Showing 12001 words to 15000 words out of 54100 words

Chapter 5 - AYNUL HAYAT COMPLETE HAUSA NOVEL

12 Dec 2024

8201

ne dan nazo kalar fatana baka?

bazance Allah yabimun hakkina akanka ba Abbu!

Haka kuma bazance na yafema abunda kamun ba Abbu...

Ahankali tajuya takoma baya tafara tafiya da niyar komawa inda tafito saboda ayanzu can din shine gatanta kuma rufin asirinta.

Saidai me ? Gabadaya kanta yakulle tarasa takamamen gidan ALI tafiya take tana dawowa yafi akirga tun tana iya tafiya harta kasa gashi daman yunwa takeji tun abincin rana ne cikinta dan jiya bata samu taci na dare ba wanan abun yafaru

Dataga babu sarki sai Allah zama tayi akan wani dutse dayake gefe takifa kanta akan gwiwoyinta tashiga rera kuka ahankali na tausayin kanta da rayuwarta

ALI datun fitowarta yabi bayanta lokacinda tajuyo zata dawo saiya labe awani lungu yana hangota

Dafata yayi da sauri tamike tana rarraba idanu cikin tsoro ganin ALI ne batasan lokacinda tasaki ajiyar zuciya tareda rungumeshi tasaka wani sabon kuka tana fadin dan Allah kamaidani natuba zan sauna da Aunty Faridah koda kasheni zatayi...


Rabata yayi da jikinsa batareda yace da ita komai yajuya yasoma tafiya

Binsa tayi abaya harda dan gudunta tana tafe tana shafe hwayenta har suka iso kofar gidan yashiga tabi bayansa saida suka shiga falo yajuyo ya kalleta da kyawawan idanunsa yace

Kina tunanin koda kin samu hanyar tafiya kinada inda zakije ne?

Mahaifinki kokin je ba barinki zaiyi gidansa ba koraki zaiyi kokin manta waye shi ne?

Kasa tayi da idanunta tana sharar hawaye batace dashi komai ba

Nan yacigaba da mata fada akan karta kuskura tasake irin wanan

Toh kawai tace dashi.


Ganin idan yafita bazata samu abunda zataci ba kuma Faridah ba girkawa zatayi tabata ba yasa yace tabiyosa kitchin

Da mamakinta tabi bayansa

Girki zanyi kinuna mun dik yanda ake nayi yafada yana shirin dauko tukunya

Cikeda mamaki tace girki kuma?

Juyowa yayi yakare mata kallo yace eh! Yajuya yadauko wasu kaya

Ajiyar zuciya tayi tace me zaka girka?

Fada mata yayi...

Nan tashiga zano masa abubuwanda ake bukata dik akwai yadauko wani kuma ta taimaka masa

Saka wanan motsa yanka wanan ahaka harsaida suka gama tsaf tarage volume din wutar dan komai yanuna yanda akeso tukuna yafita yace idan komai yayi takwashe

Dakinsa yaje yayi wanka yadawo kasa da shirinsa na fita alokacin HaYaT tana jera abincin kan table ganin alamar fita zaiyi baici abinci ba kuma gashi ko break baiyi ba yasa tace

Bazaka ci abincin kafin kafita ba???

Kallonta yayi batareda yace da ita komai ba yayi ficewarsa waje yabarta


Ganin abunda yamata ne yasa taja dan guntun tsaki tana fadin kayima kanka !

Cikinka ko nawa?

Mutum sai shegen fadin rai da nuna isa, karma kaci din yakara auki!!

Tasake jan wani dogon tsaki tana kwaikwayar yanda yake tafiya cikeda kasaita da isa kafin tanemi guri tazauna

Yau nan tazauna kamar itace Faridah takwashi girkinta iya son ranta tana fadi aranta mutumen nan ashe zai iya wani abun arziki gashi kuwa girkin yayi dadi kamar mace tayi, can tadan kwabe fuska tana fadin banji dadi dabaici abincin nan ba yafita da yunwa...


Faridah tana can kunshe cikin daki gargadin da bokanta yamata na karta kuskura tazoma ALI da maganar auren harsai in shine yafada mata inba haka ba zataga abunda zai biyo baya!

Dalilinda yasa kenan tazubama ALI ido taga iya gudun ruwansa, ga kuma haushin HaYaT daya taru yazame mata abu biyu da biyu

Dikda yunwarda takeji tasakama kanta masifa hakan baisa tasauko ta nemi abunda zataci ba ahaka tawuni cikin dakin ita kadai kamar mayya sai sakawa da kwancewa take daga karshe dai takira Auntynta kanwar Mamanta ta kwashe dik yanda suke ciki da abunda bokan yafada mata ta sanar da ita.

Nan Aunty Balki tace da ita tunda bokan yace haka tahakura tajirasa kawai, takara dacewa kinsan fa ayanzu sihiri kawai bazaiyi tasiri ba saikin kara da kissa dan haka abunda nakeso kiji shine kidaure koda shi ALI din yazo miki da zancen auren karki nuna masa bacin ranki akai kiyi farin ciki ki nuna masa ba komai kinga daga nan zai saki jiki dake mukuma mu masa ta zangon kasa kin gane...?

Aunty Balki bazan iya jurewa ba wlh ina tsananin kishin ALI kuma...

Dakata Faridah nan Aunty Balki din tashiga karanto mata tatsuniyar dodo da dabaru kala kala tareda kwantarda hankali yanda idan amaryar tashigo cikin ruwan sanyin zasu kawarda labarinta batareda kowa ya zargesu ba!

Sanan takara dacewa ita kuma wancan yar aikin kibarta nata maisauki ne mugama da wanan tukuna kinajina ko?

Toh Aunty nan tamata godiya tareda sallama kafin Auntyn tata tamata alkawarin zuwa wajen wani nata bokan taji dame zai taimaketa kuma...






Saida tayi zance da Auntynta taji zuciyarta tayi wasai taji batada sauran wata damuwa ayanzu, sai yanzu takejin yunwa kamar taci babu dan haka saukowa tayi kasa yayi daidai da HaYaT tashiga kitchin dibar ruwa juyowarda zatayi sukayi ido hudu da Faridah tsoronta ne yasa tasaki cup glass din da yake hannunta kasa ya tarwatse gabadaya

Kallonta Faridah tayi da mamakin irin dunbun tsoronta data tsinkayo a kwayar idon HaYaT kuru kuru kusan minti biyu suna kallon kallo da ita

HaYaT tuni harta fara hawaye ganin daga ita sai Faridah a kitchin gashi bawata hanyarda zata iya guduwa dan abakin kofa Faridah take tsaye

Faridah harta motsa labbanta zatayi magana saikuma tafasa tunoda maganar Aunty Balki, dan haka juyawa tayi takoma dinning tanufa tadibi abinci ta haye sama abunta.

Faridah kuwa takai minti goma tsaye awajen bata motsa ba, dikda taji alamar Faridahr takoma dakinta amma hakan bai hanata cigaba da tsayuwa ba saida tadawo hayyacinta tukuna ruwanda bata sha ba takoma dakinta bayan tashare gujtayen kwalaben tana mamakin yanda Faridah batace da ita komai ba.



Saida yabiya gun iyayensa tukuna yaje wata restaurant yasiyo abinci yanufo gida

Saida yaje yabuga kofar HaYaT tace waye bai ansa ba ajiye mata leda yayi bakin kofarta yayi tafiyarsa

Tana fitowa bayansa kawai ta hango ya haye sama saida yabacema ganinta tukuna tamaido kallonta kan ledar tadauka tashiga ciki tana mita

Abincinma baza aba mutum cikin hannunsa ba saidai abuga mar kofa a ajiye kasa idan yafito yadauka saikace wata yar kurkuku mtswwwww...



Kai tsaye dakin Faridah yanufa da ledar abinci ahanunsa ya iskota agaban madubi da alama daga wanka tafito tana ganinsa tasakar masa murmushi kamar ba abunda yafaru tsakaninsu dazu da safe

Sosai yayi mamakin saurin canzawarta shida yasan Faridah idan sukayi rigima saisufi sati dayama bata kulashi ba inhar bashine yagaji ya nemeta ba, amma yau saiyaga akasin hakan!

Daurewa yayi yamayar mata da martanin nata murmushin tareda furta uwar gida ran gida

Takaici ne yakama Faridah jin kalmar uwar gida ran gida watau takoma uwar gida tunda yasan zai auro wacce zai kirata da amarya ba!

Daurewa kawai take ta ansa da sannu da zuwa Habiebina

Yauwa sannu da gida ya ansa mata!

Tasowa tayi daga ita sai dan karamin tawol akirjinta tana tafe tana karairaya ita ala dole saitaja hankalinsa

alokacin kuwa Kare mata kallo yake tsaf yana tunano irin kyan surar HaYaT yana kallon Faridah saiyau yake ganin rashin fasalinta banda tunbi data ajiye gashi jikintama karasa fara ce ko baka...

Kamanta surarta yake data HaYaT harta iso gareshi ta sakallo hannayenta a wuyansa sai asanan yadawo duniyar tunaninda yake

Sakin kedar hannunsa yayi yajanyota ajikinsa daman sun dade basu hadu ba gashi shidin mai mugun bukatar mace ne akusa dashi koda yaushe amma Faridah tasa dole yake danne ra'ayinsa saboda sai suyi sama da sati daya bata bari yatabata ba.

Yanzu kuma daya samu dama yashiga damata yanda yakamata dikda yunwa da gajiyarda ke tattare dashi alokacin saida yamori jikin Faridah yajuye mata abunda yajima yana tarawa dikda bawani gamsar dashi take ba yanda yakeso!

Saida yayi wanka dakinta tukuna yanufi dakinsa yacanza kaya yasaka yar singileti da gajeran wando yafito falon sama yashiga kiran Faridah

Fitowa tayi cikin shigar kananun kaya wacce kallo daya yamata yadauke kansa saboda tunda yayi ido hudu da surar HaYaT wani abu daga jikin Faridah yadena tikashi da kasa sabanin da koya tayi shigarta yafara rurutata Kenan yana yaba irin kyanda tayi da kyawon surarta

Kusa dashi tazauna tareda janyo hannunsa daya tacusa arigarta tana lumshe ido ita kanta batasan meyasa yau take tsananin bukatar ALI kusa da ita ba, abunda sukayi saitaji kamar yasosa mata inda yake mata kaikayi ne amma badan tagaji dashi ba!

Kallonta yayi tareda zare hannunsa daga cikin rigarta yana fadin Matar yunwa nakeji dauko abinci muci yana dakinki

Haushi ne yakamata dan ita harta shirya ansar sakwanin ALI saboda yanda tasanshi da sha'awa akoda yaushe shirye yake da karbar tayinta amma gashi yau yawani gwasaleta!

Danne zuciyarta tayi ta tashi taje ta dauko abincin dasu plat da ruwan sha tazo ta ajiye masa agabansa takoma gefe tana kallonsa

Dakanshi yazubama kansa abincin yace ta taso suci tace akoshe take !

Me kikaci yace da ita?

Abincinda mai aiki tayi ban jima daci ba!

Jinjina kai kawai yayi yafara cin abincinsa anutse saida yagama yasha ruwa yace tadauko masa Jus tace yakare

Cikin mamaki yace yaushe Jus din yakare baki sanar dani ba?

Cikin dan bata rai tace dazun nan fa nasha nakarshen

Ook yace tareda mikewa yashiga dakinsa yafito hannunsa rikeda cheick yazo yamika mata ta ansa tana kallonsa da alamar jiran karin bayani dan million daya cur tagani akai

Saida yazauna tukuna yace taki ce

Zaro ido tayi tasake kallon cheick din tasan kota meye dakuma dalilin bata wanan kudin amma saita nuna kamar batasan na meye ba dan haka tace kyauta kabani kome?


Cikin fargaba yasanar da ita akan karin aurenda iyayensa zasu masa

Atunaninsa zata tada hankalinta suyi bala'i shiyasama ya hadata da makudan kudi haka saboda yatoshe matsifaffen bakinta

Sai kuma yaga tayi murmushi tace nagode Allah yasanya alkhairi!

Dadi ne yakama ALI atunaninsa kudin ne yasata shiga hankalinta har yana fadi azuciyarsa Mata Kenan!

Gefe daya ta ajiye cheick din takwanta ajikinsa tareda kai bakinta kan wuyansa tana lasa

Nan take kuwa tasamo ALI tsikar jikinsa ce tafara tashi ko dazun dayakejin yunwa yayi bajinta balle yanzu dayaci yakoshi

Shi daman irin haka yakeso akoda yaushe yaji mace kusa dashi yana morarta son ransa,,,, biye mata yayi yashiga wasada jikinta yarikitarda Faridah sosai tuni ta manta wacce duniyar take...



Yau sati daya Kenan da zancen, ALI yaje gidansu Amaryar tasa Sajidah

Ba laifi ya yaba da ita gatada nutsuwa ga kyau Uwa Uba fara ce sosai kamar yanda yakeson mace dan kuwa Sajidah hartafi ALI din dayake takama da farar fata haske


Sajidah kyakyawa ce ajin farko, tanada tsayi daidai misali irin matan nan ne yan duma duma wanda bazaka kirasu da marrasa jiki ba haka kuma bazaka kirata da mai jiki din nan ba tana tsaka tsakiya, sosai Sajidah takeda cikar hallitar jan hankalin dik wani da namiji lafiyayye wanda ba wanda za ama tayin aurenta yace bayaso!

Sajidah wayayya ce sosai tanada ilimin addini dana boko sosai gidansu kaf an musu shaida da samun cikakiyar tarbiya da sanin ykamata sun gada gun uwa da uba.

Yanzu haka Sajidah tana aiki ne awani asibiti mai zaman kanta Docta ce dikda shekarunta 23 ne aduniya.

Ita kanta tayaba da zabinda iyayenta suka mata danko batayi zaton ganin ALI haka ba aranta take fadin tayi dace gashi kyakyawa dan gayu yanda take mafarkin samun mijin aurenta
Gashi kuma Allah yabata tsuntsu daga sama gassashe
Sunyi musayar lambobi kafin yashiga yagaida iyayenta yamusu sallama yatafi.



HaYaT ce tsakar falon sai faman goge goge take taji wata mata tashigo tareda yin sallama tashiga ta ansa yayi daidai da lokacinda Faridah take saukowa daga bene

Da murnarta tace Aunty Balki sannu dazuwa

Wacce takira da Aunty ta ansa tana kallon HaYaT tace wanan itace yar aikin taku?

Cikin bata fuska Faridah ta kalli HaYaT tace itace Aunty!

Jinjina kai Aunty Balki tayi kafin tazauna

Faridah tace jeki dauko mata abunsha

Toh HaYaT ta ansa dashi tareda shigewa kitchin

Tana fitowa taji Aunty Balki nafadin wanan kisaka cikin abincinsa dayan nan kuma na amaryar ne akofar dakinta zaki zuba daga nan bashi ba morarta da zarar ta tsallaka shima ya tsallaka ko haihuwa saidai tagani amokata kamar yanda kike gani badai ita ta haihu agidan nan ba!

Bata rai Faridah tayi tace Aunty abun harda gori?

Yar dariya tayi tace haba Wane ni yar nan kiyi hakuri subutar baki ne!

Tsaf HaYaT taji maganganunsu akunnenta jikinta ne gabadaya yadauki rawa tsoron Faridah da shu'umancinta yasake shigarta

Trenda ta dauko ruwa aciki tsananin rawarda jikinta da yake ne yasashi yin tangal tangal tana tafiya kafafunta na hardewa dakyer ta iso inda suke ta duka ta ajiye ruwan tajuya zata tafi

Faridah tace lafiyarki kuwa?

Dan zaro ido tayi waje cikin inda inda tace lafiyana kalau Aunty !

Tsaki Faridah taja tamaida hankalinta kan Aunty Balki tana fadin Aunty kudi yabani masu yawa har million daya anjima nake shirin tafiya gida nakaimasu Mama rabin kudin sauran kuma nasaka accnt dina.

Zaro ido Aunty Balki tayi tana fadin million yar nan tareda dafe kirji kamar anyi wani abun tir

Basuko shakkar idon HaYaT suke zantukansu

Anan Aunty Balki saida tasamu yanda tayi tasamu kudi masu yawa gun Faridah da sunan zatakai amata wani aikin akan amaryar inda halima adakushe auren gabadaya!

Faridah kuwa cikeda farin ciki tayarda da Auntynta dari bisa dari...


Jin abunda suka fada ne yasa HaYaT neman mafita tarasa

Candai tayi tunani tayi abincin dare mai yawa sosai tazuba akuloli tajera akan table sauran kuma takai dakinta taboye bayan taci nata tashiga dakon Faridah

Ba jimawa kuwa Faridah tazo tabude kwanon miya tazuba maganin aciki tarufe bayan tamotsa takoma dakinta ranta fari kal dan farin ciki yau zata juya ALI son ranta
Dan Aunty ta tabbatar mata idan yaci maganin karyarsa takare sai yanda tayi dashi!

Aekuwa HaYaT datake kallonta ta cikin dakinta tana komwa dakinta tafito tadauki miyar har abincinma dik tazube tawanke kwanonin yafi akirga da sabulu kafin takaisu dakinta tazuba sauran abincinda taraga aciki tagyara takai ta ajiye cikin sauri taci sa'a kuwa ba wanda yaganta harta gama takoma dakinta sai alokacin hankalinta ya kwanta, takumaci alwashin dayan maganinma saitayi yanda zatayi tadaukoshi daga dakin Faridah...




✍🏻
[8/1, 7:01 AM] Hayat: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*AyNuL HaYaTπŸ‘„*
_MATAR ALI GADANGA_


πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWa✍🏻*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*

*NeEnA_CoOlπŸ‘©πŸ»β€πŸ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*


*_______________________*
*πŸ‡³πŸ‡ͺNiGeR Ma FiErTΓ©πŸ€™πŸ»*


*Ψ§Ω„Ω„Ω‡Ω… Ψ₯Ω†ΩŠ Ψ£Ψ³Ψ£Ω„Ωƒ Ψ­Ψ¨Ωƒ وحب ΩƒΩ„ Ω…Ω† ΩŠΨ­Ψ¨ΩƒΨŒ وحب Ω†Ψ¨ΩŠΩƒ Ω…Ψ­Ω…Ψ― Ψ΅Ω„Ω‰ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΩˆΨ³Ω„Ω….*
*وحب ΩƒΩ„ ΨΉΩ…Ω„ ΩŠΩ‚Ψ±Ψ¨Ω†ΩŠ Ψ₯Ω„Ω‰ Ψ­Ψ¨Ωƒ يارب Ψ§Ω„ΨΉΨ§Ω„Ω…ΩŠΩ†πŸ‘πŸ»*


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI✍🏻_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷







9⃣







Koda ALI yadawo Faridah dakanta taje tahada masa ruwan wanka tajirasa harya fito tazaba masa kayanda zai saka

Harya kintsa yagama bai dena mamakinta ba yanda gabadaya tacanza abubuwnda bata mishi matsayinsa na mijinta ada yanzu yimasa take,,,, aransa yace daman haka mata suke basa tashi gyara halinsu sai sunga za akaro musu kishiya tukuna dik wani lungu da sako na kyautatawa da biyayya zasu bullomaka dashi

Hhh atunaninsa Faridah tanayin haka dan kyautata masa ne kenan...

Yana cin abinci tana masa hira harya gama tsaf, hankalinta ya kwanta dan atunaninta yaci maganin shikenan yau baccinta tayi harda mishari jira kawai take maganin yafara aiki tafara shimfida mulkinta afadarta yanda taga dama!


Washe gari ALI yana fita itama nabi bayansa ba jimawa

Ganin hakane yasa HaYaY tanufi dakinta tashiga duba inda zataga maganin, saidai me ta bincika ko ina bata gani ba tsaye tayi cikin dakin tana tunani ko ina Aunty Faridah taboye maganin?

Wata zuciyar ce tace da ita ki leka kasan gado mana kiga, aekuwa dukawa tayi taleka kasan gadon saidai me?

Abunda tagani ne yamugun razanata mikewa tayi dasauri tanajan lumfashi cikeda tsoro, wata yar Babyn roba tagani akasan gadon suffarta akwai ban tsoro gashi dik an daure babyn dawasu layu dawani kullin magani acikin wata kwalla daga sama murfin kwalbar an rubuta sunan ALI GADANGA akai da mayan baki baro baro.


Fita tayi daga dakin tasauko kasa gabadaya kwanyarta ta toshe tarasa me yakamata tayi bata tunanin zata iya barin wanan abun yacigaba da zama anan dole saita fito dashi!

Toh amma tayaya? Ta tambaya kanta da kanta


Wata zuciyar ce tace da ita kidauko da bismillah kije kiyi fitsari akai saikiyi rame ki binne shikenan!
Jin abun tayi kamar ana mata rada akunne ana ingizata da aikata hakan...

Haka kuwa tadauko wanan kwalbar bandashi harda kullin maganinda take tunanin wanda aka kamata ne jiyan gabadaya tayita adu'oin karye sihiri akansu takai awa biyu tana karatunda dik yazo mata akai yi take tana tofawa kafin daga karshe tafita waje can bayan gidan wanda saiyau kafarta tafara kaiwa nan acan tayi rame mai zurfi tasakasu tukuna ta kesta musu ashana saida suka kone kurmus tukuna tamaida kasa tarufe da bismillah takoma ciki saidai hankalinta gabadaya ya ki kwanciya gabadaya taji tatsani Faridah arayuwarta

_Wanan maganin na amarya ne akofarta zaki zuba mata_

_Aunty million daya yabani..._

Sai alokacin maganganun Faridah suke dawo mata take tambayar kanta ALI aure zai kara?

Aure zaiyi kenan???

Ko wacce amaryar ce Aunty Faridah take magana akai?

Inalillillahi tafada aranta tareda dafe kirjinta gabadaya taji tatsani kanta alokacin wani irin kishin ALI ne taji yataso mata alokacinda zuciyarta take tabbatar mata da lallai ALI zai kara aure bawani ba...


Alokacinda HaYaT takona wanan babyn alokacin ALI yana zaune ofis dinsa yaji kansa yamugun sara masa da karfi da sauri yadafe kansa yana sallallami Jim kadan kuma kamar walkiya yaji gabadaya yajisa normal kamar an dauke masa wani abu nauyi akansa an kuma zare masa wani Abu dayake damun cikinsa yanzu sai yajisa da karfi da lafiya zuciyarsa wasai , haka yaji yana furta Alhmdllh Alhmdllh alhmdllh yafada har sau uku kafin yacigaba da aikinsa...


Faridah kuwa tana gidansu wajen iyayenta taji gabanta yayi mumunan faduwa haka kawai taji hankalinta gabadaya yayi akan takoma gida

Aekuwa sallama tama iyayenta tanufo hanyar gida saidai cunkoson ababen hawa yasa tadauki kusan awa daya da rabi a hanya sai faman zage zage take kamar mahaukaciya dik motarda tasha gabanta ahaka harta karaso gida takaici kamar yakasheta.

Alokacin data shigo HaYaT tana girki tanajin motsin shigowar Faridah kamar mahaukaciya Faridah sai ganinta tayi tazuba aguje tashige dakinta takulle

Mamakinta yakama Faridah watau tsoronta datakeji yanzu haryakai haka?

Tsaki taja tahaye sama tanufi dkinta yanda taganshi ne yamugun razanata komai ahargitse yake

Dasauri hankalinta yayi kasan gado gunda ajiyarta take ba shiri takai gwiwoyinta kasa tareda leka gadon aekuwa taga wayam ba komai zaro ido tayi tareda mikewa mayafinda yake kanta da bata cire ba tacire tajefar dashi kasa tanufo kasa

Da gudunta take taka matattakala saura kiris ta gangaro kasa dakyer tasauko lfy taja burki bakin kofar HaYaT tace

HaYaT me nake shirin gani haka?

Allah yasa bakece kika aikata mun wanan danyen aikin ba, dan wlh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login