Showing 27001 words to 30000 words out of 54100 words
idanunta daga kallonsa ahankali takai gwiwoyinta kasa bakinta narawa tafara fadin
Ban taba zaton inada matsayi da gatanda zaka mun irin wanan alkhairin awajenka ba ALI, furucin bakina da gangar jikina bazasu taba iya biyanka wanan ba ALI!
Nayanke kauna da karatuna tun ranarda mahaifina ya yanke shawarar aurar dani ga wanda ban sani ba, saigashi kaddara tasa kaine mijin nawa amma ta wani sigar daban!
Dan Allah ALI meyasa ka aureni? Nakasa ganewa kai mutumen kirki ne ko akasin hakan kullun canza mun kake tambar HAWAINIYA nakasa gane bayanka balle gabanka kamar hankaka kum...
Tashi ALI yayi ya isa gareta tareda saka hanneynsa dika biyu yamikarda ita tsaye yana kallonta ido cikin ido kafin yace
Gaskiyar lamari HaYaT tausayinki kawai nake, ina daukarki amatsayin kanwata kamar yanda nake daukar Salimat haka kema haka!
Kisaka aranki abunda yafaru tsakanina dake kwanan baya tsautsayi ne kawai ko nace tatsuniya ko ranar rashin macenda zata kwantar mun da hankali ne yasa hakan tafaru tsakaninmu dake, ayanzu kuma Sajidah tagama mun komai tana mun dik abunda nakeso akuma lokcinda nakeso! ki manta da komai ni yayanki ne
Zan maye maki gurbin Uwa da Uba idan kin amince?
Wani irinsa ne takaici yakumeta jin kalamansa saida taji maganarsa takarshe tukuna
Tagirgirza kanta tana fadin wanan ne bazaka iyaba ALI!
Bazance bazaka iya maye gurbin Mahaifina ba, amma ita Mahaifiya dabance!
Bazan iya zama ajikinka nayi shagwaba nagayama damuwana ba kamar yanda zan iya yi agaban Mahaifiyata ba ALI, ba lalle bane ka fahimci wasu matsalolina ba kamar yanda mahaifiyata zata iya fahimtata!
Mahaifiya zata iya sanin abunda yarta zata iya aikatawa agaban idonta ko bayan idonta amma kaifa?
Sai abunda nayi gabanka zaka iya fahimta!
Uwa kallo daya zatama yarta tagane me yar tata take tsanin so ko take bukata amma kaifa ALI?
Tafada cikin dan daga murya tana kallonsa idanunta nazubarda kwalla
Jikinsa ne yayi yakasa cewa da ita komai saida tagaji da jiran ansarsa taduka tadauki jakar harta juya zata tafi yace da ita
HaYaT cikin sanyin murya
Cak tatsaya batareda tajuyo ba
Ashirye nake dana sauwake aurena dake kanki Adik lokacinda kika bukaci hakan daga gareni!
Yana gama fadin haka yajuya ya haye sama yabarta nan tsaye
Maganarsa ta girgizata aenun juyawa tayi tana kallonsa harya shige dakinsa
Dafe kirjinta tayi lumfashinta taji yana neman ya gagareta kuka takeso tayi mai karfi amma yaki zuwa
Daidai lokacin ne Sajidah tayi sallama tashigo ganin HaYaT tsaye da jaka ne yasa tanufi inda take tana fadin kardai kice mun kema din tafiya zakiyi HaYaT?
Jin muryar Sajidah da tambayarda tajefo mata ne yasata sakin wani irin kuka tareda fadawa jikin Sajidah tacigaba da kukanda take sosai
Hankalin Sajidah ne yatashi itama kukan tafarayi tana shafa bayan HaYaT takasa cemata komai wanan karon
Sunkai minti biyar ahaka kafin HaYaT din tajanye jikinta daga na Sajidah kamar bΓ’ itaba taja yar jakar da sauri tashige dakinta ta nulle
Tsaye Sajidah tayi tana kallon kofar HaYaT tareda mamakin abunda yasata kuka saidai koma menene tasan ba karami bane sosai ta tausayama HaYaT din, ganin ALI yana nan yasa tanufi dakinsa ta tardashi yafito daga wanka yana ganin idanunta alamar tayi kuka cikin kulawa yayo kanta yana tambayar dalilin kukanta?
HaYaT Baby meya samu HaYaT take kuka? Me aka mata ko kaine?
Ni kuma mezan mata? Kinsan halin HaYaT ba lafiya ne da ita ba kilama aljanunta ne suka sakata kuka kinzo ke kuma sarkin tausayi kin tada hankalinki akan banza!
Sai alokacin hankalinta ya kwanta atunaninta gaskiya ne HaYaT nada aljanu su suke sakata yawan shiga damuwarda take da yawan daure fuska da rashin maganarda take gabadaya...
Shikuwa ALI cigaba da harakokinsa yayi kamar bashi ne yashararo karya irin wanan ma Sajidah baπ
Kukanta tacigaba dayi tana kaico da zuciyarta data kamu dason mutumenda baimasan tanayi ba wanda har yana ikirarin zaya rabu da ita adik lokacinda takeso
Ahankali tafurta da wayauna da hankalina ALI bana tunanin zan iya neman saki daga gareka saidai na mutu ahaka....
Yau takasance ranar monday tunda asuba data tashi sallah bata iya komawa bacci ba dikda tagama dik wasu ayukanta dayakamata tayi dawuri shiryawa tayi tsaf cikin doguwar riga fara iya gwiwa da wando kalar ja hijab dinta ma ja ne saidai bayada girma sosai tasaka takalmanta kalar baki sosai kayan suka ansheta takara zama wata yar karama da ita tsohon agogonta tadauko tadaura ahanunta yazauna daf gwanin ban shwa'a tafito yar black beau-fils da ita ita kanta kallon kanta take amadubi tana murmushi ganin kyanda tayi dikda ko powder bata shafa afuskanta asalin kyau kenan fatarta sai sheki take
Alokacin karfe bakwai da minti shabiyar ne zama tayi zaman jira dan batasan wazai kaita makarantar ba kawai itadai tasan yau ne takuma shirya
Sajidah taleko taganta harta shirya
Inyee yan mkaranta kinga yanda kayan nan suka miki kyau kuwa? Kai HaYaT mijinki yahuta! Kinfi fararen mata sau dubu kyau da fasali gaskia mijinki yayi dace!
Murmushi HaYaT tayi tana fadin ina kwana Aunty Sajidah
Azuciyarta kuma tana fadin ae mijinki ne mijina nasan dakin sanda wanan bazakice haka!
Lfy kalau nadameki da surutu ko?
Murmushi tasakeyi batace komai ba
Inda sabo Sajidah tasaba da halin HaYaT bata magana mai tsayi da ita dan haka bata damu ba tace
Kifito Yayanki yana jiranki kutafi
Dago ido HaYaT tayi da sauri ta kalli Sajidah yayinda taji gabanta yayi mumunan faduwa haka kawai
Dakyer tasamu tace da ita toh Aunty Sajidah ina zuwa tafada tana murmushin gefen kumatu yake kenan wanda yafi kuka ciyo
Fita Sajidah tayi alokacin ALI yazauna dinning zai break tace masa tana zuwa!
Kallonta yayi yace waima tayi break kuwa?
Dan jim tayi kafin tace bana tunanin tayi gaskiya saboda kayan nan yanda nabarsu ba ataba komai aciki ba!
Tana rufe bakinta saiga HaYaT tafito kallonsu yakoma gareta Sajidah tace yauwa gata nanma sai tazo tayi kafin kuwuce ko
Kamar kazarda kwai yafashema aciki take tafiya
Sajidah tace HaYaT zo nan
Ba musu ta isa inda take batareda tabari sun hada ido da ALI ba wanda tun fitowarta yakafeta da idanunsa kamar maye
Zauna yau kawai muyi break dake HaYaT dan Allah karki ce a'a kinji?
Kallon ALI tayi taga ita yake kallo da sauri tadauke idnunta akanshi tace a'a Aunty Sajidah banajin yunwa fa
Tashi Sajidah tayi takamo hannunta tazaunar da ita kujerarda suke kallon juna da ALI tana fadin ae wallahi baki isa ba gwara kawai kizauna kici kinsan fa yau makaranta zaki wuni ba lallai bane kisamu abincinda kikeso acan kici ki koshi musaman yau ranar farko ce rashin sabo bazai barki kici yanda yakamata ba!
Ba yanda HaYaT ta iya haka tahadama kanta Tea ta janyo bredi har alokacin batama ALI ina kwana ba shima haka bai nema ba saidai kayanda tasaka ne suka bala'in mata kyau harya kasa dauke kansa daga kallonta
Gashi takasa shan komai takasa ci, gabadaya yau saitakejinta wani irin ALI yakafeta da ido
Sajidah ce talurada HaYaT bataci
Takalli ALI da niyar masa magana saitaga gabadaya idonsa da hankalinsa suna kan HaYaT wani irin dum taji kirjinta yabuga ganin irin mayen kallonda yake mata
Ita kanta tayaba kyanda HaYaT tayi balle shi ALI dayake namiji?
Dikda tasan HaYaT da aurenta amma hakan bai hanata jin wani irin kishinta da haushin kallonda ALI yake mata ya tokare mata zuciya ba, tuni shedan yafara karanto mata wasikar jaki akan HaYaT fa kyakyawa ce dikda aurenda take dashi hakan bazai hana ALI yasota ba koda da iskanci ne ko bayan idanunki suci amanarki ba!
Tsam sukaga tamike ta tafi falo taje tadauki jakarta ta yafa mayafinta tanufi kofar fita tana fadin Baby ni natafi zanyi latti
Adawo lafiya yace da ita
HaYaT dinma mikewa tayi tsaye itama tammakalla jakarta akafada tafito waje ta tsaya tana kallon Sajidah datake shirin fita cikin motarta ajiyar zuciya tasauke tana fadi aranta rayuwa kenen...
Idan kingama kisameni amota taji yafada abayanta yayi gaba
Binsa tayi abaya...
Harsuka iso cikin harabar makarantar ba wanda yama dan uwansa magana saida aka nuna mata komai da ajinda zata zauna tukuna yatafi har lokacin magana bata hadasu ba kamar kurmaye
HaYaT daman can bamai surutu bace kowa kagani yakama abokinsa sai hira ake kafin lokacin shiga yayi ita kadai tazauna hayaniyar daliban ce tafara takurata har kanta yafara ciyo
Can taji muryar Salimat tana fadin la HaYaT???
Cikeda farin ciki HaYaT tamike tarungume Salimat tana fadin Sis Salimat Allah yasa ajin nan kike?
Wallahi anan nake kema haka kenan?
Nima haka! Amma gaskia naji dadin wanan lamarin...
Da aka tashi daga makaranta drebansu Salimat ne yakai HaYaT gida wajen karfe uku na rana, koda taje gabaya tagaji ga yunwa dan haka tana cire kayan makaranta tayi wanka taje kitchin tahada indomie da kwai tazo tazauna taci takoshi tukuna takoma dakinta ta kwanta sai baccin gajiya sallahar la'asar dinma sai wajen biyar tayi
Yau nishadi kawai takeji yau itace amakaranta burinta zai cika, fitowa tayi falo taji motsin Sajidah kitchin gurinta taje tana gaida ita
Saidai yanayin yanda Sajidah ta ansa gaisuwar ne yabata mamaki dan tunda suke da ita bata taba hade mata fuska irin yau ba, a iya tunaninta kuma ita bata mata komai ba kafin surabu dazun nan
Tabe bakinta tayi tajuya tafito daga kitchin din tayi lambu...
Ki kira HaYaT muci abinci
HaYaT kuma?
Sajidah ta maimaita sunanta tana kallon ALI dan yau ne Karo na farko dayace takira HaYaT suci abinci tare
Eh HaYaT !
Hmm yaushe muka fara haka da ita?
Yaushe tafara cin abinci tare damu?
Cikin bacin rai Sajidah take maganar
Baki saba ba! Shiyasa sam bacin rai bai miki kyau ba Sajidah, yaushe kika fara mun musu akan maganata?
Inace dazu da kanki kikace tazauna ayi break da ita? Toh daga yau atare zamu dinga cin abinci da break gabadaya ! Ko kinada ja ne?
Jikinta ne yayi sanyi batace dsshi komai ba ta tashi takira HaYaT
Ita kanta HaYaT abun yazo mata abakon lamari, saidai haka kawai tatsinci kanta da fitowa tazo tazauna tana fadin sannunku da hutawa
ALI ya ansa cikin sakin fuska yana fadin sannunki yar kamaranta! Ina fatan komai normal?
Alhmdllh kawai tace tashiga zubama kanta abinci tafara ci batareda takara bi takan su ba
Itakam Sajidah ciki ciki ta ansa gaisuwar HaYaT saikuma tashiga satar kallon ita HaYaT din da ALI
Ganin tayi HaYaT cin abincinta kawai take, ammashi ALI dik lokaci lokaci saiya zubama kyakyawar fuskarta ido
Sajidah jitake kamar ta tashi tarufe HaYaT da duka takeji
Tsananin kishi ya hanata cin abincin kirki
Itakam HaYaT tana gamawa tasha ruwa abunta tamike takoma dakinta...
,,,,,, ΨΨΨ
Janyota yayi jikinsa yana shinshinar kanshin jikinta yana fadin Babyta meye damuwarki ne wai?
Nalura tun ranarda HaYaT tafara zuwa makaranta gabadaya kin canza ko zuwan nata ne bai miki ba?
Hmmm ba wanan bane damuwana!
Sajidah tafada kamar tayi kuka
Abincinda takeci damu ne bakiso tadena?
Da sauri tadaga kanta alamar eh!
Ni gaskiya banaso tana fitowa cin abinci damu Baby, kasani fa HaYaT matar aure ce matar wani karka bari shedan yarinjayeka ka koma dana sani nan gaba
Dakatawa ALI yayi da kokarin hada bakinsa da yake da ita ya tsura mata ido natsawon dakiku kafin yace
Abunda tunaninki yabaki kenan?
Zargina kike Sajidah?
Ba zargi bane ALI! Ina maka hannunka mai sanda ne gudun abunda zai iya faruwa nan gaba shedan mugu ne!
Dik wanda yaga irin kallonda kakema HaYaT zaiyi zargin wani atsakaninku da ita ALI
Ya isheki haka Sajidah!
Idanma HaYaT batada aure nace zan aureta laifi ne?
Ba laifi bane amma abun kunya ne ka auri yar karamar yarinya mai karancin shekaru irina HaYaT !
Ok haramun ne kenan?
Ba haramun bane! Amma ana barin halak dan kunya saboda HaYaT tayi kankanta kuma matar wani ce koka manta?
Kin canza Sajidah! Gabadaya kin canza wanan ba Sajidahr da nasani bace !
Ransa abace yatashi yabar dakinta yakoma nasa dakin
Yakwanta amma bacci yakasa zuwa tunani yake meyasa Sajidah take zarginsa? Shidai yasan bason HaYaT yake ba, shin me yake agabanta dahar take zarginsa?
Yana cikin tunani ne Sajidah tashigo takwanta kusa dashi juya mata baya yayi dan da gaske tabata masa rai matuka
Saidai dayake Sajidah tasan lagwan abunta hakuri tashiga bashi ta hanyarda tasan yafi ganewa
Su ALI tuni ya manta wace duniyarma yake...
Bangaren HaYaT kuwa tun ranarda taje makarantar wani malaminsu mai suna Hamdan ya takurata idan yashiga ajinsu baida aiki sai satar kallonta
Tun ba'a ganesa harta kowa yaganeshi
Abu kadan yace HaYaT gabadaya yan ajinma sun lurada sonta yake
Itakam atakure take saboshi har makarantarma neman fita ranta take sai Salimat na karfafa mata gwiwa akan tashare shi kawai kamar batasan dashi ba
Amma takasa, saukinta daya ta iya karatu tana daukar dik wani darasinda aka koyar dasu shine abun yazo da sauri, komai da yanda yake mata tambaya kullun agaban yan ajin da ace bata ansawa bata iyaba aeda tashiga ukunta ita kam...
Yau ranar week-end ce wajen karfe tara na safe HaYaT tana chat da Salimat taji alamar sako yashigo wayarta tabude taga sabon number
Ba bata lokaci tashiga kamar haka taga an rubuta
_Assallamu alaikum Gimbiya sarautar mata ina fatan kin wuni cikin koshin lafiya yake kyakyawa sanyin idaniyata_
Ido waje tagama karanta message din
Ba bata lokaci ta ansa sallamar tareda ta tambaya waye kai?
Kamar jiranta ake taga message yashigo
_Wani bawan Allah ne mai tsananin kaunarki da burin faranta ranki yake kyakyawa mai sanyin murya_
Kalamansa sosai suka daki zuciyarta murmushi tayi azahiri kafin tarubuta
Kacika son wasa!
Dan Allah waye kai?
Bazan fada miki waye ni ba harsai kin mun alkwari guda daya, kin yarda?
Wane irin alkwari ne haka kuma?
Zan gaya miki waye ni amma ba yanzu ba harsai kin bani dama na nuna miki irin kaunarda nake miki kin fara sona da kanki tukuna yake MAI SANYI...
jim tayi tana tunanin wacce irin ansa yakamata ta tabashi?
Wata zuciyar ce tace da ita kin manta igiyoyin aurenda suke kanki HaYaT ?
Wata zuciyar kuma tace da ita ALI yabaki dikkanin damar yin abunda kikeso dan haka dole zakiyi soyayya kiyi aure nan gaba, ALI baya sonki da bakinsa yafurta dan haka gwarama kisan abunyi tun wuri!
Tayaya zan yarda dakai ban sanka ba, bansan waye kai ba, idan kazo danka cutar dani ne fa?
Bazan taba iya tunanin cutarda abar kaunata ba, wallahi wallahi kaddara bata hadamu dan na cutar dake ba MAI SANYI kawai kibani dama danki tabbatar da hakan!
Shikenan bazan iya amincewa dakai dari bisa dari ba, amma zan yarda nabaka damar mudinga gaisawa kawai dakai ka yarda?
Na amince na yarda ahakanma godiya nake MAI SANYI.....
βπ»
[8/1, 7:01 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
*Ψ§ΩΩΩΩ
Ψ₯ΩΩ Ψ£Ψ³Ψ£ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨΨ¨ ΩΩ Ω
Ω ΩΨΨ¨ΩΨ ΩΨΨ¨ ΩΨ¨ΩΩ Ω
ΨΩ
Ψ― Ψ΅ΩΩ Ψ§ΩΩΩ ΨΉΩΩΩ ΩΨ³ΩΩ
.*
*ΩΨΨ¨ ΩΩ ΨΉΩ
Ω ΩΩΨ±Ψ¨ΩΩ Ψ₯ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨ§Ψ±Ψ¨ Ψ§ΩΨΉΨ§ΩΩ
ΩΩππ»*
π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·
1β£4β£
_Kwana biyu wlh bana samun time ne shiyasa bana typing kullun, ina bukatar adu'arku plzππ»_
Yau sati daya kenan haduwar HaYaT da wanan mutumen dayace mata sunansa Salis sosai ya iya kalamu masu dadi da kwantarda hankalin mai sauraro tun HaYaT bata yawan kulasa hartazo tashiga kulashi kusan kullun suna tare awaya suna chat tun haduwarsu bai taba yimata wata maganar banza dazai saka tamasa wani kallo irina mutanen banza
Shiyasa take jin dadin mu'amala dashi idan baya online sam batajin dadi haka zata zauna tanajan tsaki wani bisa wani itace bazata nutsu ba harsai in tagansa yazo online anan ne hankalinta zai kwanta
Tuni tawatsarda wani tunanin ALI arayuwarta musaman tashiga takaka tsantsan gurin boye alakarta da Salis dikda tasan ALI bayada matsala da hakan saidai takeji aranta tana shakkar yasan tafara alaka dawani namiji daban
Lokaci na tafiya kwanaki na dada shudewa HaYaT nakara girma dik kyau da cikar na mace kara bayana yake ajikinta kullun gawani haske da take karawa asalin kyan fatartata na kara fitowa, mu'amalarta da kawayenta yasa take dada gogewa sosai tawaye naban mamaki gashi Salimat tahadata da kawayenta 'Ya'yan manya shiyasa ayanzu dik wanda yasan HaYaT abaya idan yaganta yanzu dawuya ya iya ganeta saboda yanda gabadaya tacanza tayi kyau
Mayuka masu tsada da kayan kwalliya na yan gayu Salimat take bata, sosai suke kaunar junansu da Salimat kamar yan uwan juna haka suke jin kansu, daidai da rana daya Salimat bata taba nuna banbancin matsayi tsakaninta da HaYaT ba
Ammiey ita kanta da Daddy ba wanda bai shaida kaunarda ke tsakanin yarsu da HaYaT ba, Salimat kome Ammiey zata mata biyu take ita daya HaYaT daya
kayan sakawa, takalmi, hijab ne dadai sauransu...
Wasa wasa ALI tunanin abunda yafaru dashi da HaYaT yakasa gushe masa arai, musaman yanzu data canza komai nata yazama na manyan mata ga girman jiki da take komai na cikar hallitar mace mai diri yabayana ajikinta saiyakejin sonta da kauanrta nahuda sassan jikinsa ahankali suna ratsa zuciyarsa wani irin shaukinta da begenta ne suke damunsa amma saidai girman kai wai karta renasa yahanasa nuna mata saidai yayita binta da kallo adik lokacinda suka hadu kamar tsohon maye
Itakam tun kallon nasa na damunta hartazo yadena damunta, gabadayama tadena kunyarsa...
Yau suka gama exam dinsu na farkon zango za'a basu hutu sosai takejin haushin hutunda za'a basu yau dan ita in son samunta ne bataki har hutun shekara adena badashi ba, karatu kawai!
Sun fito break ranta ba dadi yau shiru shiru da ita ko Salimat taki yima magana kamar kullun wata daliba tazo tace mata Malam Hamdan yana nemanta ofis dinsu na malamai
Ina zuwa tace da ita kafin taja wani dogon tsaki
Salimat tace kinga HaYaT tashi kitafi dan Allah kidawo karki janyo mana masifar Malam Hamdan kinsan baison raini dik cikin malamai yafi kowa zafi ba
Salimat Malamin nan yana takurani dayawa! Bansan meyakeso dani ba bayan dik abunda yake mun a classe kuma uwar me zanzo namasa a ofis? Meye hadina dashi?
Kinga HaYaT aekoya haukace bazaice yana sonki ba tunda kinga kinada aure, kuma kinga ae daga yau ne ba? Munada hutun sati biyu agabanmu bashikenan ba nikam?
Hmm ajiyar zuciya kawai HaYaT tayi tana mikewa tanufi ofis din da sallama fuskarta ba walwala
Da sallama tashiga ya ansa yadago yana kallonta tareda sakar mata wani lallausan murmushi Malam Hamdan wankan tarwada ne fatarsa mai kyau shiba baki ba kuma bazaka kirasa da farin mutum ba, dogo ne mai murjajen jiki fuskarsa ba yabo ba fallasa yanada kyau daidai gwargwado yanada fararen hakora da washirya wacce takarama fuskarsa kyan gani ba laifi
Dauke kanta tayi daga murmushinda yasakar mata gani tace Malam atakaice!
Gimbiya sarautar mata kyakyawar mace mai farar zuciya sannunki dazuwa mai SANYI...
wani irin waigowa HaYaT tayi tana kallonsa bakinta narawa take fadin