Showing 9001 words to 12000 words out of 54100 words
yake amma sam hankalinsa baya jikinsa tunani yake wacce kalar wainar zasu toya idan yatunkari Faridah da wanan maganar sarai yasan irin tashin hankalinda suke shiga idan irin wanan ta taso ko alokacin baya
Harya isa gidan yafito yashiga falon bai dena tunani ba, saidai abunda yashiga yatarar shiya kusa zautar dashi cikin mamaki yake bin falon da kallo dik falon an fasa komai ba abunda zai amfanu nan gaba
Kallonsa yakai sama yadubi hanyar dakin Faridah aransa yake fadin ya tabbatar itace da wanan danyan aiki ba wani ba!
Tuna HaYaT da yayi ne yasa yakalli kofar dakinta ahankali yaje gurin yana buga kofar yana kiran sunanta cikin rada kamar mai tsoron wani yaji kiranda yake mata
Daman idonta biyu abunda Faridah tayi agaban idanunta shiya hana bacci daukarta dan gani take kamar tahaukace ne karta kwanta tayi bacci ta iskota ta shaketaπ
Kamar rada taji ana kiran sunanta da buga kofar ahankali cikin tsoro tamike tsaye tana kallon kofar kamar ace ar tazuba aguje
Saida ta ajiye hankalinta dakyau tukuna tagano muryar ALI yake kiranta
Ajiyar zuciya tayi danko ba komai idan Faridah takai mata cabka akwai ALI zai shiga tsakaninsu ne, tsoronta daya ranarda Faridah zata gano wacece ita agidan nan kalamanta ne suka shiga dawo mata akunne akan wacce tayi kuskuren shigowa gidanta da sunan MATAR ALI...
Tuna hakan datayi ne yasa tasaki wani marayan kuka tareda nufar kofar tabude ahankali
Baya yaja tafito tamaida kofar tarufe
Shikuwa kallonta yashigayi yaga tana kuka azatonsa Faridah ta hada da ita wajen haukar tata
Saidai yaga bako dan kwarzane ajikinta tukuna ya kalleta yace waya dakeki?
Girgiza kai tayi alamar ba kowa!
Faridah tamiki wani abun ne?
A'a! tafada cikin muryar kuka
Fada tamiki?
Nanma girgiza kai tayi alamar a'a!
Hade rai yayi yace haka kawai jin dadin kukan ne yasa kikeyi kome?
Kara fashewa tayi dawani sabon kuka
Ganin abun nata yazama renin hankali yasa yadaka mata tsawa yace waya fasa dik abubuwan nan ne?
Aunty Faridah ce tafada da sauri cikin hawaye!
Toh meyasa baki gyara komai kin kwashe ba
Maza kije ki gyara falon nan banson iskanci da sakarci irin naki!
Jiki ba kwari batareda tayi magana ba taje falon tafara tattare guntayen kwalaben tana kuka abunta cikeda shagwaba
Tsaye yayi yana kallonta
Dan tausayinta ne yakamashi, ganin bazata iya yin aikin ita kadai ba yasa yaje yafara tayata batace dashi komai ba suka fara aikin tare
Sun kusa gamawa ne cikin rashin sa'a HaYaT tadauki wata guntuwar kwallar jus zata saka amazubin shara ae kuwa kwallabar taratsa hannunta
Kuzo kuga ihunda tasaka tana yarfe hannunta dan tsoron ganin jini take kamar me ihu take harda tsalle irina yara
Zaro ido ALI yayi ganin abunda take tsoronsa daya karta taso masa Faridah kallonsa yakai sama yaga ba lamarta dan haka da sauri yarufema HaYaT baki tareda janta yakaita kitchin
Hannunsa yadaura akan lebensa yana kallonta yace shiiiiiitttπ€«
Bakida hankali ne akan dan wanan yankar zaki nemi tada mana masifa?
Itakam kokarin kwace bakinta take takasa, dawane zataji da rikon bakin ko kuma da radadin zafinda hannunta yake mata?
Hawaye saibin fuskarta suke can dabara tafado mata
Ba zato ba tsammani ALI yaji ta gantsara masa wani irin cizo mai zafi
Sosai ta ciji hannun nasa cikin takaici saida tadauki sakani kafin tasaki hannun tacigabada kukanta tana yarfe hannunta saidai wanan karon tabar tsallenda take afalo
Shikuwa ALI daya saketa yakoma ta hannunsa duba hannunsa yake dan sosai yaji zafin cizon har cikin ransa kuwa
Daga hannu yayi daniyar zuba mata wani wawan mari
Ita kuwa ganin zai mareta ne tsoro yasata sakin wata kara mai karfi wanda saida ALI din yarufe kunnensa ba shiri
Kallonta yake da mamaki yanda take wanan karar cikeda haushi ba abin yagwada sake marinta ba tasake saka wata karar
Itama kallonsa take ido cikin ido zufa da majina da hawaye dik sun wanke fuskarta shabe shabe
Ahankali take sulalewa rikeda hannun idanunta akan ALI tazauna kasa kafin tadena kallonsa takai hannunta daya tacire Hijab dinta tajefar dashi gefe danji tayi gabadaya yatakurama lumfashinta
Wata doguwar rigar atamfa take sanye da ita kanta ba dan kwali gashintama bata saka chouchou ba dan haka hijab dinda tacire ne yabawa gashin kanta damar barbazuwa ako ina kan kafadarta wani kuma yarufe mata fuska
HaYaT komai take cikin yarinta wanda ita batamasan tanayi ba ta hannunta kawai take
Kallonta ALI yake cikeda mamakinta
Ahankali yadurkusa wajenta tareda kamo hannunta
Kama hannunta dayayi ne
yayi daidai da lokacinda tabude baki iya karfinta zata saka kara wacce tafi ta dazu amo
A 360 ALI ba shiri yasaka hannunsa da sauri yarufe mata baki...
βπ»
[8/1, 6:58 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
*Ψ§ΩΩΩΩ
Ψ₯ΩΩ Ψ£Ψ³Ψ£ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨΨ¨ ΩΩ Ω
Ω ΩΨΨ¨ΩΨ ΩΨΨ¨ ΩΨ¨ΩΩ Ω
ΨΩ
Ψ― Ψ΅ΩΩ Ψ§ΩΩΩ ΨΉΩΩΩ ΩΨ³ΩΩ
.*
*ΩΨΨ¨ ΩΩ ΨΉΩ
Ω ΩΩΨ±Ψ¨ΩΩ Ψ₯ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨ§Ψ±Ψ¨ Ψ§ΩΨΉΨ§ΩΩ
ΩΩππ»*
π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·
7β£
...kinsan Allah wanan karon kika mun ihu akunne saina miki dan banzan duka agidan nan kuma ba Ubanda zai kwaceki ahanuna yafada yana zare mata ido ala dole saitaji tsoronsa
Shiru tayi kuwa, ahankali yasauke hannunsa daga bakinta yana fadi duba hannun zanyi nagyara miki, nutsuwa tayi tabari yaduba hannun dikda zafinda takeji
Gashinda yarufe mata fuskarta yagyara yana mamakin arzikin gashi irin nata, ganinta bakar fata bai taba zaton tanada gashi mai tsayi da laushi irin wanan ba, ahankali yaduba lallai taji ciyo sosai yafada aransa dikda HaYaT tacika raki sosai.
Tashi yayi yace mata tajirasa yana zuwa yanzun nan
Saida yaje sama yashiga dakinsa yadauko kayan aiki na taimakon gaggawa yazo dakyer tabari ya wanke mata ciyon yasaka mata magani tareda rufe ciyon da bandeji
Falo suka dawo zamanta tayi akan kujerar falon tana kallonsa shi yayi shara ya tattare komai falon yadawo hankalinsa tukuna yace ta tashi takoma dakinta ta kwanta
Kin tashi tayi bakinta sai motsi yake alamar tanaso tayi magana
Kallonta yasake yi yace dake fa nake!
Dan Allah dan Annabi dan Allah takarasa da kuka
Shikam kallonta kawai yake cikin mamaki da takaicinta
Ganin tayi shiru sai kukanta take yasa yajuya zaibar wajen da saurinta tamike tasha gabansa
Turus yayi yana kallonta kafin tace
ALI dan Allah nayarda na amince zan zauna agidan nan har iya karshen rayuwata! amma dan Allah kasauwake mun karabani da igiyoyin aurenka dasuke kaina
Aunty Faridah kasheni zatayi inhar tagano ni din matarka ce!
Ni ni nii nitsoronta nake tafada tareda ajiye kanta kasa hawaye nabin fuskarta
Ahankali yatako har zuwa daf da ita hannu daya yasa yadago fuskarta daya hannun kuma yashiga shafa gashin kanta yana tattara wanda yazubo gaba yana maidasa baya ido kur yake kallonta kafin yadaga lebe yace
Karki damu da Faridah da matsalar Faridah wanan dik bai shafeki ba kuma bazai taba shafarki ko nan gaba ba!
Dan haka maganar sakima kibarta!
Ke haryanzu yarinya ce kinyi kankanta da akiraki da BAZAWARA ko SAKIN WAWA!
Yana gama fadin haka yajuya yabarta nan tsaye kamar mutum mutume tana jujuya maganganunsa aranta, takai minti biyar awajen kafin ta iya motsa kafafunta takoma cikin dakinta ta kwanta...
Kai tsaye dakinsa yanufa saida yayi wanka yafito da gajeren wando yanufi dakin Faridah da mamakinsa ganinta yayi kwance akasa ga magninda tasha nan gefenta dauka yayai yaduba yakarence tsaf kafin yagirgiza kansa yafita yakoma nasa dakin ya kwanta saidai bacci sam yaki zuwa idanunsa tunaninsa daya irin tashin hankalinda yake fuskantarsa nan gaba da Faridah
Wasa wasa har karfe daya tabuga bacci yakasa dibarsa dan haka tashi yayi yadauro alwarla yashiga jera nafiloli sai wajen karfe biyu yaji yakasa tukuna yazauna yayi adu'a yashafa kafin yamike tsaye yanufi frige dan kishirwa ta takurasa bai zaton rasa ruwa aciki ba wani dan tsaki yaja kafin yafita yanufi dakin Faridah itama dakin nata ba ruwa aciki hasalima ita takashe nata frige din gabadaya!
Dole saida yasauko kasa yanema,
saidai me HaYaT ya hango atsakiyar falon tana kai kawo hannunta wanda taji ciyon dashi akanta hawaye kuwa kamar an bude famfo haka suke zuba afuskarta
HaYaT ciyonda hannunta yake ne yahanata bacci kamar karta kwanta wajen karfe daya ciyon yatasheta jitayi gabadaya dakin bazai dauketa ba dan haka tafito falo
Ahankali yakarasa saukowa yanufi inda take ke yadaka mata tsawa meye haka?
Cak tatsaya tana kallonsa cikeda shagwaba tace hannuna zafi tun dazu nakasa bacci
Shi sai yanzuma yatuna bai bata maganin kashe ciyo ba, aransa yace dole ki kasa bacci HaYaT!
Ina zuwa yace da ita komawa yayi sama yaduba dik inda yake ajiye magunguna babu wanda yake nema aciki, cikeda takaici yasauko hannunsa daukeda makullin motarsa tana ganinsa yana saukowa tanufi inda yake har alokacin bata sauke hannunta dake kanta ba
Ba maganin yace da ita, amma jirani yanzu zanje nadauko nadawo saikisha!
Yana fadin haka yafara tafiya bin bayansa tayi kamar wata karamar yarinya saida yabude kofar zai fita yarufe yaga tayi wuf tafito itama da mamaki ya kalleta
Ke meye haka?
Zan bika tafada atakaice!
Banson iskanci yafada ransa abace ni sa'an wasanki ne wai?
Dan kinga ina tausaya miki shiyasa kike neman raina mun hankali ko?
Hawaye ne suka zuba fuskarta batareda tace masa komai ba tasauke idanunta akasa
Tausayi tabashi dan haka kulle kofar kawai yayi yacigaba da tafiya zuwa wajen mota tana biye dashi
Dakanshi yabude mata gaban motar tashiga yarufe saida yaje yatado mai gadi yazo yabude yafita
Ahankali yake tuki yana satar kallon yanda taketa kokarin danne kukanda yakeso yakubuce mata dan azabarda zafin hannun ne mata
Saida suka isa asibitin zata fito anan yalurada ko dan kwali bata dashi balle hijab dakatarda ita yayi daga kokarin fitarda take yace kitsaya anan naje nadawo.
Bata fuska tayi tabi harabar asibitin da kallo bawanda yake yawo dagasu sai wani namiji dayake kwance tsakar asibitin da alama dan uwan mai jinya ne yazo nan yanashan iska
Saida tagama kallo tsaf tamaida kallonta gareshi gyara zamanta tayi tadena kokarin fitarda take
Kizauna ba abunda zai sameki yanzun nan zan dawo kinji ko?
Da ido kawai tabishi yafita yakulle motar yabarta nan.
Kusan minti biyar saigashi yadawo hannunsa daukeda ledar magani da robar ruwa
Saida yabata maganin kafin yaja motar suka nufi hanyar gida, aekuwa maganin yamata aiki dan zafin yadena damunta jim kadan dashansa,,,,,, ba jimawa tafara gyangyadi kan kace me har bacci barawo yayi awon gaba da ita.
Lokacinda suka iso har lokacin bacci take batasan sun iso ba, ke yafara cewa da ita
Batako motsa ba, kiran sunanta yashiga yi nanma shiru
Wani dogon tsaki yaja tareda fitowa yarufe kofa yazagayo inda take tabata yafarayi yana kiran sunanta
Ahankali tamotsa tabude idanunta tasaukesu akansa ganin shine yasa tayi saurin bude idanunta da sauri dikda nanauyan baccinda yake damunta
Cikin sanyin murya tace yi hakuri bansan mun iso bane tafada tareda fitowa bata jirasa ba tanufi hanyar cikin gida saida takai bakin kofa dole tatsaya yazo yabude kofar
Daya iso kallonta yayi yace dana zata akwai ta inda zaki wuce ae bazaki jira nazo nabude ba yanda kikayi kuza kuza kikayo gaba dan renin sense ko murfin motar baki tsaya rufewa ba dan kin renani ba?
Itadai batace dashi komai ba, danko jinsa batayi dakyerma take bude idanunta burinta yabude kawai tashiga ta kwanta!
Yana budewa tayi wuf tashige kai tsaye dakinta tashige tana zuwa ta kwanta da bismillah ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita...
Yau bashine yatashi ba saboda makararda yayi wajen kwanciya sai ana tada Sallahr asuba dan haka anan yayi Sallahrsa agida yakoma bacci bayan yayi yan adu'oi dan bacci ne sosai a idonsa.
HaYaT kuwa daman idan ta tashi Sallah bata komawa bacci saitagama aikinta gabadaya tukuna
Yaukam takasa koda d'aura ruwan zafi ne ga bacci bai isheta ba ga hannunta kuma bazai moru ba, dan haka kawai baccinta takoma abunta yau harda mafarkai masu dadi kala kala...
Wajen karfe tara da rabi Faridah tafito bayan tayi wanka tasaka atamfarta wanan karon bata saka karin gashin dokinda kullum yana kanta ba, saima tafi kyau ahaka!
Ganinda tayi ba komai akan table yasa taleka kitchin tananma taga wayam aekuwa batasan lokacinda tafurta kan uban can inyeee yaushe tazo gidan har zata fara mana iskancin nasu na yan aiki?
Juyowa tayi tanufi hanyar dakin HaYaT buga kofar tafarayi tana kiran sunanta
HaYaT datake toilet tana wanka taji kiran gabanta ne yayi mumunar faduwa dan ita yanzu harga Allah tsoron Faridah take har ranta
Kafin wata dabara tafado mata har Faridahr tabude kofar dakin tadira ciki cikeda bala'i take fadin au toilet kika shige?
Zaki fito ne kosaina Balla kofar nan na iskoki naci Ubanki idan baki gaya mun dalilinda ya hanaki yimana break ba
HaYaT daga ita sai karamin zaninta wanda take shiga dashi idan zatayi wanka tatsane jikinta a aciki toilet din, so take tafito kuma tana kunyar yanda zata tsaya haka agaban Faridah gashi kuma batasan wane irin hukunci zata mata ba!
Ganin batada mafita dan Faridah sai masifa take batada alamar barin dakin
Hakan yasa tafito ahaka tuni harta fara kuka
Yauwa fito munafuka gaya mun wane dalilin ne yahanaki aikinda yazama dole akanki yar baka mai bakar fuska?
Hannunta take kokarin nunama Faridah tanaso tamata bayani
Saidai me kafin tace wani abu wani mahaukacin mari ne yaziyarci fuskarta batareda shiri ba tasaki wata uwar kara mai karfi cikin firgici tareda zubewa kasa dan sosai marin yashigeta bada wasa ba
Jin kararta ne yasa ALI saukowa dasauri da daman yayi shirin fita sai yaji ihun HaYaT
Wajen sauri har yana hada matattakalan benen uku uku biyu biyu
Kamar walkiya suka ganshi agabansu
Faridah datake shirin cigaba da jibgar HaYaT tsayawa tayi tana watsa masa wani irin kallo na karka kuskura kasaka bakinka aciki
Meye haka Faridah?
Ban saniba ka tambayeta! Tafada tana harararsa
HaYaT datake durkushe tana kuka jin muryarsa ne yasata saurin tashi takoma bayansa tabuya kamar wata baby tarike gefen rigarsa gam gam
Kinsaba daman dukan yan aiki akan kankanin abu, amma nagaya miki wanan amatsayin kanwata take gidan nan ba yar aiki ba, taimakonki take dan haka wlh wlh wlh Faridah karki kuskura kisake taba yarinyar nan inhar kinason kwanciyar hankali agidan nan!
Zaro ido tayi ganin wai yau ALI dakanshi yake mata barazana kuma akan wata can banza yar aiki kanwar abokinsa!
Cab lallai da sabon lalee tafada!
ALI akan wanan banzar kake gaya mun magana ni matarka ta Sunnah?
Tafada tana nuna HaYaT dake bayansa
Ke kike daukarta haka Faridah, darajar dan Adam tawuce yanda kike tunanina dan haka ki kiyaye nan gaba yazamana wanan shine nafarko kuma na karshe!
Inyeeee....
Toh wallahi yau basai gobe ba yarinyar saita bar gidan nan sainaga Ubanda yatsare mata tunda akanta kake gaya mun magana harda baraza!
Nine nan Ubanda zan tsaya mata, kuma barin gidan nan sai inke zaki barsa amma ba ita ba!
Saboda ni nasan darajar amana kema kinsan amanarta nadauko kuma akanki da banzan ra'ayinki nakin jinin talaka bazai saka nakoreta ba!
Haka kace?
Eh haka nace!
Haka kace?
Eh haka nace Faridah!!!
Yafada cikin tsawa ba alamar wasa afuskarsa.
Ba HaYaT ba hatta da Faridah saida ta tsorota dashi wanan karon!
Tuna maganar bokonta tayi akan karta kuskura tabiye mishi adik lokacinda taga irin yafaru, idan kuwa ta dage komai zai iya faruwa da aurensu dan daman can ba soyayya atsakaninsu sihiri ne yake tasiri akanshi
Kwafa tayi cikeda takaici tace dagani sai ita za abari agidan nan ae
Tana fadin haka tabar dakin cikin sauri har tana tuntube
Sakin rigarsa tayi tareda saka wani sabon kuka tanufi inda kayanta suke
Tana budewa tadauko wanan ta ajiye tadauki wancan dik tana kukanta maidan sauti saida tadauko wanda takeso tasaka tukuna tamike tsaye
Tama manta dawani ALI acikin dakin gabadaya
sakin zanenda ke daure akirjinta tayi tasaka fant dan haryanzu bata fara saka bra ba tasaka wata doguwar rigar lesh rigar tamata kyau sosai
Batabi takan gashin kanta ba wanda dik yabi yacakule kamar mahaukaciya hijab dinta tasaka tanufi hanyar fita har alokacin kuka take kamar wata karamar yarinya
ALI da tun lokacinda tasaki daurin kirjinta yazuba mata ido yana kare mata kallo gabadaya hankalinsa da imaninsa yana kanta kallon irin kyan hallitar hips dinta da Allah yabata, da yake ganin batada wasu na fulani dan yanzu nema tafara kirgon dangi tafara kan *Mom Daddy*π kafin takaiga sauran
Dan haka bai taba zaton tanada baya maikyau haka ba! Danshi haryanzu kallon karamar yarinya yake mata sosai.
Saida tagama komai idanunsa akanta tajefashi cikin wani hali mai wuyar fassarawa,,,, ganin zatabar dakin ne yasa yabi bayanta.
Atunaninsa kitchin zata nufa saiyaga tanufi hanyar fita waje gabadaya, saida takusa bakin kofa tukuna yayi saurin shan gabanta tareda jefa mata tambaya ina zata je?
Cikin kuka tace
Wlh ni bazan zauna agidan nan ba Aunty Faridah ta kasheni, kanaji fa me tace dagani sai ita zaka bari agidan nan dan haka ni tafiya zanyi!
Ook yafada tareda gyara tsayuwarsa yasaka hannayensa cikin aljuhu yace
Yanzu idan kikaje ina zaki nufa?
Kinada inda zakije ne?
Cak kukanta yatsaya tadaga idanunta alamar tunani kafin tace gidanmu zanje!
Daga kafadarsa yayi alamar ko ajikinsa tareda bata hanya ta fita.
Fitan kuwa tayi...
Da taje bakin kofar mai gadi hanata fita yayi harsaida ALI yamasa alamar yabarta ta fita tukuna yabude mata ta fita ko waiwaiye batayi ba tasa kai
Daman umarnin ALI ne, tun ranarda yakata yacema masu gadin kar wanda yabarta ta tafita harsai inshi dakanshi ne yabukaci hakan.....
_Tayaya zan gane labarin yana muku yanda kukeso bayan ban ganin comments dinku saidai akaranta ace muna jiran cigaba Neena dan Allah kimana typing mai yawa? Haba dai fans...!!!!????_
βπ»
[8/1, 7:01 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
*Ψ§ΩΩΩΩ
Ψ₯ΩΩ Ψ£Ψ³Ψ£ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨΨ¨ ΩΩ Ω
Ω ΩΨΨ¨ΩΨ ΩΨΨ¨ ΩΨ¨ΩΩ Ω
ΨΩ
Ψ― Ψ΅ΩΩ Ψ§ΩΩΩ ΨΉΩΩΩ ΩΨ³ΩΩ
.*
*ΩΨΨ¨ ΩΩ ΨΉΩ
Ω ΩΩΨ±Ψ¨ΩΩ Ψ₯ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨ§Ψ±Ψ¨ Ψ§ΩΨΉΨ§ΩΩ
ΩΩππ»*
π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·
8β£
Tafiya take batareda tasan inda take nufa ba itadai bin hanya kawai take abunda yakara rufar da ita shine gabadaya unguwar gidajen irin daya ne wanda bata lura da hakan randa sukazo da randa sukaje asibiti ba saiyau, gashi ba motsin kowa balle ta tambaya ta ina zataga titi
Ganin abun yakici yaki cinyewa ne yasa tasare da lamarin ahankali tarage saurinda take cak kuma tatsaya abunda yafaru tsakanknta da mahaifinta ne yashiga dawo mata akai kamar alokacin yake faruwa
Kuka taso tasaki mai karfi saikuma yasaka hannayenta dika biyu tadafe bakinta tana girgiza kai
Dakyer tasamu ta hadiye kukan taja wani dogon lumfashi tadaura hannunta daya akan kirjinta tace bai kamata nazubarda hawayena akanka ba Abbu kacutar dani kacutarda rayuwata katsaneni tun bansan kaina ba har izuwa girmana batareda namaka wani abun ba, shin laifina