Showing 48001 words to 51000 words out of 67868 words

Chapter 17 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15503

kashe wayoyin gaba d'aya. Ya kulle kanshi a daki shi kad'ai duk irin mutanan dake zuwa gurin shi ya hana a shigo dasu." Tv ya k'ura ido yana kallon labarai na k'arfe goma dai-dai tashan NTA sosai ya girgiza ganin yanda matasa suke tashin hankali a gari tare da kona tayoyi had'e da rigima da 'yan daba mutanan me girma Governor jama'ar gari sai gudu suke, wannan al'amari da ya faru ba iya kacin najeria ya tsaya har kasashen waje suma sai da suka nuno Company tare da rigimar da ake yi a kano din cikin labarai su na safe.

Mik'ewa yayi da sauri ya futa waje. Suna ganin futowar sa suka k'araso dukkanin su. Ya kalli Doh-doh tare da umartar sa da maza yaje gidan redio na express ya d'auko masa d'an jarida daya yana so zai yi magana.

Doh-doh ya wuce ya tafi cikin sauri. Nan harabar gurin ya zauna gurin hutawa yana sauraran dawowar sa, minti talatin a tsakani sai gasu sun shigo, ba tare da b'ata lokaci na Dan jarida ya gyara na'urarasa domin d'aukar muryar Amjadu


A nutse yayi bisimillah ya bude da addu'a sannan ya fara magana kamar haka.

*Ni Amjadu Abul Abbas ina kira ga jama'ar gari da duk wani d'an kasuwa matasa majiya k'arfi da duk wani me kishin kasa da duk wani me kishin kansa ina kira da babbar murya cewa in dai akaina kuke wannan zanga-zanga da ta hankalin Wanda basu ji ba basu gani ba, to maza Ku janye bana buk'atar haka ni Amjadu!! Nafi bukatar zaman lafiya a garin kano, saboda haka ina kira a gare Ku Ku aje makaman ku mu fuskanci abunda yake ga banmu ina me tabbatar muku da cewa ko yanzu kun tauna tsakuwa domin aya taji tsoro, shi Wanda kuke yin abun dominsa na tabbatar yanzu yana can hankalin sa a tashe, hausawa suka ce ruwa cikin cokali ya ishi me hankali yayi wanka tsalla d'aya tak!!! Za kayi ka fad'a rijiya amma sai kayi dubu baka futo ba.......Daga k'arshe nake muku albishiri da cewar duk wani Dan kasuwa da yake jin takaicin abunda ya faru to Ku kwantar da hankalin Ku sati guda yayi yawa gurin kara k'irkirar muku sabon Company me zan kansa wannan karon abunda company na na baya baya kawo muku to wannan sabon zai kawo muku samfura kaya kan farashi me sauk'i........Ni ne naku *Amjadu Abul Abbas Mai nasara!!!!!!!!*

!Yana gama maganar shi ya mik'e da sauri! Ya bar gurin d'an jarida yayi saurin nad'e kayansa yana k'okarin tafiya. Nan doh-doh ya umareshi da ya tsaya kar ya tafi. Amjadu ya futo da kud'in cikin wata farar takarda ya mik'a masa, ya karb'a yana godiya sosai da sosai sannan ya tafi.

Cikin gidan ya koma a gurguje yayi ya wanka ya futo yana goge jikinsa wani mutsiya cin yadi ya dauko piltex me mugun kyau da tsada gashi cotton bashi da nauyi ko kad'an kamar net haka yake kalar shi darkblue!! Sai yayi amfani da singilet fara tas!! Ya dora rigar akai kana ganin hasken singilet din, shi kansa d'inki abun kallo ne, ya gaji da had'uwa sosai ya tsaya gaban mirror yana gyra links din hannun rigar ya taje sumar sa tare da sanya mata maya mayai sai shek'i take. Mugun turaran shi ya d'auka ya feshe jikinshi, hula irin ta hausawa sam! Bata dame shi shiyasa bashi da ita ko guda d'aya suma kayan hausawa din yana d'inka su ne domin amfanin wata rana kamar zuwa d'aurin aure gaisuwar mutuwa ko shiga cikin wani babban taro amma Sam! A tsarin sa babu manyan kaya. *Ni ko nace *Amjadu da kasan yanda kayan hausawa suke maka kyau da ka dinga sakawa oh! Dama dai zaka sanya hula damanga nasan ba k'aramin kyau zaka yi ba, hummm!! Kuna ina ne mutanan Amjadu ya kuka hasko mutumin NAKU cikin manyan kaya😄👌🏻 nima na dan gwala masa domin na k'yasa😉🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀*


Wani helf cover naga yana sanya wa a k'afar shi fara Tass! Da ita kafa kamar bata namiji ba, ga wani ya tsunsa gashi sun bi sun kwanta abun sha'awa takalimn blue ne amma sky ya d'aura agogon shi Rolex mai mugun tsada. Cike da karsashi da jarumta ya futo , suna tsaye bakin kofa suka rufa masa baya. Rbow ya bude masa mota ya shiga suka futa daga gidan.


********

Take tashar express redio ta saki muryar Amjadu a gari, gari ya d'auka dattawa wadanda sukan sa meye duniya suke fadin "Yaron nan mai hankali ne da sanin ya kamata gashi dai karami ne me k'ananun shekaru amma yana aiki irin na manya ya iya lafuza masu kyau abunda ya kamata ace gomnati ita zata tsawayar ta kasayi shi ya futo yanayi tabbas wannan yaron zai dace da zama shugan kasa kuma shugaban al'umma domin irinsu ake so masu sanin ya kamata"!!!!........ Tofaaa!! Muna zaune muna zancan Yaya Aminu ya shigo da sauri hannunsa rike da wayarsa yana fad'in Umma kinji kalaman Young millionaire ko kai!!!! Gaskiya guy nan Dan aljanna ne wallahi." Umma ta karb'i wayar tana sauraron muryar Amjadu fuskar ta cike da farin ciki. bayan ta gama saurara tace." Allah yayi masa albarka kuma ya bashi mace ta gari wannan yaron sai naji ya shiga raina sosai." Yaya Aminu ya futa da sauri yana fad'in "Bari in mai da wa Garba wayarsa . Jiki a mutukar sanyaye na mike salau-salau na shige kuryan dakin Umammu na haye gado tare da rintse idona gabana na fad'uwa tun da Naji muryarsa na rasa kuzarina narasa wace irin masifa ce wannan.







**
Babu inda suka yi wa tsinke sai Company nan ya tarar da Aiki yayi sauki domin duk abun futo da matattatun kayan da suke ciki gami da na'urorin da suka samu matsala matasa majiya k'arfi suna ta aiki, gaskiya ya yabawa korarin su da kuma kaunar da suke masa, tsaye yayi a harabar gurin hannunshi goye a baya yana nazari, abun mamaki sai ga 'yan jarida sun yi masa caaaaa! A ka dama shi suke jira ya zo.


A nutse ya kalle su. Shi dariya masa suke bashi yace." To yanzu me kuke so nace wai." ? Daya daga cikinsu yace." Ranka ya Dade kace mutane su janye zanga-zanga da sukeyi shine muke Neman Karin baya ni."
Sosa kansa yayi ya saki wani killer smile wanda shi kadai ne tasan ma'anar sa yace."duk wani bayani da zan muku yanzu bazai gamshe Ku b, so yanzu dai abunda zance shine, duk wani mubukaci yana iya zuwa wannan company ya dauki duk abunda ya ke so na abunda akayi asara saboda ina so in fara aiki a gurin." Daga haka yaja bakinsa yayi shiru . aikuwa sun samu abun ya ya tawa atake suka fara sanarwa kafin kace kwabo zance ya baza gari mutane suka fara tururuwar tafiya domin su kwashi garab'asa







*27/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*





*Mallakar_BINTA UMAR*





*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA*.


*31*




Muna shirin cin abunci na rana sai ga aunt Hauwa ta shigo da sallama a bakinta. Muka amsa tare da yi mata sannu da zuwa, Umma na kicin tana rabon abunci tace" ke kuma daga ina kike ana rigima a gari kika futo."? Aunt hauwa na dariya tace. "Wallahi Umma daga gida nake ina gidana ina nan si babu nisa." Umma tayi shiru bata ce komai ba. Nace "aunt Hauwa ina Islam take."?
" Tana gidan Maman fa'iza na barta, saboda cikin jama'a zamu shiga." Nace." Aunt Hauwa ina zakije gari babu lafiya. " tace." Bonanza zan je in kwasa a kyauta kuyi maza Ku gama ci mu tafi don Allah kar a kwashe kayan." Umma tace." Wai ina zaku ne."? Aunt tace" Umma duk abunda ke faruwa baku sani ba."? Umma tace" sai kin fada mana yanzu."

Aunt hauwa tace." Garab'asa ga me rabo Umma kinsan anyi gobara a wannan company Dana ke baki labari ko." Umma tace"eh mana ai tun dazu muke cikin jimami da alhini." Aunt Hauwa ta cigaba da cewa"yanzu ya bada damar duk wasu kaya na ciki aje a kwashe su zai fara aikin gurin shine fa na wanko kafata in je in kwaso garab'asa." Girgiza kai Umma tayi tace." Ke kam ban San inda zaki kai kudi ba wallahi!" Dariya mukayi ni da Mimi aunt ta hau zaginmu tare da fadin " in baku zuwa inayi tafiya ta wallahi kuma duk wacce taga Abu a gurina tace tana so ubanta zanci" cikin dariya nace" zamu je Wallahi ko Dan mu bawa idonmu abunci, ko Mimi"? Daga kai tayi tana dariya aunt tace." To maza Ku tashi mu ganshi omin ban yarda ma Ku tsaya wani Wanka da kwalliya ba." Zare ido nayi nace." Gaskiya sai nayi Wanka dube ni fa, sai maiko nake. " mik'ewa tayi da sauri tana kallon Mimi tace "tashi mu tafi Mimi" ta mike da saurin ta! Nima na mike dakinmu muka shiga muka d'auka zurma-zurman hijabai muka futo, Umma tace"tafiya zakuyi baza bari Ku ci abunci ba" aunt tace" Umma in mun dawo maci" tayi gaba da sauri!

Tsayawa nayi bakin kicin din nace." Umma bamu kud'in ankon sai mu biya kasuwar kinga mun huta ma." Mik'ewa tayi ta shiga daki minti biyu ta futo da kudi a hannunta tana lissafawa dubu goma sha bakwai ne tace." Akwai kudi hannun auntnku ta cika muku." Na karb'a da sauri ina fadin" sai mun dawo Umma" tace"Allah ya kiyaye kar kuyi dare kun jiko" nace" insha Allahu Umma.


Can nesa na hango Aunt Hauwa da Mimi suna tafiya kafin in karasa hat sun tarar mana me a dai-dai muka shiga da sauri aunty cewa take" yayi sauri sauri" aikuwa ya fafari mashin kamar zai tashi damu sama.


Wai!!!!!!!!! Cunkus!! Kenan tunda muka sauka daga babur nake hango dandazon mutane bakin wangameman gete din suna turereniyar shiga gurin sai buge-buge ake maza da mata.
Aunty Hauwa nake kallo dake k'okarin tsalla titi nace." Aunt Hauwa tana ina zamu kutsa mu shiga cikin jama'ar nan."? Hararata tayi tace." Ta inda kowa yake shiga muma tanan zamu shiga." Kallonta nayi cike da mamaki nace." Ni kam wallahi bazan shiga a dauje ni a banza ba bayan haka kuma guri duk ya cika da garada maza daga ganin su za suyi tsamun hammata! Takaicina bai bar aunt tace komai ba ta kama hannun Mimi suka tsallaka titi suka barni tsaye a gurin. Ina kallonsu suna ta kutsawa cikin mutane har na daina han go su. Mintuna ashirin ina tsaye a bakin titi rana sai dukan fuskata take ga uwar yunwa dake sasakar cikina, tuni goshina ya soma tsatstsafo da gumi na fara jin jiri. K'okarin tsallaka titi nake in samu wani guri in zauna in jira su domin ni kam bazan shiga cikin wannan wahalar ba." Gefen wata bishi na zauna ina kallon yanda jama'a suke futo da kaya a daure wasu na shiga wasu na futowa. Da sauri na mike tsaye ganin wata budurwa ta futo hannunta rike da wani dogon abu tana ja da k'arfi k'ura idona nayi sosai sai naga irin material dinmu ne sak!! Na anko har kalar bandir guda ta samo a ciki 'yan uwanta sun biyo ta yuuuuuuuu! Da sauri na k'arasa gurinsu ina mik'a kaina domin in gani sai naga Sam! Bai samu matsala ba illah jik'ewa da yayi da kuma bak'in da ya fara kama jikinsa Dan ma kalarshi me haske ne, amma Sam bai kone ba." Sai murna sukeyi suna kasafi tun basu je gida ba, sai naji kamar in ce musu su yan karmana domin komai abunsu yayi musu yawa Dole su bawa wani.
Zuciyata tace min kema ki shiga ki gani ko Allah zai sa ki samu kin ga kud'in Umma sun huta, kun samu kud'in siyan takalma da haka, aikuwa ban tsaya tunani ba na durfafi kofar shiga,INA addu'ar Allah yasa na samu nima ko Mimi ta samo mana.

Daf! Da zan shiga ciki. Na hango rambow yana buge mutane dake kan hanya tare da fadin" tunda dai magana ta fatar baki batai muku ba to bari a gwada muku k'arfi da bulala duk idon Ku ya rufe, ana ta magana tun d'azu Ku bada hanya za a wuce kun ki Ku bayar."
Aikuwa sai mutane suka fara bud'e hanya cike da tsoro ganin babu Imani a don rambow.
Kafin in ankara na hango shi ya tawo cikin yanayin tafiyar sa ta jaruman maza doh-doh a bayansa da wasu 'yan jarida guda uku masu mugun nacin tsiya sunk'i tafiya. Neman gurin b'oya nake duk na gigice, da ganinshi Sam! Na tsani raini, nan take na fara Dana sanin zuwana gurin , bayana na waiwaye babu gurin b'uya mutane ne cukunsu suna Neman bangaje ni in fad'i saboda son ganin shi, 'yan matan dake gurin kuwa kamar su shid'e dan dad'i sai kara zura kai sukeyi tun kafin ya k'araso gurin ya hautsine da ihu!! Kowa na fad'ar albarka cin bakinsa akan sa,, nayi diri-diri dani gashi dai hanya ta rabu biyu gashi ina kusa da gete, daf da zai k'araso na sunkuyar da kaina kasa cike da takaici nake bin kojalallan hijabin jikina da kallo duk ya kode Allah ya isa nayiwa aunt Hauwa.

Dai-dai saiti na wani Dan jarida ya tsaida shi dole ya tsaya yana bashi amsa dai-dai da abunda ya tambaye shi.

Dan jaridar yace."* Young millionaire muna son mun san cewar yanda kake da masoya gaba da baya shin kana sha'awar siyasa ko kuwa domin ga dukkanin alamu matasa da dattawa na mutukar kaunarka kuma kai ma zakayi kyau da mulki domin anfi bukatar jajirtattu irin Ku.." Wannan maganar tasa ya tsaya yana basu amsa kamar haka.

*Sam!sam bana sha'awar siyasa bani da ra'ayin ta domin babu komai a cikinta sai zubewar mutumci bayan haka kuma ka dauki alk'awari ka kasa cikawa bana sha'awar mulki ko wane iri ne shine magana ta* gurin ya hautsine da sowa matasa na fadin "Mu muna sonka kuma zamu tsaya maka lokacin zab'e." Abun mamaki har 'yan matan dake gurin ma ihu suke yi cike da rashin kamun kai. Takaici yasa na kasa dago kai na kalle su, Allah-Allah nake ya bar gurin. To shima nashi b'angaran haka ne lallai ya yarda da aikin Jarida su ne suke tsokalowa mutum tsuliyar doh-doh yana zaman zaman sa zasu jawo masa wata uwa Siyasa sun ki su k'yale shi sai tambayar kwakwa suke masa..........Dama abunda suke so su ji kenan daga bakinsa don haka sai suka k'yale shi. Gani ya kusanto inda nake tsaye yasa na kara sauke kaina kasa kamar wata muna fuka, ya karaso cike da jarumanta yana dagawa mutane hannu fuskarsa a sake, take sosai. Wani matashin saurayin ne majiyin k'arfi ya ingiza ni gaba duk a. K'okarin shi na lallai sai Amjadu ya ganshi
Saura kad'an kaina ya daki k'irjinsa nayi saurin rik'e gefan rigar shi Dan kar hakan ta kasance, gabana ya dunga bugawa fatt!!!fatt!! Kasa d'ago kaina nayi i n kale shi domin nasan k'aryar b'oye b'oye ta kare, Allah ya Isa kwai nake wa saurayin nan................ Gefen fuskarta ya kalla ya gane ta, mamaki fal! Cikin zuciyarsa me ya kawo ta gurin nan cikin garadan maza don tashi kamun kai...Fuska!! Yayi kamar bai tab'a ganin ta ba ya mugun had'e fuskarsa tam!! Ya wuce abunsa! Ya ransa na binshi a baya, jama'a sai a sauka lafiya suke masa.

Zama yayi cikin motar zuciyarsa babu dad'i, ya kalli Rambow murya a sama yace"waccan yarinyar me ya kawo ta gurin nan.?" Rbow ya diririce! Ganin yanda ogan nasa ya tsare shi da ido! Yace." Boss myebe tazo itama ta samu rabonta ne." Cike da taikaci yace." Jeka zo min da ita." Rambow ya tafi da sauri! Dube-dube kawai yake a gurin bai ganta ba, ciki ya shiga nanma ya dunga ware ido cikin jama'a babu ita, ciki ya shiga sosai yana dubawa.

Ni ko na shiga ciki sosai ina Neman su auntn Hauwa sun bace min cikin mutane, nan cike da takaici da haushi na futo daga wani sako inda naga wasu mata sun taro a gurin suna jidar kaya, hanyar futa na nufa raina a dugunzume ! Ina jin takaicin kallon banzan da guy nan yayi ya ma nuna kamar be sanni ba lallai ma!! Ga takaicin su aunt Hauwa ya hana ni magana. Kawai naga an tari gabana. Ina daga kaina muka hada ido da Rambow naji faduwar gaba, amma dake ina da taurin rai! Nace." Meye haka." Yace." Boss ne Yace." Kizo." Harararsa nayi nace "ni matsa don Allah 'yan uwana nake nema mu tafi gida." Rbow yace." Yace in kiyi gaddama to in daukoki aka in kai masa ke.."
[10/28, 10:35 AM] .: Shek'e ke na kalle shi na sha kunu mutuk'a nace." Bisimillah sai ka d'aukar masa ni ka kai masa wallahi idan baka matsa min daga nan ba zan maka ihun kwarto in tonawa uban gidan naka asiri a gaban bainar jama'ar da suke ganin mutumcin sa." Ganin yanda nake zare ido ne yasa rambow Ciro wayarsa ina jinsa yana fadin" Boss gatanan tana gadda had'e da surutai." Ban ji me ya ce ba, kawai naga rbow ya mik'o min wayar. A banza ce na kalle shi shi da wayar na watsar tafiya na fara yi, rambow ya biyo ni a baya, ganin rbow ya nufo kofar futa ne yasa jama'ar dake kan hanya suka bud'e hanya na wuce huff!!! Da sauri na b'uya bayan wata mata, aikuwa yaron ta dake goye a bayanta ya kwala ihu ta juyo da sauri tana k'okarin sauke shi, wannan ya bawa Rambo damar gani na. Tsaki nayi na futo daga bayan matar domin bana so jama'ar dake gurin su fuskanci wani Abu,kawai sai nayi gaba, to dake suma hankalinsa na kan duba kaya Sam! Babu Wanda ya damu dani.

Tunda ta doso bakin titin yake kallonta yaga fuskarta sai shaining take ta wani kara bak'i. Tsaki yaja cikin zuciyarsa yace." Saboda rashin abinyi ta futo daga gida sai kace korarriya ko 'yar gudun hijira. Daba Dan yayi mata kyakyawan sani ba Sam ba zai ce ita CE ba. Yana kallon rambow nayi mata magana ta share

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login