Showing 27001 words to 30000 words out of 67868 words
 dufoloma su samu kafin suyi aure. Umma tace." Da ko ka kyauta wallahi amma ina ganin ai ba karatun suke so ba aure su ke so." Mimi ta mike zaune da sauri tace." A'a Umma muna so wallahi ko baba Nafi'u ma yace." Zai nema mana makaranta idan jarrabawar mu ta futo mu cigaba." Umma tace." Ai fa ke da kike da me uwa a gidin murhu." Aminu yace." Wallahi na manta dashi Bari in daina wahalar da kaina kawai tunda yana da ra'ayin Ku cigaba sai Ku cigaba kawai.
Umma tace." Amma idan miji yazo dole a ajiye karatu ayi aure. Mimi ta sunkuyar da kanta wai ita kunya, nace"a'a Umma aure sinna ce haka ma karatu yana da mutukar muhimanci garemu idan mun fara sai ayi yarjejeniya da Wanda zai auremu." Yaya Aminu ya kawo hannu zai buge min bakina na kauce da sauri yace." Shegiya me bakin magana ke ko kunya bakiji ba gaban Umma kike wannan maganar cikin kukuni nace." Ai gaskiya ce"
[10/21, 8:00 AM] 👄: Mik'ewa yayi da niyar futa na zabura! Da sauri na b'uya bayan Umma hararata yayi kurrum yace." Umma zan tafi." Umma tace." Bazaka tsaya ka karya ba." Girgiza Kai yayi yace." Muna da darasi k'arfe bakwai bana so na makara" Umma tace
" To Allah ya bada sa'a" ameen yace ya futa kafad'arsa rataye da jaka ta makaranta, murmushi nayi a fili nace "Yaya Aminu Dan makaranta" Umma tace " da kikaga ya futa ko." ? Dariya muka sa ni da Mimi Umma ta mik'e da nufi zuwa kicin tace." Ai ya kamata Ku shirya kuje gidan Kawun NAKU Nafi'u kun kwana biyu baku je ba." Nace wallahi kuwa Umma zamuje yau insha Allah" kicin ta nufa muka bita domin kama mata ayyuka yau Umma awara tayi mana da kunun tsamiya wai haka na dinga dabkar yaji duk da attaruhun da aka saka cikin awarar hummm ni kam ina son yajin barkono a rayuwata. Muna gama karyawa muka fara aikin gida ita kuma Umma tana harkar cinikin ta da yara har da Matan aure ma masu shigowa. Bayan mun gama mukayi wanka.
Mimi ta Ciro mana wani les baki da ratsin ja a jikinsa na waccan sallahr ne. Wai shi zamu sa nace "sai dai in ke kika saka wallahi kin San na tsani les din shine zaki wani Ciro mana shi." Mimi tace" naga mun Dade bamu saka shi ba." Nace." Ki saka ke ban hanaki ba." Kallo na take ina birkito kayan cikin akwatuna na futo da wata atampa haitaget anyi min doguwar Riga me madauri daga baya hannun rigar dogone amma an tsaga shi sosai duk kasan galalin hannuna in nasa rigar ana gani blue and orange ne na amma blue yafi yawa a jikinta saboda haka na d'auko mayafi orange na aje. Mimi tace" kin Mayan cewa atampar nan WALLAHI ." nace "tanayi min kyau ne Mimi." Tab'e baki tayi tace." Dinkin yana nuna tsaracin ciki kina daga hannu hammta a waje." Duka na Kai mata ta kauce da sauri tana dariya nace." K'aryar ki kice HAMMATA ta na wari ko kiga gashi ko daya kullum Cikin aski nake ke zaki fadawa wani saboda kin San na tsani warin hammata." Mimi ta kyalkyale da dariya tana fadin "wallahi har kin tuna min da Hafsat me warin." Dariya na sa nace." Ni na manta da ita wallahi." Mimi tace." Asma'u baki da mutumci WALLAHI haka kika tasa Hafsa a gaba a skull duk kika tsagwame ta da ta matso daks dimmu zaki fara tsokanrta *Me warin ham* Allah sarki Hafsa tun bata ganewa ta gane cewar da ita kike dole dai kika saka ta ta daina zuwa gurimu dimu Nace." Wallahi Mimi na tsani inga mace tana kazanta shiyasa na takurawa Hafsa in ta fahimta sai ta gyara haba!tasan zata shigo cikin makaranta cikin mutane baza ta tsaftace jikinta ba nifa wallahi mijina zai ga tsafta domin shi kanshi kullum cikin kyalkyale masa ji nake." Mimi tace." Ga manyan mata hummm mijin da bai zo ba ana masa tanadi lallai wannan me sa'a ne." Nace fad'i ki kara Mimi duk namijin da ya same ni ya tsinci dami akala domin sai na sanja masa rayuwa ummm! Mimi kenan ni nasan wacece ni." Mimi tace "maganar Umma ta futo lallai Asma'u aure kike so." Hararata nayi nace "don Allah tashi ki saka kayan ki , e aure nake so Mimi waye zaiki sinnar Annabi muhammadu." Mimi ta mike tana saka kaya tace." Babu gaskiya kam Allah dai ya zab'a mana nagari." Nace ameen ya rabbi.
Mun futo a kintse Sosai mu kayi kyau Mimi tasha kwalliyar fuska ni ko hoda kawai na saka sai kwalli Dana zirara ko man leb'e ban saka ba, Umma ta kalleni tare da fadin " Asma'u ban ce ki daina saka atampar nan ba haka kurum kinje an miki lalataccan dinki ko."? Nace Umma duba fa ki gani atampar da kyaunta kuma ni duk cikin kayana nafi sonta wallahi." Umma tace." Ke kika sani ai ba kyawun atampar ne abun dubawa dinkin ne." Nace Umma na kai wa Ummi makociya ta gyara min hannu" shiru kawai Umma tayi min domin tasan duk tsarina ne, tace." Kar Ku kai magariba baku dawo gidan nan ba." Muka ce to Umma" tace  Ku daina min da  Kawun NAKU da Mamansu Munubiya" muka je zata ji insha Allah. Nan muka futa muna taku dai-dai mussaman ni sau kace wata 'yar gidan shugaban kasa. Da kafa muka k'arasa bakin titi muka tsaya domin jiran abun hawa. Wasu 'yan mata suka zo wucewa ta gefenmu nace " Mimi kinga irin handbag dina ko ajikin waccan" Mimi ta kallesu tare da fadin "aikuwa irinta CE." Nace." Anya ko Mimi bazan je in d'auko kayata ba" tace" kin dai ji abunda Umma tace don Allah kar ki jawo mana wata Matsalar " shiru nayi mata kawai ina sak'e-sak'e. A dai-dai ta sahu ta tsayar mana tayi ciniki dashi tare da fada mana inda zai kaimu, muka shiga, mun Dan yi nisa Mimi tace." Idan mun futo daga gidan Kawu Nafi'u mu biya gudansu Hafsa mana tunda kusa ne." Nace "muje mana ai babu komai. " Mimi hira take min ni ko ina can tunanin yadda za'ayi in d'auko handbag dina gidan guy nan . mu ka sauka Titin wajan gidan marigayi Ummaru ta'ambu da kafa muka dinga shiga lungunan kafin mu Isa gidan Kawu Nafi'u muna shiga yaran gidan suka rungume Mimi suna ihu!! Kallonsu nake INA dariya nace" nu baku sann ba kenan" su dawo kaina nan Mamansa Munnu ta futo tana mana maraba tace Ku shigo ciki yara sun hanaku shigowa . nan muka shiga parlor me d'auke da kujeru biyar da kafet malale a tsakiyar gefe friji ne sai kayan kallo lavuleye kewaye a parlor ka hotunan shuwagabbanin kasa a manne a bango kana ganin tsarin gidan kasan na 'yan boko ne
Muka gaisa da ita Sosai tare da fada mata sak'on Umma tace." Tana amsawa tare da cewa "ai duk laifin Ku ne da bakwa zuwa akai akai sai Ku d'ebo wattani ba kuzo ba ke Mimi haka dangi zasu yi ta cigiyar ki." Mimi ta sunkyar da kanta cike da kunya nace." Mamansa Munnu Kawu Ba yanan ne." Tace." Bai jima da futa wallahi" nace Munnu fa." Tace" yanzu ta shiga ban daki tana Wanka " muka mike muka shiga dakin Munnu kan katifar ta muka zube ni da Mimi  Munnu ta baza hotona kan katifarta tana kallo duk irin tsaffin hotanan ne na makaranta da wasu lokacin muna yara. Wani hoto Mimi ta mik'o min tace." Asma'u kin ganki a nan"? Karb'a nayi ina dubawa Mimi tq fashe da dariya, da sauri na yi yunk'urin yaga hoton cike da takaici hoton anyi mana shine farko fara zuwa makarantar mu lokacin muna kwailaye muna sanye da sabbi unporm ko wanne da k'atuwar jakarsa sai murna muke mun shiga secondary skull Mimi ta fuzge hoton tana dariya tare da fadin" kin San Allah Asma kina kama da 'yar film din nan Nafisa Abdullahi" hararata nayi nace." Kin cuce ni Mimi". Tace. OK kina nufin kin fi Nafisa kyau kenan."? Nace" nesa ba kusa ba wallahi . Mimi tace "bari Munnu ta futo ta fada miki gaskiya." Aikuwa sai ga Munnu ta shigo dakin tana goge kanta da k'aramin towol tace." Ku kuma 'yan iska yaushe kuka zo" nace." Babynaaaaaa!!! Cike da tsoka na fad'i maganar Munnu ta kawo min duka tana warce hoton dake hannuna dariya na fashe da ita ina nuna ta da hannu. Ita ko Mimi dake mayyar dariya ce kwanciya tayi kan katifa tana sheka dariyarta. Munnu ta wuce mu cike da takaici take fadin "banza ye kawai wad'anda basa manta Abu." Ina dariya nace." Ya za'ayi mu manta Munnu ta Shamsu kenan baki da aiki sai kallon hoton Shamsu ki ishi mutane a skull da Baby na yayi kaza babyna yace zai siya min kaza hummmm! Shamsu ya San takan sace zuciyar 'yan mata gashi ya sace taki ya gudu ya barki da ciwon sonsa"
Mimi tace" wallahi kuwa kin San ko a skul aka zagi Shamsu sau kunyi fada da ita ko ta d'aura gaba dakai, ummm! Ni kaina sau nawa Munnu tana gaba dani duk akan ina mata magana ta rabu da Shamsu Dan yaudara ne.'' Nace." Nifa WALLAHI duk son da nakewa Namiji bai Isa na nuna masa ba sai dai ya gani a aikace." Munnu tace." Ni Ku k'yaleni don Allah kuyi min addu'a kawai Allah ya cire min son Shamsu daga zuciyata" nace." Munnu kina so ki rabu da soyayyar Shamsu a zuciyar ki amma kike kallon hotan sa." Shiru tamin nace." Kinga to" juyowa tayi tana kallona na daga hoton Shamsu dake hannuna na zaga shi gida uku na watsar nace" wannan shi yafi dacewa dake amma kullum kina kallon hoton sa ta Yaya zaki mance dashi." Mimi tace kinyi min dai-dai da kika yaga wallahi" Munnu ta juya ba tare da tace mana komai ba ta cigaba da kintsa jikinta mu kuma muka cigaba da caccakar Shamsu gami da tsine masa sabo yaudarar da yayiwa Munnu wacce ta saki jiki dashi sosai ya gudu ya barta.Bayan ta gama shirya ta juyo tana fuskantar mu tare da fadin " INA kukaje ne kula biyo tanan domin nasan dai ba takanas kuka zo nan ba" Mimi tace" aikuwa kin fad'i ba dai-dai ba takanas muka zo nan domin mu wuni amma za muje gidansu Hafsa me warin Ham!! Munnu ta fashe da dariya tana nuna Asma'u dariya muka kwashe da ita dukan mu sai kace wasu tab'abb'u.
*****
B'angaran Hibbah kuwa tana zaune har wajan goma na dare tana jiran dawowar *Amjadu* shiru bai dawo ba kamar ta fasa kuka haka take ji gashi bata da numbar sa ga wata sha'awrsa na damunta tunda ya d'and'ana mata zumarsa a baki shikkenan taji tana son kara kasan cewa dashi, jiki babu k'wari ta futo daga dakin tana sakkowa kasa taga haske tar mutane sai kai kawo suke tamkar rana domin wasu ma a lokacin suke shigowa gurin cikin motocinsu wasu da 'yan matansu wasu da abokan su gasu nan dai. Duk tarin mazan da suke Binta da kallon sha'awa Sam basa gabanta domin yanzu ita babu Wanda take gani a gabanta sai Sadauki *Amjadu* shi kadai ne burin ta. Motar ta bude ta shiga ta futa daga hotal din.
**********
Bayan munci abunci munyi sallah azuhur ne sannan muka sake kintse jikinmu domin zuwa gudansu Hafsa muka futo mu ka sanarwa da Mamasu Munnu tace" to daga can zaku wuce kenan."? Nace "Eh daga can zamu wuce gida" d'akinta ta shiga tana fadin "Bari in zo to" mu kowa ni da Mimi hanyar futa muka nufa saboda mun San halinta kullum in muka zo sai tace zata bamu kudi." Aikuwa sai gata ta futo hannunta da gudar Dari biyar tare da wata Leda me Zane Zane.  Ta mik'o mana tana fadin Ku karb'a Ku kara kud'in mota" nokewa mukayi cike da kunya Mimi ta karb'i ledar tana fad'in "zamu karb'i wannan amma ki bar kud'in naki" Munnu ta karb'i kud'in tana fadin" Umma kyalesu suna so wallahi munafurci ne" kawai na basu in mun futa" Ummansu Munnu tace" to Ku gaida gida Ku gaishe min da Umman taku " mukace "zataji sosai wallahi.
Muna futa na warce Dari biyar din hannun Munnu nace." Bani to salon mu manta mu tafi ki rike ko ai na gano ki" Munnu tace" to mayyar kudi kar ki jimin ciwo a banza" Mimi tace "Munnu har kij tuna min da wani Abu da ya faru shekaran jiya" Nan Mimi ta kwashe haduwar mu da guy nan ta fada mata harda watsa masa kud'in da nayi
Munnu ta dinga min masifa kamar wata uwata take "fadin WALLAHI kin cuce mu na rantse da ina gurin sai nayi miki duka kuma na tsinka ki a gurinsa ke wacece da zakiyi watsa da kudi masu yawa a daure a kyauwa 'yar bura uba kina fama da kod'add'iyar atampar ki haitaget sai shegen girman kan tsiya malam" ta k'arashe maganar cike da takaicin abunda na aikata, Mimi dariya take kamar Cikin zai ciwo ni ko sakin baki kawai nayi INA kallon Munnu tana zuba min masifa kamar ta ari baki, dariya ta kufce min na fada soron wani gida na zauna inayi biyo ni sukayi duk da haka Munnu bata daina surutai ba, nace." Munnu WALLAHI ban tab'a ganin me mugun son kudi ba irinki tabd'ijam!!! Munnu!! Na fada ina dariya. Tace" wallahi da ina gurin sai naje na tsince kudin na bashi hakuri, Um!!!! A wannan zamani yanda kudi suke wahala ana bahariyar tsiya" na mike tsaye tare da fadin"in kina so sai in raka ki idan zaki same shi ki bashi hakuri dama na manta handbag dina a gidan shi" Munnu tace"wallahi muje zan bashi hakuri sai dai Allah yasa ya bamu kudi" bani kadai ba har Mimi dariya take, nace" Munnu ya ishe ki WALLAHI kar ki mai damu mahaukata a hanya sai faman dariya kike saka mu. Tace" Ku muje na daina" muka futa daga soran gidan muka cigaba da tafiya babu Wanda ya sake cewa komai. Daf da zamu shiga gidansu Hafsa ne Munnu tace"Asama da gaske fa nake muje gidan guy nan don Allah" nace" zamu je in dare bai yi ba". Mimi dai shiru tayi mana muka shiga gidansu  Hafsa da sallama. Tana zaune kan kujera 'yar tsungo tana gyara wake ta mike da sauri saura kad'an ta zubar da waken nace" hankali dai ki zubar ki daku wallahi" da ihu!! Tayo kanmu tana murna nayi saurin gocewa don kar ta rungume ni inji tsaminta, duk sun gane dalilina nayin hakan har ita Hafsa din, dake ta san halina bata damu ba, ta rike hannunsu Mimi muka shiga d'akinta, nace." Ke Hafsa INA mamanku" kamar me jin tsorona tace"ta tafi unguwa" nace"sai kije ki siyo mana ruwa da Lemo mai sanyi"
Tace" Ke fa kin fiye Abu kinga ban kawo muku bane." Nace "si hali na sani ne rowa da......... Na ki karasawa ina b'oye dariya Hafsa ta d'auke kanta cike da jin haushina ta cigaba da hira dasu Mimi ni kuma na dinga bin dakin Hafsa da kallo ina kunshe dariya. Ta mike da sauri tare da fadin" ai yau ina da manyan baki bari in sanya yaro ya siyo muku ruwa da lemo ta futa da saurin ta.
Mimi ta kalle ni had'e da bata fuska tace"Asma'u babu kyau cin fuska  don Allah ki k'yale baiwar Allah nan haka wallahi tana d'aga miki kafa" nace" me nayi mata to" Mannu tace"ki daina kiranta da me warin HAMMATA" nace" na daina shikkenan" suka cigaba da shirarsu ni kuma ina kalle kalle a dakin can na hango Wani rubutu jikin bango anyi shi da blue din maka tare da wani k'aramin hoto  an manna gurin
 Mik'ewa nayi na isa gurin INA fadin "Su Hafsa 'yan gayu ken..... Magana tace ta mak'ale a mak'o gwarona sakamakon gani fuskar guy nan jikin picture din dake manne a bango gaba na fad'uwa na bi rubutun ina karantawa, abunda nagani an rubuta ya gigita ni gami da dimauta ni. _*Ilov my love my sweetheart yaya na farin cikina Amjadu ina bal'in son ko zuciyata tana azabutuwa da kaunar ka zan iya kashe kaina saboda kai ina mutukar kaunar ka yayanaaaaa!*
Na nemi miyau na rasa a bakina ya bushe k'amas na fara tunanin meye hadin Hasfa da guy nan to? Gashi tana kiransa da yayanta kai duk yanda akai da akwai alamar tambaya, idan Hafsa suna da alaka da guy nan me ya jawo musu talauci haka duk tsiya si zai taimaka musu. 
Motsin shigowar Hafsa naji nayi saurin komawa na zauna jikina na tsiyayar da gumi, Sam su Mimi ba su ankara da komai ba suna can suna hira, Hafsa ta shigo dakin hannuta rike da ledar ruwa pure watar da Lemo cocarcolar a ciki guda uku ta aje gabanmu tunda ta shigo nake zabga mata harara ina mata wani irin kallo, ita ko sai washe baki take tana mana labari,, sai dariya take tace"Asma'u ga lemon nan" hararata nayi ita da lemon nata ta d'auke kanta kurrum tana murmushi.
Hirarasu sukeyi babu ni a ciki sai dariya suke yi Hafsa sai tsoma ni take cikin hirarar tasu ina gwaleta.
Daf da magariba nace "Ku tashi mu tafi haka ke Munnu dama a gida kike". Mik'ewa sukayi a tare Munnu tace." Kin manta da maganrmu ko"? Nace" ban manta ba" nayi waje na kyalesu tare suka futo har Hafsa ta raka mu har bakin titi tana godiya sune kawai suke amsa mata ni ko ko kallo bata ishe ni ba. 
Har aka idar da sallahr bamu samu abun hawa ba kun San dai tadda titin k'ok'i yake a baude bayan haka kuma muna tsakiyar kasuwar kurmi. Sai muka fara tafiya a kasa, gashi gari ya soma duhu, Wani me a dai-dai sahu yazo ya tsaya gabamu tare da fadin " INA zakuje 'yan mata "? Nace." Rijiyar zaki scound get Cikin Jambulo " Mimi ta kalle ni da sauri nima na zare mata