Showing 6001 words to 9000 words out of 54100 words
benan ba yaji karar rufe kofar dakin nata dan tsayawa yayi yakalli kofar kafin yacigaba da tafiya...
Washe gari tunda ta tashi tayi sallah bata koma bacci ba, kamar yanda Faridah tanuna mata haka tayi shara da goge goge kafin tadaura ruwan Tea suna tafasa tasauke tasakasu inda yakamata dankalin turawa tafere tasoya dakwai.
Saida tagama komai tsaf gidan sai kanshi yake tashi kafin kace karfe takwas tayi tagama komai tadebi nata takoma daki saida tayi wanka tukuna tazauna taci tanaci tana tunanin girma irina gidan nan ace kuma haka zatayita aikinsa batasan ranar denawa ba kuka ne taji yazo mata ba shiri tashiga rerasa...
Dasauri yafito yana gyara agogon hannunsa yayi latti saboda yau zaiyima har mutum biyu tiyata gashi kuma yamakara, kafin yakarasa saukowa kanshin soyenda tayi ne yadaki hancinsa ahankali yarufe idanunsa yashaki kanshin gashi dama yunwa yakeji dan jiya baiwani ci abincinda yasiyo sosai ba
hadiye yawo yayi yanufi table din yashiga bude bude dikda makararda yayi yasan dolema in yaje asibitin saiya nemi abunda zaici dan bazai shiga dakin taiyata da yunwa ba!
Hada Tea yayi yanasha yanacin dankalin turawan yanda abincin yamasa dadi har wani lumshe ido yake yana budewa, azuciyarsa yake fadin dama ace Faridah ta iya wanan aeda yadace...
Daidai yakwashi loma zaikai bakinsa HaYaT tabude kofar dakinta tafito hannunta daukeda plat da cup wanda tasha Tea dashi ido biyu sukayi dashi da sauri takoma baya tareda rufo kofar gam kakeji
Shikuwa kunyace tadan kamashi yaso yatashi yadena ci gabadaya saidai yakasa saida ya tabbatar yakoshi tukuna yatashi yafita yana ayana aransa yarinyar nan haka ta iya girki dankalin turawama salon soyawarsa daban ne nata, da tunaninta aransa ya isa asibitin...
Ita kanta Faridah tayaba da yanda tafito tasamu komai normal musaman datayi break fast saitaji son zaman HaYaT yashiga ranta sosai kodan samun girki yanda yakamata.
Wajajen karfe goma taji ana kiranta tamike tafito Faridah tagani bakin kofarta da alama fita zatayi gaisheda ita tayi ta ansa ba yabo ba fallasa kafin tace
Zan fita bazan dawo ba saida yamma dan haka kiyi girkin rana iya cikinki kawai, na yamma kuma kiyi damu.
Toh Aunty tace!
Amma mezan girka da yammar?
Saida tadanyi tunani tace dik abunda yadace ki girka akwai komai!
Am kihau sama kigyara dakina dana Oga gabadaya
Toh tace da ita tareda fadin
Adawo lafiya tace
Faridah bata ansa ba tayi ficewarta abunta...
Afili tace zataci girkin nawa Kenan? Harta manta jiya zama kawai nayi akan kujera tace sains goge...
Tsaye tayi tana mamakin dakin Faridah saika rantse da Allah ba macece ke rayuwa aciki ba yanda komai ya hargitse ko ina kaya ne azube, tasha wahala kafinta daidaita komai yanda yakamata, tana gamawa tashiga dakinda ta tabbatar na ALI ne shikansa dakin nasa sai ahankali saidai yafina Faridah nutsuwa dikda kasancewarta mace.
Shima gyarashi tayi tsaf tawanke toilet tafeshe dakin da turare tagama tafito agogan falon takalla taga wajen shabiyu da rabi tafiya tayi tasake wanka saboda yanayin garin akwai zafi zafi dikda ko ina gidan akwai AC amma batayi karanbanin kunnawa ba.
Saida tayi sallah tafito taduba ktchin taga indomi jingim tadauko iya wanda zata iyaci tadaura.
Tana gamaci takoma dakinta ba jimawa baccin gajiya yadauketa abunka da baka saba ba...
Taci sa'a kuwa ana kiran sallar la'asar tafarka saida tayi sallah tareda yin wanka tafito tashiga kitchin
Tunanin me zata girka take, can kawai tadaura shinkafa da miyar hanta, cikin ikon Allah kafin karfe shidda tayi tagama komai tajera takoma dakinta danata kwanon dan bataso tasake fitowa acewarta saida safe kuma insha Allah!
Faridah tana shigowa shima ALI yakuno tashi kan motar ransa ne yayi mugun bacewa ganin alamar Faridah fita tayi batareda ta sanar dashi ba!
Tana gaba yana biye da ita suna karasowa falo yashiga zazzaga mata masifa akan meyasa tafita batareda izininsa ba?
Nanfa tace bai isa ba itama tahau kan bakinta yafada tafada saida yagaji yahaye sama yabarta nan, kiran kawarta tayi Rukky tace gobe tanason ganinta komai nema yake yalalace mata nan Rukky din tace zatazo tana kashewa takira Baby Nice itama tace tazo suhadu tanason sabon aiki akan ALI dan kwanan nan zafin kansa yayi yawa...
βπ»
[8/1, 6:58 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·
5β£
...Wanka yayi yafito yasaka farar jallabiya yafito kamar arabe ko hindu tamasa kyau sosai saukowa yayi yanufi dinnin table abincinsa yaci sosai ko takan Faridah baibi ba saboda ta bala'in bata masa rai danshi atsarinsa yatsani yaga mace na fita haka batareda neman izini ba kai gabadayama da Faridah zatabi ra'ayinsa fitarma saita zama dole tayi, shiyasa abunda tayi yamugun bata mishi rai.
Bayan yagama fita yayi yanufi gidansu nan yatardasu falo anata hira sai bayan sun gaisa ne Ammiey tacema Salimat taje tadauko masa abinci
Nan yace mata akoshe yake!
Mamaki ne yakamata dan itakam tasan babu ranarda zaizo gidan nan bai nemi abinci ba, wani lokacinma kafin yagaisa da kowa saiya nemi abinci tukuna amma gashi yau dakansa yake cewa akoshe yake? Kodai Faridah tafara sanin ciyon kanta tafara sauke hakkinda ke kanta danko da safe dayazo gaidasu bai neme break fast ba gaishesu kawai yayi yatafi!
Sosai Ammiey tayi mamaki saidai tabarshi acikinta saboda ita ba akan komai take magana ba.
Sai wajen shabiyu yatashi yatafi shima din Ammiey ce ta takurashi dole yatashi danshi saiyaji gabadaya bayason komawa gidan kwata kwata!
Daddy ne yafara magana bayan sun kwanta shida Ammiey
Yakamata yaron nan mushiga lamarinsa, dikda adu'arda muke binshi da ita bai kamata ace mun zuba masa ido muna kallonsa matarsa tana yanda taga dama dashi ba, kiduba kiga yanda kallo daya zaka masa kagane baya tattareda nutsuwarda dik wani mai mace agida ace yakasance acikinta
Ajiyar zuciya Ammiey tayi tace
Nikaina abun yana damuna matuka, amma Alhj me zamuyi?
Kana gani dai yanda ko zancen Karin aure aka masa yanda yake dauke kafarsa agidan nan gabadaya harsai in mune muka gaji muka nemesa fa?
Gashi kodaya baya son ganin laifin matarsa, tsakaninmu da yarinyar nan saidai muce Allah yabi masa alhakinsa da take dauka!
Hakane amma abun nan dole musaka hannu aciki dan bazamu zuba ido munaji muna gani rayuwarsa tayi ta tafiya ahaka ba, akwai yar abokina Kaseem ranar munyi magana dashi zamu hadashi da yar wajensa Sajida yakuma amince saidai ban boye masa dik halinda yaron nan yake ciki da matarsa ba!
Wani irin dadi ne ya mamaye Ammiey batasan lokacinda ta tashi zaune ba tace naji dadin wanan lamarin
Alhj Kaseem Allah yabiyashi da gidan aljana ya kareshi, wanan abun yay kyau!
Amma ni abu daya nakema fargaba kar yaron nan yazuba mana kasa a ido yaki amincewa shine kawai damuwar!
Ae wanan karon yayi karya yagujema zancen Karin aurenda muka nema masa, dole yabi abunda mukeso saboda mu muka haifesa bashi ne ya haifemu ba, mun bashi damar farko ya auri wacce yakeso dan haka yanzu dole ya auri zabinmu.
Allah yayi mana jagora
Amin hajiyata...
Washe gari tunda safe Ammiey takira Khadija talabarta mata zancenda ake ciki itama Khadija tayi murna sosai har cewa tayi anjima tana nan tafe gidan!
Khadija yayar ALI ce, itace ya tafarko gun Alhj Suhail mahaifin ALI da Hajiya Huda
Daga khadija sai ALI yake bi mata sai Haidar sai autarsu Salimat wacce yanzu shekarunta 15 ne aduniya.
Magana takan kama sai shirin aure ake ango bai sani ba, itakam amaryar tasani kuma mahaifinta yamata bayanin waye angon nata dayake yarinya ce yar gidan tarbiya dikda tanada wanda takeso baisa tamusama iyayenta ba...
*******************
Washe gari ALI yana fita Faridah tabi bayanshi nan suka hadu da kawayen nata daga nan suka dunguma zuwa gurin wani bokansu mai suna kare kukanka
Suna zuwa batareda sun masa bayanin komai ba yace dasu yasan meke tafe dasu, nan yalabarta musu komai harmada zancen Karin aurenda iyayen ALI sukeso sumai!
Sanan kuma yace akwai wani boyayen abu agidansu wanda shikansa yakasa gano meye balle yasanarda ita!
Hankalin Faridah yamatukar tashi zaman dirshin tayi agaban bokon harda kukanta tana fadin boka yataimaketa, dakatarda ita yayi yace tabari yayi duba sa'arta akai...
Yakusan minti goma yana surutansa kafin yadago ba alamar wasa afuskarsa yace
Ba makawa sai anyi auren!
Idan kuma kika matsa awargaje zancen auren tofa aurenki ne zai mutu tsakaninki da ALI har abada!
Sosai zancen bokan yaratsa Faridah har suka dawo gida kuka take Rukky da Baby Nice sun rarasheta harsun gaji taki tayi shiru
Sai fadi take bakusan irin kaunarda nakema ALI bane shiyasa, wlh zan iya kashe dik maccenda tayi kusa dashi da sunan soyayya balle takaiga aure!
Shegu munafukan iyayensa daman can bason aurena suke dashi ba, toh wlh saina nuna musu ni isashiya ce kuma nafi karfinsu banzaye...
Rukky ce ta yatsina fuska tace ae koma menene saiki hakura ayi tunda bokan yace kidawo bayan auren yamiki babban aiki akan ita amaryar!
Kuma banda abunki bagashi yasake sabon aiki akan ALI din ba? Kinga kuwa sai yanda kikayi dashi, iyayensama yarabashi dasu kinga bama zaije gunsu ba balle sukunsa masa shikuma yazo yakunsa miki bakin ciki!
Sai alokacin hankalin Faridah yadan kwanta.
Baby Nice ce tace ki kyaleta Rukky aeni wlh haushima take bani banda abun Faridah saikace ALI ne kawai d'a namiji aduniyar nan?
Dik tabi tawani firgice akanshi, keda manyan masu kudi da mulki sukeso kikoma harka dasu kinki kibada kai kinwani nacema ALI mtswwwwwwww
Baby Nice bakisan irin sonda nake masa bane shiyasa dan kome nafada muku bazaku fahimceni ba, dan haka abar zancen kawai muje can kuci abinci kuhuta kafin kuwuce ko?
Haka akayi suna zuwa suka baje a falo
Kira Faridah take kwalama HaYaT kamar wata makauniya
HaYaT cikin bacci taji kiran kamar bana lafiya ba da sauri tamike tafito ko dan kwali babu akanta gashin kanta yazubo abaya har tsakan gadon bayanta tsawon gashin gashida sulbi ga laushi gwanin ban sha'awa gashi baki kirin dashi irina fulanin asali
Tana murza idanunta tatsaya cikin falon kafin tabude idanunta tasaukesu akan Faridah tace Aunty gani
Basu Rukky da basusan HaYaT ba hatta Faridah yau saitaga tazame mata wata sabuwar hallita!
Ido da baki bude suke binta da kallo ganin irin arzikin gashinda Allah yabata
Faridah kasa hakura tayi saida tace HaYaT gashinki ne dik wanan?
Eh tace atakaice dakuma mamakin tambayar!
Kwafa tayi tace baki nayi jeki dauko mana abinci da lemo ki kawo mana ina jiranki.
Juyawa HaYaT tayi ranta yayi mugun baci yanzu dan tsabar iskanci abinci an girka anyi komai gashi a table tsabar wulakanci daga ita har malalatan abokan nata sudauko ne yake basu wahala?
Komawa tayi daki tasako hijab dinta tadawo takai musu abincin harda ruwan wanke hannu dan reni, takai wanan tadawo takoma takai wancan
Banda kallo ba abinda suke binta dashi daga Rukky har Baby Nice datake wani tunanin Banza akan HaYaT dan daman can Baby Nice abun nata bai tsaya akan maza kawai ba har mata nema take idan taga wacce tayi mata
Saida HaYaT tagama takoma ciki
Atare kamar jira suke tabar wajen Rukky da Baby Nice suna hada baki wajen fadin Faridah wacece wanan kyakyawar yarinyar?
Mai aikice tafada atakaice!
Baby Nice ce tace lallaikam zan more da yarinyar nan, ammafa tahadu!
Faridah ce tahade rai tana fadin iskancin naki har akan yan aiki zakiyi?
Gwarama tun wuri kisake shawara dan wanan da aurenta kuma kanwar abokinsa ce
Bayanda za ayi kisa yarinya girmana yazube gurinta tazata dik haka muke saboda akace abokin barawo barawo ne amma wani lokacin ba gaskiya bane
Saboda gashi harnayi iskancina nagama ban taba harka da mace!
Ran Baby Nice ne yabace batace da ita komai ba, saidai ta kudurta aranta cewa saitasha romon HaYaT kota wane hali ne...
Yau kwana biyu kenan Ammiey suna neman ALI ido arufe basu ganshi ba, danko kiranshi sukayi baya dagawa, daga karshe ma idan sun takura kashe wayar yake gabadaya
Hankalin su Ammiey yamatukar tashi saboda lokacin bikin sai karasowa yake gashi haryanzu ALI din baisanda zancen ba...
βπ»
[8/1, 6:58 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·
6β£
...Har asibitinsa Daddy yaje ya riskesa daya tambayeshi meyasa baya daga wayarsa kuma yadena zuwa gida kame kame yafarayi danshi kanshi bazai iya cewa ga dalilinda ya hanashi zuwa ganinsu ba
Daddy fada yamasa sosai kafin yakoma masa nasiha akan hakkin iyaye akan y'aya'nsu, kuma kasani Ammieynku hankalinta atashe yake rashin ganinka da kuma kin daga wayarta idan takiraka
Daddy kuyi hakuri nikaina bansan meke damuna ba, koda nayi niyar zuwa gida lokaci daya sainaji nafasa bazan iya zuwa ba
Yanayin yanda yake maganarma yabawa Daddy tausayi dole yasan ba abanza ALI zai dauke kafarsa daga zuwa inda suke ba, yaronda wani lokacin cikin rana daya saiyaje gidan sau biyu
Na komai Daddy yace amma kamun alkwari kome zai faru yau kayi kokari kaje saboda hankalin Ammieynku yakwanta kaji ko?
Insha Allah Daddy zanje!
Sallama sukayi yarako Daddy har gaban motarsa dakanshi yabude masa motar yashiga kafin yadawo cikin asibitin
Koda yakoma kasa yin aikin komai yayi saΓ― kanshi daya fara yimar ciyo dayaso yatakura kanshi gun tunani...
Wajen karfe shidda na yamma yajuya akalar motarsa zuwa gidansu dikda wani bala'in ciyon kaine yasakashi agaba adik lokacinda yayi tunanin tuna gidansu ko mahaifansa
Ikon Allah ne kawai yakaishi gidan lafiya.
Yana zuwa Ammiey na falon zaune dakyer yayi sallama yashiga yana zuwa yakwanta kusada Ammiey yadaura kansa akan kafafunta tareda lumshe idanunsa
Ammiey sallamarsa kawai ta ansa ganin halinda yake ciki ne yasa tashiga jero masa adu'oi tana tofa masa akai tana shafawa kamar karta fara adu'ar kansa ne yayi wani irin zafi radau batabar adu'ar ba yitake tana shafa masa cikin ikon Allah Sai gashi kan nasa yadena wanan zafinda yake dazu yadawo daidai shikuwa ALI bacci ne yayi awon gaba dashi kallonsa Ammiey take cikeda tausayin d'an nata .
Ganin bayada alamar tashi ne yasa Ammiey janye kansa daga kan kafafunta ta tashi tareda gyara masa kwanciya.
Kitchin tanufa inda Salimat take girki tace tadafa dafa dukar dankalin turawa dan shine abincinda ALI yafiso sosai musamn idan yaji nama da yaji
Ganin ana kiran sallahr magrib ne Daddy dayazo tun dazu yatsheshi ahankali abude idanunsa
Shafa kansa yayi danji yayi gabadaya ba ciyo ba zafinda yake addabarsa dazu saiyajisa wasai dashi yanzu bayada wata damuwa, gaisheda Daddy yayi
Daddy yace katashi kayi alwarllah ankira Sallah toh ya ansa.
Suna dawowa Salimat taka musu abinci anan sukaci Daddy yana yana masa nasihar yadinga kula da ibardarsa akoda yaushe yadinga yawan azkar yadena sakaci da neman kariya gun Ubanginsa daga sharrin mutum ko aljan.
Insha Allah Daddy zan kiyaye yafada, dan shikansa yasan baya wani adu'oin neman tsari gun Allah dikda baya wasa da Sallah yana kokarin kare lokacin kowace daga cikinsu Alhmdllh...
Faridah agida hankalinta inyayi dubu yatashi ganin har kusan kiran sallahr isha ALI baizo ba, ta tabbatar gidansu yaje shiyasa dik tabi tadamu tsoronta daya karsu karye sihirinda tayi akansa saboda ba yau suka faraba acewarta!
Ganin tayita kiransa bai daga ba dan daga karshema kashe wayar yayi gabadaya, danta tabbatar kiran asibitin nasa tayi dan taji yana can ko kuwa, nan aka tabbatar mata yabar asibitin tun karfe shidda.
Jifa da wayar tayi akasa take kuwa wayar ta tarwatse tayi dai daya dik wanan bai isheta ba dik wasu kayanda taci karo dasu saitayi watsi dasu wasu su fashe
Jin karar tarwatsewar abubu ne yasa HaYaT fitowa cikin dakinta da sauri ganin Faridah kamar mahaukaciya dik falon ta tarwatsa shi yasa tsoronta yakamata
Daga bakin kofar tayi tsaye tana kallon ikon Allah itakam batasan me zatayi ba, sanin halinta yasa ko hakuri takasa bata
Dinnin table tazo tayi kaca kaca da abincinda HaYaT ta girka
Daga karshe durkushewa tayi kasa tasaka kuka tana fadin wlh kunyi kadan kuga karshena karya ne wata mace tashigo gidan nan da sunan MATAR ALI wallahi!
Ko wacece tayi kuskuren shiga gonata sainayi ajalinta wallahi saidai akasheni bayan ni kasheta nasandai ban mutu nabar kishiya adoron kasa ba...
Haka tayita surutai kafin ta tashi da gudu tahaye sama, wata jakarta tanufa tadauko wasu magunguna taballe ta hadiye ko ruwa batasha ba saboda bala'i ba jimawa tafara maye kanta yafara juyawa kasa tazube nan kamar kayan wanki...
Lokacinda take fadin karya ne wata mace tashigo gidan nan da sunan MATAR ALI ba karamin tsorta HaYaT tayi da ita ba, hankalinta in yayi dubu yatashi !
Komawa tayi dakinta tazauna tarasa meke mata dadi adunuyar nan...
Kansa akasa har Daddy yagama yimasa bayanin abunda suka shirya akansa gameda zancen Karin aurensa bai dago ya kallesu ba saidai me Ammiey zata shirin gani?
Kuka ALI yake kamar wani karamin yaro kafin yafara fadin
Daddy meyasa baku nemi shawarata ba kafin ayi maganar?
Cikin tausayin d'An nasa Daddy yace koda munyi nema nasan bazaka bamu hadin kai ba kamar yanda abaya kake kin yarda ALI
Ammiey kam kuka tasaka tareda tashi tabar dakin saboda ta tabbatar tsoron Faridah ne yasaka ALI kuka dan idan taji zancen auren ba karamin kai ruwa rana zasuyi da ita ba danba yau ne Karo nafarko ba da irin wanan take faruwa akanshi yazo yana musu kuka akan cewa shi Faridah ta isheshi zaman duniya...
Daddy yace kaga Ammiey kuka take saboda taga kana kuka akan auren ALI tsoronta daya karka bamu kunya ALI kazuba mana kasz a ido kasa girmanmu yafadi
Share hawayensa yayi shikadai yasan mezai tarar idan Faridah taji karin aurensa, banda hakama gawani aurenda yake kanshi wanda bandashi iyayensa ba wanda yasan dashi, shi bakin cikinsa ace kamarsa da Mata har uku?
Atsarinsa kwata kwata baida ra'ayin ajiye mata samada d'aya agidansa.
Amma gashi yau kaddararsa ce tanuna zai zauna da mace har uku shikadai!
Cikin sanyin murya yace Daddy nayarda ku aura mun wacce kukeso zan zauna da ita har karshen rayuwata.
Murmushi ne yabayana akan fuskar Daddy sosai dafa kafadarsa yayi yace Allah yamaka albarka yasanya alkhairi yabaku zaman lfy da zuri'a dayyaba
Amin ya ansa dashi tareda fadin nagode Daddy kabawa Ammiey hakuri
Katashi katafi da bakinka kafada mata ka amince zatafi jin dadi sosai kuma hankalinta zai kwanta!
Gyada kai kawai yayi tareda mikewa yafita daga dakin
Da kallo Daddy yabishi yana fadi aransa ga namiji har namiji amma mace d'aya tana neman haukatar dashi Allah yakyauta!
Shikenan Ammiey tace Allah yamaka albarka yabaka ikon yin adalci atsakaninsu.
Amin yace.
Tashi katafi dare yayi idan kaje kuma kace ina gaida Faridah
Zataji!
Saida yakai bakin kofa yajuyo yace Ammiey kisakani a adu'a dan Allah
Gyada masa kai kawai tayi dan in tace zatayi magana kuka ne zai kwace mata alokacin, tana kallonsa harya bar dakin tabishi da adu'a.
Tuki