Showing 30001 words to 33000 words out of 54100 words

Chapter 11 - AYNUL HAYAT COMPLETE HAUSA NOVEL

12 Dec 2024

8207

a ina kaji wanan kalaman?

Waye kai?

Kardai kace mun kaine Salis?

Cikeda mamaki tajero masa wanan tambayoyin

Tambayoyi uku acikinsu wacce zan fara ansa miki MAI SANYI?


yar zufa ce taji ta taru agoshinta tasa hannu ta sharce tace Malam Hamdan dan Allah waye kai?

Salis!

Salis tamaimaita idonta waje ?


Eh ko bakiyi na'am da ganina azahiri bane HaYaT ?

Nine Salis wanda muka jima muna chat dake ina fatan zakiyi farin cikin ganina azahiri?

Girgiza kanta tayi tareda juyawa da saurinta zata fita

Ba tsammani taganshi agabanta yarike kofar kamar yayi kuka yafara magana

HaYaT dan Allah karki kujeni nasan namiki laifi boye miki koni din wanene, dikda nasan matsayina da naki ba daya bane amma wallahi ina sonki ina kaunarki wallahi bazan iya rayuwa bake ba, dan Allah karki juya mun baya


Ganin abun take kamar amafarki

Hawaye ne suka zuba fuskarta tasa bayan hannunta tagoge tace

Dan Allah Malam kabarni nafita lokacin komawa aji yayi yanzu kuma kar wani yashigo yaganmu ahaka nashiga uku

Maimaikon yabata hanya tafita saima taga yaduka har kasa yaruko hannunta yana kallonta fuskarsa damuwa tabayana akai karara

Kokarin kwacewa tayi amma takasa, sai tasaka kuka dan Allah Malam Hamdan kasakar mun hannuna ko nayima ihu

Bazan saki ba HaYaT harsai kin anshi kokon barana kin amince da tayin soyayyata agareki dan Allah

HaYaT kodan kin ganni Malamin makaranta ne yasa zaki gujeni? Kin wuce ajina ko HaYaT ? Wallahi ba laifina bane laifin zuciyata ne data kamu da kaunarki kamar yayi kuka yake maganar

Ganin bayada niyar sakin hannunta ne yasa tace na amince nima sonka!

Da gaske HaYaT ?

Eh da gaske nake har cikin zuciyata!

Sai alokacin yamike daga durkusonda yake yana murmurshi

Kallonsa tayi ta kalli hannunta dayake rike

Tsaf yagane abunda take nufi koda batayi magana ba saida yasumbaci hannunta tukuna yasaketa tareda bude mata kofar tafito da sauri har tana tuntube

Da kallo yabita yana zuba murmushi...


Salimat datake aji zaune dikta damu taga HaYaT batazo ba

Tana ganinta tashiga tambayarta HaYaT kinyi kuka ko?

Me Malam Hamdan yamiki? Dukanki yayi?

Bako daya Salimat !

Kimanta kawai da zancen kinji?

A'a HaYaT kinsan hankalina bazai taba kwanciya inhar bansan meye yamiki ba

Ganin Salimat tashiga damuwa ne yasa tace

Cewa yayi yana sona, ganin inada aure yasa nagaya masa gaskiya

Amma kukan fa?

Naga kina kuka, meya sakaki kukan toh?

Salimat mganarsa ne taban haushi shiyasa nayi kuka !


Hmmm bakida dama kekam, ki shareshi kawai kinji?

Tohm


Yauwa Safiyah yau ne ranar zagayowar ranar haihuwarta gabadaya ajin za'aje gidansu kema kizo muje dan Allah ba jimawa zamuyi ba zamu dawo

Murmushi HaYaT tayi tace mezai hanani zuwa kuwa...?




Haka kuwa akayi sun tafi tare saidai ba kamar yanda Salimat tacema HaYaT bazasu jimaba danko wasa wasa saigasu magrib ta riskesu agidan su Safiyah saidai HaYaT bataka komai aranta ba sakewa tayi akayi shagali da ita


ALI saikai kawo yake afalon kasa tun shidda yazo gidan HaYaT bata nan kuma Sajidah tace ita rabonta da ita tun safe

Kishi da takaici ne suka saka agaba ALI harma yamanta scul dinsu daya da Salimat balle yakira gidansu yaji ko suna tare, ransa in yayi dubu yabace kasa hakurama yayi saida yaje scul din akace masa tun karfe uku suka tashi hasalima anbasu hutu sai nanda sati biyu

Haka yajuyo yadawo gida yatarda har lokacin bata dawo ba, sai masifa yakema Sajidah abu kadan tayi yahauta da masifa dikda hakuri irina Sajidah saida ranta yasosu musamn data gane ALI kishin HaYaT kawai ba komai ba

Saboda idanunta akansa tunba yauba yanda yake kallon HaYaT ba irin kallon Yaya da kanwa bane irin kallon masoya ne yake mata

Dataga abun yakici yaki cinyewa falon sama tahaye tayi zamanta tana hangosa zuciyar ba dadi...


Ana kiraye kirayen Sallahr isha HaYaT tayi sallama tashigo

Ganinsa tsaye tsakar fallon ne yasa gabanta faduwa ganin yanayin fuskarsa ba annuri

Tsaye tayi takasa motsawa daga inda take sai kallon kallo suke daga inda yake tsoro yagama cika mata ciki ji take kamar tajuya takoma waje da gudu

Sajidah daga inda take tana hangosu dikkansu biyun

Ahankali yataka zuwa inda take yana jifanta da wani irin kallo na zaki gane kurenki

Tun kafin yakarasa gareta tafara hawaye

Daf da ita yatsaya cikin tsawa yace daga ina kike?

Gidan kawarmu tafada muryarta na rawa

Sake hade rai yayi yakalli jikinta yace wanan kayan fa? Dasu kika je?

Sai alokacin ta tunada saida sukaje gidansu shi ALI din suka canza kaya da Salimat tukuna suka tafi takuma manta sam data canza kafin tadawo

Wallahi Salimat tabani nasaka kuma tare muke da ita ka kirata kajima!

Dankin rena mun hankali ba?

Kigaya mun dawa kike tare tun kafin na babballaki agidan nan wallahi HaYaT dan raina yamugun baci

Cikin tsawa yayi maganar

Kuka tafashe dashi tana girgiza kai

Kukanta ne yasake tunzurashi wani irin wawan mari yakifa mata wanda yayi sanadiyar zubewarta kasa

Bai damu ba yacigabada magana toh kinyi karya badai agidan nan ba!

Maza kika fara bi? Wato za'a baku hutu shine zakibisa ku holewarku zakuyi kewar sati biyu ba?

Maganganunsa sun daki zuciyarta wani irin kuka take tana jujjaya maganganunsa azuciyarta

Masifa yashiga zazzaga mata da tijara iri iri ganin kamar zai doketa ne yasa Sajidah zuwa tashiga tsakaninsu itama ya hada da ita ya zazzaga musu masifa kafin yajuya ya haye sama yabarsu nan

Sajidah tamikarda HaYaT tsaye tajata takaita har dakinta tafito tanufi dakin ALI

Fita yace da ita banason ganin kowa akusa dani awanan lokacin

ALI magana zamuyi ba inda zani sai munyi magana!

Zama akan gado yayi tareda rufe idanunsa zuciyarsa nabugawa da sauri sauri

ALI yarinyar wacece ita?

Na tabbata akwai wani abu Wanda kake boyewa atsakaninku da ita!

Sajidah dan Allah kifita banaso muna samun sabani dake akan wanna maganar, HaYaT amanace agurina idan ban saka ido naji haushin darenda tayi inda ban sani ba ba tareda izinina ba kuma me kikeso nayi?

So kike nace mata abunda tayi daidai ne kome?

HaYaT haryanzu yarinya ce batasan meye daidai da ita bΓ’ sai ana nuna mata hanya bazan zuba ido naga ta lalace abanza ba kin gane ko?


Toh idan hakane kamaida ita gun Yayanta mana aenasan bazai rasa wajen zamanta ba agidansa komai talaucinsa kuwa!

Wani irin kallo yawatsa mata na bakisan abunda kike fada ba

Can yace naji, amma ban dauka ba!

Inhar kinga HaYaT tabar gidan nan tofa mijinta yazo dakansa yadauketa yatafi da ita amma ni bazan maida ita da hannun ba, kuma bazan saka mata ido ta lalace ba tareda nadau mataki akai ba!

OK haka kace?

Me kike nufi da haka nace Sajidah?

Wai meyasa kika canza ne kwanan nan nikam?

Cikin takaici tace

Yazama dole nacanza saboda inaji ina gani kana shirin kai kanka ga hallaka! Nida nake tsakaninku ni nasan meke wakana Baby shedan nema yake yaci galaba akanka kai bakaga irin kallnda kakema HaYaT bane? Kallon sah'awa da kauna Kake mata kullun, ko saina cemaka ALI son HaYaT kake kafin ga gane me nake nufi?


Baison maganar tayi tsayi yasa yace da ita naji zan gyara zan kiyaye kiyi hakuri kinji?

Ajiyar zuciya tasauke ba tareda tace dashi komai ba tafita...

Ranar dik gidan ba wanda yaci abincin dare kowane yakwanta zuciyarsa ba dadi kowa kuma da irin abunda yake sakawa aransa ba kamar HaYaT da kalaman ALI suka mata ciyo suka hanata bacci sai juyi take gashi kuma Malam Hamdan yadameta da kira da SMS taki ansa kodaya daga ciki, sai wajajen karfe uku bacci barawo yayi awon gaba da ita...


Haka yake gun ALI shima tunanin rashin kyautuwar kalamanda yama HaYaT ne suka hanashi bacci harya kuduri aniyar da safe zaije yabata hakuri

Kasancewar bacci bai daukesa dawuri ba yasa har karfe tara bai tashi daga bacci ba sai wajen karfe goma yayi wanka yafito

HaYaT da wayar Hamdan ta tasheta daga bacci tun wajen karfe takwas yasa ta tashi dole tayi wanka tadawo kafin da kanta takira Hamdan din

Hakuri yashiga bata akan tayafe masa takuma yarda da soyayyarsa

Taushin kalamnsa yasa HaYaT take sauraransa harma taji ya mantarda ita daga bakin cikinda ALI yajefata aciki jiya, sakewa tayi dashi suna hirarsu cikin tsafta da kwarewa irina Hamdan da kalamansa

ALI dayake shirin zuwa dakin HaYaT yaji muryarta alamar tana waya tana dariya cikin kwanciyar hankali, jin kalamanda suke fitowa daga bakinta INASONKA KUMA ASHIRYE NAKE DANA AUREKA KOMAI TALAUCINKA KASANI KUDI KO MULKI BASHINE SO BA KUMA....


Banko kafar dakinda taji anyi ne yasa wayarda ke hannunta faduwa kasa cikin tsoro takallesa yayinda shikuwa yake takawa izuwa inda take cikin bacin rai yace da ubanwa kike waya?

Nace dawa kike waya? Cikin daga murya yake maganar

Mikewa take kokarin yi amma rawarda kafafunta suke yasa takasa mikewar dik kokarinda take dole tahakura tazuana tareda takurewa guri daya

Wayar yaduka yadauka saida yacirata sama yamakota kasa tayi dai daya

Ae HaYaT batasan lokacinda tamike bq tana zaro ido ta kalli wayarta ta kalli ALI din kafin tafashe da kuka tace wayata kafasa meyasa zaka fasa mun waya?

Danko gashin kanta yayi yana huci yana fadin koke din nan saina fasa balle wayarkin banza !

Azaba taji akanta batasan lokacinda tabude baki tashiga kiran sunan Aunty Sajidah Aunty Sajidah wayyo Allah kaina zai rabe gida biyu...

Sajidah da daman take saukowa taji muryan HaYaT na ihu tana kiran sunanta da alama kuka take aeda sauri tanufi dakinta

Ganin ALI yamirde mata gashin kanta ne yana fadin tagaya masa dawa take waya gashi HaYaT da alama tanajin azaba yasa takara shiga tashin hankali takarasa inda suke tasa hannu tana kokarin janye hannun ALI daga kan HaYaT shikuwa idanunsa sun rufe baya ganin komai agabansa yasa hannunsa daya dik karfinsa yawurgarda Sajidah gefe

Wani irin azaba ne yaziyarceta lokacinda tayi karo da bango ihu tasaka tana fadin wayyo Allah cikina tazube kasa tana dafe cikinta tana murkususu

Sai alokacin ALI yafarga da abunda ya aikata sakin HaYaT yayi yakoma kan Sajidah da jini yake fitowa ta kasanta kamar an yanka karamar dabba....








_Insha Allah gobe zaku jini_

*+22792838015 wtsp*



✍🏻
[8/1, 7:01 AM] Hayat: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*AyNuL HaYaTπŸ‘„*
_MATAR ALI GADANGA_


πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWa✍🏻*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*

*NeEnA_CoOlπŸ‘©πŸ»β€πŸ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*


*_______________________*
*πŸ‡³πŸ‡ͺNiGeR Ma FiErTΓ©πŸ€™πŸ»*


*Ψ§Ω„Ω„Ω‡Ω… Ψ₯Ω†ΩŠ Ψ£Ψ³Ψ£Ω„Ωƒ Ψ­Ψ¨Ωƒ وحب ΩƒΩ„ Ω…Ω† ΩŠΨ­Ψ¨ΩƒΨŒ وحب Ω†Ψ¨ΩŠΩƒ Ω…Ψ­Ω…Ψ― Ψ΅Ω„Ω‰ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΩˆΨ³Ω„Ω….*
*وحب ΩƒΩ„ ΨΉΩ…Ω„ ΩŠΩ‚Ψ±Ψ¨Ω†ΩŠ Ψ₯Ω„Ω‰ Ψ­Ψ¨Ωƒ يارب Ψ§Ω„ΨΉΨ§Ω„Ω…ΩŠΩ†πŸ‘πŸ»*


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI✍🏻_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷



*_SIS_* JIDDAH _*INA YINKI ARADUN ALLAH😍*_






1⃣5⃣





_naji korafinku my fans akan nadingayin page biyu arana nace ko dayan aya muka kwashe daku balle biyuπŸ˜ƒ_❓





Inalillahi wa ina illaihi raji'un yake nanatawa tareda kiran sunanta

Sajidah cikinta taketa nuna masa ALI yarikice yarasa mezaiyi gabadaya kwanyarsa ta toshe yarude

Ahankali Sajidah tafara lumshe idanunta har suka rufe ruf

HaYaT datake kallonsu cikin tashin hankali tace Ya ALI mukaita asibiti mana jini yana zuba kar wani abu yasameta cikin kuka takarashe maganar

Sai alokacin ALI tunanin zuwa asibiti yazo kanshi da sauri ya cicibeta yayo waje da ita yasata bayan mota HaYaT tashiga itama bayan tareda d'aura kan Sajidah akan kafafunta tana kuka jininda yabata jikin Sajidah dik yafi daga mata hankali..

Suna isa asibitinsa akayo kansu aka shiga da ita dan bata taimakon gaggawa
da kokarin farfado da ita daga sumanda tayi

HaYaT takasa zaune takasa tsaye gashi ba kowa tarasa yanda zatayi batada waya balle takira Salimat tafada mata halinda Sajidah take ciki, ALI yana can ciki dashi ake kokarin ceto ran matarsa

Sunyi kokari da yardar Allah ta farfado saidai tarasa dan karamin cikinta na wata biyu kacal aduniya wanda ko ALI din baisan dashi ba sai yanzu da abun nan yafaru ALI harda hawayensa yana mai bakin cikin abunda ya akaitama kansa da kansa yayi sanadiyar rasa dan cikinsa wanda yayi shekara da shekaru yana nema Allah bai bashi ba sai wanan karon gashi kuma gangancinsa ne yajanyo yarasashi kuka yake da idanunsa na bakin ciki gabadaya abokanan aikinsa sun tausaya masa matuka da rasa cikin nan saboda dik wanda yake tareda ALI yasan iya tsawon lokacinda yadauka yana neman haihuwa dason yaransa bai samu ba gashi kuma abun baiyi nisa ba yarasa

Wani Dr da ake kira Dr Zain ne yashiga bashi hakuri da tunatar dashi sakamakon mai tawakalli da hakuri gun ubangiji dik abunda karasa shine mai bayarwa kuma insha Allah zai sake baka wani ALI kadinga maimaita Allahuma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha yafi wanan kukan da kake ALI

Zama yayi akan kujera dake kusa dashi yakalli Dr Zain yace

Dr nine sanadiyar zubewar cikin nan taya bazanyi kuka ba?

Cikin mamaki Dr din yace tayaya hakan tafaru? Azatona ko faduwa tayi har hakan tafaru da ita!

Girgiza kansa yayi cikin bakin ciki yace nine sanadi dazu....


Nan yakwashe komai yagaya masa shi kansa Dr din yagirgiza dajin labarin saidai ALI bai gayamasa cewa HaYaT matarsa bace

Shawara dai Dr din yabashi yanuna masa cewa kaddara ce bata wuce kan kowa...


Ankaita dakin hutu saidai bacci take har wanan lokacin HaYaT da ALI ne adakin amma ba wanda yama wani magana tunda suka fito daga gida , HaYaT tadaurama kanta laifin dik abunda yafaru da Sajidah da bataje gidansu Safiyah ba da dik wanan bai faru da Aunty Sajidah ba haka take fada azuciyarta har alokacin kuma hawaye ne sharkaf afuskarta kuka take harda shasheka

Kukanta ne yadami ALI cikin bacin rai yadago yace

Kima mutane shiru munafuka kawai kukan uban me kike bayan dik kece silar faruwar komai?

Kafin tayi magana saiga Ammiey Salimat da mahaifiyar Sajidah sun shigo tare, dan aharabar asibitin suka hadu

Yana ganinsu yamike yanufi Ammiey kamar wani karamin yaro haka yafada jikinta tareda saka kuka

Mahaifiyar Sajidah nufar 'yarta tayi tana dubata

Itakuma Ammiey rarashin danta tashigayi tana tambayarsa meya faru da Sajidahr?

Saida yanutsu tukuna yace Ammiey barin ciki tayi na wata biyu

Ammiey da mahaifiyar Sajidah suka fara salati suna sallallami

Basu Ammiey ba hatta Salimat da HaYaT sun kadu dajin abunda yafaru

HaYaT takara shiga cikin damuwa dan gabadaya gani take laifin nata ne, aekuwa Salimat takama ma HaYaT sai kuka suke kamar anyi mutuwa

Ita kanta Ammiey saida tazubarda kwalla ganin irin shekarunda ALI yadauka da aure ba haihuwa gashi yanzu yaga samu kuma yaga rashi abun dai ba dadi...


Janyo hannun Salimat HaYaT tayi suka fito waje waje suka samu waje suka zauna suna sharar wahaye Salimat take fadin

Sis HaYaT kinsan shekarunda Ya ALI yadauka yanason haihuwa kuwa? Banga laifinsa ba dan yayi kuka!
Bakiga Ammiey harda hawayenta ba?

Hannu biyu tasa ta toshe bakinta tana danne wani irin kuka mai karfi dayakeson kubuce mata kasa hadiye kukan tayi tafada jikin Salimat tana fadin dik laifina ne Sis Salimat nice sanadiyar komai nice sila Aunty Sajidah bata cancanci irin wanan sakayyar daga gareni ba...

Kece? meya faru kike d'aura alhakin akanki HaYaT ?

HaYaT takwashe abunda yafaru tagayama Salimat, Salimat najin hakan tace ae laifin bana kowa bane nata ne saboda ita ta gayyaci HaYaT da batace tazo ba aeda dik wanan bai faru ba....


Har karfe uku Sajidah bata farka ba, alokacin mahaifinta da mahaifin ALI Daddy sunzo dubata harsun koma

Yayar Khadija ce tazo daga baya, itama saida tazubarda kwalla jin abunda yafaru ta taya dan uwanta bakin ciki...



Bayan sallahar la'asar Sajidah tafarka alokacin daga HaYaT sai Salimat ne adakin Ammiey takoma gida Khadijama haka Mahaifiyar Sajidah ce tafita waje tabarsu HaYaT da zumar idan Sajidah tafarka su sanar da ita

Salimat ce tafara farga Sajidah ta tashi da sauri tanufi inda take

Ita kuwa HaYaT tafito waje ta sanarda mahaifaiyar Sajidah daga nan tashiga neman inda ofis din ALI yake danta sanar dashi farkawar Sajidah

Wata nurse tagani ta tambayeta nan tanuna mata

Tana nufar ofis din bugun zuciyarta nakaruwa

Ahankali tashiga buga kofar tajima tana bugawa kafin taji muryarsa cikin yanayin damuwa yace waye shigo

Cikin tsoro da sanyin jiki tabude kofar tareda shiga saidai batayi gangancin rufe kofar ba dan abakin kofarma tatsaya cikin rawar murya tace

Daman Aunty Sajidah ce tafarka daga baccinda take ko zakazo kadubata?

Lokacinda tashigo kansa da jikinsa ya kwanta akujera idanunsa jajur yazuba mata ido koda yaga itace baisa yamotsa daga yanda yake ba

Jin abunda tafada ne yasashi motsa bakinsa ahankali yace shigo zo nan!

Rike kofar tayi gam taki motsawa daga inda take sai kallon kallo suke tsakaninsu kowane idanunsa jajur

Ganin batada niyar yin abunda yace ne yasa yamike tsaye yanufi inda take

Kamar wacce aka dasa dikda tsoron yanayinsa baisa tamotsa daga inda take ba harya karaso daf da ita

Hannu biyu yasa yafisgota daga inda take yayi wurgi da ita tsakar ofis din yarufe kofar garam kakeji da karfi yajuyo gareta

HaYaT da saida tayi da gaske kafin ta iya tsayawa da kafafunta tukuna ido waje take kallonsa bakinta yamata nauyi so take tayi magana amma takasa

Habarta yasa hannunsa na dama yadago yana kallonta ido cikin ido itama kallonsa take da idanunta da tuni suka fara shararar hawaye ba kakautawa

Cikin dasashiyar murya yafara magana

Kece silar komai HaYaT! Kin saka da hannuna na bararda jinina wanda nayi shekara da shekaru ina nemansa ido arufe dik laifinki ne da kinzo lokacinda kika saba zuwa da dik hakan bata faru dani ba!

Kin zamar mun annoba kaka nikayi

Cikin kuka HaYaT tace kayi hakuri Ya ALI

Nayi hakuri?

Daga kanta tayi alamar eh

Sakin habarta yayi yajanyota jikinsa yamatseta da karfi saida tasaki kara kafin ya sassauta matsarda yamata yadan duko fuskarsa daidai da tata fuskar har suna jiyo bugun zuciyoyin junansu yana kallonta cikin ido yace

Bazan taba hakura da irin asararda kika janyo nayima kaina ba! Zaki biyani da dikkanin jikinki da lumfashinki wallahi wallahi saikin biya wanan da zufarki HaYaT !

Cikin rawar murya tace taya zan iya biyanka?

Ana siyarda ciki akasuwa ne ko kuma ana siyarda jarirai akasuwa ne?

Koda ana siyarwa ni banida kudinda zan siyama kodaya daga cikinsu! Takarashe maganar tana sauke idanunta kasa ita har cikin ranta tayi maganar batayi da gangan ba

Wani irin murmushin takaici yayi na gefen kumatu yace koma menene zaki sani ne nan gaba yar renin hankali!

Yana gama fadin haka yasa hannu biyu yatureta daga jikinsa tayi baya tafadi kasa dabas kara tasaka dan taji zafin faduwar sosai

Shikam bai damu ba fita yayi abunsa yanufi dakinda aka kwantarda Sajidah

Mahaifiyar Sajidah sai faman rarashin Sajidah take akan tayi hakuri da kaddara insha Allah zata samu wani cikin nan bada jimawa bΓ’

Itakam Sajidah ko sauraren Mamanta batayi kukanta kawai take Salimat na tayata

Shigowarsa ne yasa dikansu fita suka barsu

Karasa shigowa yayi ciki yajanyo kujera yazauna kusada da ita

Itakam ganinsa ne yasa takara volume din kukanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login