Showing 1 words to 3000 words out of 54100 words

Chapter 1 - AYNUL HAYAT COMPLETE HAUSA NOVEL

12 Dec 2024

8203

ο»ΏCopied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301






[8/1, 6:58 AM] Hayat: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*AyNuL HaYaTπŸ‘„*
_MATAR ALI GADANGA_
*-_-_-_-_-_-*

πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž





*_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da KuMa RuBuTaWa✍🏻*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπŸ‘©πŸ»β€πŸ¦±*
*_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*

*_____________________*
*NiGeR Ma FiErTΓ©πŸ€™πŸ»*
πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
πŸ‡³πŸ‡ͺ
*_________________________________*
*Ψ§Ω„Ω„Ω‡Ω… Ψ₯Ω†ΩŠ Ψ£Ψ³Ψ£Ω„Ωƒ Ψ­Ψ¨Ωƒ وحب ΩƒΩ„ Ω…Ω† ΩŠΨ­Ψ¨ΩƒΨŒ وحب Ω†Ψ¨ΩŠΩƒ Ω…Ψ­Ω…Ψ― Ψ΅Ω„Ω‰ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΩˆΨ³Ω„Ω…. وحب ΩƒΩ„ ΨΉΩ…Ω„ ΩŠΩ‚Ψ±Ψ¨Ω†ΩŠ Ψ₯Ω„Ω‰ Ψ­Ψ¨Ωƒ يا Ψ±Ψ¨ Ψ§Ω„ΨΉΨ§Ω„Ω…ΩŠΩ†πŸ‘πŸ»*
*_________________________________*

*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*✍🏻
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*




*_AYNUL HAYAT_* yazo muku daga maruciyar
πŸ‘‡πŸ»

_*DEEJA*_
*-_-_-_-_-_*
_*KISHIYAR AMNOOR*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
_*WASU MAZAN*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
_*NIEMATULLAH*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*_MAI KYAU_*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*



3⃣





Da hannu ya yafito ta haka tabishi kamar makaho da majayinsa.

Bude dakin yayi suka shiga sai alokacin yajuyo yakalleta fuskarsa ba annuri

Zaro ido tayi tareda komawa cikeda mamaki da razana tace OUSTAZ! Kaine?

Nine mena mamaki haka?

Kasa motsawa tayi daga inda take tsananin mamaki da tunani shine mijinta wanda mahaifinta yace ya aurarda ita gareshi ko kuwa dai gizo yake mata?

Muryarsa ce tadawo da ita daga dogon tunaninda talula

Nasan mamaki kike ko nine mijinki?

Eh nine!

Nine wanda na aureki yau din nan bada jimawa ba, mahaifinki yace sadakarki zai bani nikuma nace a'a ya yanka mun sadaki nabiya daga CFA million daya zuwa sama ko nawa ne zan biya!

Dayake tsohon daga ganinsa mai idon cin naira ne haka ya yake mun million daya zan bada nabadasu lakadan nabiya ko kwandala baya biyata!

Saidai abunda bai sani ba shine ni siyanki nayi ba aure ba!

Dan haka tun wuri kisani karki dauka matsayin matar aure zaki shigo gidana inada mata wacce nakeso fiyeda rayuwata dan haka siyanki nayi da kudina.

Dan haka kisani amatsayin yar aiki mai aikin gidana zakije ba amatsayin matar aurena ba bawai zaki shigo a *MATAR ALI GADANGA* ba!

Kina fahimtar zancena kuwa?

Durkusawa tayi kasa tasaka wani irin kuka mai tsuma zuciya tana fadin meyasa mahaifina zan mun haka?

Meyasa yazabi rabuwa dani a wanan kananun shekaruna haka?

Anya kuwa ni yarsa ce?

OUSTAZ ALI GADANGA meyasa zaka shigo rayuwata me nayima arayu ne daka zabi kacutar dani ta wanan hanyar?

Kasani nasani badan so ko kauna ka aureni ba saidan ka kuntatama rayuwata shin kodai nayima wani abun ne wanda bansani ba kake kokarin daukar fansa akaina?
Tun a makaranta katsaneni bakason ganina saboda me? Dik wanan bai isheka ba saika shigo rayuwata?

Nikam a iya sanina ban taba cutarda kowa arayuwata ba!

Meyasa

Meyasa

Meyasa...

Kuka take sosai kamar ranta zai fita

Ali maimaikon yaji tausayinta saima haushi data bashi.

Tabe bakinsa yayi yadaga kafada irin alamar ko ajikina din nan!

Kome zakice kice AyNuL HaYaT nidai aganina taimakonki nayi bawai kuntata miki ba kamar yanda kike tunani!

Karya ne tafada da daga murya karya ne Ali!

Kanaso kataimakeni ne baka bari wanda yasan kimar mace ya aureni ba?
Koda talaka ne gurgu makaho ko kuturu kabari aka badani sadaka dashi yafiye mun kai din nan azzalumi marar tunani wanda yake zalluntata batareda nadau hakkinka ba!

Bata gama rufe bakinta taji yakai mata wawan mari wanda yafirgitarda ita ainun, dafe kuncenta tayi tana kuka batasake cewa dashi komai ba.

Fita yayi yabarta tareda kulle kofar dakin tawaje yayi tafiyarsa

Tajima tana kuka tanajin wani zazzabi nason rufeta dakyer ta lallaba nan kasa tana rawar sanyi kan kace me ciyon cikinta ne yatashi gabadaya jitake mutuwa kawai zatayi tahuta da wanan azabar, kusan awa hudu tadauka awajen ko motsin kirki takasayi dikta fita hayyacinta

Yana zuwa yabude kofar yaganta kwance kamar bata motsi da sauri yanufi inda take hannunsa yakai gun hancinta yaji tana numfashi a 360 yadauketa yakaita kan gado ya ajiyeta tareda janyo bargo yarufeta da sauri yasauka yafita cikin minti goma shabiyar yadawo da kayan aiki na taimakon gaggawa nan yamata allura kafin yasaka mata karin ruwa.

Ba jimawa bacci yadauketa nan yazauna yana kare mata kallo yanda yasanta abaya yau saiyaga gabadaya tacanza tarame sosai tayi duhu kuma ba kaman da ba.

Dan tausayinta ne yaji yana shigarsa itace bata tashi ba sai ana kiran sallahr magrib ahankali tamotsa tana bude idanunta ahankali tasaukesu akanshi dayake zaune kan wata kujera datake tsakar dakin kallonsa gabadaya yana kanta

Wani irin murdawa taji cikinta yayi batasan lokacinda tasaki wata karaba tareda dafe cikin
Dasauri yamike yanufi inda take wata irin cakuma takai mishi ta kankameshi tahanashi motsawa
Cikin muryar kuka tace dan Allah kataimakeni cikina zan mutu kataimakeni Ali

Cikin daga murya yace sakeni mana meye haka?

Ba ta sakesa takoma ta kwanta tareda kankame cikinta tashiga juyi akan gado tana wani nishin azaba

Tashi yayi yakoma gefe yayi kira ba jimawa wanda sukazo dazu yashigo ba bata lokaci yashiga dubata tareda mata tambayoyi tana bashi ansa dakyer nan yagano asalin ciyonta yama Ali bayani tareda rubuta masa maganinda yakamata tasha.

Tare suka fita yaje pharmacie yasiyo yabiya super market yasiyo mata audugar mata dawasu kanan siyayya.

Dayazo yabata tareda titseta tasha bayan yabata madara tasha ana kiran sallahr isha lokacin ciyon yalafa tarufe idanunta saidai ba bacci take ba shima kansa yalurada hakan.

Ni zan tafi yace mata saida safe karki yarda kifito yanzu zan saka aka miki abinci haka nasafe bazaki ganni ba sai yamma koda wasa karki kuskura kifita daga kofar nan kinajina ko?

Sharesa tayi bata ansa ba
Nasan sarai idonki biyu kuma kinji dik abunda nace dan haka ki kiyaye!

Yana gama fadin haka yafita.

Saida yajuya tabishi da kallo da tunani kala kala fal zuciyarta

Ba jimawa kuwa aka zomata da abinci mairai da lafiya da lemoka kusan kala uku dakyer ta tashi taci kadan jus din ne dai tasha mai yar dama daman ita can tafi bukatar abu mai sanyi ba gwanar cin abinci bace mai yawa dan bata samu shiyasa tasaba. jin al'adarta tazo yasata tashi taje ta tsaftace jikinta tagama tafito ta kwanta tunanin sabuwar rayuwarda tafada take tana ayana aranta koya zata kasance tsakaninta da Ali nan gaba?


-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-

Faridah ina abincina?

Cikin shagwaba tana dafe da kanta tace Baby ban girka ba tunda safe kaina yake mun ciyo nakasa aikin komai kai kuma gashi kaki kanemo mun yar aiki balle nuhuta, kasan banason aikin wahala!

Tasake wani marairaicewa tacigabada da fadin dan Allah Baby yaushe zaka nemo ne?

Cikin kulawa da kaunarta yace karki damu ae nace miki cikin satin nan zanka miki ba?

Dikda yasan ciyon karya take hakan baisa yaji haushinta ba!

Oya yanzu shirya muje restaurant muci abinci dan yunwa nakeji sosai!

Ayya Baby yau bazakaje gidansu Ammie cin abinci bane?

Yatsina fuska yayi kafin yace

Bazanje ba yau, shawa'ar cin abinci nake da gimbiyata yau yakarashe maganar yana kashe mata ido daya.

Hmm kawai tace dan tasan karshen zancen dik lokacinda Ali yamata wanan signe din tasan da akwai abunda yakeso daga gareta ita kuma acewarta batason damuwa da takura!

Dan haka har sukaje suka dawo bata sakar masa fuska ba shikuwa sai zuba mata hira yake yana janta da zance banda eh a'a umm ba abinda take ansa masa dashi.

Dasuka shigo kowa yayi dakinsa sanin ko zasu shekara bai nemeta ba damuwa zatayi ba yasa dakanshi yanufi dakinta bayan yayi shirin bacci tana ganinsa tayi kamar bacci take!

Kashe wutar dakin yayi ya Haye gadon tareda janyota kamar jira take tafara masifa

Nikam Ali kacika jarrabar siya wlh! Kai kullum abu daya saikace ruwan sha? Wlh bazan iya ba gwarama tun wuri kadawo hayyacinka!

Banda daukar alhakima irin naka harfa nafara baccina katasheni kasan dai idan ban yafe maka ba Allah zai tambayeka!

Shiru yayi saida tagama zubarda take tukuna yanisa yace kin gama?

Yasake sasauta muryarsa kasa kasa kamar mai rokon gafara yana rarashinta akan tahakura tabashi hakkinsa.

Ita kuwa tanuna sam bai isaba!

Dayaga abun nata renin hankali ne yasa yakamata ta karfi yabiya bukatarsa son ransa da ita tukuna yatashi yabarta nan dikda bawani jin dadinta yake ba, haka yake maneji da ita dan baya ganin wata mace agabansa banda ita.

Zaginsa take iya karfinta tana barinshi da AllahπŸ˜†

Ali da matarsa Kenan Faridah!

Haka suke kullum Ali yana tsananin kaunarta shiyasa dik iskancinda take masa da take hakkinsa baya iya daukar wani matakin azo agani akanta!
Daga karshema ita zata masa laifi shikuma yazo yana bata hakuri dan baison ganin bacin ranta ko kadan!

Abunda Ali bai saniba shine Faridah tagama asirceshi tun ranarda tadaura ido akanshi tun kafin aurensu.
Dika dika haduwarsu da aurensu bai dauki dogon lokaci ba dan ji yayi inba ita bazai iya rayuwa ba, Faridah tsohuwar mace ce sosai dan zata kai shekaru 28 shikuwa Ali ayanzu yanada shekara 29 ne.

Faridah kallo daya zaka mata kagane irin matan nan ne yan barike saboda yanda zaka gano yanayin fatar jikinta ba farin asali ne da itaba dik wanda yasani daga yakalleta zai gano tana shafe shafe saboda fuskarta ne kawai keda haske sosai jikintama ba laifi amma fuskar tafi daukar mai a inda kuwa yan yatsunta sunyi baki sosai atakaice dai banda shi Ali din ba wanda zai ganta yace tadace da Ali dan kowa mamakin yanda akayi Ali ya aureta yake dikda kyau gayu da daukar kai irin nashi!

Faridah gajera ce wacce gajarcin haryaso mata illa dan idan suna tafiya da Ali zaka ganta wata yar tsurut can kasa dashi tanada jiki ba sosai ba saidai tafi auki Samanta saboda irin matan nan ne wanda na fulaninsu yarinjayi mazaunansu.

Ahaka kuma Faridah bata ganin kamarta, sam itada familles din Ali basa shiri musaman kaninsa mata, Muttalib ne dai inya shekara ba ruwansa da ita danko kallo bata isheshi, ita Ammie tasan yaronta ba ahayyacinsa yake ba saidai Daddy yace mata tadauke idanunta ga lamarin surukarta kawai tabi shi Ali din da adu'a inma da wani abu akasa dole watarana gaskia zatai halinta!

Shiyasa ko haduwa akayi biki Ammie bata nuna mata tsana mutunci ne sosai atsakaninsu harda Daddy dinma.

Yau shekarar Ali da Faridah uku kenan da aure amma ko batan wata bata taba yiba, ita kadai tasan bazata iya taba haihuwa ba saboda tun tana yar shekara shabiyar take yawon tazubar tasha zubarda ciki harba adadi daga karshe tasamu babbar matsala da mahaifarta wanda likitanta ya shaida mata cewa itada haihuwa saidai tagani anayi amma ba ita ba!

Shiyasa tashirya ta kewaye Ali da sihiri wanda baya taba ganin kyan wata y'a mace bayanta!
Itace kadai zai kalla amatsayin macenda zai iya kasnacewa da ita har abada!

Washe gari oganiyar tafito ta gansa kitchin yana hada karin kumalo ko uffun bata ce dashi ba ita ala dole yamata ba daidai ba jiya!

Shima din shareta yayi bayan yagama abunda yakeso yaci yadauki jakarsa yanufi asibitinsa shi yakaranci tiyata ne tanan yafi kauri!
Aiki biyu yake hadawa yatsara komai yanda yakeso randa bayada majinyaci wanda zaima aiki to yana scul yana bada karatu!

Ammie da Daddy sunyi sunyi yabar koyarwa yaki yace yana sha'awar abun ne kawai abarshi!

Aranar yanada aikin tiyata har biyu bashi yasamu kansa ba sai kusan sallahr azhur hankalinsa gabadaya yanakan AyNuL HaYaT koya take da jikinta?
Sai alokacin yakejin bai mata adalci ba barinta da yayi ita kadai takwana bayan batada lafiya!

Saida yahuta sosai bayan yagama sallah yanufi hΓ΄tel din, yanda yaganta taji sauki saiyaji dadi aransa amma sam bai nuna damuwarsa akanta azahiri ba sai wani daure fuska yake mata, abinci ne yalurada yanda aka ka na safe haka yake haryanzu dana rana ba wanda ta taba!

Ba bata lokaci yakira aka kawo wani sabon abinci

Yace taci tace takoshi!

Dole yasata taci badan taso ba dan harda kukanta takoshima yace saita cinyesa tsaf kafin yabarta dan keta, tanaci tana yunkurin yin amai ahaka harta cinye abincinda in tana gida saitayi kwana uku bataci kamarsa ba, tana gamawa taji cikinta gabadaya ya hade mata kuka tasaka na gaske tana rike cikinta

Shikuwa sakata yayi agaba yana kallo dan haushi take bashi gani yake dik abunda take da gangan take kawai tsabar iskanci ne!

Har tsawa yadaka mata atunaninsa zatayi shiru taji tsoronsa maimaikon hakanma saikara sautin kukanta tayi batako bi takanshiπŸ˜†

Daya gaji tashi yayi yafita yabar mata dakin gabadaya!

Yau sati daya Kenan tana rayuwa cikin hΓ΄tel adaki ita kadai tun tana tsoro harta dena abinci ne dai bata rashinsa cikin kankanin lokaci tadanyi kiba tasake saidai da damuwa sosai azuciyarta!

Koda yashigo tana sallah dayake wajen karfe takwas ne yayi mamakin da yanzu take sallah, saida tagama yake cewa

Sallahrma bazakiyita akan lokaci ba?

Itadai batace dashi Komai ba saida tagama adu'ointa ta tashi tareda gaidashi bai ansa ba saima cewa da yayi

Kishirya yau zan kaiki gidana amma ba tsayin *MATAR ALI* ba matsayin yar aikin gidan ALI zakije!

Da fatan kin gane?

Ahankali ta gyada masa kanta alamar eh.

Nan yashiga jero mata sharudda yanda yaketa nanatawa takiyaye bacin ran matarsa dik abunda tace tayi karta kuskura tace bazatayi ba inba haka ba kuma jikinta ne zai gaya mata!

Yakuma gargadinta kome zai faru karta kuskura tafadi cewa ita din *MATAR ALI* ce koda wasa!

Cikin sanyin murya tace
Tunda haka kakeso haka kake ganin daidai ne nayima alkhairi komai daren dadewa komi runtsi kome zai faru bazan taba fadar cewar ni din *MATAR ALI ce ba!

Sanan kuma bazan sabawa matarka ba kamar yanda kabukata ba zaka sameni mai biyayya agareku nagode tafada daga karshe!

Tabe bakinsa yayi yace kin kyautama kanki idan kika kiyaye!

Zan tafi inada aikinyi da yamma zanzo nadaukeki nakaiki matsayin yar aiki...


_wacce irin AyNuL HaYaT zatayi agidan Ali? Yazata kasance da Faridah da matar Ali din?_



*WANAN SOMIN TABI KENAN, LITTAFIINDA ZAIZO MUKU AGORON SALLAH KENAN INSHA ALLAH DA YARDAR UBANGIJI!*
*KARKU BARI ABAKU LABARI.*
[8/1, 6:58 AM] Hayat: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

*AyNuL HaYaTπŸ‘„*
_MATAR ALI GADANGA_

πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž





*_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da KuMa RuBuTaWa✍🏻*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπŸ‘©πŸ»β€πŸ¦±*
*_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*

*_____________________*
*NiGeR Ma FiErTΓ©πŸ€™πŸ»*
πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
πŸ‡³πŸ‡ͺ
*_________________________________*
*Ψ§Ω„Ω„Ω‡Ω… Ψ₯Ω†ΩŠ Ψ£Ψ³Ψ£Ω„Ωƒ Ψ­Ψ¨Ωƒ وحب ΩƒΩ„ Ω…Ω† ΩŠΨ­Ψ¨ΩƒΨŒ وحب Ω†Ψ¨ΩŠΩƒ Ω…Ψ­Ω…Ψ― Ψ΅Ω„Ω‰ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΩˆΨ³Ω„Ω…. وحب ΩƒΩ„ ΨΉΩ…Ω„ ΩŠΩ‚Ψ±Ψ¨Ω†ΩŠ Ψ₯Ω„Ω‰ Ψ­Ψ¨Ωƒ يا Ψ±Ψ¨ Ψ§Ω„ΨΉΨ§Ω„Ω…ΩŠΩ†πŸ‘πŸ»*
*_________________________________*

*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*✍🏻
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*


_Masoya da abokan arziki yauma ni din ce nasake zo muku dawani sabon labari domin nishadantar daku dakuma fadar daku karki yarda karka yarda abaka labari wanan daban yake dana baya._
_Ina rokon Allah yanda nafara lafiya Allah yasa nagama lafiya haka Amin_


*_AYNUL HAYAT_* yazo muku daga maruciyar
πŸ‘‡πŸ»

_*DEEJA*_
*-_-_-_-_-_*
_*KISHIYAR AMNOOR*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
_*WASU MAZAN*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
_*NIEMATULLAH*_
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*_MAI KYAU_*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*



1⃣




Sauri take kamar ta tashi sama yaukam ta tabbatar ba abunda zai hana OUZTAZ ALI GADANGA yadaketa saboda lattinda tayi gashi Allah yazuba mata wani shegen tsoronsa wanda ko muryarsa taji saita firgita gashi kuma dason dizga mutum agaban ko waye ba ruwansa sam OUSTAZ ALI GADANGA baya karbar uzuri haka kina laifi komi kankantarshi saiyaci ubanki musaman ace kin makara koda da minti daya ne tofa kashinki yabushe awajensa!

Wani lokacin idan yatashi tsiyarsa hanaki shiga yake classe muddin yariga yasaka kafarsa a classe koda kina bayansa bazai bari kishiga ba shikenan kuma leΓ§on dinsa yawuceki.

Agogon hannunta takalla ganin karfe takwas harda minti biyar yasa batasan lokacinda hawaye suka zubo mata ba tareda kara saurinda take kamar me

Tana isowa bakin ajin taji kamar suna surutu da alama yau OUSTAZ ALI GADANGA baishigo da wuri ba nanda nan tasauke wata irin ajiyar zuciya tareda hamdallah har zata saka kafarta daya acikin classe din taji an daka mata tsawa abayanta tsawarda takusa sakata sakin futsari awando ko bata juyoba tasan shine cikin rawar jiki takomo baya batareda tahada ido dashi ba tana fadin kayi hakuri OUSTAZ bansan kana bayana ba!

Wani dogon tsaki yaja tareda fadin wanan kazamin jikin naki da bakar fuskarki karki kuskura kiyarda kihada ido dani maza koma baya!
Sainaga ubanda yasa kiyi latti haka ga yan uwanki can tun kafin ashiga aji zaka gansu amma ke kullum latti kike bakauya kawai!

Cikin kuka da shasheka tafara fadin OUSTAZ ba laifina bane kuma..

Yimun shiru yafada tareda shigewa aji yabarta nan tsaye tana kuka tareda yimata gargadin karta kuskura tashigo muddin yana nan yau ya haramta mata shiga classe din!


Inda sabo yaci ace HaYaT tasaba da irin wanan tsangwamar gida da waje haka take rayuwa kullum cikin kyara da hantara take agida bata tsira ba hakama scul OUZTAZ ALI GADANGA yasakata agaba dik ranarda akace sunada leΓ§on dashi take shiga cikin halin damuwa harsai ranar tawuce sam yatsani yaganta kamar agidansu mahaifintama baya sonta balle wasu can yan uwanta na jini!

Dikansu abu daya suke cemata kazama yar baka mai bakar fuska saikace ita ta hallici kanta!

Haka tazauna can nesa da classe dinsu taciro wani littafi tana karatu wanda na malaminda zai shigar musu ne
Awa daya nayi tasamu tashiga classe din, kamar kullum kaf ajin bamai kokarin kawo karatu da saurin fahimta irinta banda OUZTAZ ALI mai koyardasu harshen larabci dik sauran malaman suna sonta saboda gwazonta da jajircewa akan karatu, wanan ne yajanyo mata bakin jini gun yan ajin gabadaya bawanda yake shiri da ita ba kamar yar uwarta tajini Amal tafi kowa nuna tsanarta akan AyNuL HaYaT agida ne ko amakaranta.

Suna fitowa cin abinci ita daman ba kudi ake bata ba shiyasama bata wahalarda kanta wajen fita zamanta take tayi karatunta sai lokacin yakare sucigaba da karatun har atashi gabadaya.

Yauma kamar kullum tanaji tana gani su Amal dreba yazo yadaukesu yabarta nan tsaye abun duniya dik yabi ya isheta duba nisan gidansu take kuma ahaka zata taka taje da kafa.

Tafiya take tana tunani aranta cewar da mahaifiyarta na raye ta tabbatar bazata fuskanci matsin rayuwa irin wanan ba!

Waima meye laifinta anan dan tana baka? Aeba ita ta hallici kanta ba!

Haka dai tayita sake sake aranta harta isa gidan alokacin ana kiraye kirayen sallahr la'asar awa biyu yake daukarta kafin ta iso gida.

Tana zuwa tafada dakinta tacire kayanta tashiga tawatso ruwa tafito tasaka kayan zaman gida taso ta kwanta tahuta bayan tagama sallah nan fa cikinta yace bata isa ba!
Tunawa tayi rabonta da abinci tun dan guntun karinda tayi tun safe
Tashi tayi tafita ta tarda Inna lariya tana kokarin dora girkin dare cikin ladabi ta gaisheda ita tareda tambayar ina abincinta?

Inna lariya saida taduduba ko ina taga ba kowa tukuna taje tadauko mata abinci da kullum take diba tana boyema HaYaT saboda agidan sam batada rabon abinci saidai ko in anraga tagani tadauka taci.

Shiyasa Inna lariya tafito da dabarar diba tana ajiye mata inta dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login