Showing 45001 words to 48000 words out of 67868 words

Chapter 16 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15500

yasha ruwan ne me girma governor ya kalle shi a nutse yace." Hausawa suka ce maganar gizo bata wuce ta k'ok'i na San ka fahimci dalilin da yasa na kira ka."? Yace." Ban fahimci komai ba ina Neman Karin bayani." Governor ya gyara zama tare da fadin." Har yanzu muna kan bakanmu na ka rushe company naka ko kuma ka tsawwala farashin kayanka, saboda ni kaina na zauna nayi nazari da tunani ba 'yan kasuwa kad'ai abun yake tab'awa ba har da gomnati ina fatan ka fahimta, gomnati na karb'ar haraji a hannun 'yan kasuwa idan ba k'ara farashin kayan ka ba to tabbas zamu tsawwala wa 'yan kasuwa kud'in haraji kuma za mu rushe shagunanmu Wanda gomnati ta gina zamu kori duk wani dan tebur da Wanda bashi da shago zamu watsa su daga kan titi, wannan shine matakin da muka d'auka.

Ido jazur! Ya d'ago kansa yana kallon governor din yace."Allah shi baka nasara da kanka kake wannan ikirarin? Wato har kamanta ranar rantsuwa kenan ? Ka manta ranar da ka dafa alk'urani me girma ka rantse dashi? Ka manta ranar zab'e da wahalar da talakawa suka sha akanka rana zafi sanyi ruwa talaka ya tsaya kai dafata ya dangwala maka kuri'a duk ka manta wannan ranar me girma Governor. " ya k'arasa maganar tasa cike da tuhuma."

Me girma governor yaji duk jikinsa yayi sanyi jin yaron yana so yayi masa warwara nan take ya fara nad'e tabarmar kunya ta hanyar buga tebur din dake gabansa yace." Duk wannan abunda kake fada basu shafeka ba, lokacin zab'e na futo da kudi Wanda ni kaina bansan iya adadinsu ba, an rabawa talaka INA so ka sani talaka a yanzu ya fi bukatar ka bashi Dari biyar ko ka bashi sabulun Wanka sink'i d'aya akan 'yan cinsa, saboda haka rik'e alkawari da sauransu duk bai shafe ka ni dai ga hukuncin da na yanke! Idan kuma kak'i karb'a kai kanka sai mun rusa ka da duk abunda kake tak'ama dashi."

Murmushi me ciwo yayi ido jazur yake kallon governor din yace." Ita kuma rantsuwar da kayi fa? Allah ba abun wasa bane."
Governor ya daga masa hannu a fusace! Yace." Kai kasan Allah ne ? Dubi askin dake kanka, duk abunda kake muna da labarin sa ka bude hotal har guda biyu ana tata iskanci a ciki kai kanka kana iskancin ka da mata zaka zo kana fada min Allah anan gurin." Murmushi Amjad yayi cike da takaici wai shi governor zaiyi wa gurin yana Neman mata, mutumin da kowa yasan shi mugun asharari ne me mugun son mata da shaye-shaye shiyasa lokacin zab'e 'yan daba ya baza ko ina suna raba kudi tare da tsorata alumma da jajayen idonsu mik'ewa yayi a fusace! Ya kalle shi yace." Ina nan kan bakana babu gudu babu ja da baya company kuma yana zaune daram! Sannan kuma bazan kara farashin kaya na ba." Yana gama maganar sa ya futa daga ofis din cikin zafi.!


Governor ya bishi da kallo da baki a sake, waya ya d'auka ya kira shugaban kasuwar k'wari yace." Yanzu-yanzu a rufe a shaguna kuma a watsa 'yan tebur da suke kan hanya.

Aikuwa haka ce ta kasance 'yan kasuwa na hidima da kaswancin su tare da customs kawai sak'on shugaban kasuwa ya riske su, da ya yawun me girma governor, hankali a tashe suka fara rufe shaguna kowa na fad'in." Albarka cin bakinsa.
Tun kafin ya isa gida labari ya riske shi, ranshi a b'ace ya dauki wayarsa ya kira governor din shi kuma a nashi b'angaran ya dauki wayar da sauri yana wani mugun murmushi ya d'auka Amjad din ya sauko daga kan kudirinsa yasan dai yanzu labari ya same shi, muryar shi sama-sama yace." Ina kan hanya ta ta komawa gida na samu labarin abunda ya faru yanzu, ina so in fada maka wani abu, daga nan ba zan zame ko INA ba sai gidan redio zanje in warware musu zare da abawa." Saura kad'an governor yayi hantsile daga kan kujerar da yake zaune baki narawa yace." Kar ka kashe min waya ka bari kaji abunda zan ce da kai." Murmushin takaici yayi yace." A banza abunda baka sani ba shine duk wata shira da ta gabata a tsakanina da kai ina d'auke da ita cikin wayata so a tafin hannuna kake." governor ya goge wani zazzafan gumi da yake tsatstsafo masa a goshi lallai yaron nan bashi da mutumci wato ya samu zagin da jama'ar gari suke masa kwana biyu ya lafa shine zai dawo dashi, baki na rawa yace." Kar........Amjadu ya katse ta hanyar fadin " baka da abunda zaka ce min a halin yanzu kawai ka janye kudirin ka nima in janye nawa." Governor yace." Na janye gobe kowa ya futa kasuwa kai kuma ka saurari abunda zai biyo baya." Murmushi kawai yayi ya kashe wayar ba tare da yace uffan ba."
.governor ya tsaya kawai yana kallon fuskar wayarsa yana mamakin yaya akayi yaron ya samu dama akanshi har ya raina shi, da matsayinsa yana matsayin shugaba amma yake kashe masa waya lallai ya zama dole ya hukunta shi.


Rai a bace ya shiga gida ana ta kiran sallahar magariba alwala ya d'aura nan cikin bedroom d'insa yayi sallah, waya ya kira Rambow ya je ya siyo masa abunci domin wata yunwa yake ji,ga uban hayak'in sigari da ya babbakawa cikinshi a mota sai da ya shanye a kwali guda kafin su shigo gida.

Mintuna ashirin tsakani Rambow ya shigo dakin hannunsa rik'e da wata Leda me kyau da k'yalli ya aje masa tare da jira ko akwai wani umarni daga masa hannu kurum yayi alamun ya futa, cike da bin umarni ya futa daga dakin. Ledar take away din ya jawo yana dubawa abuncin be masa ba ya rufe jingina yayi jikin gadon shi yana tunanin yanda za'ayi ya warware wannan Matsalar da take tun karo shi.


*******
11:00 dai-dai abun ya afku gidajan redio na shirin rufewa suka samu labari babu shiri suka tafi domin d'auko rahoto, yana zaune inda yake tun d'azu ya fara jin kira na shigowa wayoyin shi, daukowa yayi yana dubawa Wani d'an kasuwa ne da ya shara ya kira shi suka gaisa hankali a tashe yace." Yallab'ai Ashe abunda ya faru kenan kai Ubangiji Allah ya tsare ya kiyaye gaba gaskiya muna cikin tashin hankali." Amjad ya kasa fahimtar maganar sa kawai ya aje wayar ya dauki dayar zance dai guda ake masa, Zumbur ya mike ya futo parlor yana shirin bude kofa ya futa sai suka buga karo da rambow zai shigo hankali a tashe, abunda ya d'auke masa hankali abunda yaji wani Dan jarida na fada a wayar Rambow inda yake cewa" *Inna lillahi wa ina ilahi raji'un, a yanzu ne muka samu labarin mummunar gobarar da ta afku a katafaran company nan na Amjadu ABUL Abbas company da ya shahara gurin kawo kaya masu kyau da karko gami da sauk'i da saukakawa talaka......."*














*26/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: [10/26, 11:33 PM *BABBAN YARO*




*Mallakar_BINTA UMAR*






*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*





*30*




*Innalillahi wa'inna ilahi raji'un."* shine abunda ya futo daga bakin *Amjadu* da sauri ya koma bedroom din nasa jikinsa na kyarma! Ya dauki wayarsa yana laluben numbar manager, har wayar ta katse bai d'aga ba, ya kara kira a karo na biyu shiru bai d'auka ba. Parlor ya futo yana kara kiran wayar.wannan karon tana shiga manager ya d'auka babu abunda ya futo daga bakin Amjadu sai "Bashir ina fatan babu Wanda ya rasa ransa ko."? Manager yace." Eh yallabai babu Wanda ya rasa ransa sai dai akwai wad'anda suka samu rauni gurin ceton ransu." Yace." Maza ka had'a Kansu Ku wuce hospital me zaman kansa ganin zuwa." Manegar yace." Insha Allahu haka za'ayi." Kashe wayar yayi ya dauki dayar da take aje kan bed an kira yafi sau goma, Sam bai tsaya daga wa ba domin yasan duk zance daya ne. Futowa yayi rambow da doh-doh suka rufa masa baya.

Kai tsaye company suka nufa cike da tashin hankali da tarrarabi, kafofin yad'a labarai sun rud'e da zancan ko wacce ka kamo maganar gobarar ake wanda suke fad'in an rasa meye musabbabin ta. Kafin kace kwabo labari ya watsu a birnin kano da kewayen ta, cikin daran 'yan kasuwa suka dinga futowa daga gidajansu suna jajantawa junansu kungiya wasu sukayi suka nufi company cike da alhini da tashin hankali.


Ido jazur!! Yake bin company ninsa da kallo ya k'one kurmus! Ko ina ka d'aga kai sai hayak'i yana tashi gurin ya hautsine da 'yan kwana-kwana gami da mutanan gari kowa na bada gudumar sa." 'Yan jarida sun kewaye shi sun fi su goma dukaninsu suna son suji ta bakinsa. Duk inda yayi sai sun bishi suna fadin." Young millionaire *Amjadu* "Ko zaka fad'a mana wane irin hali kake ciki na wannan Abu da ya faru da company min ka me tarin albarka muna bukatar jin ta bakin ka." Shiru yayi musu kawai hannusa goye a bayansa yana zaga loko da sako na ko ina hannunsa ya mik'a ya karb'i wayarsa gurin rambow, nan ma 'yan jarida suka yi masa caaaa!!! Masu d'aukar sa hoto nayi masu vedio nayi masu kafa masa lasifika a dai-dai bakin sa nayi, wai Dole sai sunji me zai ce a wayar.
Numbar Manager ya kira bugu d'aya ya d'auka tare da fad'in." Ranka ya dad'e." Cikin jarumta da dakiyar zuciya yace." Yaya ina fatan babu wata matsala duk Wanda yake bukatar taimakon gaggawa ayi mishi kan lokaci. " manager yace." Insha Allah ranka ya dad'e gashinan ma ana musu dressing raunin ka da suka samu." "Kuna wane hospital ne."? Manager yace." Malam. Aminu kano." Ok ganin zuwa." Ya fad'a yana kashe wayar." Yuuuuuuuu!!! Suka bi bayansa tare da sake maimaita masa maganar d'azu. Doh-doh ya juya da sauri yana zare musu ido!! Oho ko a jikinsu, hummm! D'an jarida da nacin tsiya. Wani ne yayi tsagal!! Ta tari gabansa ya kafa masa lasifik'a a baki Tare da fadin." Ranka ya Dade ka taima kayi mana magana muna mutukar bukatar muji ta bakin ka akan wannan al'amari da ya afku."!!
Murmushi yayi Wanda kana ganinsa kasan na bakin ciki ne, yace." Kuna so ku ji ta bakina."? Duka suka ce k'warai kuwa ranka ya dad'e. Cikin basarwa yace." Komai dai ya samu bawa daga Allah ne cikar mutum mumini yarda da k'addara me kyau da mara kyau.amma wani abu yakan samu d'an adam wani ya zama shine mujaza faruwan al'amarin,saboda haka ina me tabbatar muku da cewar wannan abun da ya faru to daga sama ne kuma wasu ne suka zama silar faruwan shi, zan muku misali. D'azu misalin k'arfe shida da rabi na yamma kun Sanar a k'afafun yad'a labaran Ku cewar 'yan kasuwa su dakata da futa sai zuwa ranar da gomnati ta umareshi, kafin awa guda da yad'a labaran Ku kuma Ku k'ara 'yada wa cewa umarni daga gidan gomnati wannan magana an janye ta, da wannan nake rufe magana ta, dukkanin ku kuje ku tsaya kuyi binkice kanta sai Ku samu abun yad'awa a duniya." Tsitt!!! Gurin yayi tun sanda ya fara magana har ya k'are kowa na sauraren sa, wucewa yayi da sauri yaran shi suka rufa masa baya. Kafin kace kwabo gurin ya kara hargitsewa kowa na fad'in albarkacin bakinsa, mutane da dama sun fi zargin wannan al'amari daga abokan adawar sa ne, wasu kuma suna zargin daga gidan gomnati ne kowa dai da abunda yake fad'a.
Kai tsaye hospital Malam Aminu kano suka nufa, sai da ya tabbatar da duk Wanda ya samu hadari a jikinsa ya samu kulawa sannan hankalinsa ya kwanta. Suka kara dawo wa company Wanda har yanzu ake aikin gurin tare da futo da kayan da sukayi dame ji wasu a jibgi-jingi wasu sun ci wuta wasu kuma ta fara cinsu basu gama k'one wa ba, sama da k'asa ko ina ka kalla bak'ikirin babu kyawun gani babu wani abun da za'a mora a gurin. Wani ofis ne a harabar gurin, nan yaranshi suka shiga suka gyara mishi dake akwai guraran da wutar bata same su a kasan gurin, nan ya shiga ya kwanta kan wata k'atuwar kujera ya rintse idonsa zuciyarsa kamar zata futo fili.babu Wanda ya fad'o masa a rai sai mahaifin sa, a take ya mik'e ya dauro alwala ya shimfid'a abun sallah dai-dai ta tsayiwarsi yayi gaban sarki jallah wa ala yana mik'a mishi bukatunsa, sosai yayiwa iyayansa addu'a ya shafa, sai yaji zuciyarsa tayi sanyi, a gogon hannunsa ya kalla uku da rabi na dare, har yanzu yana jiyo hayaniya,jama'a a waje da alama har yanzu basu gama futo da kaya ba, mik'ewa yayi ya nufi window tare da dage labulen yana lek'en gurin. Aiki kurum suke kamar kara cab'a gurin suke, ga uban kaya nan dila-dila a watse a harabar gurin duk sunyi dame ji. Ko mawa yayi ya zauna yana tunanin wane mataki zai d'auka kansu Alhaji Hashimu me citta dashi kanshi me girma governor nan.
A takaice dai *Amjad* da duk wani me kaunar sa a ranar kwana sukayi cike da bakin ciki gami da damuwar abunda ya faru. K'arfe shida dai-dai na safe k'afafun yad'a labarai suka fara labaran su, inda kowa ce tasha ka kunno a lokacin sautin muryar *Amjadu* ce inda yake yiwa 'yan jarida baya ni. Tofaaaa!! Gari ya haustine kowa na zagin me girma governor tare da fadin cewar da sanya hannunsa haka ta faru tunda shi Amjadu a baya nin da yayi yayi magana me kamar jiryewa Wanda hausawa suke cewa me kamar Wanka. Tuni k'ananun'yan kasuwa suka shirya zanga-zanga tare da makamai da tayoyi suka nufi gidan gomnati. Matasan gari marasa aikin yi suma suka rufa musu baya. Hankalin me girma governor ya kai k'oluluwar tashi! Sam! Ba zaici haka jama'ar gari zasu tada hankalin su ba, tuni ya baza matakan tsaro cewar a tsare hanya kar a bari kowa ya k'araso a rufe titi gami da dakatar da ababen hawa.


Muna zaune a rumfa ni Mimi Ummanmu muna karyawa sai ga Yaya Aminu ya shigo hankali a tashe! Umma tace." Yaya ka dawo kuma."? Cike da tashin hankali ya zauna kusa da ita tare da fad'in" Umma ina naga ta futa zuwa skull gari ya hautsine!!! Tace." Me yake faruwa ne. " yace." Wai ina redion ki ne tun jiya ake tashin hankali a gari an je an kone company nan me zaman kansa. " tace." Wane company ni ne."? Baki na rawa Aminu yace." *Amjadu AbulAbbas materials* dummmm!!!!!? Gabana ya buga na tsurawa bakin Yaya Aminu ido ina kallonsa. Umma tace." Ni ko a bakin wa naji wannan sunan."? Mimi tace." Bakin aunty Hauwa." Tace "yawwa hakane " sai kuma ta rafka salati tana tada hannunta cike da tashin hankali.
Ni da Mimi muka kalli juna rai duk babu dad'i. Umma tace." Ni ina zan sani redio ta ta lalace dama wayata nake kunnawa to kasan jiya bamu kwana da wuta ba." Yaya Aminu yace." Aikuwa gari a hargitse yake domin 'yan kasuwa sunan nam suna zanga-zanga kuma an hana futa da abun hawa. Umarni daga governor. "
[10/27, 12:00 AM] 👄: Umma tace." Gaskiya na jinjina wannan al'amari ikon Allah ko meye ya haddasa gobarar oho. " yaya Aminu yace." Mutane dai suna zargin 'yan adawarsa ne, wasu kuma suna zargin da sa hannun gomnati har yanzu dai an kasa gano meye ya haddasa gobarar." Cike da al'ajabi Umma tace." Ai dole yaron nan yayi makiya da mahassada wallahi tunda yana son talakawa da tsoron Allah, kaga kuwa masu kud'in kasa zasu sanya shi a gaba." Yaya Aminu ya mike tare da fadin 'Bari in karb'i wayar Garba yayi rocouding din muryar shi lokacin da yake jawabi ke kanki Umma ki ka sauarari maganar sa zaki San abun shiryayye ne." Futa yayi ya barmu da jiki a sanyaye, niko tsabar zura jiki sai na fara tunanin ko a wane hali yake ciki.har na k'agara Ya Aminu ya kawo wayar inji muryarsa wani irin mugun tausayin sa na damun zuciyata, to b'angaran Mimi ma haka yake domin ita har ta fara k'ananun hawaye.

Ya Aminu ya shigo da waya a hannunsa ya zauna kusa da Umma ya kunna mata voice din *Amjadu* lokacin da yake magana da 'yan jarida jiya.

Tunda ya fara maganar nayi sak! Ina sauraron sa, muryarsa radau! Kamar Wanda baya cikin tashin hankali babu karaya da rawar murya a lafazin sa, kana ji kasan shine me gaskiya, Umma tace." Ai daga jin wannan maganar ma kasan shiryayyiya ce makirci ne, kawai da hassada kuma zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi." Yaya Aminu yace" Wallahi kuwa Umma, nake fada miki, guy yayi a rayuwa yana mutukar kaunar talaka da cigaban matasa Sam dukiyarsa bata rufe masa ido ba, dukiyarsa ta talakawa ce gami da mabukata da marayu, to Kin San an ce mutum tara yake bai cika goma ba, duk da haka mutanan gari suna zarginsa da neman mata wai har hotal ne dashi da karuwai suke watse wa." Umma tace." Wa'iya zubbilah kai jama'a mutane ba a iya musu dama hakane duk inda Allah ya daukaka bawa to sai ya samu yan hassada Allah kasa mufi k'arfin zukatanmu." Yaya Aminu yace" ameen suma ameen. Suka cigaba da tattauana maganar.ni da Mimi shiru babu bakin magana, tunda ya Aminu ya fara maganar sa nake addu'ar Allah yasa sharrin mutanan gari ne guy baya Neman mata, domin a lokacin ji nayi wani irin Abu yazo min wuya na bakin ciki. Wani gefe na zuciyata Yace min a kanki zaki gazgata shin shi din mane min mata ne ko kuwa bayan ke ga Alina,, kuma zuciyata ta dinga min sak'e-sak'e a kanshi gefe guda kuma ina tunanin ko wane hali yake cikiA yaanzu


******
Duk inda aka zauna can kenan gungun matasa da magidanta 'yan kasuwa kai har da ma'aikatan ma suma wasu daga cikinsu suna jajanta al'amari, waya kuwa *Amjadu* har daina d'agawa yayi da k'arshe ma da abun ya dame shi, rambow yasa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login