Showing 42001 words to 45000 words out of 67868 words

Chapter 15 - BABAN YARO PART 1

30 Jun 2024

15510

b'arawo ya kwashe ni, Mimi tayi min tashin duniya na kasa tashi haka ta futa taje ta dauro alwalar sallahr asubahi

Sai misalin bakwai da rabi na tashi shima Ya Aminu ne ya shigo har dakin namu yana tashi ne da masifa tare da fad'in "na kwanta bacci na manta yau zamu je dubo jarrabawar mu, na mike zaune ina mutsika idona, kallona yayi cikin tuhuma yace." Ciwon ido kike yi naga idon ki yayi jazur." Mimi tace." Nima abunda zan tambaya kenan. " Mik'ewa nayi a daddafe saboda yanda nake jin marata nayi min wani irin suka . kwata kwata nakasa had'a ido dasu simi-simi na futa daga dakin, INA addu'ar Allah yasa Ummamu bata tsakar gida, aikuwa Allah ya amshi addu'a ta na cikin d'akinta nayi saurin shigewa ban d'aki.












*25/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*


*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA*



*28*




Raina a b'ace na futo daga band'akin, na shiga dakinmu Mimi ta bini da kallo d'auke kaina nayi na fara birkito da kayan sawa ta, tace." kizo mu fara karya sannan ki saka kayan." A fusace! Nace.' Dole sai da ni sannan zaki karya to ki daskare anan." Tab'e baki tayi ta juya kawai ta fara kurb'ar kununta tana had'awa da soyayyar Dan kalin Hausa, a hankali naji tace." Da sanyi Safiya zaki fara rashin mutumci." Shuru nayi mata kawai ina jin zafi a zuciyata Wanda na rasa ko bakin cikin me ye yake damuna oho. Ina gama shiryawa na mik'e tare da kallonta nace." Idan baki yi sauri ba wallahi tafiya zanyi." Mimi ta hasalo itama tace." To kiyi tafiyar ki mana Asma'u ai na San hanya,kawai sai ki dinga min tsawa kamar uwata wallahi baki isabah!!!"" Tsaki naja na futa daga d'akin fuuuuu!! Umma na zaune a rumfa tana lissafa kud'in cinikinta na shiga da sallama, kallona take cikin nazari sai nayi saurin gyara yanayin fuska ta na zauna kusa da ita ina gaisheta.Ta amsa babu yabo babu fallasa tace." Me ya hanaki tashi da wuri yau abunda ba sabon ki bane." Kasa nayi da kaina ina shiryo k'aryar da zanyi mata. Tace." Tambayar ki nake." Da sauri nace." Umma kin San dama bana sake wa a gidan mutane inyi bacci Wallahi jiya kwata-kwata banyi bacci a gudansu Munnu ba shine dalilin da yasa na makara." Tace." Yayi kyau hakan." Yanda ta fad'i maganar yasa na soma zargin kaina sunkuyar da kaina nayi ina addu'ar Allah yasa kar ta fahimci wani Abu. Kamar daga sama naji tace." Nishi! Da surutun me naji kinayi jiya da daddare." ? Gaban yayi bala'in fad'uwa." Jarumta na aro da dauri na d'ago kaina ina kallonta nace." Umma nishi! Kuma."? Hararata tayi ta cigaba da lissafin ta, tace." Ko k'arya nake."? Girgiza kai na nayi nace." A'a."! Murmushi tayi kawai tana girgiza kai tace."Asma'u nice na haife ki babu abunda zaki layance min, dukanin Ku a tafin hannuna kuke na dad'e da sanin halin da kike ciki saboda haka nake baki shawarar ki tsare kanki da martabar ki ta d'iya mace ki kula kada sha'awa tasa ki jefa kanki cikin halaka kad'a shaid'an ya ribace ki ki aikata sab'on Allah ko kice zaki nemi hanyar biya wa kanki buk'ata ta ko wace siga ki tsare kanki daga nan har lokacin da Allah zai futo miki da mijin aure." Umma ta k'arashe maganar ta babu abunda ya dame ta.
Wata irin kunya ce ta lullub'e ni dama nasan Umma sai ta fahimta nasan ta da mugun saka ido akanmu sunkuyar da kaina kawai nayi domin bani da tacewa. Haka Mimi ta shigo ta same mu ,da sauri na mike na futa ko sallama banyi wa Umma ba, Mimi CE ta tsaya ta karb'ar mana kud'in abun hawa.

Ban jira Mimi ba nayi tafiya ta har na Isa bakin titi bata k'araso ba, tsaki naja kawai ina kallon hanya can na hango ta ta tawo na d'auke kaina cike da haushin ta, me a dai-dai ta na tsayar mana, muka shiga tare da fad'a masa inda zamu . haka mukayi tafiyar kowa zuciyarsa babu dad'i.

Tun daga bakin get din makarantar mu muka soma cin karo da k'awayenmu da ihu!! Suka zo suna rungume ni tare da taya mu murna ni da Mimi mun ci jarrabawa nima sai na saki fuska sosai na kutsa cikin jama'a domin idona ya gane min, duk mun cinye maths ne kawai muka fad'i shima ba sosai ba, wasu na murna wasu na bakin ciki nima tsabar murna tasa na manta da komai na shiga cikin k'awayenmu muka fara ihu! Da dariya wadan da suka fad'i ciki ko har da Alina tana tsaye jikin motar ta kamar ta kurma Ihu! Munnu na kalla cikin dariya na nuna mata Alina ina fad'in" Munnu dubi Alina da fuska sai kace soyayyan k'osai sai maiko take cikin rana." Munnu ta shek'e da dariya tana fadin" shegiyar ba fuska taci bleecing ciki ko oho dama yaushe zata ci jarrabawa tana can tana yawon iskan ci." Dariya muka shek'e da ita. Mimi tace." Ku Wallahi kun fiye Neman fitina kuzo mu tafi tunda dai mun gama abunda ya kawo mu" hararta nayi nace." Wallahi baza mu tafi yanzu ba sai nagama kallon 'yan bakin ciki da masu kuka irin su Ooo" na nuna Alina da bakina . a fusace! Ta tawo inda muke tsaye ta nuni da ya tsa tare da fad'in" ke Ki shiga hankalin ki wallahi ko in sauke fushina a kanki yanzu". Kallon banza na watsa mata nace ."da gaske kike." ? Tace." Zan sanya ne ayi min k'asa-k'asa dake shigeya 'yar gidan malam Shehu sai tsabar girman kan tsaya." Wawan mari na Kai mata ta dafe kuncin ta cike da tsoro! Ina numfar fashi nace." Wato har kin manta dabi na dake ko? Shine kike ikirarin sawa a dake,to don durun Uwar ki ki saka ayi gunduwa-gunduwa dani shine kad'ai zai nuna min ke 'yar gidan Bulget ce ubanki ba Santana ba ne."

Ca kumo wuyana tayi ta hau d'ura min ashar!! Idonta yayi jazur!! Kafin ta Ankara na daki bakinta da gwiwar hannuna nace." Dama Neman ki nake ruwa a jallo shegiya karuwa." Ai kafin kace kwabo gurin ya soma cika da mutane Alina ta fad'i a gurin tana wani k'ifkifta ido bakinta na kumfa,dama ta saba daga zarar an fara fada da ita zata fad'i kasa tana burgima wai ita me aljanu.

Mimi da Munnu hankalin su ya tashi suka nufi offece din principal da sauri sauran 'yan makaranta suka fara guduwa domin sun tsorata da abunda Alina take ni ko ina tsaye a kanta ko d'ar ba nayi. Malama Rakiya ce da aunt Lahira suka k'araso gurin hankali a tashe suka fara yi mata tofi, mintuna kusan ashirin sannan ta dawo dai-dai duk suka tattaramu suka tasa mu gaba zuwa offece din principal me gaba d'aya.
Fad'a sosai shugaban makaranta yayi mana tare da gargadin cewa idan mun San rigima za mu zo muyi ta zai soke mana shagalin murnar da mu tana da ranar candy sai kawai kowa yazo ya karb'i takkadun sa, ya tafi, hakuri muka bashi sosai sannan ya sallame mu muka futa daga ofis din gruop-gruop an tsaya sai gulma ake haka Alina ta futo jiki babu k'wari ta shiga motar ta ta tafi, mu kuwa sai bayan sallahr azuhur sannan mukayi sallama da k'awayenmu bayan mun tsaida ranar da zamu gudanar da murnar kammala makaranmu sati guda me zuwa, tare da futar da anko har kala uku duk ranar zamu sanya shi. Muka futo titi muna Neman abun hawa rana ta kwalle sosai gumi kawai nake ga wata irin yunwa na damuna dama ban karya ba gwara Mimi ta karya da k'yar muka samu a dai-dai sahu muka shiga, ya dauki hanya sai gida. Hira muke sosai cikin adai-dai tar kowa na fadin albarcin bakinsa, danja ta tsai damu, cike da jin haushi nace." Na tsani ina cikin abun hawa danja ta tsaidani wallah.........maganar tawa ta katse hango gefan fuskar sa da nayi kwance a cikin wata mutsiyaciyar mota silver sai shak'i take a can tsallakenmu, da sauri na d'auke kaina gabana na dukan uku-uku addu'a nake kar Allah yasa Mimi ko Munnu wata ta hango shi, a sace na k'ara kallon gefan haguna sai naga ya mak'ala airpix a kunne shi tare da gyara zaman shi ya d'ora pcap me wani irin ado a jikinta gani nayi yayi min wani bala'in kyau ban gane ko wane dressing ne a jikinshi ba, amma na tabbata k'ananun kaya ne tunda INA hango hannunshi yana latsa wayar sa, ga Rambow a gefan shi sai zare ido yake.

D'auke kaina nayi jin miyan bakina ya daskare ban tab'a tsayuwa na kare masa kallo ba sai yau, a zuciyata Nace "Ashe haka yake da bal'in kyau!!!!!












*25/October/2019*
[11/1, 10:55 PM] .: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*




*29*





Ban sake kallon gefan da yake ba har aka bamu hannu, muka wuce Munnu ta kalle ni tare da fad'in"wai ya kikayi shiru sarkin kaud'i." Ya mutse fuska ta tanayi nace." Yunwa nake ji Wallahi." Tace." Ba Dole ba wannan uban ihu da kika sha, shiru kawai nayi mata zuciyata nacan ga tunanin guy nan, cikin zuciyata nace sai kyau amma babu kyawun hali. Munnu aka fara saukewa ta kalli ni tare da fad'i wa kika ce zamu bawa dinkimu "? Nace." Kinsan dai ba zamu bawa Ummi ba ta lalata mana yadi maza zamu bawa dinkimu." Tace." Shikkenan yaushe zamu gidan aunty Hauwa ko kuma da kanmu zamu shiga kwari." Nace." Ki rabu da aunty Hauwa kawai muje da kanmu."tace." To shikkenan sai goben" muka ce "Allah ya kaimu ni da Mimi .me a dai-dai ya ja mu muka tafi ita kuma Munnu ta tsallaka titi ta shige layinsh.



A hankali motar ta silala ta shiga cikin harabar gidan. Rambow ya futo da sauri ya bud'e masa kofar motar tare da k'okarin karb'ar wayoyin hannunsa.
Girgiza masa kai kurrum yayi ya wuce shi cikin sassarafa, suka rufa masa baya.


Dattijiwa kamillaliya na zaune cikin kujera tana sanye da atampah Ghana kamar ko da yaushe sai kamshi parlor yake tana zaune tana kallon tv tashar sunnah tv suna wa'azi, gefan ta wata matashiyar budurwa ce a zaune tana kallo ita.

Ya shiga da Sallama a bakinsa. Da sauri Hafsa ta kalli kofar shigowa jin muryarsa taji wani sanyi na kwarara a cikin zuciyarta. Cike da kunya ta d'auke kanta.

Granny tace." Dan halak kaki jinin ambato dama yanzu nake fada miki zai shigo tunda yau juma'a."

Hafsa ta yi k'asa da kanta tana murmushi . cikin yanayin tafiyar sa ya k'araso kusa da kakar tasa ya zauna gefan ta, tare da gaishe ta. Ta amsa cike da walwala da farin ciki tace." Ga k'anwar ka nan tana zaman jiran kazo Ku gaisa." Cikin rashin fahimta yake kallon Hafsa dake sine kai yace." Granny wacece wannan."? Cike da takaici tace." Hafsa zaka ce baka sani ba kai kuwa." Sosa kansa yayi tare da fad'in" banda abunki to a ina zan santa na dai ga tana kama da Innah Suwaiba." Granny tace." To 'yar autar ta ce ai." Sosa kansa yayi a karo na biyu yace." Ayya! Ai kin San ni ba sanin 'yayan ta nayi ba sosai wallahi in banda Musbahu da Zaraddini suka kadai zan sheda a cikinsu."

Granny tace." Ai dole kai da ba ziyara kake ba dole ka kasa saninta , sunanta Hafsatu." Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya kalli Hafsa a nutse yace." Hafsa ya gida ya makaranta." Ba kinta na rawa tace." Lafiya Lou alhamdullahi. " yace." Ina Ina Suwaibah tana lafiya."? "Lafiyan ta lau tace ma a gaishe ka tunda ka daina zuwa." Murmushi yayi kawai be komai ba." Granny tace. "Ai ka saba dama da anyi magana ka sosa kai ya kamata dai cikin wannan satin kaje." Yace." Insha Allah zanje ayyuka ne suka min yawa ke kanki kin sani." Tace" na sani amma ai ana barin halak da kunya." Shiru kawai yayi mata tana surutai wayarsa yake dannawa yayin da Hafsa take ta satar kallonsa tana ji kamar ta had'iye shi ta huta.

Ina Suawaiba mahaifiyar Hafsa yayar Aisha ce wato mahaifiyar Amjadu itace babba a d'akinsa Hafsa kenan a matsayin kanwarsa take.

Kallon da take masa ne ya dame shi kwata-kwata a rayuwarsa ya tsani kallo shi kam, b'ata fuska yayi ya mik'e tsaye tare da kallon agogon hannunsa, ya kalli Granny tare da fad'in ni zan tafi." Cike da mamaki tace" zaka tafi kamar yaya? Baza ka tsaya ka ci mutumin naka ba gashi na kwad'anta maka." Tana nufin zogale. Girgiza kansa yayi kawai ya nufi hanyar futa, kallo tabi shi dashi cike da takaici tace." Ka tsaya ka ragewa Kanwar ta hanya mana." Ba tare da ya wai wayo ba yace." Ki bata kud'in abun hawa mana." Yayo fucewarsa ya gane manufar granny na aje yarinyar da tayi Dama wancan satin da yazo ta fada masa tayi masa budurwa lallai granny tana da aiki a gabanta.

Hafsa kuwa ji tayi kamar ta tashi ta dawo dashi domin Sam bata gaji da kallonsa ba, ita dai Allah ya sanya mata k'aunarsa a ranta tana fatan Allah ya sa granny tace dole ya aure ta tunda ta lura Sam bata gabansa amma tayi mamaki sosai yanda ya amsa mata gaisuwarta a sake ta d'auka yana da girman Kai ashe ba haka yake ba.

Yana futa wayar shi ta fara k'ara dubawa yayi cike da mamaki numbar me girma governor ya gani, sai da ta kusa katse wa sannan ya daga wayar da muryarsa irin ta jarumai, suka gaisa da shi cikin nutsuwa daga d'ayan b'angaran me girima governor yace." Kazo Gidan gwamnati musalin k'arfe biyar na yamma ina Neman ka." Yace." Insha Allah inan tafe." Sallama sukayi gaba dayansu kowa ya kashe wayarsa. Murmushin gefan baki yayi kawai yasan karshen zancan wato shime governor yana goyawa su Me citta baya kenan , lallai dole ya tashi tsaye akan haka.


*******

Tunda nayi masa wannan ganin shikkenan na nemi kuzari na na rasa haka muka shiga gida jikina babu k'wari Mimi CE kawai take ta murna tana baya Umma labari, itama sai murna take tace." Nasan kun kwaso yunwa to ga abunci can cikin Fula's a kicin yau har nama na siya muku na sanya muku a miya." Mimi ta tashi da sauri taje ta d'auko mana, tare da d'ebo mana ruwa me sanyi na cikin randa, cin abuncin kawai nakeyi kwata-kwata bana jin tes d'insa a bakina, ganin Umma tana kallona a fakaice yasa na fara yak'e INA biyewa Mimi muna ta labari. Mimi tace." Umma kinga ankon da muka futar za muyi." Umma ta karb'a tana dubawa tace." Aikuwa dai atampar tayi kyau kuma daga ni me tsada CE." Nace." Umma ai material din yafi ta tsada shi dubu goma sha biyu ne fa." Umma ta b'ude bakinta cike da mamaki tace." Da ubanku ina zan samu kud'in siya muki har dubu ashirin da hudu bayan kud'in dinki." Nayi karaf nace." Umma gaba daya Dana lissafa kud'in sun kai dubu arba'in da bakwai da atampar da material din da shaddar." Umma ta gyad'a kawai tare da fadin " kun shirya ruguza ni kenan yo ni ina naga dubu arba'in har da bakwai a Hamsin kad'an ne babu, so kuke in rusa jarina inyi muku anko kunga daga baya sai mu koma mu tsuguna muna tsotsar tsamiya." Jin abunda Umma tace yasa gabana fad'uwa dan gaskiya bana kaunar harkar k'aranta a rayuwa ta bana so ace ba muyi ko wane anko ba, in San samu ne ma da sabbin takalimi da jaka da mayafi." B'ata fuska nayi ina cin abuncin kamar bana so. Ta kalle ni a nutse tace. " naga kin b'ata fuska don ubanki so kike in siya muku anko ni kuma Ku karya ni ko, to bazan siya duka ba, Ku zab'i daya a cikin guda ukun, dama si kullum abunda ake fada muku kenan Sana'a tana da dad'i da kuna Sanar Ku da duk babu abunda zai gagareku, ko kuyi bakwa yi da aunty Ku tasan duk hanyar da zata bi ta nemi kudi saboda haka ni babu ruwana." Shiru mukayi duk murnar mu ta koma ciki. Wasu hawaye ne suka fara zubo min na takaici! Mimi ma ina kallo idonta duk ya ciki mda k'walla Umma tace "kuyi kukan jina ma ni babu ruwana." Yaya Aminu ne ya shigo dakin da sallama a bakinsa Umma ta amsa masa ya zauna yana kallonmu cike da mamaki hankalin shi yafi karkata kan Mimi yace." Meye suke kuka." Nan Umma ta warware masa abunda yake faruwa.

Dariya yasa tare da nuna Mimi da hannu yace." Sam kuka baya yi miki kyau gwara ma ki daina."Mimi ta zumb'ura bakinta yace." Nawa ne kud'in atampar."? Da sauri nace" dubu hudu ce ." yace." To zan bada shikkenan ko." Sakin fuska mukayi dukaninmu nace "to shaddar fa."? Hararata yayi yace." Wannan kuma sai Ku nemi Wanda zai siya muku." Mimi tace." Asma'u ina ganin in muka samu guda biyu ma ai mungode Allah." Shiru nayi mata domin ba haka naso ba." Umma tace "sai Ku nemi kud'in dinki don wallahi kuka d'auko dinki me tsada me cin kayan dinki to bazan biya ba." Nace. " Umma kinsan shi material din fa dole sai anyi masa bauta an siyi shafi da sauransu gaskiya zai ci kudi sosai, bayan haka kuma don Allah ki siya mana sabbin takalma". Hararata tayi kawai ta juya suna magana da Ya Aminu.


******
Biyar dai_dai yana gidan gomnati nan aka yi masa ido har ofis dine me girma governor ya zauna kan wata lumtsime miyar kujera suka gaisa a tsana ke, me girma governor ya kallashi sai ya ji gabansa na fad'uwa ganin yanda Yaro yayi masa mugun kwarjini, yace." Bisimillah ga ruwa kasha." Amjad yayi murmushi tare da fadin." Nagode me girma shugaba." Bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login