma sosai ina fad'in "Idan baka bud'e mun kofar nan na futa ba kai ba d'an hakan bane, d'an iska asharari"!! Duk yana jin haukan da take wai shi take zagi harda su d'an iska asharari wai ma meye alk'ar shi da yarinyar ne da har ta samu dama akan shi shine Mara tarbiyya Wanda iyayensa suka lalata shi, ya zama dole yarinyar ta karb'i hukunci a gurin shi, fuskarsa ya kara hadewa ya Isa tsakiyar parlor inda ya hango su Mimi tsaye bakin kofa suna zare ido dama yasan dasu tunda ya gansu cikin CCTV Camera, Cikin jarumta ya durfafe su,sai ga Munnu tana rawar k'afa ganin wani ingarmar namiji na kusan to su, cike da tsoro ta zube bakin kofar. Ita ko Mimi suma ne kawai bata yi ba daga ninsa tunda ya futo ta tsora mishi ido tana kallonsa wata muguwar soyayyar sa na kara nunkuwa a cikin zuciyarta. Kallonsu yayi a nutse yace." Ku ne 'yan rakiyar ta"? Munnu ta gyad'a kanta alamar "Eh bakinta na rawa tace" ina wuni" ko kallonta baiyi ba ya bud'e kofar parlor ya futa, minti biyar ya dawo yana kallonsu tare da fad'in" Ku tashi a mai daku gida". Cikin dauriya Mimi tace" Asma'u fa". Da gefan ido ya kalleta ya d'auke kansa tare da fadin." Nace tazo a kai ku gida tace baza ta tafi ba so kuyi tafiyar Ku kawai Ku k'yaleta duk sanda ta ga damar tafiya sai ta tafi." Jikinsu ya soma b'ari Mimi tace" kayi hakuri don Allah kaji"" miskilin murmushi yayi ya Dan Sosa kansa Wanda hakan ya zame masa jiki yace." Ke ba laifina bane fa nata ne, kunga ni ita ta kawo kanta har gidana ta bude min daki ta shiga ta zage ni ta fad'a min duk maganar da tazo bakinta to babu laifi na" hanya ya nuna musu da hannu a karo na biyu yace." Doh-doh na jiran Ku a mota a sauka lafiya." Simi-simi suka wuce suna waiwaye gefe guda kuma suna mamakin abunda Asma'u ta aikata domin sun gazgata maganar sa saboda sanin halin kaifin harshe na Asma'u. Zama yayi a parlor ya rik'e kansa zuciyarsa na masa zafi sosai yake tunanin hukunci da ya kamata yayi wa yarinyar, murmushin mugunta ya saki da ya tuno wani abu kawai ya mike ya isa gaban TV ya kunna ya zauna cikin kujera yana kallonshi wani american film yake kallo ya manta da wata Asma'u dake d'akinsa a kulle sosai film din ya d'auke masa hankali.


Gajiya nayi da dukan kofar na zube bakin kofar ina mai da nuffashi wani abu me nauyi yazo ya tokare min a mak'ogwaro na a fili nace "wai me guy nan yake nufi ne da nine? Babu me bani amsa Mik'ewa nayi da sauri na Isa window na yaye labule INA lek'en waje tunani nake ko zan samu hanyar futa, ko alama babu wata hanya, nafi minti goma a tsaye a gurin gabana na fad'uwa, na juyo na kalli a gogo dake manne a dakin 9:53 na dare goma shaura minti bakwai kenan. Sai naji kafafuna baza su iya daukata ba, na duba wayata da sauri nake lalubar numbar Mimi na kira babu kudi a cikin wayar, da sauri na tafi cin bashi, da k'yar suka bani naira Hamsin dama suna bina bashi, Mimi na daga wayar nace." Kuna ina ne"? Tace." Muna gidan su Munnu yaushe zan koma gida ni kadai in cewa Umma me? Murya na rawa nace Mimi guy nan bai da mutumci wallahi ya kulle ni a d'akinsa" Mimi tace" Yace ke ce kika ce baza ki tafi gida ba". Cike da mamaki nace" Mimi sharri yayi min kawai kyaleshi" tace" nasan kin masa rashin mutumci shiyasa yayi miki haka" ga yanayin yadda Mimi tayi magana na gane ranta a bace yake nace." Mimi nayi masa din in zaki rama masa bisimillah" na katse wayar cike da taikacin ta wato ita bata jin ciwon kulle ni da yayi shi take k'okarin karewa,

Zarya na fara a dakin ina kaiwa ina kawo wa, da sauri naje na daki kofar! Da kafata kamar wata wacce ta samu tab'in hankali da k'arfi nace Idan baka bude min kofar nan ba kai ba d'an halak bane wallahi!!!Abunka da dare shiru ko INA yasa magana ta ta cika parlor murmushi ya saki a hankali yace." Yarinya inan zuwa gurin ki,zaki fada min wace irin alk'ace a tsakanin dake da har kika samu dama a kaina....











*22/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.


*22*




Sama-sama Asma'u take jin Mimi tana magana wani irin sarawa kanta yakeyi ga wani sanyi me ratsa jiki tana ji a jikinta,dishi-dishi ta ke kallon Mimi tana sallah lumshe idonta tayi tana kara takure jikinta.Mimi ta idar sallahr ko addu'a bata yi ta mike tana ninke abun sallah ta futa waje da sauri.Umma na kicin tana k'okarin raba abinci tace." Umma In Kin zuba mana namu bani in je muci domin muje chamis din kinsan dole su taimabaya ko ta ci abunci nasan dai allura ce za ayi mata." Umma ta mik'o mata Fula's MA dai-dai ci cike da shinkafa da faduka da kifi d'anya abunci dai-dai na talaka tace." Aikuwa domin Kin San wannam zazzab'in na maleria dole sai da allura." Su duk a tunaninsu maleria ce take damun Asma'u. Mimi ta wuce da sauri tana shiga ta hau kiran sunanta "Asma'u tashi muci abunci muje a dubaki." Bude idona nayi a hankali nace."Mimi k'yaleni da chamis din nan don Allah." Sakin baki tayi tana kallona naja bargo na rufe kaina gaba daya ina takure wa." Tace "Dole fa ki tashi WALLAHI ke taurin kanki ne matsala." A hasale nace." Dallah ki kyale ni wai jikin ki ko nawa da zaki dame ni." K'arar!a kunnen Umma ta daga labule ta shigo rai a bace tace." Gwara ma ki tashi tun kafin ranki ya b'aci ita meye laifin ta kawai Dan ta damu da lafiyarki shine kike mata tsawa." Nace." Umma nifa lafiya ta lao". Tsaki taja tace." Kin saba karya dama duk abunda ya same ki ke kika jawowa kanki wanka da magariba saboda haka ki tashi tun kafin raina ya b'aci." Tana gama maganar ta ta fuce daga dakin.
Cike da jin haushin Mimi na tashi zaune ina hararta had'e cinyoyina nayi ina ya mutse fuska tace." Ki sauk'o kasa mana." A hasale nace." Anki a sauko ki d'auko Fula's din abunci ki dawo dashi kusa dani in kin damu."Mimi tace." Banza masifaffiya." Shiru nayi mata ina hararata gefe guda ina matse cinyata Dan karta gane halin da nake ciki. Ta kalle ni cike da nazari tace." Wai meye tun d'azu kike matse cinjyar ki kamar wacce taji ciwo." "Ban sani ba." Abunda nace da ita kenan na sha kunu. Tab'e bakinta tayi tace." Mutum babu lafiya ma sai masifar tsiya." Share ta nayi kawai na fara cin abunci a ya tsine.Kad'an na iya ci na mike a daddafe na futa waje domin wanke hannuna, sauri sauri Mimi ta gama ci itama ta futo hannuta rike da hijabai ta mik'a min na sanya itama tasa ta wanke hannunta muka tafi. Ko da Anas me chamis ya gama duba ni sam bai ga wata maleria ba maganin zazzab'i kawai ya bani muka dawo gida, nace." Ki damu sai munje to munje muguwa kawai allurar dai da kike min fata bata samu ba." Dariya Mimi ta sanya tana zolaya ta ni ko na sha kunu.muna shiga gida na dauki buta na d'aura alwala can dakin Umma na shiga nayi sallahr mariba da Isha'i na kwanta kan daddumar ina addua'a Allah yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login