Showing 9001 words to 12000 words out of 67868 words
 irin muryar ya fara ambaton sunanta "Asma'u" Ke Asma'u!!!
Kamar a mafarki naji ana kiran sunana
Da sauri na mik'e zaune ina ja da baya ganin yanda yayi min rumfa, muryashi me taushi yace." Tashi ki bani guri inyi sallah."   d'auke kaina nayi daka kanshi ina Ala wadai ds tur da halinshi, ya gama aikata alfasha ya ishi mutane da sallah.
A hankali na mike na koma can gefe guda gami da takure jikina, daddumar ya daga ya karkad'eta ya mayar ya shimfid'a data, ina kallonsa ya tada sallah raka'a biyu yayi ya salle me yayi addu'oin sa sannan ya mike a nutse ya futa daga dakin.
Ajiyar zuciya na sauke zuciya ta na sake-sake akansa tabbas Akwai wani al'amari nashi dake rufe 
Jin ana kiran sallah ne yasa na mike da sauri na futa daga dakin tunda ya bud'e tsayawa nayi ina bin dank'areran falon da kallo ya had'u k'arshe fad'ar kyawunshi da tsaruwar shi bata lokaci ne ko ina tar haske  Mimi nake lalube can na hango ta cikin kujera me cin mutum daya ta mak'ure jikinta da sauri na k'arasa inda take ina kiran sunanta.
Ta bude ido a furgice tana kallona sai kuma ta fashe da kuka sosai, sauri nayi na rufe mata bakinta na kamata ta tashi, hanyar futa muka nufa.
A bude take, abun mamaki muna dosar ta kofar sai ta fara tafiya suuuuuuuuu ta rufe kanta, Jan hannun Mimi nayi da gudu muke k'okarin ture  kofar, abun nasara tuni ta rufe har tana hadawa da hannu  ihu na kurma ina matse shi. 
Mimi tace." Kinga Asma'u kiran sallah ake muje muyi alwala tun daga toilet can muyi sallah mu jira gari yayi haske."
Babu yanda na iya haka muka koma ciki Mimi ta shiga toilet ni kuma na zauna jiran futowar ta
Minti biyu da zamana sai ga Alina ta futo daga wani bedroom tana sanye da wata mutsitsiyar Riga da gajeran wando cinyoyinta duk a waje, Attachment din kanta duk ta duje. Shek'eke na kalleta naja tsaki gami da fad'in." 'Yar isakar k'arya da wofi."
Da sauri ta juyo tana kallon inda nake zaune domin Sam batayi tunanin akwai mutum a gurin ba.
Cikin jin zafin abunda nace mata tace." Wallahi Asma'u zagin da kike min ya ishe ki tun jiya kike zagina saboda tsaurin ido irin naki har kina kamani da kokawa,wallahi kinci sa'a a gaban *Amjad* ina tsoran fushinsa amma da sai nayi miki rashin mutumci kin San dai halina ko a skull bani da kyau bana barin ta kwana." Tsaye na mike nayi kanta cike da masifa da neman tashin hankali nace." Durun uwar ki Alina don Allah Ki dauki mataki kan abunda na miki ehee ni kinsan irin masifa da bala'in da kika sanya ni a ciki tsakanin jiya da yau? Kin fi kowa sanin wacece ni kin san na fiki rashin mutumci wallahi sai na rama abunda kika sa wannan Dan iskan yayi min."
Rik'e baki tayi cike da mamaki tace." *Amjad* din kike zagi Asma'u tun jiya fa naji kina aibata shi gami da zaginshi wallahi ki kuka da kanki, Dan baki San waye shi ba kuma baki San me ya taka ba bakin san d'aurin gindin da yake dashi na a kasarnan.". 
A har zuk'e nace." An zageshi din shi waye ko a gabansa ma zan zageshi ba wani abun bane idan kin Isa ki fada masa in ya shigo, ke dashi duk 'yayan iska, 'yar durun uwa kawai.'
Alina ta fusata! Iya fusata jin ina zaginta lallai baza ta lamunta ba, da gudu tayo kaina muka sark'e da kokawa sosai.
Mimi ta futo taga abunda yake faruwa kanmu tayi tana k'okarin rabamu muna bugeta sai ta koma gefe tana kallon ikon Allah.
Yana bud'e kofa yaga abunda yake faruwa, duk bamu lura da shigowar sa ba Mimi ce kawai ta lura tsabar kwarjinsa yasa ta kasa fada masa abunda ya hadamu sunkuyar da kanta kurrum tayi ya wuce ta cike da karsashi ya durfafo mu fuskarsa kamar an aiko da mala'ikan mutuwa.
Alina na mukure jikin bango tana kifta ido saboda shak'ar da nayi mata, sai kakari take tana k'okarin k'watar kanta ni kuma ina kara matseta tare da fadin." Nace miki ki kwaci kanki a hannuna, ni zaki yaudara ki sa muzo birthday din ki, ki jefa mu halin masifa eheeee! Kin San irin jarfar da kika sanya ni a ciki tsakanin jiya da yau, bayan wannan ma me kike so muce idan mun koma gida. Alina sai na dauki fansar abunda kika mun dake d'an Iska *Amjad* da kike damuna da shi."
Hannunsa guda ya sanya ya funcike ni daga jikin Alina ya yarfar dani guri guda, yana wani irin huci!! Da mugun gudu na mike na kara komawa kan Alina, yayi saurin tare ni da gangar jikinsa, ya matse a bango!! Muka fara kallon kallo, lumsassun idonsa ya zuba min sunyi ja saboda b'acin rai. babu walwala ko ta kwabo a tare dashi.
Kirjina ya matse da nawa kirjin sosai ya zura hannunsa ta bayana yana shafo mazaunai na cikin wani irin dan iskan salo.
Numfashina ya dunga futa sama-sama lokaci kankani na susuce   yayi lakwas duk kuzarin da nake ji dashi ya gudu, sai naji gwiwa ta tayi sanyi k'alau ina nema in zube a gurin.
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA. 
*15*
 Saki na yayi na zube a gurin, ya tsaya kaina yana sakin wani muskilin murmushi tare da shafa kwantaccan gashin dake fuskar shi.
Saurin kauda kaina nayi da kansa leb'ena sai rawa yake ni kadai nasan halin da nake ciki a lokacin.
Murza hannunsa yayi kamar yarda ya saba ya kauce da kaina, a hankali ya tsugana kusa da Alina dake nishin wahala ya dagota tare da rungume kungunta suka nufi bedroom d'insa.
Kallo na bisu dashi yayin da naji wani irin k'aton Abu yazo ya tokare min a mak'ogaro ganin yanda hannunshi yake tab'a mazaunai Alina.
Mimi ta k'araso inda nake takure tace." Asma'u ina hadaki da girman Allah da Annabi ki iya bakin ki kibari mu rabu da guy nan lafiya duk wannan abun da kikeyi bakya nasara akansa, wahalar da kanki kike."
Cikin jin zafin Abunda tace." Nace." Ni kiyi min shiru don Allah don dai ke ba ke akaiwa abunda akaimin ba shiyasa kike fadin haka."
Rike baki Mimi tayi tace." Wallahi abunda ya faru dake ji nake tamkar ni akayi wa dadin da naji kawai yanda naga kin futo daga dakin k'alau dake wannan yana nuna min cewar baiyi raping din ki ba."
Kaina na sunkuyar kasa cikin zuciyata nace." Ke kike maganar raping Mimi ni kadai nasan halin da ya sanya ni tsakanin jiya da yau.
Mimi ta zauna tana rarrashina cewar don Allah ko ya futo kar in kara tanka masa kawai muyi kokari mu rabu lafiya dashi.
To nima na yarda da shawararta domin ina ganin idan ba haka ba mutumin nan zai iya sakawa na mutu saboda abunda nake ji in ya rabe ni.
Awarsu hud'u a cikin dakin sannan suka futo. Muna zaune ni da Mimi kujera guda lokacin Fleengs din da nake ji a game dashi ya rago sai abunda baza'a rasaba.
Da sauri na kauda kaina ganin yanda yayi min wani mugun kyau Sosai ya dauki wanka dress din ya mutukar yi masa kyau, yana sanye da wani bleu jinsh wanda yake gwiwoyinsa duk a fashe wanda be san tsadar shi ba sai yace yasa wando lallatace.
 Tare da wata shart me k'aramin hannu itama pink color rigar ta matse shi mussaman daga gurin hannunwansa  kayan sunyi masa cif a jiki kasan cewar sa mutum me kyawun jiki Sam babu rama a jikinsa ko ina a jiki take,da alama yana yawan motsa jikinsa.
Kasa hak'ura nayi a fakaice na kara kallon inda suke shida Alina itama tayi Wanka ta sanja sabbin kaya. Wuyanshi na kallah naga wata siriryar sark'e kamar daimond sai shek'i take  hannunshi tsaddadan agogo ne Rolex sai walwali yake, hular shi hana sallah ya juya ta ma'ana gaba ya koma baya- baya ya koma gaba.
A zuciya ta nace kyau babu kyawun hali Allah ya sawake dube shi kamar ba shine ya gama sallah da addu'oi ba amma dubi yanda yayi wata shiga sai kace arne wanda ya futo daga kudu.
Mimi ya kalla fuskar shi babu walwala yace." Ku tashi ku muje." Mimi ta mike Zumbur . yayi gaba be ko kalli inda nake ba. Nima harara na bishi da ita na mike ina gyara zaman hijab dina,gefe guda kuma ina tunanin k'aryar da zamu sharara a gida, domin ina sane na kashe wayata saboda nasan za'ayi ta damuna da kira bani da amsar bayarwa.
Muna futa bodyguard d'insa na tsaye bakin kofa duk suna sanye da bakaken kaya hannunwan su da safa bak'a kana kallon fuskarsu zaka San babu wasa.
Suka fara kawo gaisuwa gurin ogansu, kallon banza nayi musu nayi gaba Mimi ta biyo bayana Simi-simi.
Doh!-doh ne naga yazo ya wuce ni da sauri yaje ya bud'e wata arniyar mota ba irin ta jiya ba, wannan daga ni ma sabuwa ce kalar ta ruwan zuma ne gaskiya motar ta burge ni. 
Tun kafin ya k'araso saboda k'arfin hali irin nawa naje na kama murfin baya zan bude in shiga.
Wata azabbabiyar tsawa doh-doh ya buga mun fa sauri na saki murfin na m ma gefe ina zare ido.  
Cike da karsashi ya k'araso ya shiga Alina ta shiga ta zauna kusa dashi, harararta nayi ina jin wani mugun haushin ta. Doh-doh ya maida murfin ya rufe ya zaga da sauri ya shiga  Mazaunin sa.
Rambow ne ya zauna kusa dashi sai Alina sai ni Mimi ce ta k'arshe shiga.
Cike da ladabi Doh- doh yace." Boss ina muka nufa ne."?
Mimi ya d'an kalla da gefen ido yace." Wace unguwa ne."? Baki na rawa tace." Badawa ne wajan giginyu."
Yace." To kaji ko".?
"Yes sir." Doh-doh ya fada yana k'okarin futa daga gidan.
 Shiru motar babu wanda ya ce ci kanka gudu kawai take kan kwalta. Ina kallonshi a fakaice, ya makala airphone a kunnenshi sai gyad'a kai yake yana bin wak'ar da yake ji, ba daina najin muryar mawak'iyar daga bakinshi na fahimci janeefar Lopez ce.cikin wak'ar me taken *a into mamah.*  
Kalle kalle nake domin in tantace wace anguwa ne muke ciki, *Jambulo* sai yanzu na gane unguwar akwai wata friend dinmu dake unguwar mun tab'a zuwa duba mahaifin wani lokaci da yayi hatsari. Muzo dai-dai kan kwana inda wasu gungun almajirai suke zaune da 'yayansu maza da mata.
A hankali naji yace." Tsaya anan."
Doh-doh ya samu guri yayi parking.  Da sauri shadow ya futo ya bude masa kofa ya futa. Ido na bishi dashi cike da mamaki ganin yana zuwa gurin almajiran nan. Aikuwa suma suna ganinshi suka fara gyarawa 
D'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana saka musu kudi Wanda ban San adadin su nasan dai 'yan dubu-dubu ne. Duk yawansu sai da suka samu.
Cikin sauri ya dawo motar Shadow ya maida murfin ya rufe muka bar gurin.
Gaskiya ni da Mimi munyi mamaki sosai da sosai da lamarinsa  daga k'arshe muka cigaba da tunanin yadda zata bulle mana a gida.
Kallon shi nake so nayi zuciyata tana hana ni, a sace na d'ago kaina muka had'a ido dashi ta mirror wani miskilin murmushi ya Sakar min yana sosa sumar shi. Na kauda kaina INA jan k'aramin tsaki, har yanzu da akwai k'ulli a kaina dangane da Alina.
Kwanar gidanmu Mimi ta nunawa Doh-doh nayi saurin dago kaina tare da fad'in." Kai sauke mu nan ma k'arasa da k'afafun mu."
Ina da manufa ta tafad'ar haka.
A hankali motar tayi parking gefen hanya. Na kama murfin motar da sauri zan bude na kasa sai da Shadow ya futo ya bude mana, na futa ina gallah masa harara.
Ido yayi wa Shadow magana naga ya zura kansa ta window motar wani abu ya mik'o masa, yana dagowa naga kud'i daure da kyuare 'yan dubu-dubu.
Shadow ya mik'o min tare da fad'in".Gashi oga yace a baki." 
Kud'in na kalla shekeke ina sauri mubar gurin domin nasan halin 'yan unguwar mu abun magana baya yi musu wahala. 
Mimi sarki 'yan san kudi ta dinga zungurin kafad'a ta wai in karb'a
Tuni zuciya ta tafara min wasiwasi kan wannan uban kud'in da yace a bani,wato yana nufin ya biya ni kud'in iskancin da yayi min kome oho,me yasa bai bawa Mimi ba. 
A tunzure na karb'i kud'in kai tsaye gurin shi na nufa, na zura kaina ta window na motar na cire kyauran dake daure da kud'in.
Kallon juna muke ni dashi, fuskarta babu fara'a na fara zuba masa kud'in a jikinsa tare da fad'in." Wannan kud'in da ka bani basu isa su siye ni ba, baka da abunda zaka yaudare ni dashi, kasani inanan sai nayi maka illah a rayuwar ka tunda ka sake ka shiga rayuwata sai kayi daka sani wallahi."
Da mugun gudu Shadow ya kawo min duka na kifa kaina cikin motar har ina buge goshina. Da sauri na dago Shadow ya daga hannu zai kwada min mari!!!!!!!
"Shadow!!! ".
Ya fad'a cikin wata irin murya wacce ban san shi da ita ba, muryar dai tafi kama da ta Wanda yake cikin tsantsar b'acin rai."!
Shadow!! Ya sauke hannunsa yana wani irin huci!! Jikinsa sai tsuma! Yake.
Ni kuma duk na furgice  so nake kawai Shadow ya bani hanya in wuce kar wani Wanda muka sani ya futo daga cikin layin mu."
K'asa-k'asa naji yace." Shigo mota mu tafi." Shadow yayi min wani irin kallo me nuna zamu had'e dake ne watarana ya bude mota ya shiga.
Ina Kallon Alina tana kwashe masa kud'in da na baza a jikinsa sai harararmu take.
Tsaki naja na matsa gefe ina taufar da yawu.
Hannun Mimi na kama muka fara tafiya Mimi bina take simi-simi jikinta DUK yayi sanyi da abunda nake aikata wa.
*Ajiyar zuciya!* kawai yake saukewa zuciyarsa tana masa sak'e-sak'e akan yarinyar tunda yake a rayuwa babu macan da ta tab'a yi masa Abu irin Wanda yarinyar tayi masa.
 Sam baya so ya nuna mata hakikanin waye shi baya so ya nuna mata mugunta saboda shi mutum ne me tausayin talaka a duk inda yake ya lura kuma takalawa ne sosai babban abunda ya kashe masa jiki dasu jin abunda d'ayar take fada masa jiya cewar su marayu ne babu uba ya tabbata mahaifiyar su tana fama dasu, amma ya lura sai ya saita yarinyar domin abun nata yayi yawa, yanzu dai tayi na farko tayi na k'arshe kuma sun rabu domin babu ita a rayuwarsa a yanzu amma mutukar ta shigo gonar sa ko Allah zai sake had'a su a wani guri to tabbas zai nuna mata true colour d'insa sai ya gigita mata rayuwa, da wannan tunanin ya cire abunda tayi masa a ransa ya bawa Doh-doh umarnin tafiya.
Cike da tsoro muka lab'e soran wani gida nida Mimi muna shawarar wace irin k'arya zamu girbawa Umammu  in muka je gida.
*Meye Asalinsu ne*?
Asalin su shine.............
Zamu had'u dake a pege nagaba
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA. 
*16*
 Malam Sulaiman mai madara shine mahaifin Asma'u d'an Asalin garin kano unguwar k'oki a ka haife shi, su goma sha shida ne gurin iyayensu maza goma mata shida maihaifinsu da mahaifiyar su duk sun rasu  ba dadaewa ba, lokacin ma an haifi Asama'u  kasancewar dama ba wani arziki ne dasu ba yasa babu wani gado da suka bar musu 'yan uwansu mata duk sunyi aure suna gidajan mazajansu suna sana'oinsu da zaman aure to suma haka take a garesu duk suna da aure da yara ko wanne na buge bugen sa na kasuwanci da aiki yanda zai rufawa kansa asiri, kwata-kwata basu da zumumci ga junansu kowa kansa ya sani da 'yayansa  idan ba wani taro ake ba babu me ziyartar d'an uwansa  daga matan har mazan duk da cewa 'yayan mutu d'aya ne kowa harkar gabansa yake.
******
Malam Sulaiman yana aiki a company madara ta cowbell wanda yake sharad'a  dake ya jima yana aiki sai suka bashi gida a Badawa sai ya bar hayar da yake yana murna ya koma gidan kansa tare da iyalinsa.
Matar shi Mariya 'yar nan makotansu ce sukayi auran soyayya suna da yara hud'u maza biyu mata biyu  Hauwa'u itace ta farko tayi aure a giginyu kusa dasu tana da 'yarta d'aya Islam. Aminu shine na biyu yanzu haka yayi diploma da dabara yana so ya cigaba DOMIN ya samu digree babu kudi sai buge-buge yake, Asma'u itace ta uku gurin iyayen ta, ta kasance Mara jin magana me taurin kai tunda ta taso haka take da bushashiyar zuciya ko fada suke da yara bata kuka, tana tsananin kama da mahaifin ta sosai shiyasa yake mutukar kaunar ta duk abunda tayi dai-dai ne
Asma'u tana da kyau na ban mamaki da tsarin jiki me kyau b'aka ce amma ba sosai ba Sam baza a sakata a layin farare ba, tana hanji da manya ido gami da k'aramin baki, tana da yalwar gashi kanta da gira gashin idonta gazar-gazar dasu sun kawata mata ido tana manya nonowa a tsaye k'yam dasu sharp dinta ya futo sosai cikinta a dame yanayin tafiyar ta sauri-sauri  yanayin zafin ta da yanayin saurin bakinta domin wata maganar ma in ta fada mutum bazai ji ta saboda saurin bakin ta.
Mimi marainiya ce 'yar k'anwar Mariya ce Umma kenan mahaifiyar su As'amau ta d'auko ta ta shayar da ita tare da Asam'au Mimi ta girmi Asma'u da wata hud'u.babu Wanda zai ce ba Mariya ce ta haife ta ba duk abunda za tayiwa Mimi tare take musu shima Sulaiman ya rike ta amana kamar 'yar cikinsa
Yanzu haka suna da shekaru goma sha shida a duniya matakin karatu kuma sunyi saukar alk'urani me girma, b'angaran boko kuma suna ajin k'arshe a suna jarrabawar futa makarantar da sukeyi ta kudi ce sosai da sosai wan Baban Mimi shine ya tsaya musu dake lecturer ne yana da hanyoyi da dama  suna gane karatu sosai da sosai.
Alina 'yar wani hamshak'in me kud'i ne anan unguwar