Showing 18001 words to 21000 words out of 54100 words
kwantar mata da hankali da kalamai masu dadi...
Kaf maganganunsa ba wanda yamata dadi jinsu take kamar renin wayau ne irina ALI da gaske sonta yake ae bazai kara aure ba zai zauna daga ita shaishi ne har abada, sanan yake cewa su samu yara ae tunda bazan haihu agidan nan ba wlh banga shegiyarda zan yarda tafasa kwanta agidan nan ba inaji ina gani sai inda karfina yakare! Dik azuciyarta take magana
Azahiri kuma kukan bakin ciki tasaka darasahin sanin abunyi awanan daren
Tausayinta ne yakamashi janyota jikinsa yayi yahada bakinsa da nata yashiga rarashin biye mishi tayi atunaninta maganinta ne yake aiki zata iya hanasa zuwa dakin amarya
Itako bata saniba tausayinta kawai da adalci irin nasa yakeso ya rarasheta ta wanan hanyar, ganin tana kokarin wuce gona da irin ne yasashi janye bakinsa daga nata ahankali yazuba mata idanunsa dasuka rikida daga farare suka koma kalar ja
Ganin halinda yashiga na sha'awa ne haushi yakara kamata danta tabbar wanan sha'awar ba akanta zai huce haushinta ba akan wata matane sabanin ita dan haka tashi tayi tafita tabar dakin ko mukwana lafiya bata mishi ba!
Da kallo yabita harta bacema ganinsa tukuna yamike manyan kayansa yacire yashiga yayi wanka yafito saida yakintsa cikin shigar bacci yanufi dakin amarya wacce tuni bacci yafara dibarta ta kwanta abunta
Da sallama yashigo ganinta yayi tsakar gado harta fara bacci tsaye yayi yana kare mata kallo yana tunanin yabarta tayi baccinta ko kuwa ya tasheta gashi ko abinci bataci ba, saidai bama zai iya raga mata awanan daren ba, yanda yake jin kansa idan bai kusanceta ba komai zai faruwa akansa dan haka nufar gadon yayi yashiga tashinta ahankali yana kiran sunanta
Ahankali tafara bude idanunta kafin ta tashi zaune
Murmushi yasakar mata itama tamaida masa da martanin nata lalausar murmushin harsaida kumatunta suka lotsa
Har kinyi bacci ne amarya yafada idanunsa kyar akanta
Hmm kawai tace cikin kunya kanta akasa
Umarni yamata ta taso suci abincin ba musu tasauko daga kan gadon taje toilet tawanko bakinta tafito tazauna inda taganshi nan kasa yajingina da gado idanunsa akanta harta karaso tazauna
Bismillah yace da ita yafaraci itama ci take amma ba sosai ba saida suka gamaci yace taje tadauro alwarllah taje tayi sukayi sallah raka'a biyu yakama kanta yayi adu'oi tukuna yace taje ta kwanta
Mikewa tayi tanufi gado ganin batada shirin canza kaya izuwa kayan bacci ne yasa yamata magana
Da wanan kayan zaki kwanta?
Fasa hawa gadon tayi taje tadauko wasu rigar bacci masu kauri da laushi taje toilet tasaka tasaka hijab tukuna tafito taje ta kwanta batareda tacire hijab din ba
Murmushi kawai yayi yatashi yakashe wutar dakin yanufi kan gadon ya kwanta
Ita kam Sajidah gabanta ne yashiga dukan uku uku ganin yamatso kusa da ita tareda kama hannunta yana fadin kinyi bacci ne?
Cikin rawar murya tace a'a inaso nayi!
Shiru ne yabiyo baya yana rikeda hannunta tunaninsa ta ina zai bullo mata yazai fara da ita? Candai yashiga shafa jikinta ahankali kafin yajanyota jikinsa yashiga rabata da kayan jikinta...
Faridah ce tace nasan yanzu yanacan yana nuna mata irin soyayyarda yake nuna mun wanan kadai ya isheni bakin ciki itama zata dandani zumarda yake jiyar dani
Rukky ce tace nikam kodai natashi na sauraro miki halinda suke ciki ne?
Girgiza kanta tayi tace banaso idan kika fada mun halinda suke ciki zuciyata zata iya bugawa namutu gabadaya Rukky barsu kawai!
Baby Nice ce taja wani dogon tsoki tajuya tareda gyara kwanciyarta kamar so take tayi bacci sun hanata sai shegen surutu suke
Cikin bacin rai tace wai nikam bazaku bacci bane? Kishiya akanki aka fara Faridah kinbi kin damemu saikace amayar cinye ALI din zatayi gabadaya kinbi kin tashi hankalinki akai mtswwwww
Basuce da ita komai ba saΓ― kashe wutar dakin Faridah tayi ta kwanta zuciyarta acunkushe
Ita Baby Nice so take suyi bacci ta tashi taje gun HaYaT koda karfin tsiya ne tacimma burinta akanta kota halin yaya...
ALI yafara adu'ar saduwa da iyali kanen yana shirin cinmma burinsa yajiyo ihun HaYaT kamar akunnensa takeyi tsananin karar ihun aekuwa ba shiri yamirgina yakwanta gefe yana sauke lumfashi soyake yadawo hayyacinta yatashi yaje yaga meya faru abunda kawai yafado masa arai shine Faridah ce take dukanta ba komai ba!
Tashi yayi dakyer yasaka jallabiyarsa yafito yayi daidai da lokacinda suma su Faridah suka fito suna tambayar junansu lafiya
Mamaki ne yakama ALI ganin ga Faridah nan da alama itama jin ihun ne yasasu fitowa
Sauri yayi yasauka kasa yanufi dakin HaYaT su Faridah na mara masa baya itada Rukky da Baby Nice
ALI yana zuwa yatarda HaYaT sai faman ihu take itakadai daga ita fant dayake jikinta dik kayan jikinta ta yayyagasu tana ganinsa kuwa tasake saka wata irin kara tareda gaura kanta da bango tadago tasake maka kanta da bango nan take kuwa jini yawanke fuskarta
Kafin ALI ya isa gareta tabuga kanta yakai sau uku dankota yayi yana fadin bakida hankali ne HaYaT me kikema kanki haka meke damunki?
Dariya tasaka tana magana cikin wata irin murya tace ba HaYaT bace kasheta zanyi nine ajalinta tana gama fadin haka tayi wurgi da ALI saida yafadi kasa aekuwa su Faridah suka sha jinin jikinsu dikda Faridah tasan aikinta ne amma ita kanta tatsorata da halinda HaYaT take ciki
Kafin ALI yayi wani yunkuri harta nufi su Faridah ta danko wuyan Faridah dana Rukky tashakesu tana wata irin dariya maiban tsoro
Da saurinsa yataso yashiga kokarin kwatarsu ahanunta saida sukasha wahala dakyer yasamu yarabasu da ita, Rukky kuwa dataga haka gudu tayi tahaye sama tareda kulle kofar dakin Faridah cikin tsoro
Sukuwa suna samu ALI yarabasu da ita kowace takwasa aguje suna tsere gun hawa sama Faridah cikin rashin sa'a saida takai karshen benan kafarta tasulbe sai ganinta kake ta gangaro tun daga sama har kasa kamar an cilla ball saida takai kasa wani table din da yake tsakar falon yatsaida ita, abun mamaki idan kaga inda Faridah tafado zaka iya rantsewa da Allah bazata sake moruwa ba musaman irin raunukanda tasha amma ahakan tsabar tsoronda yashigeta yasa tamike a 360 tasake hayewa saman da gudunta tana zuwa da nufin tashiga dakinta tajisa gam gam alamar akulle yake jin dariyar HaYaT ne tana kokarin hawa saman benan ALI na riketa haka suketa kokawa dashi yasa tasake kwasawa aguje sai dakin amarya Sajidah yayi daidai lokacinda Sajidah tagama saka kayanta da ALI yarabata dasu kenan tana kokarin fitowa taka bakin kofa kenan Faridah tazo da gudunta aekuwa ta bangajeta saida tafadi kasa tim kakejinta
Faridah batako kulata ba dakin tashige kamar tsohon nata harda saka kye tahaye kan gado can karshen gadon ta takure kanta afili tace yau nashiga ukuna tajama kaina bala'i
Wallahi safiya nayi zan koma gun boka ajanye aljanin nan daya shiga jikin yarinyar nan inba hakaba ni zata kashe kafin yafara kasheta, taba wuyanta tayi inda tasha shaka gashi har hannun HaYaT yakwanta baro baro awuyanta...
Cikin karfin hali Sajidah tamike yayi daidai lokacinda HaYaT takarasa hayowa sama suna hada ido da Sajidah tatsala wani irin ihu tana komawa baya sai alokacin ALI yasamu yakamata
Ganin halinda take kici ne dikda Sajidah batasan wacece itaba bai hanata nufarta tana karanta adu'oi tana tofa mata ba
Wani irin gurnani HaYaT take tana kokarin kwacewa daga hannun ALI yasa karfi sosai yariketa shima yashiga jera mata nasa adu'oin yana tofeta dasu
Tun tanada karfin fizge fizge hartayi lakwas nan tazube ta kwanta kasa kamar mai bacci sai alokacin hankalin ALI yakai da batada kaya ajinkinta itama Sajidah haka tare sukayi tunanin kafin yayi magana harta cire hijab dinda yake jikinta tarufe HaYaT dashi tazauna da kayan baccin kawai ajikinta saboda tasan Faridah tashiga ta kulle cikin dakin nata
Daukar HaYaT ALI yayi yakaita kan kujerun falon sama yashimfideta akan babbar kujerar mazaunin mutum uku
Zama sukayi cirko cirko da Sajidah suna kallon HaYaT kowane da irin kalar tunaninda yake aransa.
Ita Sajidah tambayar kanta take wacece wanan kuma?
Shikuwa ALI tambayar kansa yake daman HaYaT nada aljanu basu taba tashi ba saiyau?
Shin kodai iskanci ne kawai da kishinda tasaka aranta takeso tanuna masa kalar nata haukar?
Wata zuciyar ce tace dashi wanan ba gaskia bane HaYaT batada karfinda zata gagareka rikewa balle harta jefar dakai kasa!
Wanan saidai aljanu.....
*Vote*
*Comments*
*Chareπ*
βπ»
[8/1, 7:01 AM] Hayat: πππππππππ
πππππππππ
*AyNuL HaYaTπ*
_MATAR ALI GADANGA_
πππππππππ
πππππππππ
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-*
*LaBaRi Da RuBuTaWaβπ»*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*NeEnA_CoOlπ©π»βπ¦±*
*-_-_-_-_-_-_-_-_-_*
*_______________________*
*π³πͺNiGeR Ma FiErTΓ©π€π»*
*Ψ§ΩΩΩΩ
Ψ₯ΩΩ Ψ£Ψ³Ψ£ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨΨ¨ ΩΩ Ω
Ω ΩΨΨ¨ΩΨ ΩΨΨ¨ ΩΨ¨ΩΩ Ω
ΨΩ
Ψ― Ψ΅ΩΩ Ψ§ΩΩΩ ΨΉΩΩΩ ΩΨ³ΩΩ
.*
*ΩΨΨ¨ ΩΩ ΨΉΩ
Ω ΩΩΨ±Ψ¨ΩΩ Ψ₯ΩΩ ΨΨ¨Ω ΩΨ§Ψ±Ψ¨ Ψ§ΩΨΉΨ§ΩΩ
ΩΩππ»*
π·π·π·π·π·π·π·π·
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAIβπ»_
π·π·π·π·π·π·π·π·
1β£1β£
_Kwana biyu munyi biki ta yanda ban zauna ba balle nasamu nutsuwar yimuku typing, dikda haryanzu muna cikin bikin ne amma ganin yanda ake nema na ake bina ta prvt saboda book din yasa nadaure ahaka zanyi typing saboda masoyanaπ nagode sosai da kulawarkuπ€π» insha Allah ana tare wanda suka mun message grps grps ko PC ban ansa ba suyi hakuriππ»_
Ahaka suka kwana har safe zaune gwara ita Sajidahr tadan kishingida kan kujera shikam ALI ko motsin kirki HaYaT tayi saiya dubeta yana karanto adu'oi yana tofa mata
Da asubama ALI sallahr agida yayita saidai arwallar saida yaje wani dakinda ba kowa can sukayi da amarya Sajidah dan dik dakunansu akulle suke, Baby nice na cikin nasa dakin ita itakuma Sajidah Faridah ce cikin nata dan haka dole saida suka nufi dakinda ba komai aciki sukayi amfani dashi.
Da safe wajajen karfe takwas ALI yaje yashiga buga kofofinda suka rufe Rukky da Baby Nice dakyer da wallahaulla suka bude aekuwa suna fitowa suka hangi HaYaT kwance kowace takwasa da gudu sukayi kasa ko takalma babu akafafunsu sukayi waje itakam Sajidah har alokacin da ido kawai take binsu lokacinda suka fita tana kasa tagama hada break fast banda mamaki da suke bata wanan karon harda dariyarta saboda yanda Rukky da Baby Nice suke rige rigan fita kofar falon gashi bata daukarsu dikansu kuma cikinsu bawanda zai yarda wata tariga fita tabarta dakyer suka kukuta suka fice abun ban dariya
Daga dakin Sajidah nake jiyo muryar Faridah da alama tasha kuka harta koshi tana fadin wlh ALI bazan iya tashi nabude kofar nan ba hannuna da kafana dik ciyo da alama targade nayi ko kariya dan Allah ka karya kofar nan kazo kadaukeni ka kaini asibiti wlh kafana ta kumbura daga nan tafashe da kuka
Kufula ALI yayi dan yajima yana buga kofar tabude taki azatonsa kawai iskanci ne irina Faridah haka kawai tasa ya balla kofar, jin abunda tafada baisa ya yarda da ita ba
Cikin bacin rai yace idan kinga dama ki bude ruwanki idan kuma baki buden ba ma ruwanki!
Yana fadin haka yajuya yayi dakinsa wanka yashiga yayi yafito cikin shigar kananan kaya yayi kyau sosai abunsa saida yadubi kofa yaga alamaun har lokacin Faridah bata fito ba sake hade rai yayi gaba bayan yaduba HaYaT yaga har lokacin bacci take
Kasa yasauko Sajidah baiwar Allah bayan tagama jera kayan break tazauna kan kujera tareda daura kanta akan table ahaka bacci barawo yayi gaba da ita, lokacinda yasauko yaganta tausayinta ne yakamashi ahankali yakaraso gareta yana kiran sunanta tashi tayi tana murtsuka idanunta kafin tace ina kwana
Ba walwala afuskarsa ya ansa da lafiya lau tareda fadin kitashi kiyi wanka kizo muyi break
Tabude ne? Ta tambaya cikin sanyin murya
A'a yace tareda nufar falo yazauna
Tashi tayi taje tayi wanka dakinsa tasake maida kayan jikinta tadawo falo idanunsa arufe yaji motsin shigowarta amma hakan baisa yabude idanunsa ba
Dataga bayada alamar tasowa ne yasa tahado masa tea da kwai dinda tasoya atire taka falo tace gashi katashi kaci
Ahankali yabude idanunsa dusuka rine sukayi jajur yace banaci kici naki kawai!
Cikin sanyi jiki takoma tamaida kayan taci kadan tareda yin zamanta acan idanunta fal bacci ne acikinsu tana tunanin tarihin daren aurenta irina gidan ALI GADANGA...
Sautin kukan Faridah da ihunta ne yasa suka nufi sama wanan karon dole yasa ALI balla kofar yashiga Sajidah na bayansa
Inalillahi wa ina iallaihi raji un yafada lokacinda ya hango Faridah tsakar gado jini dikya bata shimfida kafarta da gasken ta kumbura kamar yanda tafada hannuntama fitarda jini yake haka goshinta ba abarshi abaya ba, aekuwa tana ganinsa tasake sakin wani sabon kuka na takaici da zafin halinda take ciki
Caccabarta ALI yayi yasauko da ita tana ihu dan ko ina na jikinta yayi tsami ita kanta batasan taji ciyo haka ba sai yau da safe dan jiya tsananin tsoronda taji ne yahanata fahimtar hakan
Saida yasata mota yajiyo yacema Sajidah kizauna gun HaYaT karta tashi ba kowa agurinta
Allah ya kiyaye ta ansa tareda shigewa cikin gida, aekuwa ta tarda HaYaT ta tashi harta sauko kasa sai kalle kalle take kamar tashigo sabon waje ko kuma taga wata sabuwar hallita haka take kallon Sajidah
Kin tashi? Sajidah ta fada tana kallonta da dan murmushi afuskarta
Maimaikon HaYaT tabata ansa saita saka kuka tanaja da baya saida takai karshen bango tukuna tazube anan tacigabada kukanta kanta tacuka tsakanin kafafunta
Itakam Sajidah yau taga ikon Allah tafada aranta!
Kallon HaYaT tayi taso tayi magana kuma saita fasa kulle kofar falo tayi tadawo ta kwanta akan babbar kujera ta kwanta idanunta kyar akan HaYaT tana nazarinta tareda karanto adu'oi ahankali tana tofawa ko ina na falon...
Ihu sosai take ko ina asibitin ba inda baka jiyo kararta sai gulma ake ma aikata da yan jinya ana matar ALI GADANGA ce targade tayi ana mata gyara shine fa! Abunda Yake fitowa daga bakunan mutane Kenan wasu na ganin tacika raki wasu kuma cewa suke iskanci ne kawai ke damunta saikace ba mace ba...
Gabadaya Faridah tafita hayyacinta dan kafarta karewa tayi hannunta daya kuwa targade goshinta kuwa sosai taji ciyo akai, yanda take ihu tana cakumo wuyan ALI ne yabashi haushi kamar mahaukaciya bata nuna juriya ko kadan ba kowa sai magana ake ALI matarka batada juriya gashi kuma taki bari ataba kafar shiyasa aka mata ta karfi zafi kan zafi Kenan.
Wajen karfe daya suka dawo gida dan sai masifa take da iface iface kamar zararra acikin asibitin har likitocinda suka mata gyara bata kyalesu ba, ran ALI yayi mugun bacewa tun yana mata magana da tsawa tayi shiru harya dena !
Sakawa yayi aka kaita mota suka dawo gida cikin motar keken guragu yashigo da ita yabude da kye dinda yake hannunsa saidai ba kowa falon dakyer ya haura da ita sama yadawo yadauki keken dik yakaisu dakinta yana kokarin fitowa ne tasaka kuka tana rokonsa yadawo wajenta tana tsananin bukatarsa kusa da ita fiyeda amaryar zafi zai kasheta taketa fada
Ganin irin kukanda tasaka ne yasa yadawo amma hankalinsa gabadaya yana kan HaYaT bama amaryarsa Sajidah ba, saida yasamu tayi bacci tukuna yafito kai tsaye dakin Sajidah yanufa nan yatarda HaYaT zaune tsakar dakin tana rarraba idanu kallo daya zaka mata ka gane tana tareda jinnu yanda idanunta suka firfito waje abun saiya baka tsoro
Saidai tadena fisge fusge da bige bigenda take yanzu banda kallo ba abunda take
Itakam Sajidah bacci take jim kadan bayan tajayo hannun HaYaT sun hau sama ta kwanta sai bacci daman ga gajiyar biki jiya haka bata samu tayi bacci ba shiyasa yau ko yaya tadan zauna bacci ne yake awon gaba da ita
HaYaT yakira sunanta tana ganinsa tamike tsaye tareda fashewa da kuka
Dan karta tashi Sajidah yasa da sauri yanufi inda take yakamo hannunta yana janta tana tittirjewa ganin zata tashi Sajidah ne yasa dasauri yadauketa cak yanufi dakinsa da ita abakin gado ya ajiyeta aekuwa tashi tayi tanufi kofa zata fita da sauri yarigata isa kofar yakulle tareda cire makullin yasake janyo hannunta yazaunar da ita abakin gado kuka tasaka mai karfi tana kyarma dik jikinta ganin hakane yasashi karanto mata adu'oi yana tofa mata ahankali tafara rage sautin kukanda take takoma ajiyar zuciya
Saida ya tabbatar ta nutsu tukuna yakira sunanta HaYaT cikin sanyin murya yana kallonta
Dagowa tayi ta kalleshi ido cikin ido kafin tadubi rigarda take jikinta da sauri tasaka hannayenta biyu tana kare kirjinta ido waje tasake kallon ALI din dayake tsugune gabanta yana kallonta
Me nakeyi anan?
Waya kani dakin nan?
Hamdallah yayi aransa ganin tadawo daidai sai alokacin yakare mata kallo ganin tana kare jikinta rigarda Sajidah tasaka mata bawai tana nuna tsiraici bane karara a'a amma komai na suffar mutum tana nunawa
Mikewa yayi tsaye yana kallonta yace me kike tunani?
Zan kaki dakina ne dan nasamu wani abu daga jikinki ko namiki wani abu?
Idanunta tasauke kasa cikeda kunya da takaici dan ita sam bata tuna komai daga abunda yafaru da ita jiya ba sam!
Mamakinta metazo yi dakin ALI?
Yaushe tazo bata sani ba?
Kokarin mikewa tsaye take yasa hannu yazaunar da ita ba shiri takoma tazuana tana kallonsa mikewa yayi yaje yadauko kayan wanke ciyo goshinta da jiya tajima akanta yakeso ya wanke mata
Kallonsa take tana mamakin me zaiyi da kayan, ganin ya tsuguna agabanta ne yasa tasake kallonsa ta kalli kayan kafin tace me zakayi dasu?
Hannuna yayi sauki ae tafada tana nuna masa
Goshinki zan gyara yace da ita
Cikin alamar tamabya zatayi magana kenan taji yadaura auduga da magani akan goshinta azabarda taji ta ziyarceta ne yasata yin shiru dole tadanyi ihu marar sauti tareda kame hannunsa
Kallonta yayi ba alamar wasa afuskarsa ba shiri tasaki hannunsa tafara kuka cikeda shagwaba saidai kukan nata marar sauti
Har yayi yagama bata kuma yunkurin hanasa ba saidai hawaye fuskarta sunyi shabe shabe harda majina
Yana gamawa yakalleta da sauri yadauke fuskarsa yana fadin kazama kawai dubeki katuwa dake harda majina idan kina kuka?
Ita dai batace dashi komai ba kukanta take ahankali
Ganin batada alamar tsagaita kukan ne yasa yace da ita idan bakiyi shiru ba zan sake kwance ciyon nasake wankewa fa
Tana jin haka tayi shiru tadena kukan kamar an dauke ruwan sama
Takure jikinta tayi guri daya sai yanzu taji ko ina na jikinta namata ciyo gashi tana wani tsami jikinta ba wanka tana pΓ©riode
Kamar yasan tunaninda take aranta yace kitsahi kije kiyi wanka
Kabude mana tace
Anan zakiyi yafada yana mikewa yamaida kayan inda yadauko tareda cire maballan rigarsa saida yagama yacire rigar yakuma cire dogon wando yarage dagashi sai guntun wando
Dauke kanta tayi daga kallonsa gabanta na dukan uku uku karo nafarko Kenan dataga namiji haka agabanta aranta take fadin ALI bayada kunya baisan me yake ba, banda haka meye hadinta dashi dazaiyi tsirara agabanta haka ko kunyarta bayayi?
Maganarsa ce ta katse mata tunaninta