Showing 48001 words to 51000 words out of 54100 words

Chapter 17 - AYNUL HAYAT COMPLETE HAUSA NOVEL

12 Dec 2024

8208

da kinsan kukan nan naki yanda yake dakar mun zuciya da bakiyi ba, ki gaya mun me kikeso zan mikishi koma menene kinji?

Yakarashe maganar tareda dago fuskarta yazuba mata ido yana jiran ansarda zata bashi

Kallonsa tayi fuskarta cikeda hawaye ta lumshe idanunta kafin tabude bakinta ahankali labbanta suka furta Ya ALI so nake kamun irin yanda kake ma Aunty Sajidah...

Mamakinta ne yakamashi sarai yagane abunda take nufi, saidai tuna irin yanayin hallitar HaYaT ne yasa yakauda dik wani mamakinda yake akanta

Sakin habarta yayi tareda gyara zamansa amazauninsa aransa yake fadin faduwa ce tazo daidai da zama HaYaT dankoni nan amatse nake da bukatarki...

Itakam hada kanta tayi da gwiwoyinta tana mai kunyar hada ido da ALI da kunyar abunda tafada sai yanzu takejin haushin kanta da kanta....

Wata hadaddiyar hôtel yanufa wacce sai wane da wane yake iya hayar daki na awa dayama aciki can nesa da gari take, daki mafi tsada acikin hôtel din yabiya aka basu kye din....


Sosai suka nuna irin kewar junanda sukayi tsakaninsu ba kamar HaYaT dan yaukam tabawa ALI mamaki cire kunyarsa tayi da kinsa da take ada ta ajiyesu gefe tashayar dashi mamaki da irin sallonta, ALI ji yayi kamar yau ne rana tafarko daya fara tarawa da HaYaT saboda yanda yasake riskarta kamar burduwa...

Saida suka nutsu tukuna sukayi wanka suna fitowa ana kiran sallahr magrib ALI yanufi masallacinda yake cikin hôtel din HaYaT kuma tagabatarda sallahrta anan

Tana gamawa tamike ta linke abun sallaya wanda anan cikin dakin yake tana ajiyewa taji ALI yashigo da Sallamma

Kanta akasa ta ansa sallamar cikeda kunyarsa sosai

Murmushi yayi yanajin kaunarta nakara narkarda zuciyarsa

Karasowa yayi kan kujerarda tazauna yana fadin

Yanzun nan za'aka mana abinci kijira muci saimu tafi kinji

Dagowa tayi takalleshi ahankali kuma ta ajiye idanunta kasa tace ni banaci akoshe nake

A'a aekuwa baki isa ba abincin nan atare zamuci dan bazanyi asarar kudina ba ehe!

Yana rufe bakinsa sai sukaji ana buga kofar da alamar daya daga cikin ma'aikatan hôtel din ne, tashi ALI yayi yaje ya anso yadawo ya ajiye agabanta yana fadin oya sauko muci

Ba musu ta sauko saidai da gaske bataso saboda cikinta akoshe take kadan ta tsakura tace masa takoshi kallonta yayi baice da ita komai ba yacigaba dacin abincinsa saida yakoshi tukuna yatashi yanufi toilet jim kadan yafito

Da mamakinta maimakon taga yanufi kofa tabi bayanshi saitaga yanufi kan gado tareda ware mata hannayensa alamar tazo yana sakar mata murmushinsa mai tsada...

Zumburo baki tayi kafin tace

Nifa kamaidani gida dare yayi!

Hade rai yayi yace nifa ban koshi ba! Dan haka kizo kiban Malama nasan kema kina bukatar kari....

Yakarashe maganar tareda yimata gwalo

Kamar tayi kuka kunya da haushinsa suka kamata kin zuwa tayi, tace nidai banaso kazo muje dan Allah tafada cikeda shagwaba

Ganin batada alamar zuwa ne yasa yataso ya iso inda take tareda kamo hannunta yanufi kan gado da ita yacire mata Hijab yana fadin ae wallahi baki isa ba! ni nabiya miki bukatarki ke bazaki biya mun tawa ba?

Ganin da gaske yake yasa tasaka kuka tana fadin dan Allah Ya ALI kabarni muje gida kar Ammiey sugane mu kaga yanzu dare yayi kuma Aunty Sajidah tana jiranka

Jin abunda tafada ne yasashi hade rai yana fadin

Waike baki kishina ne? Kina tareda mijinki kike kawo zancen kishiya tsakaninmu

Kwace hannunta tayi tana fadin kamanta yarjejeniyarmu ne ae ina gama biyanka Babynka zanyi aurena dawani bakai ba dan haka Sajidah amatsayin Auntyna take haryanzu ba kishiya ba har abada...

Kuma...

Kafin tasake cewa wani abu ya hada bakinsa da nata yashiga aika mata dan sako dan bayason jin tana ambaton zata rabu dashi ta auri wani daban...



Wasa wasa ALI ya hana HaYaT zuwa gida anan suka kwana yana kwasar ni'imarta bayan yakira Sajidah yazuka mata irin karyarda yasaba yimata abaya

Su Ammiey'ma kiransu yayi yace HaYaT agidan Yayanta zata kwana sai gobe tazo dan yabarta can...

Allah yakaimu goben Ammiey tace sukayi sallahma yakashe wayar tareda ajiyeta bayansa yamaido hankalinsa gun HaYaT datake rigima akan ita lallai ba anan zata kwana ba jin karyarda yasharara ne yasata sakin baki tana kallonsa tareda jinjina karyar aranta...


Da Asuba tasaka mishi kuka yamaida ita gida

Rarashinta yashigayi tareda fadin yanzu idan nakaiki gida da Asubar nan aesai Ammiey tazargi wani abu HaYaT dan haka kiyi hakuri zuwa karfe goma ko tara saina maida ke!

Dakyer tahakura ta zauna danta gaji da jarrabar ALI har cikin ranta tayi dana sanin biyosa da tayi aranta take fadin mutum ace dik jima jima abu daya baya isarsa? Wanan idan idan tayi shekara daya dashi aeba za'a iya ganeta ba nan gaba dan tsufa zatayi kamar silifas, yanzuma tana jinsa yana shafar kanta tasan kwanan zancen hakan yasa ta kyaleshi dikda haka bata tsira ba, saida yasake kashe arnawa saba'in...

Tsaf suka fito cikin shirunsu fuskar HaYaT ahade shikam ALI sai dariyarsa yake yana zolayarta akan dan Allah gobema tayi yanda za'ayi suhadu irin hakan nan

Kyaleshi tayi saida yayi dan kansa yagaji yayi shiru yana gaba tana biye dashi suna isa réception abunda HaYaT tagani ne yakusa sumarda ita

Zaro ido tayi waje bakinta na furta Amal?

Kece ahaka? Amal me kikazo yi a hôtel keda wanan saurayin bayan nasan ba aure kikayi ba?

Duba shigarki Amal meyasa?

Amal datake sanyeda wani matsatsan wando iya gwuiwa da wata yar karamar riga marar hannu fara sai wani uban gashin dokinda tasha yacanza mata kamani kamar wata arniya ta kalli HaYaT cikin wulakanci kasa da sama kafin taraba jikinta dana saurayinda ke tare da ita tana fadin

Wai kuji fa Kura ke cema Kare maye?

Ke in banda rainin hankali irin naki harkin isa kibude baki ki tambayeni me nazoyi a Hôtel yar renin hammata?

Toh sauraran wa'azi nazoyi Malama mai hijab din munafuci yar iska kawai karuwa wanan gandamin waye shi?

Ubanki ne ko Mijinki?

Wato kin saba bashi a scul shine kinyi aurema bazaki hakura da jarraba ba?


Amal tafada tana nuna ALI dayake tsaye yana kallon ikon Allah

Jin abunda Amal tafada ne ya tunzurashi, ba zato ba tsammani Amal taji saukar yatsu biyar akuncenta tuni idanun ALI suka kada sukayi ja dan takaicin kalaman Amal akan HaYaT nunata da hannu yashigayi yana fadin

Ahir dinki! Karki kuskura naji wasu munanan kalamai daga bakinki akan HaYaT inba haka ba saina batar dake koke wacece! Banza wacce batasan darajar kanta ba

Wani irin kukan kura Amal tayi kafin kace me takifama HaYaT mari mai zafi tana fadin

Yoo harni za'a nunama bariki? Kayi karya dan bariki irinka yadaga hannunsa yamareni batareda namaida martani ba! Ba akanka kuma zan rama ba akan wanan zan rama saboda nasan zaifi yimaka ciyo idan narama akanta fiyeda kai tana nuna HaYaT

Saurayinda yake tare da ita ne yarikota yana fadin Amal meye haka kibari mana

Juyowa tayi cikin zafi ta turesa tana fadin Allah wadaran bariki agabanka aka mareni bakayi kokarin rama mun ba, bayan narama kuma shine harda tareni dan gidan marrasa zuciya?

Ba tareda saurayin yace da ita komai ba yajuya yafita abunsa daman jiya suka fara haduwa dashi shine suka kwana anan

Matsifa tashigayi da zage zage

ALI tun lokacinda Amal tamari HaYaT yayi yunkurin marinta karo na biyu HaYaT tayi saurin shan gabansa tana girgiza masa kai cikin kuka kafin taja hannunsa sukaje mayarda kye din dakin suka fito

Saida suka bar hôtel Amal bata dena matsifa ba, saida aka saka sécurité sukayi waje da ita dan ganin abokanan yinta sunbar wajen amma taki denewa

Kallo daya zakama Amal kagane takusa zautuwa saboda irin yawan shan kwayoyin mayenda take sun fara taba kwanyarta...


Tuki yake ahankali tun yana daurema jin shashekar kukanta harya kasa, faka motar yayi agefen titi yakalli bangarenda yana fadin

Haba HaYaT tun yaushe nake baki hakuri kiyi shiru kinki? Me kikeso namiki ne? Idan da sabo ae baikamata kisaka damuwar Amal aranki ba hartazo tadameki abanza

Kara fashewa tayi da kuka tana fadin Ya ALI bakaga yanayin shigarta bane? Duba saurayinda take tare dashi da alamama anan suka kwana!

Toh ke ina ruwanki dasu meye hadinki da ita?

Share hawayenta tayi tana fadin kanwar tawa? Ubanmu daya da ita fa taya bazan damu da lamuranta ba? Taya hankalina bazai tashi da ganinta a irin wanan yanayin ba?

Kamo hannunsa tayi tarike tana kallonsa idanunsa taf kwalla tace dan Allah Ya ALI ka kaini gidanmu nasanarma su Abbu irin halinda Amal take ciki tun wuri adau mataki akanta plzzz

Kallonta yayi cikeda tausayawa ganin dik irin wulakancinda tasha a hannun famille dinta baisa tadena sonsu ba ko taji haushinsu ba

Ajiyar zuciya yasauke yana fadin

Shikenan zan kaiki! Amma kiyi shiru don banason kukan nan naki da kike taban zuciya yake HaYaT

Bataka komai aranta ba tashare hawayenta tareda yin shiru batace dashi komai ba ta kwanta jikin kujera tareda lumshe idanunta tana tariyo abunda yafaru tsakaninsu da Amal yanzun nan....

Har suka iso bakin gidansu bata sani ba saida ALI yace da ita mun iso!

Tana bude idanunta tazubasu akan kofar gidansu gabanta na faduwa, ahankali kuma tashiga tunano ranarda tabar gidan nan cikin kuka da tashin hankali da yanda suka rabu da Abbunta....

Wani irin dogon lumfashi taja tareda ajiyar zuciya lokaci daya kuma talumshe idanunta tareda budewa tasake kallon kofar gidan ahankali labbanta suka motsa alamar guntun murmushi yabayana afuskarta tuno zataga yan kaninninta tagwaye Jamila da Jamal da kuma mai aikinsu larai mai kaunarta da sonta tsakani da Allah...

Tama manta da ALI agurin daya zuba ido yana kallon dik wani motsinta

Da mamakinsa ganin yayi tabude motar tafita cikin azzama fuskarta na fadada murmushi kai tsaye tabude kofar tanufi cikin gidan


Jamal Jamila takira sunayensu yafi sau uku ba ansa kai tsaye tashiga falon tana dube dube

Anna da take daki tajiyo muryar HaYaT da sauri tafito ganin kodai kunnenta ne ke mata karya jin muryar HaYaT

Ido hudu sukayi da Anna da sauri HaYaT tanufi inda take da nufin fadawa jikinta ta rungumeta tana murmushi dajin dadin ganin Anna

Wata tsawa Anna ta daka mata tana fadin karki kuskura ki tabani!

Me kikazo yi agidan nan yar baka mai bakar fuska mayya?

Cak HaYaT tatsaya kukanda tadenayi dazu shine yadawo kallon Anna tayi tace

Anna bakiyi kewata bane? Muryarta na rawa tayi maganar

Mtswwww uban me kike mun dazanyi kewarki? Waima meya kaki gidan nan ne annoba?

Share hawayenta tayi tana fadin

Anna Amal nagani a hôtel cikin wata irin shiga marar kyau da saurayinta kuma ni asanina ba aure Amal tayi ba shine nazo nasanar daku tun wuri adau mataki akanta

Hhh hhh kaji kwararriyar yar bariki? Ke Ubanwa kikaje dauka a hôtel din har kika ganota can ?

Anna...

Ke munafuka maza kifice kibar gidan nan inba haka ba wallahi sainayi ajalinki kamar yanda nayi sanadin Uwarki banza mai bakar fuska

Wani irin dum HaYaT taji akirjinta jin abunda Anna tafada

Anna kece kika kashe mun Ummana?

Kika maidani marainiya daman ba mutuwar Allah da Annabi tayi ba?

Meyasa? meta tare miki?

Wanan wane irin masifaffen kishi ne haka dahar idonki zai rufe kiyi sanadin rai?

Anna kinsan irin girman hakkin rai kuwa?

Fita kibar nan Anna tafada tana nuna mata hanyar waje

Kuma wallahi in wani abu yasamu Amal sainayi sanadin ranki saina batar dake

Kuma fatan iskancinda kike mata na zuwa hôtel yakare akanki keda kika saba dabin Maza, jiyan Amal dakaina nakaita gidan Aunty Nan yanzu kizo kice mun kin ganta a hôtel ?

Toh kinga kan uwarki ba Amal ba!

Maza wuce ki bace mun dagani

Sum sum HaYaT tajuya tafita dakyar kafafunta sun mata wani irin nauyi dakyar take tafiya wani irin jiri na dibarta

Ahaka tafito waje tama manta dawa take tare kama hanya tayi harta wuce motar ALI bata sani ba maganganun Anna ne kawai ke mata yawo aranta

ALI ne yalurada bata cikin hayyacinta ganin yanda take tafiya kuma hartazo tawuce shi bata sani ba
Fita yayi ya isa inda take tareda kamo hannunta yajuyoda ita yana fadin HaYaT lafiya kike kuwa?

Dafe kanta tayi idanunta na rufewa tana budesu dakyar tace

Ya ALI bazan iya jurewa ba Ya ALI bazan iya b...

Gabadaya tayi baya zata fadu ALI yayi saurin tararta tafada jikinsa kiran sunanta yashigayi yana jijigata amma ina HaYaT ko motsi batayi gabadaya lumfashinta yadauke kasan kafarta kuwa jini ne yake zuba

Gabadaya hankalin ALI yatashi yarikice daukarta yayi yasata mota yazagaya yashiga yafizgi motar yabar unguwar...

Ikon Allah ne kadai yakaishi lfy clinique din Dr Khaleed saboda tafi kusa daga inda yake

Da yake kafin ya isa yakira Khaleed dan haka yana isa akayi ciki da ita

ALI yana gefen HaYaT rikeda hannunta tausayinta da tausayin kansa yake dan cikinda tasamu ne yake kokarin barewa yafita daga jikinta cikinda baisan dashi ba harna tsawon wata biyu ba abunda yake sai adu'a Allah ya dauwamarda cikin yazauna harta haifeshi lafiya...

Cikin ikon Allah Dr Khaleed da taimakon wani likita suka shayo kan matsalar harta farfado daga sumanda tayi saidai sun mata allurar bacci mai nauyi saboda yanayinda take ciki...

Kallonta yake ganin yanda lokaci daya tayi rama tayi wani fayau da ita gwanin ban tausayi

Adole yasa yakira su Ammiey yasanar dasu HaYaT batada lfy tareda fada musu inda take

Ba shiri Ammiey Salimat Haidar harda Auta Shuraime sukazo dan Daddy baya gari

Da Ammiey tanemi ba'asin zancen ALI cemata yayi yana gida tunda safe Yayan HaYaT yakirasa wai an musu rasuwa kauyensu kuma ga HaYaT batada lfy shine naje nadaukota nayo da ita asibitin nan saboda tafi kusa daga inda suke

Ammiey tace toh inashi Yayan nata?

Ammiey yatafi da Matarsa kauyen sunje gaisuwa saboda ba yanda zaiyi dole saiyaje din!

Ajiyar zuciya Ammiey tasauke tamaida kallonta ga HaYaT zuciyarta na mata wani tunani akanta..
Da sauri kuma Ammiey takauda tunanin tana istigifari...

Sai wajajen karfe shidda HaYaT ta farka Salimat na mata sannu dan ji take kamar ace ciyon yadawo jikinta yabar HaYaT

Idanunta sun kumbura da kallo tabi Salimat ba tareda ta ansa sannunda take mata ba tace ina Ammiey ?

Sorry HaYaT Ammiey dazun nan ta tafi gida amma zata dawo anjima tace!

Jin jina kai HaYaT tayi tareda dafe goshinta dan wani azabar ciyo yake mata mai tattareda zafi

Salimat ce talurada hakan mikewa tayi tafita, jim kadan saiga ALI yashigo fuskarsa daukeda damuwa da tausayi

HaYaT tana ganinsa tasaka kuka

Cikin damuwa yake tambayarta meke damunta? Salimat tace mun kanki yana ciyo ko?

Gyada masa kai tayi tana fadin gida zan koma ka kaini gun Ammiey mutuwa zanyi

Rikicewa ALI yayi yana fadin HaYaT kidena fadin haka ba abunda zai sameki insha Allah saikin aurarda yaranki da kanki har jikokinki kinji?

Shiru batace dashi komai ba

Mikewa yayi yaje yadauko allura dawasu magunguna yadawo

Saida yasha fama da shagwabarta kafin ta yarda yamata allurar takuma sha maganin...

Kwananta biyu a asibitin takoma gida

Dayake cikin jikinta bamai laulayi bane yasa ko ita kanta batasan tanada shiba, saidai kallo daya zakama HaYaT kasan tacanza saboda yanda kirjinta yake kara cikowa yana kara fitowa dakyau kugunta kuma yakara fadi sosai cikin yamata kyau sai wani kyalli take karawa da kyau saidai tarame

Ammiey kullun kallon HaYaT take tanaso tace wani abu saidai bataso tunaninta yazama gaskiya saboda a iya saninda tayi Mijin HaYaT baya kasar nan gabadaya...


Hamdan ranar tutse HaYaT yayi harda hawayensa cewa tagaya masa laifin me yamata tazabi hukuntashi ta hanyar sharesa ko kiranta yayi bata cika dagawa ba?

Ganin Hamdan na kuka wanan ne yakaryarda zuciyarta itama hawaye take tausayinsa ne yakamata matuka ganin irin sonda yake mata tsakani da Allah da zuciya daya

Kallonsa tayi tace

Ya Hamdan zaka iya auren bazawara wacce ta taba haihuwa?

Kallonta yayi yace meyasa kika tambayeni HaYaT ?

Share hawayenta tayi da bayan hannunta tasake kallonsa cikin ido tace

So nake kawai naji ansa kuma ka tabbatar har cikin zuciyarka abunda kafada ba shakka

Zaka iya auren bazawara wacce ta taba haihuwa dawani Namijin?

Murmushi yayi yana kallonta yace ba fata ba HaYaT ina mai tabbatar miki cewa indai kece irin so da kaunarda nake miki koda bada aure ba akace kin haihu awaje koda kin haifi Yara samada biyar zan iya manta komai na aureki na zauna dake cikin soyayya da kauna na rungumeki da yaranki na nuna miki kauna da soyayya bazan canza daga Hamdan inda kika sani abaya ba!

Ajiyar zuciya tasauke karo na farko tasaka hannunta takama hannunsa tana kallonsa tace

Lallai na jinjina irin wanan kaunar taka gareni Hamdan tabbas bazan taba gangancin barin masoyi irinka ba, ni HaYaT takace har abada kajirani kawai nanda wani dan lokaci zan zama mallakinka har iya karshen rayuwarmu...

Hamdan nan gaba zaka san koni wacece inada tabbacin bazaka gujeni ba idan kasan ni wacece nan gaba na hango gaskiyar dik abunda kafada akwayar idanunka

Inaso dan girman Allah kada kataba tambayana gameda labarina da kalamaina nayau harsai in nice da kaina nagayama...

Tana gama fadin haka tasaki hannunsa ta tafi...


Tun ranarda aka sallamota daga asibiti rabonda wata maganar arziki tashiga tsakanin ALI da HaYaT

Dikda kusan kullun yana gidan ba dare ba rana har Ammiey taga abun nasa yayi yawa tamasa fada akan yawan zamansa gida baya bawa Sajidah lokacinta

Ita Ammiey bata sani ba ALI zaman hokon HaYaT yake

So yake yafada musu gaskiya tsakaninshi da HaYaT kuma yana tsoro,,, daga karshe ya yanke shawarar dik lokacinda ciki yabayana Ammiey tasan dashi zai fito fili yasanar dasu alakarda ke tsakaninshi da ita...

Abun yana damunsa ganin HaYaT koda sunyi sa'ar kebewa daga ita saishi bata wani kulashi daga gaisuwa kawai saita shareshi tacigabada harkokinta

Idan kuma yafitoda wata dabararda zata saka sufita saita dage ita bazata ita kadai ba sai tareda Salimat!

Ammiey kuma ta daure mata gindi

ALI yanaji yana gani tsakaninsa da HaYaT sai kallo, yanaso yaji dumin jikinta yaji lafiyar Babynsa amma ba dama...


Ana hutun makaranta zango na biyu aka shirya yin bikin Haidar

Gabadaya shirin biki ake ba kama hannun yaro baki tako ina zuwa suke yan uwa da abokanan arziki

Ana jibi daurin auren ne gabadaya dangin ango akaje kai lefen amarya banda HaYaT datakejin wani zazzabi zazzabi da ciyon baya suna son kwantarda ita, itada kanta tasan bukatar namiji take akusa da ita musaman yan kwanakin nan da wata irin sha'awa ta addabeta koya tayi bacci saitayi mafarki wankan dole yakamata ba tareda taso ba!

Cikin sa'a ALI yashigo gidan ganin ba kowa ne daman mai gadin yasanar dashi dik sun fita shima kuwa yasanda yau ne zasukai lefe gidansu Amarya saidai banda Ammiey kawai ce bataje ba

Da sallahma yashigo ganin ba kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login