Showing 45001 words to 48000 words out of 54100 words

Chapter 16 - AYNUL HAYAT COMPLETE HAUSA NOVEL

12 Dec 2024

8205

takoma takwanta saidai bacci yagagara daukarta saboda tana rufe idanunta ALI take hangowa cikin wani irin mumunan hali marar kyan misaltawa yana kiran sunanta da neman agaji...

Haka abun yake gun HaYaT kusan karfe uku tafarka afirgice bakinta daukeda salati jikinta sharkaf yajike da zufa tattaba wuyanta tashigayi taji jikinta yadauki wani irin zafi radau ga tsoro daya kamata ganin irin mafarkinda tayi marar kyan ji gameda ALI

Lalubo wayarta tayi taduba agogo kafin tamike tashiga toilet tadauro alwarlla tazo tashiga jera sallaloli wanda ita kanta batasan iyakacin adadin wanda tayi ba

Kowace raka'a kuma acikin sujjadarta take nema ma ALI tsari daga mumunan mafarkinda tayi akansa

Bayan tagama ma anan ta zauna tacigaba da adu'a akan sallaya bacci barawo yayi awon gaba da ita...


Wajajen karfe bakwai Ammiey da tunda tayi Sallahr asuba bata koma bacci ba take kan sallaya tana adu'oi taji wayarta kira yashigo mikewa tayi tadauko tadawo tazauna abakin gado ganin number Haidar ne yake kiranta abun yabata mamaki, afili tafurta Haidar kuma da sassafen nan?

Cikin fargaba tadaga kiran da sallahma

Yanda taji muryar Haidar ya ansa sallamar ne abun yabata tsoro shiru tayi tana jiran me zai ce

Jin Ammiey tayi shiru ne Haidar yace Ammiey kiyi hakuri da abunda zakiji yanzu dan Allah Ammiey karki daga hankalinki ana nan ana bincike insha Allah ba abunda zai faru dashi

Shiwa? Ammiey ta tambaya cikin rawar murya

Ammiey ALI ne wajen karfe shidda yan sanda suka kirani nazo anga motarsa agefen titi da jini akasa kusada motar amma shi ba'a ganshi ba yanzu haka nasaka yan sanda yawo ako ine aduba dan haka Ammiey karki damu nakira Daddy daman yana kan hanya akoda yaushe zai iya shigowa gari

Sallallami Ammiey taketa nanatawa kafin tace Allahuma ajirni fil musubati wa aklifni khairan minha...

Ammiey tajima zaune kafin tasamu kwarin gwuiwar tashi taje tabuga kofar dakinsu Salimat da HaYaT tace sufito

Azaune suka riski Ammiey tadafe kanta cikeda matsananciyar damuwa tana ganinsu tadago kanta tazuba musu ido ba kamar HaYaT dahar cikin jikinta yafara kunno kai gashi tafito da rigar bacci gabadaya takara tona asirin cikinta, Ammiey taso tayi magana saidai yanzu ba wanan ne agabanta ba

Saida suka zauna Ammiey cikin nauyin baki da jimami tace Yayanku ALI ba abunda yake bukata daga gareku yanzu illa adu'arku...

Nan tamusu bayanin abunda Haidar yasanar da ita

Jin abunda Ammiey tafada ne yasa HaYaT mikewa tsaye ta furta Ya ALI dai?

Ammiey Ya ALI jiyan nan fa yaturo mun sako taya za'ace yabata?

Hakane HaYaT kinsan kaddara tariga fata jiyan nan yazo sai wajen shadaya yabar nan amma ya zamuyi?

Hakuri da adu'a kawai!

A'a Ammiey!

A'a Ammiey Ya bazai mutu yanzu ba sam wanan jinin daya zuba ba nashi bane Amm...

Kafin Ammiey tace wani abu sai ganin HaYaT sukayi ta sulale kasa sumamiya

Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana ranar su Ammiey sun gansa ganin idonsu, asibiti suka kai HaYaT asibitin ALI anan ne likitan daya duba HaYaT yafito yana cemusu sun samu nasarar tafarfado da ita kuma abunda yake cikinta yana nan cikin koshin lafiya karsu damu...

Daga Ammiey har Salimat dake kuka kasa motsin kirki sukayi balle su magantu dajin abunda likitan yafada saida yagama yajuya yatafi basu ce dashi kala ba!

Azuciyar Ammiey take fadin wanan wane irin tashin hankali ne?

Dame zataji da batan ALI ko mutuwarsa zatace ko kuma da cikinda yabayana ajikin HaYaT wanda a iya saninta da tsawon zamanda sukayi da ita mijinta bai taba zuwa sun ganshi ba ko kuma HaYaT tabasu labarin sun hadu wani wajen toh daga ina tasamo cikin?

Waye Uban cikin nan nata?

Ah iya tunanin Ammiey HaYaT ko fita batayi haka kawai indai ba tareda ALI ba ko kuma Salimat...!


Tunda suka dauki hanyar zuwa gida sautin kukan HaYaT kawai ke tashi cikin motar ita kadai tasan abunda takema kuka

Ita kadai tasan tashin hankalinda yake tunkararta nan gaba

Ita kadai tasan halinda zata shiga nan gaba! Ya zatayi idan ALI mutuwa yayi yabarta anan duniya ba tareda ya fallasa alakarda take tsakaninsu da ita ba?

Wane irin kalamai zata fada dan ayarda da ita bayan dik irin karairakinda suka jima suna shirgawa itada ALI gameda dangantakarsu?

Yau ga ranar karyar nan tazo!

Banda wanan ma ya zatayi da girman alkwarinda tadaukama ALI akan komai rintsi komai wuya bazata fadar cewa ita din MATAR ALI bace ?

Shikenan tafada aranta inaji ina gani duniya zata sheganta mun abunda zan haifa ba abunda zan iya akai saboda kona fadi gaskia ba wanda zai yarda dani har abada...

Har suka iso gida tashige dakinta Ammiey bata mata magana ba hakama Salimat, kowanensu damuwa biyu da biyu tahadu ta tayar musu da hankali

Suna dawowa suka isko Daddy yadawo sai alokacin Ammiey tasamu damar zubarda hawaye, kuka take sosai musaman data tuna yanda ALI yamusu bankwana kafin yafita da gafararda yaroka agaresu

Cikin kuka tace Allah sarki ALI ashe rabuwarmu dakai kenan?

Kaico...

Dakyar da haka Daddy ya rarasheta tayi shiru, saidai shikansa dauriya kawai yake dan sosai batan ALI yake tayar mishi da hankali musaman inya tuna wanan zamanin yanda yalalace mutane ba tsoron Allah akan kyalekyalen duniya saisu dau ran mutum su kashe ba tareda wata damuwa ba ko tsoron haduwarsu da Ubangiji...

Allah yakyauta!

Dazai fita Ammiey tadage kafarta kafarsa ba yanda Daddy ya iya haka sukaje suna yawan nemansa atare da hotonsa suna nunawa ko akwai wanda yasanshi lungu da sako, har yamma ba labarinsa Ammiey taki saka komai acikinta rabonta da abinci tun jiya ruwa kawai takesha shima sai Daddy ya takurata tukuna gabadaya tafita hayyacinta...

Kan kace me labarin batarsa takarade ko ina gidan TV dana radio ana cigiyarsa da kyautar kudi masu tsokar gaske wanda Daddy yasaka ga dik wanda yaji labarinsa ko kuma yaganshi zaici!

Sajidah tuni iyayenta sukazo suka tafi da ita dan yar karamar haukace takamata jin batan mijinta ba abunda take fada sai jiyan nan yakirani yace yana hanya nadaura masa ruwan zafi idan yazo zaisha Tea

Saida aka shiga yimata adu'oi kafin asamu kanta dakyar...


HaYaT kuwa tafi kowa shiga tashin hankali, gabadaya tafita hayyacinta rabonta data saka wani abu acikinta harta manta! Dan gabadayama ta manta dawani abu mai suna abinci arayuwa yunwar gabadaya ta kaurace mata

Batada aikinyi sai kuka idan tagaji ta tashi tadauro alwarlla tashiga jera salloli da adu'oi ba adadi akan Allah yabayana ALI, zazzabi kuwa kusan tarewa yayi ajikinta gabadaya dan kullun cikin zazzabi take da ciyon kai gashi kuma yanzu gidan kaf bamai bi takanta tarasa dalili kowa sha'aninsa yake ba ruwan kowa da damuwarta...

Yau wata daya kenan ana abu daya amma haryanzu shiru kakeji kamar an aika bawa garinsu ba ALI ba labarinsa

Ammiey kullun fadi take dama ko gawarsa ne tagani zaifi mata kwanciyar hanakali da dangana akan ace yabata ba'a ganshi ba anbarsu cikin zullumi da rashin sanin wane hali yake ciki

HaYaT kuwa tun ranar tadawo wata silence da ita acikin gidan har Daddy yasanda batun bullar cikinta gabadaya gidan har Ammiey da Salimat sun juya mata baya ba wanda yake shiga harkarta tun ranarda Ammiey da Daddy suka titseta akan tagaya musu waye yamata ciki taki musu magana banda kuka ba abunda take saida suka gaji da tambayarta suka hakura badan sunso ba suka zuba mata ido...

Neman ALI kuwa har gobe yi suke basu dena ba, Daddy yasa ansauke alkur'ani yafi sau goma har yanzu kuma bai gaji ba sadaka yi ake kullun...

Itakam cewa take bazata taba dangana da rashin ganin ALI ba harsai in taganshi yadawo ko kuma an nuna mata gawarsa anan zata yarda tahakura...

Lokacinda ALI yabata Dr Khaleed baya kasar sai bayan wata biyu da faruwar lamarin yadawo yakejin labari sosai hankalinsa yatashi aenun da sauri yagarzaya izuwa gidansu ALI danjin wane irin hali HaYaT take ciki

Dan tabbas ALI yagaya masa bazai sanardasu Ammiey alakarsa da HaYaT ba harsai ranarda cikin yabayana kowa yasanda shi tukuna...

Bayan sungaisa da Ammiey yamusu jaje yabukaci ganin HaYaT

Ammiey ce ta cema Salimat jeki ki kirata

Lokacinda Salimat taje kiranta tana zaune tajingina da kan gado kanta sama hawaye nabin fuskarta wanda HaYaT ayanzu batada aiki saina kuka akoda yaushe shine aikinta

Salimat ce tace kinyi bako kifito inji Ammiey

Da sauri HaYaT tadiro daga kan gado ko nauyin cikinta bataji da saurinta tasha gaban Salimat tariko hannunta ta kalleta cikin rawar murya tace Sis Salimat dan Allah meyasa kika canza mun ne?

Gabadaya kin juya mun baya ko gaisheki nayi bakya ansawa!

wane irin laifi namiki ne mai girma haka dahar kika dauki irin wanan mumunan matakin akaina?

Fisge hannunta Salimat tayi ta harari HaYaT tace

Har kinada bakin magana kina tambaya me kika mun?

Toh idan baki sani ba so nake nasani wanan cikin na Uban waye ajikinki?

Mtswwww barema nasan bazaki bani ansa ba! Ae narigada nasan komai! Nasan irin alajarda take tsakaninku da Malam Hamdan tuni naharbo jirginku!

Amma wallahi HaYaT kin bani kunya kin cucemu kin cuci kanki kin kumaci amanar Mijinki, kinci amanar Ya ALI daya daukoki danya rufa miki asiri gashi kinja mana abun kunya wanda zai dinga bibiyarmu har abada

Bazamu koreki daga gidan nan ba saboda irin girman alkwarinda Ya ALI yadauka akanki na kula dake

Amma ba komai duniya ce wanda baizo bama jiransa take balle keda kike cikinta!

Salimat tana gama fadin haka tajuya ta tafi

Wani irin murmushi mai ciyo HaYaT tayi jin irin bakaken maganganun da Salimat tagaya mata wanda bata taba zaton Salimat zata gaya mata suba kome zata aikata mai muni arayuwa

Dakyar taja kumburarun kafafunta da tulelen cikinta taje tadauko hijab dinta har kasa tasaka tafito

Ahanya tahadu da Ammiey cikin rawar murya ta gaisheda ita

Ko kallon inda take Ammiey batayi ba tayi shigewarta daki

Girgiza kai kawai HaYaT tayi wasu sabbin hawaye sukabiyo kuncenta tasa bayan hannunta ta goge...

Cikin karfin hali ta isa falon tareda sallama tagaisheda Dr Khaleed

Cikeda tausayinta ya ansa yana mata sannu

Murmushin karfin hali kawai tayi ba tareda ta ansa ba

HaYaT yakira sunanta

Dagowa tayi ta kalleshi ba tareda ta ansa ba

Dr Khaleed yace

Kibani izini nasarwa su Ammiey alakarku da ALI dan kisamu sassauci daga matsinda kike ciki dakuma irin kallonda ake miki na marar kamun kai

Girgiza kanta tayi tace

Banaso kafada! haka nima har iya karshen rayuwarta bazan taba fadin alakarmu da ALI ba, saidai nayafe masa dik irin laifukanda suke tsakaninshi dani ina fatan Allah yabayanasa cikin koshin lafiya nabashi abunda zan haifa da hannuna daga nan zan fita rayuwarsa dana iyayensa gabadaya nima naje nabude sabon babin rayuwata fatana Kenan

Inhar kacika aboki nagari Dr Khaleed karka sanarwa kowa wanan zancen kamar yanda Ya ALI yabukata dan Allah

Nisawa yayi kafin yace shikenan yamike tareda zaro katinsa yabata tareda wasu damen kudi masu yawa yace ashirye nake adik lokacinda kike bukatar taimako zan taimaka miki kinji? Dan Allah kidaukeni amatsayin Yayanki zan zamo garkuwarki adik lokacinda kika bukata, wanan katina ne adik lokacinda kikeda bukatar taimakona ki kirani kawai!

Ansa tayi tamasa godiya yafice takoma dakinta ta saka hoton dp din ALI agaba tana kallo tana sharar hawaye...


Bayan fitar Khaleed Ammiey takirasa awaya tana tambayarsa koya san wani abu gameda cikin HaYaT?

Nuna mata yayi baisan komai akai ba! Shidai kawai yasan HaYaT kanwar wani abokinsu ne kuma yanzu haka baya garin!

Shikenan Ammiey tace sukayi sallama takashe wayar...


Yanda cikinta yaturo saikace yau ko gobe HaYaT zata iya haihuwa saboda cikin yagirma sosai gashi kuma dika dika watansa bakwai ne haryanzu tanada sauran wata biyu agaba kafin tahaifesa

Yau akabasu hutun karshen shekara bayan tazana jarrabawarta dakyar dalibai kowa yawatse da kewar juna, da drebansu yazo cema Salimat tayi suje ita zata taka akafa saboda yanda kafafunta suka kumbura ko zataji saukinsu

Harara Salimat tawatsa mata kafin ta kalli dreban tace kaje kawai zamuzo

Murmushi HaYaT tayi aranta tace Sis Salimat haryanzu kina kaunata nasani! abunda kike mun ayanzu nasani na cancanci hakan daga gareki danko nice abunda zanyi kenan...

Salimat gaba tayi tana turo baki tabar HaYaT baya datake tafiya ahankali kuma dakyar

Saidai Salimat idan taga tayima HaYaT nisa sosai saita tsaya saitaga HaYaT takusa isa gareta tukuna tacigaba da tafiyarta kamar doleπŸ˜‚

Murmushi kawai HaYaT take saboda Salimat tabata dariya wato bataso ta tafi tabarta kuma bataso tanuna tadamu da ita

Hamdan ne ya hangesu da sauri ya isa gun HaYaT suka shiga tafiya tare ahankali suna hirarsu ta masoya

HaYaT aranta take fadin ina jinjina irin sonda kake mun Hamdan dikda cikinda yagani ajikinta bayan baisan tanada aure ba hakan baisa yacanza irin sonda yake mata ba daidai da dai rana saima wani tausayinta dayake saboda yasan tanashan wahalar cikin nan sosai dubaga yanda kafafunta suka kumbura dakyar take takasu

Jiyake dazaiyu cikin yadawo gareshi harya ya haife tukuna yabata tayi reno shi dinma zai tayata da kashi 50%

Sai faman sannu yake mata suna hira ahankali suna tafiya yana sanarda ita irin kewarta dazaiyi saboda yanzu ba makaranta saidai su dingajin junansu awaya kawai

Rokona gareki daya ne HaYaT karna hadu da ranarda zan kiraki kiki dagawa dan Allah tunda kinga kin hanani zuwa gidanku na gabatarda kaina asanni balle nafara zuwa tad'i!

Saidai kisani zuciyata tana nan jingim da tarin tambayoyi akanki, ina nan ina jiran ranarda kikace zaki sanar mun da komai akanki, saidai Allah yasa bazai dau lokaci ba!

Saboda kinsan me?

Yafada yana kallonta yana murmushi

A'a tace itama fuskarta daukeda murmushi

So nake kafin akoma makaranta na angwance dan gaskiya nagaji da tuzurancin nan danake wlh!

Kullun Maa gori take mun naki aure nazama tuzuru so nake nabata mamaki nanda wasu yan watani na angwance nima kona huta!

Murmushi sosai HaYaT tayi tace saura kadan komai yakusa zuwa karshe insha Allah kafara shiri!

Cikina watansa bakwai nanda wata biyu zan haihuwa komai yazo karshe kaga kuwa saura kiris!

Allah da gaske kike MAI SANYI?
Cikin murna da zumudi yayi tambayar

Allah ko tafada tana zuba mishi murmushi cikeda shaukin kaunarsa

Allah yakaimu yace

Amin...

Ahaka har suka isa bakin kofar gida Salimat tayi shigewarta tabarsu nan saida sukadan dau lokaci kafin suyi Sallama HaYaT tashigo gida

Ammiey ta tarar afalo ta gaisheda ita ciki ciki ta ansa tana duban HaYaT kasa kasa ganin yanda kafafunta suka kumbura takasa jurewa dan Ammiey akwai tausayi musaman datasan halinda mace mai ciki take shiga awanan matakin cikin na HaYaT tana bukatar kulawa tausayawa da nuna mata soyayya

Dik azuciya Ammiey take wanan tunanin tana kallon HaYaT

Dafda HaYaT zata shiga dakinta Ammiey takira sunansa tace zo nan

Dan zuciyar Ammiey takasa jurewa

Zuwa HaYaT tayi tana kakorin zama kusada kafafun Ammiey akasa

A'a zauna nan Ammiey tafada tana nuna mata kusa da ita

Kallon Ammiey tayi cikin mamaki kafin tazauna

Kallonta Ammiey tayi tanajin wani irin tausayinta nashigarta dikda tasan HaYaT mai laifi ce agareta amma bazata iya zuba ido tana ganinta tana wahala haka batareda tashiga lamarinta ba saboda ita din Uwa ce!

Wata nawa cikinki yanzu? Ammiey ta tambaya cikin daure fuska

Cikin sanyin murya HaYaT tace bakwai!

Kallonta Ammiey tasakayi dakyau kafin tace tashi ki canza kayanki kizo kici abinci muje asibiti adubaki ji yanda kafafunki suka kumbura kinajin dadin tafiya kuwa?

Murmushin dadi HaYaT tayi ganin yau Ammiey ta kulata harda damuwa da yanayin jikinta

Bakinta har kunne tace Ammiey da dan zafi wani lokacin amma ba sosai ba!

Naji tashi shiga kifito muje

Toh Ammiey tace ranta yayi fari ganin yau Ammiey takukata harda damuwa da halinda take ciki sosai abun yafaranta ranta matuka

Da kwarinta ta mike wanan karon tama manta cikinda ke jikinta
Ammiey tace yi ahankali mana HaYaT wanan wane irin rashin hankali ne saikin jima kanki ciyo da abunda ke cikinki?

Shigewarta tayi tana murmushi ba tareda ta ansa ma Ammiey ba

Girgiza kai Ammiey tayi tana fadi aranta Allah yakyauta haryanzu kurciya na damun yarinyar nan!


Ammiey saida ta tabbatar lafyanta kalau da abunda ke cikinta aka basu magunguna da dik wani abu daya dace da mace mai ciki tukuna suka dawo gida

Daki Ammiey takirata tana mata tambaya akan cikinta waye Ubansa azaton Ammiey wanan karon HaYaT zata sanarda ita komai

Saidai ko wanan karon HaYaT kuka tasaka mata sanin damuwa batada kyau gun mai juna biyu yasa tahakura tabar HaYaT badan taso ba saidai tace dole idan ta haihu zata tutsata dole tagaya mata ko kuma tadauki mumunan mataki akanta....





Cikin HaYaT yashiga watansa na haihuwa yanzu dole take zuwa yawon mike kafa Salimat na rakata harsu dawo suna yar hirarsu sama sama...

Yau ranar laraba HaYaT taji tanason zuwa yawo gashi kuma Salimat taje gidan Aunty Khadija itada Shuraime

Fitowa tayi da Hijab dinta har kasa tacema Ammiey zata dan zagaya tadawo

A'a HaYaT kijira Salimat sudawo mana ke kadai zaki tafi ba dan rakiya idan nakuda takamaki ahanya fa ya zakiyi?

Ammiey ba jimawa zanyi ba, bazanyi nisa ba nanda bakin titi zan dawo kafafuna ne Ammiey sun mun nauyi sosai idan banyi tafiyar nan banajin dadinsu, gashi kuma Salimat sai dare tace zata dawo!

Toh shikenan Ammiey tace amma kije da wayarki koya kikaji wani canji daga jikinki ki kirani ko kuma kiyi sauri kidawo gida kinji ko?

Toh Ammiey insha Allah...


Ahankali take tafiya harta iso bakin titi wani taron jama'a tagani can tsallaken titi dik wanda yabiyo tanan awajen taron take gani yaja burki yanabawa idonsa abinci

HaYaT muryarda taji tana tashi ne acikin jama'ar yasa gabadaya jikinta daukar rawa

Ahankali tasamu ta tsallaka titin tashiga kusawa cikin jama'ar danta samu ta isa gunda takejin muryar na tashi....









✍🏻
[8/1, 7:01 AM] Hayat: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*AyNuL HaYaTπŸ‘„*
_MATAR ALI GADANGA_


πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWa✍🏻*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*

*NeEnA_CoOlπŸ‘©πŸ»β€πŸ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*


*_______________________*
*πŸ‡³πŸ‡ͺNiGeR Ma FiErTΓ©πŸ€™πŸ»*


*Ψ§Ω„Ω„Ω‡Ω… Ψ₯Ω†ΩŠ Ψ£Ψ³Ψ£Ω„Ωƒ Ψ­Ψ¨Ωƒ وحب ΩƒΩ„ Ω…Ω† ΩŠΨ­Ψ¨ΩƒΨŒ وحب Ω†Ψ¨ΩŠΩƒ Ω…Ψ­Ω…Ψ― Ψ΅Ω„Ω‰ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΩˆΨ³Ω„Ω….*
*وحب ΩƒΩ„ ΨΉΩ…Ω„ ΩŠΩ‚Ψ±Ψ¨Ω†ΩŠ Ψ₯Ω„Ω‰ Ψ­Ψ¨Ωƒ يارب Ψ§Ω„ΨΉΨ§Ω„Ω…ΩŠΩ†πŸ‘πŸ»*


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI✍🏻_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷




Neenacool280@gmail.com





1⃣9⃣







Tunda suka dau hanya ba wanda yace dawani uffun saida yayi tafiya mai nisa yanemi guri gefen titi yatsaya tareda juyoda kallonsa gareta yana fadin

Malama kin barni sai tafiya nake bayan ke kika sakani fitowa dan haka ki gaya mun ina zamu nufa? Gidan wane Yayan naki zan kaiki?

Turo bakinta tayi batace dashi komai ba tareda maida kallonta kan titi

Kallonta yake saida yagaji yaga batada alamar magana koda kwana zasuyi anan yasa yasake magana ransa adan bace yace

Wai badake nake bane yar renin hankali?

Jin tsawarda yamata ne yasata sakin kuka dan ita batasan me zatace dashi ba, bazata iya fitowa kuru kuru tace masa ga bukatarta ba...

Wajen minti biyar yadauka yana kallonta tana kukan kafin yashiga rarashinta janyota yayi jikinsa ahankali yake magana

HaYaTyy kiyi shiru dan Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login