Showing 51001 words to 54000 words out of 67868 words

Chapter 18 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15511

shi. A fili yace "dama irinku munana kun fi wulakanci.

Asma'u kuwa kai tsaye titi ta nufa ta fara tafiya domin yanzu hankalinta yayi Gida ta nemi su aunt Hauwa ta rasa ga Uwar yunwa na damunta gefe guda kuma matsanancin tsoron rbow ya fara shigar ta ganin da tayi yana bin ta duk inda ta sanya k'afar ta sai kace tsohon maye titi ta mik'a sosai tana Neman a dai-dai ta sahu. Tsoro take kar mutane sum ganta da rambow din.


Umarni ya bawa doh-doh kan ya ja motar a hankali ya fara Jan motar har suka iso daf! Da ita, sauke gilashin motar yayi . gabana ya fad'i nayi saurin kauda kaina gami da kara sauri!!! Rbow ya tari gabana cike da b'acin rai! Yace
" kawai ki bi umarni shine mutumci ki domin duk Babur din da kika tsayar baza mu barshi ya d'auke ki ba, kije kiji me oga zai fada miki."



Babu yanda na iya haka na koma baya fuskata kirne....... Na tsaya gaban motar INA kallonsa gami da fadin "gani" girgiza Kai yayi fuskarsa a had'e yace." Shiga mota mu tafi."

Shiga mota mu tafi." Na maimamata maganar da yayi a fili cikin sigar tambaya.?
Kai ya gyda min yana wani lumshe min mutsiyatan idanunsa masu dafi.! Kai tsaye! Nace" ina zaka kaini in na shiga motar taka."? Kallona ya danyi a fakaice yace." Gidanku. Naga rana tayi kingaji ga alamu nan sun nuna fuskar ki sai maiko take sai kace an toya mankuli.
Da sauri! Sanya gefan hijab dina na hau gogewa ina zabga masa muguwar harara. Murmushi naga yayi ya Dan kanne min ido daya cike da iya shege! Kauda kaina nayi cike da takaici nayi gaba da sauri!! Hannusa ya zuro ta tagar motar da k'arfi ya rike min gefan hijab dina, yana fad'in " yarinya za'a taimake ta tana k'i saboda tsabar gaddama idan baki shigo ba zan zo in d'auke ki a ka". Yanda ya fad'i maganar yasa na juyo ina kallonsa a fusace!!! Nace "Sakar min hijabi na." Shan kunu ! Yayi sosai ya kalli rbow yana masa magana da ido! Tsorata nayi ganin rambow yayo kaina gadan-gadan, da sauri na bude mota na shiga! Gefe naga ya matsa yana d'an ya mutse fuskarsa bai ce komai ba Rambow ya maida murfin ya rufe ya zagaya kusa da doh-doh ya zauna sannan muka tafi.


A hankali naji yace. " Rambow mik'o min turaran k'amshin nan." Wani durmeman turare rbow ya miko masa cikin kwalinsa ya bude ya hau fesawa cikin motar ya dawo kaina yana min feshi, saurin kauda kaina nayi ina kare fuskata, lokaci kankani na fara atishawa, sai da motar ta d'umame da kamshi sannan a maida turaran cikin kwalinsa.

Yanzu na gane dalilinsa na fesa turare cikin motar wato yana nufin wari nake kome? Aikuwa kafin in gama tunani na naji shi yana fadin." Duk kin sauya min k'amshin motar da warin rana 'yan mata masu daraja." Shiru kamar ruwa ya cinye ni, ji nake kamar in d'aura hannu aka in ta kurma ihu! Ko nasamu sassauci a zuciyata nace ban tab'a ganin Mara mutumci ba irin guy nan wallahi.

*Ni ko nace Ashe babu dad'i Asma'u ita Hafsa ba mutum bace kenan😄*


Kafin in gama tunani na naji shi yana fad'in" muje gida ki dauki a jiyar ki dama Neman ki nake." Kallonsa nayi da idona da ya fara ciko da kwallah nace" wace ajiyr ? Kaga malam ka kaini gida kamar yanda kace cikar mutum rike alkawari." Murmushin gefan baki yayi na kauda kaina ganin yanda yayi wani bala'in kyau kullum kara mishi kyau ake da kwarjini yadin jikinsa yayi masa bala'in kyau!!! Yace." Kin manta ne kawai amma muje zan nuna miki ko meye? Nace." Babu inda zanje ni."

"owk wai ma me ya kawo ki gurinan ne kina a matsayin mace me daraja kin zo kina bugun kirji da gogayya da maza wannan shine darajar."? Ya fada cikin sigar tambaya gashi ya wani sha kunu!
Rashin abun cewa ne yasa nayi shiru ina sadda kaina kasa nasan dai wannan tambayar da yake min ta rainin hankali ce tunda dai ya san ko meye ya kawo ni........."Uhum ke nake sauraro."? Yafad'a cikin wani irin hosky voice, ji nayi jikina ya soma rawa muryar da yayi amfani da ita tayi bala'in tasiri a gare ni.... Shiru nayi kawai yace." Ok na fahimta." Yanda ya fad'i maganar yasa na d'ago Kai ina kallonshi cike da jin haushi nace" kar kayi tunanin muma munzo ne domin mu d'ebi sharar company nin ka, ko d'aya hanya ce ta biyo damu ni da 'yan uwana." Na k'arashe maganar a daburce!! Wani kallo yayi min kana ganin kallon kasan na iskan ci ne a hankali yace." Allah ko."? Nace." K'warai kuwa domin ni banzo nan domin in samu sutturar sawa a jikina ba tunda ina dasu." Munafukin murmushi yayi yace." Shiyasa naga kin dage kina gogayya da garada kina turmutsawa cikin jama'a domin ki shiga to me zaki shiga kiyi uhummmmm."!!!!!! Wasu tagwayen hawaye ne suke k'okarin tsinke min.sai na aro dauriya da jarumta na kalle shi had'e da kankance idona nace." Eh hakane to yanzu ai sai ka duba ka gani ko na d'auko wani Abu da na shiga ciki. Ma 'yan uwana nake nema mu tafi gid............. Katse ni yayi ta hanyar fad'in" wannan duk preetandig din da kike bashi da amfani ni dai nasan duk Wanda yazo gurina to akwai abunda ya kawo shi." Da sauri na bude handbag dita na Ciro kud'in ankon mu cikin gadara nace." Kaga kudinmu nan yanzu haka kasuwa zamu shiga muyi siyayyar kayan sawarmu babu abunda kayan ka zasuyi mana." Kud'in ya wafce!! Daga hannuna." Na kalle shi a tsorace! Cikin aljuhu ya zura. Nace "me kake nufi"? Ba tare da ya kalle ni ba yace." Nima Dan kasuwa ne bayan haka kuma dama na karye makiya sun taso ni a gaba ina Neman jari ki taimaka ki bar min su." Nasan Neman magana yake kawai sai naja bakina nayi shiru.

Shima shiru yayi bai sake cewa komai ba, minti biyar a tsakani wayarsa ta fara k'ara, d'auka yayi cike da karsashi yayi sallama, naji yana fad'in"Kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta me citta burinku ya cika." Banji abunda yake ce masa, sai dai ganin da nayi ya zabura!!! Had'e da dukan glass din motar da hannunsa yace." Da kai da shi me girma governor dukanin Ku a tafin hannuna kuke wallahi akawai ranar tonan asiri. Kuma Ku zuba ido nan da sati guda kuga abunda zai faru."

Yana gama maganar shi ya kashe wayar gaba daya yana wani irin huci!
Kallonshi nayi a sace sai naga fuskarsa a had'e kamar bai tab'a dariya ba, kauda kaina nayi kurrum ina sak'e -sak'e a zuciyata a game dashi.

Shiru motar sai gudu take zubawa kan kwalta babu Wanda yayi magana, a hankali naji yace." Doh-doh juya da motar nan muje Mudansir and brothers dake Sharad'a kwanar ganduje." Da sauri doh-doh ya juya motar yana fadin "Yes sir" ni dai shiru kawai nayi ina bin titi da kallo har muka Isa make kenan gurin inda naga manya manya motoci a fake a gurin had'e da had'addan 'yan mata masu aji da waye wa wasu na shiga wasu na futowa.

Parking yayi gurin da aka tana da ya futo da sauri had'e da budewa oganshi motar ya futo fuskar nan kamar hadari ya kalle ni cike da bada umarni yace." Futo mu shiga ciki ji zab'i duk abunda yayi miki."

Gabana ya fad'i! Na hau duba jikina cike da tsarguwa. Shima kallona yake yi minti biyu yace." Ki futo mana ai naji dad'i da kika sanyo wannan hijabin domin ya kara miki masifar muni nasan babu Wanda zakiyi wa kwarjini." Hararsa nayi tare da cewa." Ce maka akayi ina bukatar wani Abu a gurin nan." Girgiza kai yayi yace." Baki fada ba ni nayi niyar siya miki ai nasan kin fi k'arfin su Big girl.""""" Yanda ya fad'i maganar a tsaye yasa na gane shagub'e yayi min. Cike da takaici na bude motar na futo duk sai na tsargu da kaina sai gyara hijab nake ina goge fuskata cikin wayancewa.

Gaba yayi cikin takunshi na jarumai na bi bayansa kamar munafuka, su rbow suka rufa mana baya.tunda muka doso kofar shiga mutane sukayi mana chaaaa!! Da ido sosai mussaman 'yan Matan dake gurin kai har da Matan aure ma, ma'aikatan gurin sai kwasar gaisuwa a gurinsa, yana amsawa ta hanyar daga masu hannu, ganin yanda 'yan Matan suke kallonsa ne ya bani haushi wasu kuma sai watsa min kallon kyama suke yi cike da raini da takaicin ganinmu tare dashi, sunkuyar da kaina nayi a zuciyata nace"Allah yasa dai kar jama'ar dake gurinan suma suyi min kallon 'yar gudun hijira.....













*28/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*




*32*





Masu tsaron kofar ne suka mik'e tsaye cike da girma mawa suke gaishe shi ya amsa a nutse, had.e da hawa stepe domin shiga ciki bayansa nake bi kamar munafuka, muka shiga, da sauri rambow ya d'auko masa wata lafiyyayer kujera ya zauna yana d'an nazarin gurin a nutse yace." Ku shiga da ita ciki duk abunda take so ta d'auka." Rambow yace." OK sir." Suka yi gaba ni kuma na tsaya, so nake mu hada ido dashi ya k'i ya kalleni har yanzu ina jin ciwon rashin mutum cin da yayi min a mota, na fi minti uku a tsaye bai ce min komai ba, nace" bani kudina ." ko kallo ban ishe ba. Ya d'auko wayarsa yana dubawa, k'aramin tsaki naja nabi bayan su Rambow ..... Shi kuwa Amjadu a tsarge yake zaune s gurin yasan dama dole haka zata kasance dashi a rayuwarsa ya tsani kallo wallahi bai San me yasa ba mata suke damunshi da kallon tsiya, tsaki yayi ya mik'e da sassarfa ya futa daga gurin, kai tsaye mota ya nufa

Yana barin gurin jama'a suka fara surutu wasu 'yan mata dake gefena naji suna fad'in" Ikon Allah ko meye alak'ar young millionaire da wannan 'yar talakawan dube ta don Allah wata mummuna da ita."

Ta gefanta tace." Kin San guy fa yana da tausayi da tausayawa talaka mybe kawai tausayi ta bashi ganin bata da sutturar arziki yasa ya kawo ta ta zab'a amma nasan yanda yake da kyau uwa uba dukiya babu abunda zai ci da wannan abar dube ta fa ki gani kamar kwancan hauka."
[10/28, 5:44 PM] .: Wani k'ululun bak'in ciki ne yazo ya tokare min a mak'ogwaro na,wai me 'yan mata suka d'auki mutumin nan ? Ya ilahi sai kace shi kad'ai ne namiji a duniyar nan da har suke wannan maganganun, raina a dugunzume na isa inda suke, wacce tayi maganar na nuna da hannuna cikin kaushin murya nace." Ke ki kishaga taitayin ki, duk naji irin surutun da kuke a kaina to bari kuji wallahi nafi Ku iskanci idan tak'amar Ku a kano kuke to nima haka kuma ni 'yar bakin kasuwa ce karewar tashan ci dai-dai nake daku, duk muni na ban kai ki ba ke maganar banza kawai dube ki fuskar ki a k'one da bleccing. " ina huci!! Na karasa maganar. Cike da mamaki suke kallona wacce nayi wa rashin mutumci tayo kaina a fusace! Kamar zata Doke ni!! Dayar tayi saurin rik'e hannunta tana hana ta, kallon banza nayi musu nace." Tsautsayi yasa ki hannun ki ya taba jikina wallahi sai na karya shi." Dariya suka saka had'e da zare ido naji d'ayar na cewa "Kema Safiyya me zai sa ka ki tsaya fada da wannan kucakar salon ta gogo miki karzuwa talauci ne kawai yake damunta shiyasa ta zauce!!!! Suka kwashe da dariya. A zafafe! Na futar da hannuna na tsinka ma me maganar mari, ina kallon d'ayar nace" kice takk!! Kema ki samu rabon ki." Shiru sukayi cike da mamaki suke kallona,, su Rbow suka k'araso gurin da sauri suna tambayar ba'asi banza nayi musu na matsa gefe gami da duba kaya kamar gaske har yanzu ban dauki komai ba.

Ina jinsu suna fada musu abunda ya faru wacce na Mara din tana share hawaye tare da cin alwashi a kaina ko kallo bata ishe ni ba, rambow ne ya tasa su a gaba har gurin biyan kudi suka biya sai da ya tabbatar sun shiga motar su sannan ya dawo gare ni yana min hayaniya, zare masa ido nayi cike da jin haushi nace "ni nace ina bukatar kayan gurin nan da za'a kawo ni har wasu banzaye su zage ni kuma in kyalesu bazai yi wu ba, kar ka dame ni."




Cike da mamaki rambow yake bin yarinyar da kallo chaaaa!!! Gaskiya tana da tsiwa!! Babu Wanda zai yi maganin ta sai *Amjadu* gurin ya bari kawai cike da jin haushin ta


Gaba nayi ina duba kaya burina kurum in hango material irin na ankon mu in d'auka tuna ya karb'e min kudina, da k'yar na hangu irin shi nacewa yaron gurin ya d'auko da sauri ya d'auko yana warware wa nace." Yanka Mana yado goma, sha biyar,har Munnu sai ta samu. Aikuwa da sauri ya fara yankawa ya nade sosai had'e da dauko wata k'atuwar Leda ya zura ya d'auko landing din shi ya yanka shima ya sanya a Leda da ban, karb'a nayi na bar gurin na nufi gurin takalma wasu plate na hango set uku had'e da jakkunan su golden ne sai shaki suke da alama fatar da akayi su mai tsada CE, nace wa yaron dake gurin ya Ciro duk ukun aikuwa ya Ciro da sauri ya dauko wata doguwar lede me tambari sunan Mai gurin wato Mudansir and brothers ya zura su dama jakar bata da girma sosai nan ya mik'o min nace" ka biyo ni dasu a baya don bazan iya d'auka ba." Aikuwa jiki na kyarma ya mike da sauri ni kuma na nufi gurin sark'oki wasu lafiyyayun Fashion na d'aukar mana sunji stons sai k'yalli suke da walwali daga zasu ja kudi masu kyau!! Nasa yaron gurin ya ciro mana agogo uku na zallar fata multi coular, gaba nayi yaro ya biyo bayana hannunsa nike nike gurin mayafai na nufa, nan ma na duba kalar material dinmu wato purple nace ya dauko guda uku jiki na kyarma ya dauko masu mugun tsada... Daga haka kawai na kad'a kaina nayi han har futa, rambow da doh-doh suka taso daga inda suke suka biyo bayanmu ni da Dan dakona suka karb'i kayan a hannunsa,, INA futa tana kara daure fuska tamau!! Na isa gurin motar tare da tsayawa tunani nake ina yake Sam banyi tunani yana cikin motar ba tunda me bakin glass ce tintac Rambow ya bude bayan motar ya zuba kayan ya rufe da sauri ya bude murfin motar. Gabana ya fad'i ganin shi a ciki nace Ashe yana kallonmu da duk abunda muke shiga nayi ina d'auke kaina, sautin wak'ar Joy ne yake tashi a hankali me taken *Because love me* shiru nayi ina sauraran wak'ar ko wane baiti kalaman soyyaya ne, muryar Joy akwai sanyi da saka nutsuwa sai naji wani irin yanayi a jikina nayi kasak'e ina sauraron wakar......... Shiru bai ce komai ba yana kwance cikin motar idanunsa a lumshe! Na saci kallonsa kad'an.. Sai naga bakinshi yana motsi da alama wak'ar yake bi...









*28/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*





*Mallakar_BINTA UMAR*





*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*






*33*


V


Sai da motar ta fara tafiya kan kwalata sannan ya bude lumsassun idonsa yana Dan gyara zaman shi. Agogon hannun shi naga ya kalla ya Dan girgiza kansa, kallona yayi nayi saurin d'auke kaina ganin yanda idonsa yayi ja, cikin kasalalliyar murya yace." Kin samu abunda kike so." Banza nayi dashi kamar ban San yana gurin ba." A hankali yace." Mata masu daraja ina magana fa." Cike da takaici na kalle shi had'e da cewa"tunda ka karb'e min kudina ai dole in dauki abun kudina kuma dole ka biyasu." Babu yabo babu fallasa yace. " ni ko duka kayan gurin kika ce kina so sai in siya miki mutukar zaki min Abu daya." Ya karashe maganr a hankali saboda su Rbow. A hangunce na kalle shi muka hada ido a karo na biyu, gani nayi idonsa ya kankamce ba kamar d'azu ba, nace" wane Abu ne." Da idon shi ya nuna bakina." Na kasa fahimtar sa, yace." Kin gane ko"? Girgiza kai nayi cike da tsarguwa ganin yanda ya kurawa fuskata ido kome yake kallo oho!! Hannu ya kawo zai tab'a leb'ena nayi saurin gocewa ina watsa masa harara. Takure jikina nayi jikin kujera gabana na fad'uwa domin yanzu na fahimci abunda yake nufi.

Shima fuska! Yayi kamar bashi ba, ya dauko wayarsa yana latsawa ammafa fuskar nan tasa babu dad'i
Daf da zamu shiga layin mu nace "a sauke ni anan ya Isa." Umarni ya bawa doh-doh yayo parking yana tsayawa na soma k'okarin bude motar da sauri ya rike min hannuna. Cike da bada umarni yace." Doh-doh Ku bamu guri zamuyi magana." Aikuwa suka futa daga motar da sauri. Ni kuwa ai tuni na fara rawar disco jin yanda yake murzamin hannuna, so nake ince ya sake ni na kasa fad'i

Fuskarta ya juyo da tafukan hannunsa ya kurawa bakina ido a hankali yace." Ki zo muje gida ki dauki pant dinki kinji!!!! Na fuzge fuskarta da sauri ina addu'a kar Allah ya bashi nasara a kaina, yace." Meye haka kike ni babu abunda zan miki kawai ina so in rage damuwar da take damuna ne." Muryarta na rawa nace"kaji tsoran Allah Wanda ya hallice ka ka bude min kofa na futa.". Sosa sumar shi yayi yana min munafukin kallo yace." Zan bude miki yanzu amma ki bani in sha." Na kasa fahimta me yake nufi. "Kinji!!!!!!* Yafadi maganar cikin wani irin voice tuni naji kuzari ya sare jikina ya soma sanyi,, nace " ban fahimce ka ba."? Bakina ya nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login