Showing 24001 words to 27000 words out of 67868 words
 son wakokinsu Dan bai fiye sauraran mawakan na lokacin ba, gwara Usha da wzky yana sauraron nasu, kallon Hausa ko jin wakokin Hausa Sam bai dame shi ba, gashi dai yana jahar Kano dandalin Hausa da film din Hausa a cewar sa duk shirme suke da shashanci don in yaga Adam A zango yana Abu na nigogi Dari kwai yake masa ya wuce abun yana bashi mamaki in yaga yadda matasa suke kwaikwayonsa.
Duk sutturun shi babu namu na Hausa duka kananu ne ga wani uban gashi da yake tarawa a kanshi kunsan dai yadda bafulatanin mutum yake da kyawun gashi gami da baki to haka ma na  Amjad yake saboda tsabar gyara da yake sha gami da mayuka masu tsada har wani tattatewa yake askin shi abun kallo ne har inda ya futa ba tare da mota ba 'yan mata susucewa suke yi sai su dinga ganin kamar d'an India Wato Allu arjun DOMIN suna mutukar kama dashi, shiyasa yake wayan shiga mota ko da ko tafiyar da zaiyi ba me nisa bace , gudun kallon matan Kano Wanda yake ganin hakan tsabar k'auyanci ne da gidadanci sai kaga mace har mace ta tsaya tana kallonsa wasu ma yana cikin mota suna mota zasu dinga zuro kai suna lek'ensa tsaki kurum yake ya d'auke kansa
 Maman shi me damuwa da yanayin shigar shi tayi tai masa fada watarana in taga ya sanya siririyar sark'a a wuyansa turke shi take tace dole sai ya cire domin bazai futa da ita ba, ita ko granny dake haka ya ke kiranta tace masa bata son wannan sunan domin na arna ne yak'i ya daina saboda ya lura bata so duk sanda ya kirata da wannan sunan sai taki amsawa sai ya kirata da Innah sannan zata amsa. Cewa take ki kyaleshi dai ya cigaba da irinn wannan shigar Cikin kano sai ya rasa matar aure domin 'yan Matan kano idan ba jampa da kufta kayi musu ado dashi ba babu me auran ka nu kuma ka dawo gare ni in ce a kai kasuwa. Dariya yake duk lokacin da tayi wannan maganar sai yace." Ke an fada miki ni zan auri 'yar kano gidadawa dasu Wanda babu abunda suka iya sai kallo da ihu!  Ga Adam A zango ga Ali nuhu dama me suka sani in banda bleccing." Granny tace." Ranar da bakanuwa zata rike maka wuya yanan zuwa" tsaki kurum yake ya barta a gurin. Ganin ya tsaida sallolinsa biyar yasa Alhaji Abbas baya ta kura masa kan abunda yake yi domin sallahr Asubah bata wuce *Amjad* yana riga kowa tashi a gidan to itama Hajiya Aisha sai ta kwantar da hankalin ta.
Ko da yaje London sai Abu ya kara k'aimi saboda haduwa da yayi da turawa  masu irin ra'ayin shi harda bakaken fata ma "ya gari daban-daban, sai ya saje dasu kawai ya koma tamkar wani bature har ta kai ta kawo yana zuwa barbing saloon Wanda ya amsa sunansa ya zube kudi masu kyau! Ayi masa kitso Wanda muke kira zane manya ake masa guda shida ko biyar, ya futo abunsa babu Wanda zai kalleshi tace. Mahaifitarsa bakar fata ce KUMA ya hada jib'i da Hausa Fulani saboda yadda ya saje ya koma tamkar d'an sarauniyar Ingila.
 Shekararsa biyu a can, wata rana Dady dinshi yayi masa waya cewar zasu je Chadi ziyara, yaji ina ma yananan aje dashi yayi musu fatan dawo wa lafiya tare da cewa a mik'a masa gaisuwa gurin 'yan uwa, aikuwa haka a kayi suka shirya tsaf suka bi jirgi 1:00 pm tare da guzurinsu ga 'yan uwa Innah sai murna take da farin ciki zata ga 'yan uwanta,  daf  da zasu sauka daga jirgi Allah ya saukar da al'amarinsa i n jirgi daga sama ya samu tangard'a nan take ma'aikatan hankalinsu ya tashi suka fara kai kawao drabobin jirgin suka gigice domin son su shawo kan matsalar inahh! Duk abunda Allah ya hukunta zai faru sai ya faru duk k'okarin su na son su sauka kasa Allah bai nufa ba daga sama jirgin ya tawo a gicceye a sauka cikin wani daji take ya fara hayak'i kafin kace kwabo ya fara wuta jika Tass tass mutane suka fara k'okarin ceton ransu kofa ta rufe ga shi wuta ce kawai take ci  mutane Abu a cikin daji nan take Alhaji Abbas ya turo mahaifiyar sa ta fado kasa can gefe kanta ya bugu da bishiya suna yunk'urin futowa jirgin yayi bundiga inda wuta ta tashi gaba dayansa  cikinsu babu Wanda yayi rai sai Wanda suka futo daga ciki suma duk da haka sun kone gami da daddaujewa ga abu a daji.
Hayakin da gurin yake ne yasa hankalin jama'ar gari tashi  domin hayak'i har cikin dakunansu nan take kowa ya furfuto masu tsaron lafiyar mutane suka fuskamci daga inda hayakin yake suka nufi gurin cikin shiri
Tashin hankalin da suka gani ya dimauta su jama'ar gari sai kuka suke duk Wanda yake cikin jirgin na n ya kone kurmusu DOMIN wasu har sun zama gawayi saboda konewa take ma'akata suka fara aikin gaggawa.
Wa'yanda suka rayu aka wuce da hospital domin a dubasu sukuwa Wanda suka mutu nan aka tattarasu guri guda tare yayyafa musu ruwa aka sallace su kana aka haka rami aka bune su duka.
*Sai dai muce Allah ya jikan muslmai*
Wannan al'amari da ya faru ya zagawa ko wace kasa a fadin duniyar nan domun 'yan jarida ma daga kasashen waje sai da suka zo d'aukar rahoto inda abun ya faru. Suka je Hospital suka hira da Wanda suka rayu a ciki, kuwa harda Innah Wanda akayi hira da ita tana kuka ta fad'i duk yanda Abu ya faru tare da addu'a ga danta da matarsa kuka sosai take tana kiran *Amjadu*
 Yana can yana ta kiran wayoyin iyayen nasa a kashe tuni jikinsa ya bashi akwai matsala domin a ranar kwana yayi yana mugayyan mafarkai akansu, suna tare da abokanshi  Rafiq da Irfan Larabawa ne karatu ya hadasu sai wani bature Dan America me suna Sony kallo suke ana american film amma na nigas kwata-kwata Amjad baya jin dadin kallon yayi shiru kawai Linda ta shigo tana sanye da dogon wando tare da Riga me madauri a baya bayanta da cibiyarta duk a waje. Da turanci tace . Su kamo tashar larabai suka abun tausayi jirgi ya fad'i a Chadi gaban shi ya fad'i ya fuzge romt din a hannun Irfan ya fara k'okarin kama tasha, idonsa ne ya sauka kan Granny zaune a gadon asibiti kanta nan nade da bandeji sai kuka take tana kiran sunansa. Su Irfan hankalin su ya tashi ganin yanda ya mike tsaye a zabure yake fadin ." innallahi wainnalihi raji'un." Suka mike suma , tare da kurawa TV ido ga gawawwaki  nan ana bunne su ga jirgi a kone. Zubewa yayi kan kujera yana zubar da hawaye tare da cewa Allah ya jikanku Iyayena duk cikin turanci yake maganar Linda tq zube a gabansa tana kuka tana k'okarin rungume shi, tana bashi hakuri to suma su Tariq zama sukayi suna rarrashin sa tare da bashi hakuri. 
Ko kwana ba ayi ba ya fara shirye-shiryen tafiya domin dubo granny yana ganin yanzu ita kadai ce tayi masa saura hukumar makaranta ya sanarwa sosai suka jajanta masa. Yayi sallama da abokan shi Linda tana ji kamar ta bishi domin ta mugun sonsa a rayuwarta, haka dai suka rakashi har filin jirgi ya hau suna daga masa hannu.
 ******
Lokacin da Innah ta ganshi kukanta sai ya dawo sabo ta rungume shi tana kuka sosai tare da yiwa iyayanshi addu'a daurewa kawai yake domun baya so yayi hawaye a gabanta, ya nemi sallama daga hukumar asubitin domun yana so suka Isa can mahaifar tasu kamar yanda granny ta bukata cewar ya kaita ta gaisa da 'yan uwanta tunda Allah yasa tana da rabo ganawa dasu.
Da suka Isa "yan uwa sun koka sosai da mutuwar Alhaji Abbas DOMIN shine jigonsu ta dalilinsa matane da dama sun far fado daga kangi na talauci,  sukayi tayi masa addu'a shi da matar shi tare da fatan samun rahama gurin Ubangiji.
Satin uku suka dawo najeria inda labarin mutuwar Alhaji Abbas ya karad'e ko ina mussaman cikin kasuwanni  Alhaji Hashim me citta duniya sabuwa a fili yayi ta nuna jajansa da mutuwar amma a zuciyarsa fal take da farin ciki yana gani duk wata duniyar Alhaji Abbas zata zama mallakinsa domin sun hada kasuwanci banking su daya duk wasu shagunanan Alhaji Abbas ya kane yanzu shi yake bada ido duk ciniki da akai yana lissafi Alhaji Dan Akushi na kara tunzurasa kullum suna mak'ale da juna suna kus-kus.
Kwanaki arba'in da faruwar al'amarin Amjadu ya fara bunkice kan dukiyar mahaifinsa duk wasu kadarori gami da shagunansa sai da ya bunkito da  takkadun baking da yake ajiyar sun kai goma kowanne yana ajiya ga share iri-iri yana dasu  a wannan lokaci in ka kalle shi sai ya baka tsoro saboda yadda ya koma hero saboda rashin fara'a kullum fuskarsa a murtuke take, har gida labari yq same shi cewar gasu Alhaji citta can suna facaka da dukiyar mahaifinsa yaji haka daga bakin mutum kusan biyar, kawai ya shirya zuwa kasuwar cikin shigar k'ananun kaya yaje vest ne da wando 3Qutar wuyanshi da siriryar sark' haka kunnenshi da barma sai shek'i take ga uban kitsonshi wando ya nannade a bayanshi duk Wanda ya kalleshi a lokacin sai yace ba musulmi bane, ya dura cikin kasuwa jama'a suka dinga kallonsa wasu gani suke bature ne ko Dan India saboda Sam bai kama da baushen mutum ba, sai da sukaji Hausa a bakinsu suka tsinke da lamarinsa, d'aya daga cikin shagunan mahaifinsa ya zauna yasa aka kira masa me citta yana can sauran shagunan yana mulki da kallon yanda ake sauka kaya. Jin kira daga sama ya taso domin ya d'auka masu d'aukar kaya ne, ya zuwa idonsa yayi masa tozali da *Amjadu* gabansa ya fad'i cikin zuciyarsa yace me kuma ya dawo da yaron nan domin sun taba maganar da Alh Abbas cewa ba yanzu *Amjad* zai dawo ba sai yayi shekara hud'u daya zuciyar tace masa ki'la ya dawo ne kan mutuwar mahaifinsa, sai ya nufe shi yana da fara"a yana fadin' Yaro na ka dawo Ashe."?
 *Amjadu* ya mik'e tsaye da sauri tare da daga masa hannu fuska a murtuke yace." Duk wani Abu da kasan mallakin mahaifina ne ina bukatar ka hado ka kawo min har gida, nasan iya adadin dukiyar mahaifina dake hannunka saboda haka mutukar kana son zaman lafiya ka zare dukiyar ka domin bana bukatar ta a cikin tawa ina fatan ga gane." Mai citta ya saki baki yana kallonsa cike da mamaki tabd'ijam ai abunda bazai yiwu bane ya fada a zuciyarsa, kwantar da muryarsa yayi zai rarrashe shi *Amjad* ya daka masa tsawa tare da fad'in " INA da labarin b'arnar da kake kan dukiyar saboda haka babu abunda zaka CE min na baka daga nan zuwa dare ka hado takkadu ka kawo min ko in sanya a rufe shagunan kowa ya huta."
Yana gama maganar sa ya fuce cikin zafin nama!
Me citta ya bishi da kallo gumi na tsiyaya a jikinsa yaran kanti suka fara murna domin zalintarsu kawai yakeyi zama yayi kan kujerar da Amjad din ya tashi yana jan numfashi, Zumbur!!! Ya mike ya futa kamar mahaukaci ya  motarsa ya shige ya zauna tare da d'auko wayarsa wasu 'yan daba ya kira da suke wata unguwa da tashahara a birnin kano sun kware gurin daba da sare kan mutane take ya fada musu abunda zasuyi masa,ya basu address din gidan Alhaji Abbas Wanda yanzu ya zama mallakin Amjadu.
Dari misalin sha biyu yana zaune harabar gidan shi kadai  da karan sigari a hannunshi yana zuka zuciyarsa na saka masa yanda zaiyi da Mai citta kawai yaga suna haurowa daga sama DUK da security da aka keyawe gurin dashi.Mik'ewa yayi a nutse *Amjad* Jarumi ne sosai babu abunda yake furgita shi can yaga sun nufa bayan window din dakunansu suna zazzaga fetur, cikin zafin nama ya tafi da gudu ya sanya gwiwar hannusa guda ya daki kan d'aya tare da tad'o k'afar d'ayan suka zube a gurin suna nishi! Da hannu daya ya dunga Kansu har ya kaisu aininhin main parlor ya zauna kan kujera fuskarsa a murtuke yace." Waye ya aiko Ku."?
Ganin yanda muscle d'insa suke motsi sai abun ya basu tsoro suka nemi jarumantar su suka rasa baki na rawa daya daga cikinsu yace." Me citta!!!!! Ne ya aiko mu mu kone gidan gaba daya yayi mana alk'awarin kudi har miliyan biyar biyar."!
Murmushi yayi murya a sama yace". Gud"!! Alhaji Hashimu me citta!!!!? D'ayan yace." Yes sir." Gyad'a kai yayi ya mike a zafafe! Ya daki bango ! Yakai  ya kawo Cikin razananniyar tsawa yace." Meye sunayen Ku."?
Hada baki suka yi 
Ma'aruf Amma ana kirana da "Rambow"
D'ayan yace." Ni kuma Nasiru amma ana kirana da Doh-doh". Gyad'a kai yayi yace." Meye Matsalar Ku a rayuwa."?
Sukayi shiru yace." Baku da aiki sai kisan kai wato an turo Ku Ku kashe ni ko."?
Sukayi shiru. Tsawa ya buga musu tare da sake fadin." Meye Matsalar Ku a rayuwa ina tambayarku." Suka hada baki gurin fadin." KUDI ne sir."
"Very Gud"!! Yafad'a da k'arfi. Mik'ewa yayi ya durfafi d'akinsa sai gashi ya futo da d'aurin KUDI da yawa a hannusa ya watsa musu a jiki gami da fadin " gasu nan.
 Cike da tsoro suke bin kud'in da ya watse a kasa kunya ta rufe su 
 suka sunkyar da Kansu kasa suna bashi hakuri zama yayi cikin kujera yana kallonsu mazaje sosai amma babu Sanar yi yace ." Ku bani takaitaccan tarihin Ku."
A takaice suka gabatar masa da Kansu yace." Zan d'auke Ku aiki  zaku zama yarana INA fatan babu matsala, Har kusan kuka sukayi saboda farin ciki Ashe alheri ne ya shigo dasu gidan,lallai idan Allah yaso ka da alkairi babu mahalukin da ya iyasa ya hana, a takaice dai nan suka kwana. Da safe *Amjad* yasa suka kimtsa sosai suka shiga mota kai tsaye babu inda suka nufa sai  court nan *Amjad* ya shigar da kara a ka karbo sammaci su ya sanya suka kai ma me citta har cikin kasuwa Wanda yake zaune yana jiran tsammani yaji labarin daga su Rambow kawai yaga sun mik'a masa takkada daga hair court kiran gaggawa. Ya dinga kallonsu bakinsa na rawa,ko saurarensa basuyi ba suka barshi a gurin yana zufa!!
Alkali yayiwa me citta fata-fata tare da tonan asiri gaban bainar jama'a da iyalansa me citta kuka ne kawai bai yi alkali yace dole kuma sai ya bawa *Amjad* tara ta miliyan biyar ko ya zauna gidan yari tsawon shekara biyar. A lokacin me citta ya dinga share hawaye tabbas idan ya bada miliyan biyar aka biyar na dukiyarsa ta yi kasa dama yaudarar su Rambow yake da yace zai basu miliyan biyan. Kawai sai ya zab'i zaman gidan yarin domin shi mutum ne me mugun San kud'in tsiya, aikuwa nan take Alkali yasa aka tasa keyarsa zuwa gidan kaso iyalinsa na kuka. 
Ganin kukan da iyalinsa suke ne yasa Amjad ya kuduri niyar futo dashi amma ba yanzu ba sai yayi shekara biyu tukkuna ya San mecece duniya 
Me citta na cika shekara biyu *Amjad* ya karb'o shi daga gidan kaso tare da saka hannun alkali me makon me citta ya gane mecece duniya bayan ya futo sai ya sake d'aura damarar ganin bayan *Amjad* ko ta halin k'aka ne
Wannan shine mussababin abunda ya tsananta gaba a tsakanin sa da Alhaji Hashimu me citta.
*Zamu dawo ainihin labari a pege na gaba*
*19/October/2009*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA. 
*23*
 Kallo Umma ta bini dashi har na shige d'akinta simi-simi ina addu'ar Allah yasa kar ta tuheme ni da wata magana. Aikuwa ina cikin kuryar d'akinta bayan na idar da sallah ina Jan carbi Ta kwala min kira tana daga parlor gabana ya fad'i sosai na mike na futa lokacin gari ya soma haske Mimi na kwance a kan abun sallah a gefan ta da alama ta idar da sallah ne, tace." Zauna in yi mini tsaye aka." Zama nayi kusa da ita ta aje carbin hannunta tana kallona cikin nazari daga bisani ta ambaci sunana da "Asma'u" na d'ago kaina tare da amsawa cike da tuhuma tace "wankan me kikayi da asubar fari" shiru nayi saboda bani da amsar da zan bata domin dai tunda nake ban taba Wanka da asubah  ko da ko wankan tsarki ne na alada tace "ba dake nake magana bane." Zuciyata ta saka min wani Abu da sauri nace." Umma kin San jiya na Sha magugguna to shine na tashi naji jikina ya jike da gumi ina jin zafi sosai shine na watsa ruwa." Na kare maganar bakina na rawa. Shiru tayi tana nazarin magana ta minti biyar tace." Ban yarda da maganar ki ba Asma'u. " na dago kaina ina kallonta nace." To Umma ke wane Wanka kike tunani zanyi da asubah.? Umma tace." Na sani ko kin fara mafarki aure kike so." K'irjina na dafe ina zaro ido nace." Wallahi a'a Umma.' Tace" bana son munafurci wallahi idan aure kike so sai kicewa Musa ya futo kawai ni ba yarinya bace duk abunda kike ciki kamar a tafin hannuna kike." Ina kallon Mimi tana kunshe dariya, hararata nayi cike da takaici nace." Umma ki bar maganar nan don Allah ni kam Musa bai min ba wallahi." Na fada ina zumb'ura baki tace." To sai ki nemo wani domin naga aure ki kike so sai ai miki. " kafin ince komai sai ga Yaya Aminu ya futo Cikin shirin makaranta ya watsa mugun kallo tare da fadin." Wallahi Umma yarinyar bata da mutumci d'azu ina mata magana ta wuce tana k'okarin zagina." Yafad'a yana k'okarin zama, Umma tace." Nima fad'in da nake Mata kenan ai Yaya Aminu yace." Idan jarrabawar su ta futo Zan musu kokari su samu su je legal ko FCE ko