Showing 30001 words to 33000 words out of 92896 words
kin bokan nasu wan da yajima yanayi musu aiki tun da daɗewa.
Wani dariyar ya kecewa da shi yaɗa go yana dubansu, cikin wannan kazam tacciyar dariyar da yake ya ce
"An gama komai sai dai a jira lokaci".
Zama Na'ima ta gyara ta ce
"Ban gane ba boka wancan lokacin ma haka kace har yanzu shiru, ni kawai a yi mai yuwuwa in ma kuɗi kake so na kara maka ni bana da matsala da su a ƙwaisu, ni dai kawai na dai na ganin ta cikin gidan".
Raliya ta amshi zancen
"Ƙwarai kuwa boka mu dai a fitar da ita a gidan shine kawai, zamu kara maka kuɗi kasan zuba kuɗi har idan ai ki zaici ba a bune mai wuya a gurin muba".
Wani irin ihu mai haɗe da fito bokan yayi kana yace
"Aduk cikin buka tunku da kuke zuwa da shi kufaɗa min wannene bai taɓa ciba!?".
Yafaɗa cikin karaji da sai da suka razana, kana yanuna Raliya da gashin dabbar da ke hannun sa ya ce
"Ke wani irin kuɗine baƙya karɓa a hannun manyan attajiran garinnan duk ai kin wanene?".
Yakuma faɗa cikin muryar nan nasa mara daɗin ji da sauraro.
Yakuma nuna Na'ima yace
"Mu mukayi miki ai ki da har kika samu *Parmsec* *ABDALLAH IDRIS ABDALLAH* a matsayin miji kinfi kowa sanin haka".
da sauri ta ce
"A gafarce mu boka basai an yi tone-tone ba zamuje muciga ba da jira sai a bin da kace".
Yakuma kecewa da dariya yakara karkaɗa gashin dabbar da ke hannun nan na sa kan ƙwaryar, kana yaɗa go yana faɗin
"Aljani Durkus ya hatsala kunimi gafarar sa."
yafaɗa yana nuna cikin ƙwaryar wan da sai fidda wani irin bakin hayaki yake,
Da sauri suka sunkuyo da kan su kan ƙwaryar suna faɗin
"A gafarce mu ai mana afuwa".
Shiru yayi kamar mai sauraran wani abu sai kuma yashiga gyaɗa kai yana washe haƙora kana yace
"Aljani Durkus yagafar ta muku kutashi kuje".
Da sauri Na'ima tabuɗe jaka taciro kuɗi masu yawa ta a je gaban bokan kana suka mike suka nufi in da suka faka motar su,
A cikin motar Raliya da ke jan motar tajuya ta kalli kawar tata da ta jingina da jikin kujera sai taunar baki da girgiza kai take,
ta ce
"Kawata ya dai naga kamar har yanzu hankalin ki bai ƙwanta ba?".
Da sauri Na'ima kamar mai zaman jiran tambayar ta ce.
"Ba dole hankalina ya kasa ƙwanciya ba, wata uku na ɗibarwa yarinyar nan, sai gashi har yau kimanin watan ta 6 kenan'
ke sanin kankine tun tana wata uku muka zo gun boka kan ya fidda ta a gidan, yace muje an gama amma har yanzu shiru, still yau ma irin abun da yafaɗa mana wata uku da suka wuce shi yau yakuma mai-maita mana,
Nifa har nafara tunanin an ya bazan canza wani malamin ba kuwa?".
Raliya ta ce
"Duk faɗin garinnan babu bokan da yakai malam na kan tudu iya ai ki kamar yankan wuka, ke kanki shai da ce wani irin guraren malamai ne bamu leka ba waya kai shi ai ki kamar yankan wuka,
Yanzu haka kiran da a ke tamin tun dazu ɗin nan wani Alhaji ne da zamu haɗu yanzu haka kuɗin shi ya isa cikin account ɗina,
Duk wasu manyan garin nan masu bukatar harka babu wan da bana gogawa da su, duk kuma ta sana diyar ai kin malam na kan tudu ne. ke kanki kinsan yayi miki babban ai kin da mamanki da baban ki ma ba zasu iya yimiki shi ba,
dan haka bai ma kamata ki karaya da abin da yace miki ba, kidai jira ɗin kamar yan da yace".
Numfashi Na'ima tasauke ta ce
"To shike nan amma wlh ko muryar yarinyar nan naji yana sani faɗuwar gaba, bare kuma na ganta bana kaunar nabuɗe idanuna na ganta cikin gidan".
Haka suka rika tattauna matsalar su da kulle-kullen su wan da su suka san ma a nar sa,sai da Raliya tabi gidan Na'ima tasau keta kafin tawuce gun Alhajin ta da ke jiran ta.
★★★
Yau a na tashi a makaranta napep na hayo na dawo gida sabo da wayar da mukayi da Aunty Rafee'at ɗazu da safe, tace min zatazo da karfe 2 shi yasa ban ɓata lokaci ba nayi gida.
Wanka na shi ga a gaggauce dan biyu tayi har ta gota,
Ina daga cikin bayin naji tsayuwar mota da muryar Dr Faruq mijin Aunty Rafee'at suna gai sawa da ma ai katan gidan, da sauri-sauri na karasa wankan na ɗauro towel nafito,
babban hijabi nazura nayi waje.
A jikin mota na hangi Aunty Rafee'at suna sallama da mijin ta,
na karaso jikin motar da sauri ina faɗin
"Au tafiya zaka yi in na kara zuwa gidan ka."
Dariya Dr Faruq yayi ya ce
"Laifin Aunty kine ai ƴar gidan Inna, yanzu haka daga offece ta ɗagoni nace tabari na sallami mutane sai na kawota taki,nabar mutane suna jirana badun haka ba da tare zamu wuni, amma dai a tai maka a kara zuwa gida na".
Yakarashe maganar da dariya.
Kai na gyaɗa na ce
"To shike nan albarkacin marasa lafiya".
dariya yakuma kana ya ce
"Ngd da naci albarkacin marasa lafiyar".
Mukayi sallama yaja motar sa ya tafi, mukuma muka shige ciki,
Muka wuce bedroom,muna shiga na tuɓe hijabin,
"Oh HAMDAH da ma bakaya jikin ki?".
Aunty Rafee'at tafaɗa tana zama bakin gado.
dariya nayi na ce
"Ai ina bayi naji tsayuwar motar ku shine nafito".
kai ta girgiza tare da faɗin
"To sa kaya kizo ki karɓi tsara bar ki".
To. na ce da sauri na isa gaban wardrobe na ciro kaya na saka, dasauri na hayo gadon na zauna kusa da ita ina faɗin
"To bani tsarabar Aunty Rafee'at".
Jakan ta tajan yo tana cewa
"Ɗaura ɗan ƙwalin mana, tsaraba kam tun da nazo ai sai na baki, tun daga Jos nasa aminiya ta ASMA'U taturo min da su domin ki".
Baki na washe nasoma ɗaura ɗan ƙwalin da na hayo gadon rike da shi a hannu, sabo da sau rin na zo ta bani tsarabar da tace tazo min da shi.
Wasu ƴan kananun fararen robobi masu murafe da goruna ƴan ma dai-dai ta taciro a cikin jakar
ta, ta dubeni ta ce
"Je kitchen ki ɗauko madara na ruwa da cup da cokali kizo da shi".
Na ce
"To". Na sauko daga kan gadon da sauri na tafi kitchen na ɗauko madarar gwan-gwani na ruwa na huda gwan-gwani a gun, kana na ɗau cup da spoon na dawo da sauri na diresu gaban ta.
Buɗe robobin tayi tasa cokali tarika ɗiban abubuwan da ke cikin kowami robar tazuba a cikin cup ɗin, kana tazu ba madarar duka a ciki tamosa sosai,
Ni dai sai baza ido nake ina lasar baki namasu tabani na taɓa naji a bun da a ka zuba mishi madara mai yawan nan,
sosai ta motsa kana tamiko min kofin ta ce
"Am shi ki sha".
Tun kan ta karasa faɗa, na karɓi cup ɗin da sauri nagyara zamata na kai cup ɗin baki,
ina kurbar a bin da ke cikin cup ɗin nayi saurin cire bakina, ji nayi kamar nayi a mai da kyar na iya haɗiye wan da ke cikin bakina.
Fuska na yamutsa na ce
"Aunty Rafee'at wannan ne tsarabar Ni dai gara ma kibani wannan da nagani kamar kunun a yace a ciki".
Nanuna ɗaya daga cikin goru nan.
Ta ce "Maza shanye kibani kofin, duk wani tsarabar da zan baki ai a bayan wannan yake, kinsan am fanin wannan da tasirin shi a jikin ki kuwa?,
Wannan ba irin sauran magunguna kamar ko wanne bane zan iya cewa a duk faɗin a rewacin Nigeria ASMA'U Jos ita kaɗai ke da lakanin su, magani ne da ke zama a jikin mace har na kimanin shekaru 5, itace wacce a kewa lakabi da mai da tsohuwa yarin ya,budurwa wacce ke tattare da budurcin ta kuwa ya kara mata ɗanɗano a kan wan da take tare da shi,
Sanan niyace ita sosai dan har kasashen ketare suna oder'n kayan ta, bakiga kaɗan-kaɗan nazuba miki ba sabo da yana da karfi sosai,
Ɗazun nan tasa a mota a ka kawo min ".
Ido kawai na zuba mata ba don na fahimci abin da take faɗa ba,
Murmushi nayi na ce
"To Aunty Rafee'at yau Aunty Asma'u ce ban san taba?".
Itama murmushi'n tayi kana tace
"Nasan kin san ta mana, amma yanzu ina faɗa Miki ne a bin da baki sani game da ita ba, a baya ai ban sanar Miki ba yanzu da hakan ta kama shi yasa nake faɗa miki, duk da nasan bazaki fahimci a bin da nake nufi yanzu ba sai kin kara hankali, yanzu dai shanye wannan ɗin sai kisha nacikin gorar".
Na ce
"Babu daɗi fa".
Ta ce "Ai da ma a baki bashi da daɗi".
Ina yamusa fuska da matse ido na shanye, ta ɗan siyaye min na cikin gorar shima nasha shikam nasha har ina latse baki dan zaki ne da shi.
Naje na wanko cup ɗin a bayi nadawo,hira sosai muka buɗe muna cikin hirar wayar ta yafara ringing.
Ta janyo wayar tare da kallon screen ɗin wayar, da ɗan mamaki take kallon sunan da ke yawo kan screen ɗin wayar,sai kuma ta ɗago ta kalleni ta ce
"Ya SALEEM na gida ne?".
kafaɗa na ɗaga nace
"Oho nima ban sani ba".
Kai kawai ta girgiza kana tayi picking cal ɗin,ta kai kunne tare da yin sallama kana ta ce
"Barka da rana Ya SALEEM".
Shiru tayi da alama tana sauraran sane, can kuma tace
"Eh". sai takuma yin shiru naƴan dakiku kana tace
"To". sai tasauke wayar tamike daga kishin giɗen da take
tadubeni ta ce
"Wai kije in ji Ya SALEEM".
Ido nawaro nace "Ni". nafada tare da nuna kai na, kai ta gyaɗa a lamar Eh
ji nayi gaban kirjina ya yanke murya na rawa dan na mugun tsorata da jin irin wannan kiran bazatan na ce
"To ni me namishi Allah babu a bin da namishi".
Nan da nan hawaye yataru a idona kiris yarage suzubo.
murmushi Aunty Rafee'at tayi kana tace
"To in ban da ke dan ya kira ki sai yazamo wani laifin kika ai kata, kidai tashi kije kada kuma garin tsoro ki ɗaura laifin wa kanki yanzu gara dai kiyi sauri".
tuni ɗan guntun hawayen yazubo jin kalmar ta na karshe da sauri na mike. dariya Aunty Rafee'at tasaka tariko hannuna ta ce
"Ke da alla share hawayen ba komai fa wakai cewa yayi kizo kuma cikin sanyin murya ma yayi maganar".
Kai na gyaɗa namike nanufi side ɗin sa.
Tun daga kofar parlour'n sa nafara sallama, na daɗe ina tsaye ina ta rafka uban sallama, dan ban mance dokokin da ya gin da yamin a gidan Inna a Dass ba,
Jin shirun yayi yawa yasani tura kofar naɗan leko kaina, babu kowa cikin parlour'n sai na tura kofar gaba ɗaya tare da kuma yin sallama cikin ɗaga sauti,
Namma shiru babu motsin kowa, a hankali na taka na isa bakin kofar bedroom ɗin sa.
Cikin ɗaga murya nashiga yin sallama tare da ɗan bubbuga kofar a hankali,
daga cikin ɗakin a kace shigo, ɗan jim nayi sai kuma na tura kofar ina kusa kai na cikin ɗakin sai..............
*HAMDAH SHALELE FANS GROUP*
👇🏻
*Duk naji kora fin ku kuma duk ina sane da komai kubiyoni a nex page zakuji am soshin ku in Sha Allah*🥰
Mommyn Twins ce
*🌺HAMDAH🌺*
*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*
_(Book one)_
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*
*Free page*
My no 08034690723
🅿️12
*KAMAR YAD DA NACE IN SHA ALLAH ZAN BAKU DUK KANIN AM SOSHIN KU ƳAN HAMDAH SHALELE FANS GROUP TO GA AMSAR KU A GURGUJE*
👇🏻
*tabbas nayi alkawarin cewa book ɗin HAMDAH kyautace tun daga farkon sa har karshen sa a baya tun lokacin da nafa posting ɗin sa tun a january. tabbas Ni nafaɗi hakan*
*Sannan kuma yan zu dana dawo naci gaba da typing nasa nace na mai dashi na kuɗi.*
*Eh tabbas na janye alkawarin da na ɗauka na cewa ƙyauta zanyi shi a bisa da lili mai karfi kamar ha.*
👇🏻
*bazan zauna na bata lokacina na kashe duk wasu sab gogina nayi typing a cemin Thanks ko kuma a turamin sticker kaɗai ba👌🏻*
*Na kuɗi kuwa dole sai kinsa nairan ki kafin kisameshi ko kiyi min sharye da comments ko karkiyi bai dameni ba na fanshe da nairan ki*
*Abu na karshe shine idan kuka gyara naci gaba da ganin ruwan in gantaccen comments da sharhi mai rasa zuciya ba ku kaɗai ba har da sauran group's ɗin da nake posting a ciki bawai nace ba ƙwayi bane amma dai kukara Ni kuma nayi muku alkawari har idan nacigaba da ganin sharhi na musamman narantse duk wan da na karɓi kuɗin sa zan mai da mishi naci gaba da posting ƙyauta.*🤗
Sai naja na tsaya da sauri nan bakin kofar, hango Aunty Na'ima da Ya SALEEM ƙwance a kan gado, Na'ima na gefen sa manne da shi daga ita sai wani ɗan yalolon gyale da tayi ɗaurin kirji da shi.
Yana ƙwance yabata baya fuskarsa na kallon garu, single da boxes ne kaɗai a jikin sa yana ƙwance rike da waya yana latsawa.
da sauri na janye idanuna a kansu
nayi baya da hannuna nariko handlle ina kokarin boɗe kofar najiyo muryar ta,
"HAMDAH".
takira sunana juyowa nayi naɗan kalli in da take batare da na am sa ba,wani irin mika mai haɗe da hamma tayi tasuke voice ɗin ta taɗan ɗago tadube Ni cikin muryar gajiya ta ce
"Jeki girka ruwan zafi a kitchen ki kawo".
Da sauri na waro idanuna a kanta jin a bin da tafaɗa,
fuska ta yamutsa tana faɗin ko baki ji bane?".
ƙwayar idanuna najuya kan Ya SALEEM da ke ƙwance kamar baya gun sai faman latsa wayarsa yake, sai na mai da dubana gare ta na kaɗa kai tare da murguɗa mata baki najuya nayi waje.
Kitchen ɗin babban parlour nashiga na kunna Gas kana na cika ruwa cikin tukunya mai ɗan girma na ɗaura kan gas ɗin,
naja kujera na zauna ina zaman jiran ruwan yayi zafi.
Ina nan zaune har ruwan yayi zafi naɗau boket da na ganshi a cikin kitchen ɗin na juye ruwan a ciki naɗau ka nanufi side ɗin shi,
Sallama nayi daga bakin kofar bedroom ko da a ka amsa ban shiga ba sai da naɗan tsaya kaɗan kafin daga bisani na tura kofar.
Wannan karon yana zaune a kan kujera, ita kuma tananan in da na barta ɗazu tayi shame-shame,
Kokarin dire boket ɗin nake nan tsakiyar ɗakin tayi saurin cewa
"Shiga dashi cikin bayi mana".
A sannu nanufi kofar bayin ina shiga ciki bra da pant ɗin ta nafara ka karo da su yashe a kasan bayin,kafa nasaka na turesu gefe na isa na a je boket ɗin najuya nafita.
Koda na koma part ɗina a ƙawance na iske Aunty Rafee'at tana ganina tayi murmushi tare da faɗin
"Um mata masu miji daga tafi amsa kira sai a mance da ni har na fara tunanin ko in tafi ne".
Murmushi nayi na ce
"Ai girka ruwan da nayi ne yasa na daɗe ayya Aunty Rafee'at da tafiya zakiyi?".
Nayi maganar a marairaice,
tace
"Ruwa kuma?".na ce
"Eh ai Aunty Na'ima ce tace na girka musu ruwan wanka da ita da Ya SALEEM shi yasa ma na daɗe".
Da sauri tamike zaune tare da waro ido tace
"Mene girka musu ruwan wanka da ita da Ya SALEEM??!"..
kai na gyaɗa,
daɗa waro idonanun ta tayi da ƙyau da ƙyau tace
"Ke baki da hankali ne nikam ke HAMDAH wace iri ce ke, ke babu zu ciya ne a jikin ki, HAMDAH yaushe zakiyi hankali ne kam wai har yanzu bakisan ciwon kankiba baƙyajin wani a bu a cikin zuciyar ki ke,
Ke bakida kishine a rayuwar ki, girka musu ruwan wanka??!
sugama a bin da zasu yi kece ƴar girka ruwan wanka dan tsabar rashin mutun ci da rainin wayo babu ruwan zafi ne a bayi da har sai kinje kin girka musu a kitchen kin kawo musu,
dayake kema sha-sha-sha ce mara zuciya shine zaki biye musu.
to wlh bari na faɗa miki daga yau sai yau nakarajin makamancin irin haka sai ranki ya ɓaci. da ma a she har yanzu tana kan saki ai kin kina yima ta??"....
Kai na girgiza na ce
"Allah bana yi".
Ta ce
"Bagashi yanzu tasaki kinyi ba".
"Aunty Rafee'at yanzufa yana nan Allah in banyi ba duka na zai yi".
tace
"Ya kashe ki ya kashe kima, dan rainin wayo sai kace ƴar ai ki a ka kawo masa gida wlh Allah bazai barshi ba".
Haka tarika masifa Ni dai shiru nayi nazuba mata ido,
ta mike taja maya finta taɗau jakar ta, tace har idan ban gyara ba babu ruwan ta da Ni kuma bazata sake zuwa gida naba, haka tatafi da ɓacin rai.
Ko da tafita a farfajiyar gidan suka haɗu da Ya SALEEM ko kallon in da yake batayi ba tafice daga gidan,
koda cewa Ya SALEEM ɗin wanta ne wan da suka fita ciki ɗaya, amma sam bata jin daɗin rashin daraja wa da nuna rashin kulawar da yake yi kan HAMDAH.....★
★★★
Yau tun kafin a tashimu a makaranta hadari ya haɗu baki kirin,kan kace me ruwa yafara sauka, koda a ka tashe mu haka ɗalibai suka zauna cikin aji wasu kuma motocin gidan su suka zo suka ɗauke su.
Muna zaune da wasu ƴan a jin mu hira a ke amma ni gaba ɗaya hankali na da ido na nawaje kan ruwan da ake shekawa, a hankali namike nadubi
Bilkisu wacce sit ɗinmu ɗaya da ita nace
"Bilkisu Ni zan tafi ga jakata ki tafi min dashi gidan ku gobe sai kizo min dashi?".
Ido tawaro tace
"Acikin ruwan nan kidubafa ruwan karuwa yake daɗa yi ki bari mana a ɗauke tukun".
Mika mata jakar nayi ina faɗin
"Gashi Ni dai natafi bana son ruwan yajikamin littattafai ne" .
tana amsa najuya da sauri nafita dan gaba ɗaya na masu najini cikin ruwan.
Haka nafita a cikin makarantar naɗau hanyar gida a kafa,
ahankali nake tafiya ruwan na sauka a kai na,
har na iso kofar gida zuwa lokacin kam ruwan yafara sauki natura karamar kofar get nashi.
Ina isowa dai-dai parking space kamar an ce na waigo kuwa ina juyawa muka haɗa ido da shi, yana tsaye cikin parking space ɗin