Showing 51001 words to 54000 words out of 54100 words

Chapter 18 - AYNUL HAYAT COMPLETE HAUSA NOVEL

12 Dec 2024

8212

afalon yasa yaje kitchin yadauko ruwa yasha da harzai koma wata zuciyar tace dashi kaleka dakin HaYaT mana kasani ko banda ita acikin masu kai lefen?


Haka kuwa akayi yana lekawa can ya hangota tsakiyar gado kudundune cikin bargo yajima yana nazarinta kafin yamaida kofar ahankali yatako zuwa kan gadon

Jin an hau gadon ne yasata juyawa da sauri taga ko waye

Suna hada ido dashi yasakar mata murmushi mai laushi

Dauke kanta tayi daga kallonsa ganin shine wani abu taji yatokare mata kahon zuciya tarasa farin cikin ganinsa tayi ko sabanin hakan
Lumshe idanunta tayi takwanta

Shiru tayi tana jinsa yashigo bargonda take yakwanta bayanta tareda zagayo hannunsa ya mannata da jikinsa yana shakar kanshin jikinta wata irin ajiyar zuciya yasauke cikin wata irin murya yace

HaYaTyy kinsan irin kewarki da nake kuwa?

Meyasa kike guduna kike kin yimun magana adik lokacinda nabukaci haka?

HaYaT mena miki ne wai?


Motsi tayi ahankali taja jikinta daga jikinsa tayi gaba kadan bata mishi magana ba

Kara matsawa yayi ya hade jikinsa da ita

Sai alokacin HaYaT ta tashi tareda yafe bargon daga jikinta cikin masifa tace

Wai meye haka ALI?

Meyasa kakeson takura rayuwata ne?

Meye hadina dakai?

Dan Allah katashi kafita kabar dakin nan karufa mun asiri tun kafin wani yashigo yaganmu nashiga uku!

Toh saime?

Keba Matata bace?

Kai kasanda wanan!

Amma nidai kawai katashi kafita tafada tana nuna masa kofa

In kuma naki fa? Yafada yana kallonta

Maimaikon tabashi ansa saita saka mishi kuka tareda komawa ta kwanta ta takure guri daya ahankali tafara magana

Ya ALI ciki ne dani! Yau watana biyar Kenan banga al'adana ba ni kaina ban ankara ba sai kwanan nan, nashiga uku Ya ALI meye makomata agidan nan ?

Meye makomar abunda ke cikina?

Wane irin kallo jama'ar gidan nan zasu mun?

Wacce irin ansa zan basu adik lokacinda cikin nan ya bayana kowa yasan dashi?

Na tabbatar nan gaba zan fuskanci matsala da kuncin rayuwa fiyeda wacce nafito cikinsa abaya!

Janyota yayi yana rarashinta ta hanyar hada bakinsa da nata yashiga aikinsa ba tareda yace da ita kalla ba

Dayake ita dinma nema take haka tabiye mishi saida suka biya bukatar junansu bayan sunyi wanka yasaka kayansa har alokacin baice da ita komai zai fita takira sunansa ahankali

Juyowa yayi ya kalleta yana jiran me zatace

Ya ALI abunda yakaka gurina kenan?

Banida wani amfani agareka saita irin wanan hanyar? Takarashe maganar tana kuka maicin zuciya

Dawowa yayi ahankali yazo inda take yatsuguna yana shafa kanta tareda share mata hawayenta yana fadin

Kiyi hakuri HaYaT lokaci na nan zuwa dazan sanarma kowa alakata dake zaki koma dakinki kiyi zaman aure kamar yanda ko wacce mace take kinji?

Girgiza masa kai tayi tana fadin

Nanda wata hudu zamu rabu kacika mun alkwarina kamar yanda nima zan cika maka naka alkwarin Ya ALI ina haihuwa zan baka abunda na haifa alokacin nakeso ka sauwake mun nikuma nakama gabana

Jin kalamanta yayi kamar zubar ruwan dalma azuciyarsa daurewa kawai yayi ya kakaro murmushi yace

Shikenan karki damu da wanan Allah yakaimu lokacin!

Yana gama fadin haka yatashi yafita zuciyarsa na kuna

Itakam saida tasha kukanta mai isarta tukuna nan bacci yayi awon gaba da ita zazzabinda takeji dazu yadawo mata sabo...

Anyi biki an watse lafiya washe garin ALI yazo dayake akwai sauran yan biki basu je gida ba afalo yazauna ana fira dashi harda Khadija tana nan

Cikin wasa da dariya ALI yace toh fa jama'a kowa ya yafeni indan duniyar nan ta yanzu ba'asan gawar farin ba

Dik falon tsik sukayi na sakani biyar kafin Ammiey tace hakane Allah ya yafe mana baki daya kowa ya ansa da Amin
Saidai Ammiey taji wani abu aranta...


Yadan jima anan yana zuba ido yaga ko HaYaT zata fito amma yajita shiru, saida yagaji kafin yatafi yarubuta mata sako ta Watsapp kamar haka

_Sallam HaYaTyy da fatan kin wuni cikin koshin lafiya da babyna Allah yasa hakan Amin! Inaso a iya zamana dake nasan namiki abubuwa dayawa arayuwa dan Allah ki manta da komai kiyafe mun koda bayan kin haihu agaskiya bazan iya sakinki ba da hankalina da wayauna ina mai baki hakuri daki yarda dani muyi zama na amana da gaskia, HaYaT ina sonki ina kaunarki ina kuma kishinki dan Allah karki sake yimun zancen wani Hamdan atsakaninmu kinji? Ina jiran ansarki daga mijinki Uban 'Ya'yanki ALI GADANGA nabarki lafiya._

Yana gama rubutawa yatura mata yama su Ammiey saida safe yatafi

Da kallo Ammiey tabishi tanaji aranta kamar tace yadawo karya tafi, saidai bazaiyuba saboda yazama dole yaje gidansa inda iyalinsa...


ALI yana kan hanyarsa yaga wani akwance gaban inda zai wuce kamar mutumen yayi hatsari ne, dayake wajajen shadaya na dare yasa yafurta subhanallah da sauri yatsaida motarsa gefe tareda nufar mutumen nan yana fadin Malam lafiya?

Kafin yasake magana saijin kan bindiga ALI yayi akansa an buga masa ita d'ร  karfin tsiya dafe kansa yayi tareda zubewa kasa asume

Dikda haka bai ishi wanan mutumenba saida yasaita bindigar akirjin ALI ya harba masa ita harbi har biyu agurare daban daban

Dayake bindigar irin silence din nan ce wacce bata kara yasa harya gama abunda zaiyi yaciro wayarsa yadanna wata number kara daya biyu aka daga yace OGA nagama aikin fa!

Yayi shiru alamar yana jiran abunda za'ace dashi

Can kuma yace angama Oga!

Kashe wayar yayi yadauki ALI dayake kwance cikin jini ba alamar rai atattare dashi yadaukeshi hoto tareda turawa ta numberda sunan OGA ta wtspp

Ko seconde talatin ba'ayi ba aka maido kira da number mai suna OGA wanan da alama cikin fushi OGAN yake magana

Sory sorry OGA wanda yayi harbin yaketa nanatawa kafin yakashe wayar yaduka yacicibi gawar ALI yasaka cikin motarsa yashiga yabar wajen da sauri kamar zai tashi sama...



Bangaren HaYaT kuwa lokacinda Message din yashigo mata saida taji yayan cikinta sun kada haka kawai batasan dalili ba jikinta ne taji gabadaya yamutu gabanta na dukan uku uku

Kometa tuna kuma saita mike zunbur tafito falo tana dube dube

Ammiey ce talurada ita tace HaYaT lafiya? Nazata kinyi bacci ae!

Ba komai tace Ammiey tana murmushin yake tajuya takoma dakinta ta kwanta gabadaya batajin dadin kwanciyar tashi tayi tazauna tareda lalubo wayarta

Cikin sanyin jiki ta danna number ALI saidai wayar tayita kara harta tsinke ba'a daga ba

Takira kusan sau uku tukuna ta hakura takoma ta kwanta badan tanajin dadin kwanciyar ba

Wata zuciyar ce tace da ita kika sani ko yana tareda matarsa Sajidah bazai iya daga kiranki ba?

Nan take taji kishinsa yakamata dajin haushin Sajidah....











โœ๐Ÿป
[8/1, 7:01 AM] Hayat: ๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž
๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž

*AyNuL HaYaT๐Ÿ‘„*
_MATAR ALI GADANGA_


๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž
๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž๐Ÿ’Ž





*_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da KuMa RuBuTaWaโœ๐Ÿป*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOl๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿฆฑ*
*_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*

*_____________________*
*NiGeR Ma FiErTรฉ๐Ÿค™๐Ÿป*
๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช
๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช
๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช
*_________________________________*
*ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุณุฃู„ูƒ ุญุจูƒ ูˆุญุจ ูƒู„ ู…ู† ูŠุญุจูƒุŒ ูˆุญุจ ู†ุจูŠูƒ ู…ุญู…ุฏ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…. ูˆุญุจ ูƒู„ ุนู…ู„ ูŠู‚ุฑุจู†ูŠ ุฅู„ู‰ ุญุจูƒ ูŠุง ุฑุจ ุงู„ุนุงู„ู…ูŠู†๐Ÿ‘๐Ÿป*
*_________________________________*

*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*โœ๐Ÿป
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*





*_AYNUL HAYAT_* yazo muku daga maruciyar
๐Ÿ‘‡๐Ÿป

_*DEEJA*_
*-_-_-_-_-_*
_*KISHIYAR AMNOOR*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
_*WASU MAZAN*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
_*NIEMATULLAH*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*_MAI KYAU_*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*





2โƒฃ





Daya gama bada karatunsa yafito kallo daya yamata yadauke kansa cikin isa yace kisameni ofis!

Yi tayi kamar bataji shiba!

Bakiji dake nake ba?

Naji OUSTAZ ina zuwa! Tafada cikin daga murya.

Mamakinta ne yakamashi saidai baice da ita komai ba yayi gaba.

Batabi takan shi ba classe tashiga abunta akayi karatu da ita, saida aka sauko break tukuna tanufi ofis dinsa da sallama tashiga ya ansa batareda yadago kanshi yakalleta ba dan baima shaida muryarta ba yacigabada da rubutunda yake

Kusan minti biyar yaji shirun yay yawa yana dago ido yaganta tsaye da alama tagaji da tsayinda take sai faman cika take tana batsewa

Malama lafiya kikazo kika mun kerere aka haka?

Akufule tace bansani ba!
Ina kai kakirani kace nasameka ba?

Nifa nagaji da wulakancinda kake mun batareda namaka wani abun ba OUSTAZ!
Haka kawai dik kabi katsaneni bakason ganina akan me?
Naji da abunda yake damuna agida mana!

Toh kasani bazan sake dauka ba wlh dik lokacinda kasake yimun wani abun saina baka mamaki agaban dalibai inma dukana zakayi ruwanka daman kasaba abunda nayima za akala ba dukanka kamun ba ehe!

Ta inda tashiga ba tanan take fita ba

Shikam sakatoto yayi yana kallonta saida tagama dan kanta tayi shiru tareda fita waje kofarma abude tabarta bata rufe ba๐Ÿ˜†

Saida yajima yana mamakinta karamar yarinya irin wanan tasameshi tagaya mar maganganu iri haka?

Lallai ko zaiyi maganinta nan gaba!

Tashi yayi yarufo kofar yadawo yazauna yaso yacigabada aikinda yake amma abunda AyNuL HaYaT tamasa yadamesa ainun yakasa tabuka komai dan haka tashi yayi kawai yanufi waje motarsa yanufa yashiga tareda barin scul din.

Kai tsaye gidansa yanufa dayake unguwar francophonie wani kantareran gida naga yatsaya tareda yin oda nan da nan mai gadin ya wale masa kofar gida yashiga masu aiki sai kwasar gaisuwa suke yana ansawa kamar bayaso.

Yana shiga yatarda ita falo bayan sallama dayayi yashige dakinsa yanda kansa ke sara masa ne yasa yakwanta kan bayansa yana kallon rufin daki.

Ba sallama tashigo tayi wani salle tafada jikinsa tana fadin ALI'na yaka shigo haka ko oyoyo baka mun ba kawuceni kashigo daki ina fatan dai lafiya?

Cikin sanyin murya yace haba tawan ba sannu da zuwa kawai saiki fado mun jiki haka?

Tashi tayi daga jikinsa ta kalleshi tana wani yatsina fuska tace

Gani nayi kashigo yau ba kamar yanda kasaba shigowa ba shiyasa! Takarashe maganar tana kallonsa

Batareda yasake kallonta ba yace bata mun rai wata daliba tayi shiyasa yanzu hakama kaina yafara ciyo.

Wani dogon tsaki taja tareda mikewa tsaye tana kallonshi tace indai wanan ne kadanma kagani wlh tunda kanace saika bada karatu daman ba abunda yasa kanace so kawai kake kana ganin yan mata iri iri suna yawo agabanka, wata kilama yarinyar cewa kayi kana sonta taki kulaka shiyasa mtswwwwwwwww

Banda haka ace mutum yanda asibiti takansa amma yazo yamakallema karantarwa?
Nan gaba ciyon zuciya zasu sakama bana kai ba!


Wani irin mikewa yayi tareda cakumota harya daga hannu zai mareta sai kuma yafasa!
Idanunsa jajur yace ki godema Allah ina sonki dayawa shiyasa amma badan haka ba wlh dayau sainaci mutuncinki agidan nan!

Sakinta yayi tareda shigewa toilet yabarta nan sai faman masifa take...


Daya dawo daga sallahr isha yunwa yakeji kamar yaci babu yana zuwa yatardata zaune tana kallo

Can ciki ta ansa sallamarsa

Dinnin table yanufa ganinsa wayam yasa yajuyo yatambayeta ina abincina Farida?

Ban girka ba!

Tafada kai tsaye batareda shakkar komai ba.

Haushi ne yakumeshi dan haka baice da ita komai ba dan bayason karin damuwa akan wata damuwar!

Shiga dakinsa yayi yadauko key dinsa yanufi waje kai tsaye gidansu yanufa.

Yana zuwa yatarda Mahaifiyarsa da kaninsa falo bayan sun gaisa ne yacema Salimat jeki dauko mun abinci naci.

A'a ina matarka kai kullum zuwa gida cin abinci ALI? Toh meye amfanin auren indai bata iya daukar nauyin cikinka?

Cewar Ammie

Maama nidai aban inci Faridah batada lafiya ne shiyasa yau batayi girki ba!

Murmushi kawai Ammie tayi dan tasan komai, sam bayason laifin matarsa shikuwa irin tashi jarrabar Kenan!

Indai kanason ganin bacin ran Ali tofa kafadi aebun Faridah yanzun zakaga yacanzama gabadaya!

Cin abinci yayi son ransa yazauna suna hira da Ammie nan Daddy yatardashi bayan sun gaisa anjima kadan yamusu sallama yatafi.

Koda yakoma tuni tayi bacci aikin Kenan yafada!

Batada aiki saina bacci wani sauke hakkin miji wanan bata sanshi ba, sai uban korafi kamar me!

Saida yakamala dik abunda yake tukuna ya kwanta saidai yakasa bacci wulakancinda AyNuL HaYaT tamishi yashiga dawo masa alokacin dakyer da haka bacci barawo yayi awon gaba dashi cikeda burin abunda zaima AyNuL HaYaT in sun hadu.

Haka yauma bata makara ba Anna tace taje tareda su Amal din.

Basuda shi farkon leรงon saida malamin mathรฉmatique yafita tukuna yashigo sanye yake cikin kananun kaya sun matukar masa kyau ba kadan ba
Dik yan matan classe din ba wacce bata rude ganin Ali ba haka kowace adu'a take Allah yasa yace yana sonta!

Sabanin AyNuL HaYaT wacce sam tunanin so ko wata soyayya bai taba zuwa kanta ba, daya shigoma ko kallo bai isheta ba.
Tanajin yanda yan matan kusada ita zuke zuzuta kyansa da kwarjininsa ita dai tace kansu akeji!

Sai wani shan kamshi yake musaman yanda yaga yan matan ajin sun rudu da ganinsa dama shi hakan yake birgeshi yasha ado yan mata suyita mutuwa akanshi burinsa Kenan๐Ÿ˜† yau harda wani uban gilashi yasaka baki kirin wanda ko kwayar idonsa mutum baya iya hangowa aciki.


Daya da ya yake kallonsu can yasauke idanunsa kan AyNuL HaYaT ganin yay itako takansa batabi.
Karatunta take kawai abun yabashi haushi sosai wanda baisan dalilin jin haushinta ba dan bata kalleshi ba.

Karatunsa yabada yagama cikin minti talatin haryanzu kuma baici sa ar ganin tadago ta kalleshi ba, sai yake gani kamar harda karatun hankalinta baya kai da gangan yace zai musu texte akan karatunda yayi yau!

Nanfa yan ajin kowa hankalinsa yatashi sai zare zare ido suke wasu harda zufa๐Ÿ˜… saboda sarai sukasan halin OUSTAZ yaci ubansu idan basu samu ba ba komai bane agareshi!

Da gangan yarubuta tambayoyin masu wuyar ganewa saboda kawai AyNuL HaYaT takasa yaci zalunta๐Ÿ˜‚

Cikin ikon Allah saida kowa yagama kai nasa da daya daya yana ansa yaduba in yaga kayi daidai yabaka maki in kuma baka samu ba kashiga layin yan jiran ansar hukunci.

Tashi tayi takai tatsaya ansa ganin tasamu dika ne abun yabashi mamaki kaf ajin itane kawai tasamu dika, bata yayi takoma tazauna haushin samunda tayi ne yasaukeshi akan yan ajin!

Ranar dik yaci ubansu manyan yan mata harda kukansu๐Ÿ˜‚

Bayan an sauko ba irin zaginda Ali baisha ba gun dalibansa ba harda fata.

Kusan sati daya kullum saiya musu texte amma yakasa samunta dan kullum ci take, ahaka har akazo jarrabawar karshen shekara, matsinda take fuskanta gun mahaifinta yasa karatunta ayanzu yaja baya tafadi sosai bangaren arabiya wanda OUSTAZ ALI sosai yayi mamakin ganin yanda taja baya haka.

Kasa jurewa yayi saida yakirata ofis wanan karon zuwa tayi akan lokaci saboda OUSTAZ ALI din yabar takurata kamar da.

Da sallama tashiga cikin muryarta mai sanyi yadago ya ansa tareda bata umarnin zama.
Ba musu tazauna kanta akasa tashiga wasada yan yatsunta.

Can yakira sunanta tareda miko mata rรฉsultat dinta na Arabe yana fadin duba kiga

Saida ta kalla sosai taci 12/20 shiru tayi batace dashi Komai ba.

Shine yaga shirun yay yawa yace me yake damunki ne kwanan nan karatunki yaja baya sosai haka AyNuL HaYaT?

Ba komai tace!

Dan murmushi yayi yace ba gaskia bane!

Kifada mun meke damunki amatsayina na malaminki idan ba damuwa.

Maimaikon ansa saita saka mishi kuka dakyer tasamu kukan yatsaya tashiga koro masa bayani kamar haka

OUSTAZ gida ne mahaifina zai badani sadaka yace nafitoda mijin aure nikuma banida wani wanda yataba cewa yana sona, wlh banison aure karatu nakeso nayi ga yar uwata nan shekarunmu daya da ita amma saini kawai zasuma aure dan mahaifiyata bata raye abun ne yake damuna ni kaina bansan wanan exam din banyi kokari ba sai yanzu!

Takarashe da kuka tasa hannayenta dika biyu tarufe fuskarta tacigaba kukanta

Bai rarasheta saida tayi iya son ranta tukuna tayi shiru dan kanta, sai alokacin yake cemata kiyi hakuri bin nagaba bin Allah wata kila irin taki kadarar Kenan indai mijinda zaki aura zai barki kicigabada da karatunki aeba damuwa bane wanan!

Sam ALI GADANGA bai nuna jin tausayinta afuskarsa ba.


Nagode kawai tasamu tace dashi ta tashi tafita.

Resul dinsu tafito taci saidai mutum uku ne suka shiga gabanta, aekuwa Anna tasamu abun fadi tace aekuwa lailai yarinyar nan aure takeso!

Koda Abbu yadawo tagaya mishi karya da gaskia wai tafara bin maza a scul

Nan yace sati daya yabata tafitoda miji bai shiga hakkinta ba yabata dama idan tayi wasada da damar zatayi mamaki ne!



-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-
Ali nifa wallahi nagaji gwarama kanemo yar aiki idan zaka nemo haba kullum nice shara wanke wanke guga saikace yar aiki?


Faridah bakida hankali ne zakizo akaina ko sannu dazuwa babu kina mun masifa akan naka miki yar aiki? Ba halinki bane yake korar miki su? Bawace zata iya zama dake muddin baki canza irin wulakancinda kike musu akullum ba!
Ace sam bakisan darajar dan Adam ba?

Eh! Akarkashina suke dan haka dole natakasu yanda naga dama aeba haka kawai suke mun ba biyansu nake!

Toh shikenan!

Kisa kafarki kifita kinemo wacce kikasan zata zauna dake da halinki da kanki.

Wlh bazan je ba! Ina zan samosu kasan banida kowa anan shiyasa kake mun abunda kaga dama nan tasaka kuka gogan naku kuwa tuni yasauko yashiga rarashinta tareda mata alkwarin zai nemo mata mai aikin cikin satin nan!


-_-_-_-_-_-_--_-_-_-_-
Zaune take banda aikin kuka ba abunda take yaune mahaifinta ya tabbatar mata ana gama sallar azhur za'a daura aurenta da wanda yaga dama wai acewarsa tun bata janyo mishi abun kunya ba.

Abu biyu ne suka hade mata guri daya ga ciyon cikinda take dik wata tanaji yana zuwa ahankali ahankali dan gobe ne lokacin farawanta gabadaya taji duniyar tamata zafi.

Ba abun taje gun dangin Mamanta ba dik kanwar ja ce! Suma bawani sonta suke ba, dikda dik yawancinsu suna kauye mutum biyu ne tasani da sunan dangin Mamanta anan garin kuma suma basu damu da ita ba!

Mikawa Allah lamarinta tayi yazaba mata abunda yafi alkhairi agareta.

Lokaci natafiya bugun zuciyarta nakaruwa, jitayi kamar zata shide lokacinda taji mahaifinta yashigo yana kwala mata kira tafito.

Jiri na dibarta tafito rikeda cikinta kanta ko dan kwali babu taje ta tsuguna gaban mahaifinta kudi yamika mata tasa hannu takarba tana jiran jin na meye?

Kafin tace wani abu saitaji yana fadin sadakin aurenki ne!
Nafita hakkinki maza kishiga kifito mijinki yana kofar gida da abokinsa yana jiranki.

Suma ne kawai batayi agurin ba, wani iri takejin kanta hartake tambayar kanta anya Abbu mahaifinta ne wanda ya haifeta kuwa? Anya kuwa ita yar cikinsa ce?

Idan kuwa ita yar cikinsa ce ina wanan soyayyarda take tsakanin d'a da mahaifinsa tashiga?

Ganin taki tashi ne yasa Anna tasaka Amal dobo kayanta tasaka ajaka takawo.

Haka suka tasa keyarta agaba saida tashiga mota idanunta dik sun rufe ko ganin gabanta batayi tanemi kukan tarasa gabadaya!

Wani abu kululu takeji yamata babakere amakogwaro bata kalli suwaye amotar ba danko gani batayi yanda yakamata ayanzu.

Wata hรดtel suka nufa mai suna hรดtel gawai saida suka tsaida motar taji ance fito ba musu tabi bayansu sai alokacin tadaga kai taga cikin hรดtel suke tsoro ne yamugun kamata kardai babanta siyarda ita yayi ga yan iska banda haka mezai kasu hรดtel tana matarsa?

Wata zuciyar ce tace da ita kika sani ko badan garin bane shiyasa yasauka hรดtel?

Sai alokacin tadanji sanyi aranta.

Wajen rรฉception suka nufa dik bayan mutanen biyu take gani bataga fuskokinsu ba.

Anan dayan yatsaya sukayi musabaha zai tafi yace kibi mijinki Allah yabaku zaman lafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login