Showing 3001 words to 6000 words out of 54100 words
saita bata taci dik aboye!
Saida tagama ci tukuna takalli Inna lariya tace nagode sosai Inna lariya badanke agidan nan bansan ya rayuwata zata kuma kasancewa ba!
Allah yabar mun ke har karshen rayuwata Inna lariya
Shafa kanta Inna lariya tayi tashiga yimata nasiha tacigabada hakuri insha Allah komai mai karewa ne nan gaba!
Inna lariya kullum haka kike cemun amma kinga haryanzu Abbu baya sona!
Allah sarki HaYaT kidaiyi hakuri kinji?
Kina adu'oi danace kiyi kullum?
Gyada kai tayi tace inayi kullum fa!
Yauwa yar Albarka tashi ki koma kar wani yazo yaganki anan kuma wata fitinar ta kunno kai.
Badan tasoba ta tashi takoma dakinta wanda yakeda gado da katifa aciki akwai toilet wajen saka kaya dakuma katon madubi da wajen ajiye kayan shafe shafe saidai ko mai nashafawa babu akai balle wata fowder ko Jan baki.
Dakinta bayada laifi saidai idan kaga nasauran yaran ne zaka rena natan saboda akomai sun banbamta
Banda kayan makaranta HaYaT batada wasu kayan azo agani nasakawa haka take daban cikin yara.
HaYaT yace ga Alhj Abdul hameed Al abbas, itace yarsa tafarko da matarsa uwar gidansa ta haifa masa wacce bayan haihuwar AyNuL HaYaT da kwana uku tace ga garinku haihuwar AyNuL HaYaT tazoma Alhj Abdul hameed Al abbas da rudani kasancewarsa bafulatani fari ne sol kamar yanda yake ikirarin kaf danginsu ba bakin mutum aciki haka itama mahaifiyar AyNuL HaYaT fara ce sosai ta bugawa amujala amma cikin ikon Allah tahaifo yarta AyNuL HaYaT wacce tun ajarintarta baka ce dikda bawai bakace sosai ba kalarta mai kyau ce sosai amma ga wanda yasan asalin kyau, tunda aka haifeta mahaifinta yanuna kiyayya kiri kiri da launin fatarda tazo dashi, koda mahaifiyarta ta rasu bayan suna dakanshi yasaka mata sunan AyNuL HaYaT tundaga ranar yadauki mai aiki yatattara dik lamuranta yasakarma mai aikin gabadaya dikda amaryarsa Hannat tana nan itama din tsanar yarinyar take.
Bayan wata uku da haihuwar AyNuL HaYaT Hannat tahaifo yarta wacce taci sunanta Amal yarinyarda ake nunawa gata tun ajarintarta bayan shekara uku kuma Hannat tasake haifo yaranta yan biyu Jamal da Jamila daga kansu kuma Hannat bata sake haihuwa ba.
Ikon Allah ne kawai yasa AyNuL HaYaT tanada sauran shan ruwa aduniya saboda sam bata samun kulawa yanda yakamata.
Tun tana yar karama ta taso cikin zafin rashin Mahaifiya Abbunsu ma baya sonta wani lokacin ko abinci sukeci intazo wucewa awajen saisu tashi wai tana wari
Hakadai rayuwa tacigabada tafiya yanzu AyNuL HaYaT tana shekararta ta karshe a karamar secondary itada Amal ajinsu daya sosai tafi Amal kokari akaratu dikda ita Amal din tanada mai koya mata agida ita kuma AyNuL HaYaT din bata dashi haka Allah yayita da kwakwalwa.
Haka tagamuda OUZTAZ ALI GADANGA wanda tun zuwansa ba wacce yatsana yagani kamarta abu kadan yake jira tayi yadaketa, dikda dik ajin ba wacce take karatu irinta kullum itace ta daya a ajin amma hakan bai hanashi tsanarta ba!
Shima acewarsa baka ce kuma kazama wai idanunta ke bashi tsoro gasu manya kuma farare kamar aljana sai karamin bakinta dayake ja ne batareda tashafa mishi Jan baki ba haka Allah yamata shi jajur dashi kamar ita tazanama kanta shi.
Dikda ayanzu shekarunta shabiyar ne haka bazai hanaka gano irin yanayin jikinta ba wanda kirar coca cola ne AyNuL HaYaT ita ba doguwa ba kuma bazaka sakata cikin gajeru ba tana nan tsaka tsakiya.
Tanada dogon hanci wanda yakusa tabo lebenta nasama yayi daidai da fuskarta tanada gashi sosai ga laushi ga tsawo ga wanda yasan me ake kira da kyau zai saka AyNuL HaYaT cikin jerin sarauniyar kyau ta duniya.
Kasancewarta cikin fararen fulani yan uwanta gaba da baya yasa suke ganin aebun fatarta.
Kwance take tana tunani taji Abbunsu yashigo da alama tsaraba yasiyo dan yanda taji Jamila da Jamal suna tsalle da ihu
Can taji sunyi shiru taji kuma kamar Abbun nasu yace akirata da sauri jin motsin zuwa inda take yasa tarufe idanunta kamar mai bacci
Jamal ne yashigo ganin tana bacci yasa yakoma, bayan minti biyu tasakejin alamar ana zuwa wajenta haka takuma rufe idanunta
Wata leda taga yashigo da ita ya ajiye mata agefen gado yafita.
Yana fita ta tashi dasaurinta tadauko ledar tabude chocolat ne tagani kusan kala biyar saida kwalla tazubo mata ganin yau antuna dawata AyNuL HaYaT agidan harda bata rabonta!
Nan tace aranta ko du'arda Inna lariya tace tadinga yi ne tafara aiki?
Washe gari haka ta tashi yaukam batayi latti ba dan haka tayi karatunta cikin kwanciyar hankali kasancewar basuda leΓ§on da OUSTAZ ALI GADANGA.
Bayan sun sauko daidai zata fita shima yayi daidai lokacinda zai shigo saida yawatsa mata wata irin harara tukuna yawuce.
Itakam aranta take fadin wanan wane irin mugu ne? Haka kawai ban masa komai ba yatsaneni!
Wata zuciyar ce tace da ita aekin kusa rabuwa dashi kihuta daga wanan shekarar ne keda shi bye bye...
Yau week-end tunda ta tashi takejin wani irin ciyon ciki wanda tun tana hakuri harta kasa jurewa daman gata da shagwaba dikda batada gata haka hallitarta take bata iya jure ciyo koya yake!
Kuka take ganin abun sai gaba yake yasa tashiga kiran Anna Anna Anna da dikkanin karfinta
Hajiya Hannat tana farlo dasu Salma takejin muryar AyNuL HaYaT na kiranta dayake bata taba yimata irin wanan Kiran ba yasa ta tashi ba tareda bata lokaci ba tanufi dakin tana fadin lafiya kike kirana saikace sa'ar wasanki?
Ganin HaYaT tana murkususu ne yasata isa gareta tana dagota taga alamar jini akasanta da sauri tasaketa tana fadin daman dan wanan abun ne yasa kika rikitani haka banza?
Anna dan Allah kutaimaka mun wlh mutuwa zanyi kikaini asibiti na rokeki Anna tafada tana neman shidewa
Kafin Annar tace wani abu sai ganin tayi HaYaT tasuma aeba shiri takira dreba yakaisu asibiti saida aka karbeta tacema dreban yakoma gida yadauko kayanta tacanza dan wanan yabace da jini.
Allura aka mata tafarfado tareda saka mata karin ruwa, ba abunda yake damunta sai tsananin ciyon mara wanda wanan ne na farkon farawarta shiyasa takasa jurewa!
Magunguna aka rubuto mata suka nufo gida tun amota Anna take zuba mata ashar wai saikace ba mace ba? Akanta aka fara balaga sakarci yamata yawa da shagwaba!
Haka dai tayita zuba kamar taci babu itadai AyNuL HaYaT shiru tayi ta takure gefe daya saida suka iso gida tafito ahankali suna shiga falo tawatso mata magungunan tana fadin idan kinga dama kisha!
Dukawa tayi tadauka tashiga dakinta dasu.
Da Abbu yazo Anna tagaya mishi dik abunda yafaru tadaura da fadin ae yanzu yarinya tagirma sai aure!
Wanan shegen ciwon marar idan mace tanayi saifa ta nemi namiji idan ba hakaba kuma taja musu abun kunya nan gaba!
Dan haka tun wuri yasan abunyi.
Ba kunya Abbu yaje har dakinta yashiga matsifa marar kan gado daga karshe dai yace tafitoda miji yamata aure tunda yanzu tagirma karta jawo mishi abun kunya idan kuma taki wlh sadaka zai bayarda ita kowama yahuta!
Kuka tasaka tana fadin Abbu kayafe mun yanzu fa shekaruna shabiyar ne kawai kuma ni banida saurayi bawanda yataba cewa yana sona!
Abbu karka mun aure yanzu karatu nakeso nayi dan Allah Abbu har kasa taduka tana rokonsa amma yace yana nan akan bakarsa ana basu hutun karshen shekara indai bata fitoda miji ba zai badata sadaka ne!
Haka yafita yabarta abun duniya dik yabi ya isheta tunanin neman mafita take amma bata samu ba daga karshe baccin wahala ne yayi awon gaba da ita
Yau kwana uku tana jinya ba laifi Anna dakanta take zuwa tadubata takuma bata abinci idanma takici ta takurata dole saitaci!
Yau kwananta hudu bataje scul ba hankalinta dik yana can washe gari dikda jikinta ba kwari haka tashirya zata tafi Anna tace taje tareda yan uwanta kafin tayi sauki tunda ita din mayyar karatu ce batada lafiyama amma tadage saita je!
Yau kawai taji kamar tarungume Anna dan dadi da murnarta tashiga motar saidai tana shiga yaran dik suka rufe hancinsu wai tana wari!
Itadai bata kulasu ba, ana isa makarantar saita tsinci kanta da yin yanga itama fa yau tazo akan lokaci kuma cikin mota saida tayi wani irin action kafin tafito so take kowa yasan tazo amota yau sai wani uban murmushi take kamar mai tallar makilinπ
Shigowarsa keda wuya yaduba mazauninta yaganta yahade rai kafin yace AyNuL HaYaT Abdul hameed Al abbas tana nan?
Jikinta har bari yake tamike tsaye tareda fadin na'am OUZTAZ
Wani wawan kallo yamata kafin yawatsa mata tambaya kwana hudu bakizo scul ba nagani a list absence dik sunanki ne aciki wanan satin zan iya sanin dalilin kin zuwanki?
Kamar tayi kuka dan tasan baya karbar uzuri tace OUZTAZ banida lafiya ne shiyasa!
Meyasa baki turo an sanar ba?
Nanfa tayi narai narai da ido sanin kotace Amal tasani bazata fadi gaskia ba!
Dan haka tayi shiru kawai yafi mata alkhairi!
Ganin taki ansa masa ne yasa yace tazo gaban kowa tayi tsaye harsaiya fita daga ajin tukuna wanan shine hukuncinta.
Wani irin kuka AyNuL HaYaT tasaka sanin yau awa biyu OUSTAZ din zai musu gashi haryanzu jikinta da saura shiyasa tasaka kuka taki motsawa daga wajenta
Ba irin barazarda OUSTAZ ALI bai mata ba amma taki dagawa daga inda take
Hakan datayi ba kamaramin kular dashi tayi ba!
karshe dai yace tafita tabar masa aji haka takwashe kayanta tafito da tsantsar tsanarsa aranta kamar me...
βπ»
[8/1, 6:58 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
π·π·π·π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·π·π·π·
_BAYAN LONG TEMPS SAIGASHI ALLAH YAYI NASAKE DAWOWA, MASOYANA INA ALFAHARI DAKU FATAN ALKHAIRI AGAREKU GABADAYANKUπ·_
4β£
Tunda suka shiga motar ta takure guri daya ko kwakwaran motsi batayi ita kadai tasan me takeji aranta
Tunaninta daya ne wacce irin rayuwa zata tarar agaba?
Rokon Allah take koma wacce iri ce yabata hakuri da juriya ta cinye dik wata jarrabawarda tashiga arayuwarta
Bangaren Ali kuwa wata zuciyar kokarin nusar dashi take akan abunda yake shirin aikatawa ba daidai bane, koma meye ae HaYaT matarsa ayanzu yanda yake daukar Faridah da muhimancin da daraja itama haka yakamata yadauketa koda aurensu bana shiri bane kuma iyayansa basu sani ba itama tanada hakki akanka!
Wata zuciyar ce tace dashi ae taimakonta kayi, dan taje amatsayin yar aikin gidanka aeba laifi bane shima ibada ce, ahankali yakai kallonsa gareta yanda dik tabi ta takure jikinta guri daya da yanda fuskarta ta nuna alamar damuwa karara akai taso tabashi tausayi, saidai tuna rashin kunyarda tamasa amakaranta yasa tausayin nata kaura daga zuciyarsa gabadaya...
Ko wanne da irin tunaninda yake aaransa har suka iso kofar gidan aka bude yashiga.
Saidai yanemi guri yatsaya amma yakasa Bude motar yafita itakam sai kokarin bude murfin motar take takasa dan yakulleta
Ahankali tajuyo ta kalleshi suna hada ido dashi gabanta yayi mumunan faduwa dan ita yanzu tsoronsa take ganinsa take kamar dodo agabanta da sauri takauda kanta daga kallaonsa ahankali takoma ta takure kamar yanda take dazu.
Saida yagama shan kamshi da miskilancinsa yakare mata kallo tsaf tukuna cikeda isa yace kina jina ko?
Eh tafada ahankali!
Kindaiji dik abunda nace miki dan haka inhar kinason zaman lfy agidan nan ki kiyaye karki kuskura naji wani korafi ko wani abu daban kinji ko?
Tana gyada kai hawaye nabin kumatunta masu zafi, hade rai yayi ganin hawayenda take banson munafunci ba!!!
Kikasan mena tsara zan fada aciki da zakizo kina mun kukan iskanci haka kawai?
Tsawa yadaka mata yana fadin shiruπ€«
Aekuwa tsananin tsoro sai neman kukan tayi tarasa gabadaya.
Anan yashiga yimata fada da gargadi hannunka mai sanda kafin sushiga cikin falon da sallama ba kowa falon nuni yamata da kujera tazauna
Zama tayi da jakar kayanta kusa da ita, shikuwa ya haye sama da alama kaf dakunan gidan asama suke.
Sai bayan yatafi ne take karema falon kallo
Sosai nan take yaba haduwar falon da dinbun dukiyarda aka zuba aciki dan gaskia falon ya hadu iya haduwa.
Ganin irin kyan gidan yasa take ayana aranta lallai dole ALI yarena mata irinsu wanda yakeda irin wanan dankareran gidan ae matar cikinsa za'asha kallo idan aka ganta, dik aranta take fadin ta tabbatar matarsa irin matan nan ne wanda ake kirada hurul ayn!
Kusan awa daya tadauka azaune tun tana saka ran fitowarsu harta cire, zaman ne ya gundureta gashi ba TV ba waya balle tadebe mata kewa ba kowa kuma sai kifci take kamar mayya.
Can taji alamar bude kofa da sauri tagyara zamanta ta tattaro nutsuwarta guri daya
Ahankali take saukowa cikeda yanga tana wani yatsina fuska bakinta tana taunar cingam kas kas kakeji kamar wata karuwar waje
Tunda take saukowa idanunta akan HaYaT suke nazarinta take kayanda ke jikinta da jakar kayanta ne suka matukar bata mamaki
Har tagama saukowa bata sani ba dayake hanyar kitchin kai tsaye daga kasauko daga kan benen cikin bata saniba tanufi hanyar kitchin din saida takusa shiga tukuna tadawo hankalinta!
Amma dan karta kwafsa agaban mai aikinta yasa takarasa shiga din, ba jimawa tafito itadai HaYaT da ido take binta tana tambayar kanta ita kuma wanan wacce irin marar kunya ce daga zuwa gidan mutane kisaka kayanda ko matar gidan inhar mai kunya ce bazata sakasu tafito ba!
Kur HaYaT take kallonta cikeda mamaki wanan kamar dodaniya doguwar rigace sanyeda faridah ta matseta sosai wanda komai na jikinta abayane yake tumbinta kuwa kamar na saniya yatara ruwa ko tafiya take saiya motsa gwarama atamfa idan tasaka tafi rufa mata asiri, tsawon rigar iya gwiwa ne tayi karin gashi shi yakara maida ita wata kura kura kamar tace tak kazuba da guduπ
Harta zauna HaYaT bata saniba tashagala da kallonta baki bude mamakin macen fal zuciyarta.
Keeee baki iya gaisuwa bane sai kallo?
Sai alokacin HaYaT tadawo duniyarta cikin inda inda tagaisheda ita
Bata ansa ba saima wani kallon wulakanci data jefeta dashi tace kece mai aikinda kikazo?
Ahankali tace nice!
Zauna kasa Faridah tafada cikeda kyankyami
Kallonta HaYaT tayi tana tunanin kodai bataji me matar tafada bane?
Ke waike kurma ce ko meye?
Kizauna kasa nace ba kinzo dawani kazamin jikinki kin zaunama mutane akan kujera kamar wacce kika kawo daga gidanku, toh kina jina ko?
Abunda zakiyi nafarko shine da safe ki goge kujerar nan tas kafin kifara komai!
Toh kawai HaYaT tace! Saidai tana mamakin wanan wacece haka da izzar mulki saikace masu gidan?
Dan ita sam hankalinta bai bata cewa wanan itace matar ALI din ba, saboda yanda ALI yake kodata da fadin akiyaye bacin ranta aganinta zatafi haka kyau tunaninta.
Saida tagama shan kamshi tukuna tace ta tashi tanuna mata komai, haka HaYaT take biye da ita ta nuna mata komai har sama takaita ko ina saida tanuna mata banda dakin mai gidan tace idan yafito shima hardashi zaki dinga gyarawa!
Cikin mamaki HaYaT take magana aranta daman wanan itace matar ALI ?
Cab!
Wani daki can kasa kusada kitchin ta Nuna mata tace nan shine dakin naki, anan zaki dinga kwana.
Nagode tace da ita atakaice, zuwa tayi tajanyo jakar kayanta takai dakinda ba komai acikinsa sai wata katifa itace kawai mallakin dakin, saidai dakin da toilet acikinsa.
Neman guri tayi ta ajiye jakarta taciro abun sallaya dan jin ana kiran sallahr isha tashiga tadauro alwarlla tafito ta gabatarda sallah anan kan sallayar tayi zamanta tana aduo'i da istigifar bacci yanaso yadauketa amma takasa yi saboda yunwarda takeji kamar me saboda rabonta da abinci tun abincin rana ne acikinta shima fargabar zuwa gidan ALI ya hanata cinsa takoshi kamar kullum.
***************
ALI kafada mun gaskiya wacece wanan? Saboda sam ni hankalina bai kwanta da ita ba!
Kace mun yar aiki ce, amma sam daga kayan jikinta har jakar kayanta irina masu kudi ne na tabbatar akwai abunda kake boye mun bakaso nasani gameda ita!
Yar zufa ce ta taru agoshinsa danshi sam baiyi tunanin kayan jikinta ba balle akaiga jakar kayanta.
Tabbas dik mai hankali yadubi HaYaT yasan cewa sam batayi kamada masu aiki aiki ba!
Balle yakarema kayan jikinta kallo dikda bawasu sabbin kaya bane amma kallo daya zaka musu kasan da kudi dayawa aka siyosu!
Tsarensa da idonda tayi ne yasashi dan rikicewa
Taso taganoshi can yaji wata dabara tafado masa
Cikin tabbatarwa yace kanwar wani abokina ce aikin shara da guga yake asibiti ni nace masa yanemo mun mai aiki shine yace akwai kanwarsa da yanzu take zaune gida batada aiki amma yace mun agidan gomna maici tayi aiki shekara biyu Kenan wani dalili ne yasa aka sallamota shiyasa
Yama cemun tanada aure, mijinta yatafi neman nakansa kinsan halin yan kauye katafi nema kabar matarka agida shekara da shekaru dalilinda yasa kenan tafara aiki!
Shine yasa nace yaka mun ita tarinka tayaki daman muna nema.
Idan kuma ban miki gwaninta ba sai gobe namaida ita inda nadaukota!
Jinda tayi yace yarinyar tanada aure ne yasa hankalinta yakwanta, saidai akaramar kwakwalwarta sam tunaninta baikaga duban kananun shekaru irina HaYaT ace tayi shekara biyu da aure ba.
Dan murmushi tayi tace ni na isa! Yanda nake wahalar nan ina aikin gidan nasamu yar aiki kuma nace banaso? Kaima aikasan dawasa kake!
Shafa fuskarta yayi yana fadin kin fiye son jiki matar nan!
Murmushi tayi tana fadin wayaki hutu?
Yauwa abunda na manta ban sanadar dake ba shine yarinyar nan tana karatu fa, agidan gomnan sun riketa kamar yar cikinsu ne shiyasa karatu kowane fanni tanayi danma yanzu ana hutu ne shiyasa.
Dan haka daga ankoma makaranta zata cigaba!
Hade rai tayi tace shi dan aiki talaka har wani yanci gareshi na karatu? Ae karatun ba dole bane dan haka ba ita ba karatu!
Wanan ne kuma baki isa ba!
Nayi da Yayanta zatayi karatu dan haka ke baki isa kihanani cika alkawarinda nadaukar masa ba, saidai kizaba idan bakison zamanta shikenan saiki cigabada aikinki amma wlh tallahi rantsuwarda ban kaffara idan har kikabari namaida yarinyar nan bake ba yar aiki har abada arayuwarki kuma dole kiyi aikinda dik yakamata maccen aure tayi agidanta!
Ganin yacanza mata yanda in yayi sosai takejin shakkarsa yasa tayi shiru, ita kanta tasan yana kokari akanta ba kowane dan aiki bane zai iya zama da ita da halinta ba.
Cikin shekara daya saitayi yan aiki fiyeda goma suna guduwa saboda mugun hali irin nata!
Can tace idan tafara zuwa makarantar ya aikin kenan?
Baiko kalli inda take ba yace Allah yakaimu lokacin sai atsara yanda za'ayi!!!
Sanin daman ba abincin zatayi ba yasa yafita yasiyo leda biyu yana dawowa Faridah bata falo din hakan yabashi damar shiga dakin HaYaT kwance yatarda ita akan sallaya idanunta arufe saidai daga ganinta kasan ba bacci take ba saboda yanda kwayar idanunta suke kai kawo.
Dikda jin motsin shigowa kanshin turarensa ne ya isarda sakonsa gareta hakan ne yasa taki motsawa tayi kamar tana bacci ajiye mata ledar yayi kusa da ita yafito abinsa.
Bayansa tabi da kallo saida yafita tashi tayi dasauri tarufe kofar dakin harda saka makulli takulle.
Bai karasa hawan