Showing 27001 words to 30000 words out of 92896 words

Chapter 10 - HAMDAH part 1 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

11897

bukatar sa, duk da ranar in Ina cikin ɓacin ran wancan shegiya mai jan fuskar, amma karkiji wani gefen zuciyata in da yacika da farin ciki ba,duk da bai buɗe min sirrin bukatar tasa ɓaro-ɓaro yanuna min ba, cikin halin nan nasa na isa da kasaita izza miskilanci, yagwada min a lokacin nasan nesa takusa zuwa kusa. sai dai fa tun wan can ranar harfa hau baikuma tinkarata da bukatar sa kwatan kwacin irin na wancan ranar ba, sai dai ni idan naji lungu na namin kaikayi na kai masa yasosa min."

Raliya tace "Kada ki damu zan zo mukoma gurin nan tare idan yaga idon ki sai yafi bamu manyan makamai".
"An gama kawata sai na ganki".
Nan suka cigaba da kulle-kullen su wan da su suka san ma a narshi.


Ina fita adai-daita natara zuwa gidan mu da ke state locos har kofar gida yakai Ni nasauka nabiya sa kuɗin sa nanufi ciki,
Da sallama na turo karamar kofa da ke gefe da jikin get,
da sauri baba mai gadi dake zaune nan gefen ɗakin sa yana al'wala yamike yana faɗin
"Wane ne haka ba ƙwanƙwasa kofa?".
Zai kuma magana nakarasa shiga ciki, baki ya washe yana faɗin
"A'a HAMDAH ce Barka da zuwa".
Nace "Ina yini Baba mai gadi".
Ban jira amsawar sa ba nayi cikin gidan da sauri, da direct part ɗin Ummi na na nufa tun daga kofar parlour nafara faɗin
"Ummi, Ummi na nazo".
Shiru parlour'n babu kowa nashige cikin bedroom Ina cigaba da kiran sunan ta.
Kasake Ummi da ke zaune bakin gado tayi, da sauri haɗe da sassarfa na karaso in da take na wurga jakata kan gado nafaɗa jikin ta ina faɗin
"Oyoyo Ummi nazo".
girgiza kai Ummi tayi tare da yin murmushi taɗago ni tana cewa
"To sai kin nukurkusani kafin nasan kinzo".


Baki na washe namike nazauna gefen ta
"Ummi ai duk murnar ganin kine".
tace
"Sai Kuma a haɗa da shiririta".
Murmushi nayi itama murmushin tayi tana bina da kallo na tabbata itama tayi missing ɗina.
Nace "Ummi Abba fa?".
"Ai bai dawo daga offece ba".
Nace "To Fauzan fa".
tace "Yana can sashin Mamie'n ku yanzu suka bar nan shida Nusaiba da Adil da Abid".

Da sauri na mike tsaye ina faɗin
"Laa sun zo ne har da su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela ɗin?".
Tace "A'a babanun su ne suka kawo su".

Gyalen jikina na zame na aje bakin gadon najuya zan sa gudu Ummi ta ruko hannuna najuyo ina fuskan tarta,
tace
"Kitafi a nutse ki dai na wannan guje-gujen".
Kai nagyaɗa mata na zame hannuna nafita da sauri na nufi part ɗin Mamie..

A parlour na iskesu gaba ɗayan su Mamie
Nusaiba Fauzan Adil Abid. suna ganina suka taso da gudu suka rungume ni muka sa ihun murna muna tsalle,
dariya Mamie tabimu da shi, nasakesu na karaso in da take na zauna gefen ta tare da ƙwantar da kaina a kafaɗar ta, murmushi mai sauti tayi tashafa kai na tana cewa
"A'a HAMDAH anzo ne?".
cikin muryar dariya nace "Eh Mamie ina yini".
ta amsa ɗauke da dariya a bakin ta.
Nan muka buɗe hira sai da a kafara huɗuba a masallaci kafin Mamie tace wa Fauzan yakama Adil da Abid sutafi masallaci ni da Nusaiba kuma muje muyi al'wala muyi sallah.koda mukayi sallar a binci mukaci muka ɗaura daga in da mukatsaya.


Har yamma ina shashin Mamie sai da na dumfari dai-dai lokacin dawowar su Abba da Abbu kafin nafita na nufi parlour'n da suke yada zangon su a duk san da suka dawo daga offece, da sallama nashiga gaba ɗayan su suka mai da hankali kai na tare da amsa sallamar,
A kasan carpet na zauna kusa da kafafun su nashiga gaida su,
fuska ɗauke da murmushi suka amsa.
Abbu yace
"To ya karatun ana kan yi dai ko?".
Kai na gyaɗa alamar Eh.
yace "to madalla Allah ya taimaka.
Amin Abba ya amsa dashi sannan ya ɗaura da faɗin
"Ina yayan naki ko ya sauke kine yakoma?".
"A'a ni kaɗai nazo".
Ido Abba ya zubamin yace
"Ke kaɗai kikazo bai masan kinzo ba kenan?".
Kai na gyaɗa a lamar Eh.
cikin muryar faɗa yace
"To tashi maza ki koma zaki fito bai saniba waya faɗa miki a nayin haka daga yanzu inda zaki sake fita ki tabbatar kin sanar masa".
Baki na tura nayi narai-narai da ido,
Abbu yace "A'a Shu'aibu kyale ta ai gida tazo"
Abba yace "Yaya ko gida ne ai bai kamata tafito bai sani ba".
"Naji. tashi kishiga ciki".
Abbu yafaɗa yana yimin a lama da in tashi, da sauri na mike natafi part ɗin Ummi.


Da daddare bayan sallar Isha ina ƙwance kan gadon Ummi dan tun shigowata ban kuma fita ba, dan nasan halin Abba sai ya iya zuwa yakorani.
Ummi da yanzu shigo warta ta takaraso bakin gadon tace
"Ke HAMDAH kinyi Sallah ne kika haye gado".
"Eh Ummi nayi".
Tace "To sauko kici a binci".
tafaɗa tana dire plt ɗin da tashigo rike da shi a kasa kusa da gadon.
a hankali na mike zaune cikin yin kasa da murya nace
"Ummi Abba yashigo ne?".
Ganin yanayin da nayi maganar sai ta ɗan tsuramin ido
kana tace
"Kinyi masa laifi ko".
Kai na girgiza nace
"Waifa dan nazo shine wai meyasa ban faɗa wa Ya SALEEM kafin nazo ba, kuma ai Abbu yace nazo na zauna abina".
"Tafican da alla ai gaskiyar sace dama ya korakin ne kyasa kafa kifito bai sani ba".
Kai na langwaɓar cikin yin muryar tausayi nace
"Nikam ma gun Inna zan tafi gobe".
tace
"Ga hanya Bismillah".
Tajuya tayi waje.
Murmushi nayi nasauko nasoma cin a bincin.
Washegari part ɗin Mamie na gudu da sassafe a can nayi breakfast ban dawo part ɗin Ummi ba sai rana.


Ranar Lahadi da yamma Ya SALEEM yazo gidan direct parlour'n Mamie yanufa tana zaune saman kujera yakaraso yazauna kan kujerar da ke gefen ta.
Cike da kulawa Mamie ke duban sa tare da amsa gaisuwar da yake yi mata, kana ta ɗaura da faɗin
"Har kun dawo daga Dass ɗin inasu Abbu'n naku?".
Zamansa ya gyara yaɗan kishin giɗa gefen sa da jikin kujerar
A hankali kamar wan da a ka sa dole yayi maganar yace
"Suna can wancan tsohuwar bata gama yi musu bitar fitina ba".
"Kaci gidan ku Inna'r ce mai bitar fitinar? haka za'a faɗa wa naka iyayen".
Baki ya taɓe yazaro wayarsa yasoma latsawa,ita kuma tamike taje ta kawo masa drink da perpesun kaza wan da yaji kayan kamshi da ɗan-ɗano. Drink ɗin kawai yasha yaɗan zamo bakin kujerar tare da duban a gogon dake ɗaure a hannunsa yace
"Bari nashiga gun Ummi mugai sa".
Mamie tace
"Toh daga gun zaku wuce da HAMDAH kenan?".
ɗan jimm yayi sai kuma yaɗa go yace
"HAMDAH?". yayi tanbayar da fuskar mamaki, dan shi ƙwata-ƙwata bai masan bata can gidan nasa ba, to yaushe nema tazo? yayi ƙwafa a file.
Da mamaki Mamie ke kallonsa kana tace
"Eh ita ko kana nufin bakasan tana gidan nan bane yau ƙwana biyu". Sumar kansa ya shafa izuwa
bayan keyarsa.
Mamie kuwa kallon tuhuma tabisa da shi kana ta ɗaura da faɗin
"Kenan kana nufin bakama san bata gidan kaba?".
Yace "To Mamie ya za'ayi tafita bata sanar min ba har ƙwanan ta biyu, in badun nan ɗin tazoba ba, irin haka ba sai tasa mutane wahala ba aje a ta niman ta in wani gun taje ba nan ɗin ba".

Baki Mamie tabuɗe tana kallon sa har yakai karshen maganar sa wan da duk maganar da yake ida nunsa nakan wayar hannun sa dake ta faman latsawa,
Da muryar faɗa Mamie tace
"Kai bakaji kunya ba a kuya a ka ɗaure maka a cikin gidan naka? yau ko a kuyace ka mata rikon ko oho. yarinya tabar gidan ka tsawon ƙwana biyu kuma kana gidan amma baka saniba? to taya za'ayi tanimi izinin fita a gurin ka bayan baka masan tana gidan ba".

Mikewa yayi yana faɗin yarinyar nan fa bajin magana takeba, to koma mene ne Mamie sai tafita ba tare da tasanar ba, taya zanyi nasan tafita tun da bata faɗa ba".

"kadai gyara mu'a malan gidan ka dan wannan dai ba halin kirki bane nafa maka kenan".

Kofa yanufa batare da yakuma cewa komai ba yafice daga part ɗin,
Da sallama yashiga parlour'n Ummi
Ummi da fito warta daga kitchen kenan rike da tray mai ɗauke da foodflaks, ta amsa masa fuska ɗauke da murmushi tana faɗin "maraba".
Yakaraso ciki ita kuma tawuce saman dinning area ta aje tray'n,ɗaya daga cikin kulolin dake saman tray'n ta buɗe tuwon farar shinkafa ce sai tiriri yake da alama ba'a jima da gamashi ba, taciro malmala ɗaya tasaka cikin plt, kana tabuɗe ɗayan kular miyar ɗanyen kuɓewa ce wacce taji busashen kifi da nama sai tashi da daddaɗan kamshi yake,tazare laidan tuwan tazuba miyar a gefen tuwan,
kana tabuɗe wata ƴar karamar kula soyayyen man shanu ne a ciki tasulalashi kan tuwon ta saka spoon cikin plt ɗin,sannan taje tabuɗe Fridge da ke nan saman dinning ɗin taɗau gorar ruwa haɗe da cup ta ta kwasosu tasauko cikin parlour'n tadire shi gabansa.
Sau kowa yayi daga saman kujera yazauna kasan carpet yana faɗin
"Sannu da ai ki Ummi".
"Yauwa". tace tare da duban kofar kitchen tana murmushi dan tasan ba ita tayi girkin ba HAMDAH ce ita nata kwasowa ne.


Kafafun sa ya tanƙwashe yamaso da plt ɗin a bincin gaban sa yayi Bismillah yasoma ci, suna ɗan taɓa hira kamar yan da suka saba a koda yaushe idan yazo gai data.
Sosai yaci tuwon har yakusa cinye malmala guda kaɗan yarage yatura plt ɗin gefe yakara da ruwa.
mikewa yayi yakoma kan kujerar yana dai-dai ta zaman sa yayi gyatsa tare da faɗin "Alhmdllh Ummi sannu da ai".
murmushi Ummi tabishi da shi dan tana matukar jin daɗin duk san da yazo tabashi a binci ko a koshe yake sai ya taɓa ko kaɗan ne,hakan kuma halinsa ne tun yana yaro har kuma yanzu bai fasa ba.
Mikewa tayi taɗau plt ɗin tanufi kitchen tana a je plt ɗin tafito tashiga bedroom.

Jin motsin ruwa a bayi sai tamaso kofar bayin ta bubbuga tana faɗin
"Ke HAMDAH fito da alla tun ɗazu wanka yakici yaki cinyewa canza fatar zaki".
Fita nayi daga cikin ruwan da najima zaune a cikin sa, tun ɗazu nagama wankan ina dai zaune cikin ruwan ne kawai".
naɗauro towel tana tsaye a bakin kofar har nafito,
tace
"Maza jekisa kaya kizo ga yayanku can yana jiranki kada ki ɓata masa lokaci".
baki na turo zanyi magana tayi saurin cewa
"Kiyi hanzari kije ki shirya kafin Abba'n ku yazo yasa meki".
tajuya tafita.

Na isa in da jakata yake nasoma shirin cikin tura baki.ina gamawa na yafa gyale naɗau jakata nafito yana ganina yamike tsaye yana faɗin
"Sai da safe Ummi".
"Allah yabamu alkhairi".
tafaɗa tana mikewa,
Yana gaba ina biye da shi har in da yafa motar sa ya shiga mazaunin driver niko naboɗe gefen mai zaman banza nashiga yayiwa motar key muka fice cikin gidan.


Muna isa nasa hannu na buɗe marfin nafita da sauri kafin nagama fita daga cikin parking lot najiyo muryarsa daf da ni
"Idan kina wasa kisake sakafa kifita!".
yana kaiwa nan yagota ta gefena yawuce.
Numfashi nasauke jin iya nan yatsaya da sauri na nufi ciki.


Washegari Monday bayan dawowata daga makaranta ko uniform ban cire ba Rufa'ila tazo kira na,
tare muka koma da ita side ɗin Na'ima
Naɗau sintsiya nasoma shara kamar koda yaushe.


Motar mijin Aunty Rafee'at ne yafaka kofar gidan Ya SALEEM akofar gidan ya sauke ta yawuce ita kuma tashiga cikita,
Direct side ɗin HAMDAH tashiga tun daga bakin kofar parlour take sallama har tashiga ciki tarika sallama jin shiru yasata wucewa cikin bedroom,
Nan ma shiru har kitchen tashiga ganin dai bata sashin gaba ɗaya, sai tafita tanufi side ɗin Na'ima tana sa kafarta cikin parlour'n tayi arba da HAMDAH tana mopin Na'ima kuma na hakimce saman kujera tana danne-dannen waya.

Raguwar sallamar da bata karasa shi ba kenan,
Na'ima taɗago cike da makirci tace
"A'a yau manyan ba'ine a gidan namu sannu da zuwa".
Aunty Rafee'at tagirgiza kai tabita da kallon makira a tafin hannuna kike.takaraso ciki tazauna kana tasaki murmushi tana faɗin
"Yauwa sannun ki".
Mopar nasake kasa cike da murnar ganin ta nanufi in da take ina faɗin
"Oyoyo Aunty Rafee'at".
Harara ta sakar min sai tamayar da kallonta kan
Na'ima da take cewa
"Rufa'ila kawo mata ruwa".
"A'a barshi wlh a koshe nake".
Aunty Rafee'at tafaɗa tana mikewa.

Tanufi kofar fita nabi bayanta da sauri muna fita daga cikin parlour'n taruko hannuna
Bata tsaya ko inaba sai bedroom ɗina
a bakin gado ta zauna ganin haka nima na zauna,
Hannu tashiga nunani da shi tana faɗin.


"Menake gani haka HAMDAH yaushe kika dawo ƴar wanke-wanke da shara?, tana zaune kina yimata ai ki HAMDAH. daga yau kada nasake gani ko jin cewa kina yimata ai ki, ko tasaki kice bazakiyi ba".
Ido na waro
"Aunty Rafee'at Ya SALEEM fa shi yakece nayi mata".
Da mamaki ace
"Ya SALEEM ɗin".
Nace "Ai in ta kirani tace nazo nayi mata shara in naki sai yace nayi".
Shiru taɗanyi sai kuma tace
"Ina sai in yana nan ne yakece kiyin ko shine yake kiranki kizo kimatan".
nace
"A'a ita ne".
tace
"To ko takirakin kada kije tun da sai in takirakin kafin yakece kiyin, kuma bari kiji matsayin ki da nata ɗaya ne a cikin gidan nan, ke kinma fita matsayi
da iko da gidan nan ke matar sa ce kuma jinin sa,ita kuma aure ne kaɗai
ya haɗa su, nan gidan kine ke yakamata kisa wasu ba a sakiba
kikula HAMDAH!".


Ranar wuni Aunty Rafee'at tayi bata bar gidan ba sai dare.

★★★

Bayan ƙwana biyu

Ina zaune a parlour Aunty Na'ima tashigo cikin parlour'n kamar wan da a ka wurgota tana zuwa ta kai hannu ta............



😂🤗 *Wasa farin girki yanzu za a fara wasan*




*Zakujini shiru na ƙwana biyu daga kan gobe Alhamis zuwa ranar Monday saboda bikin da zamuyi daga kan gobe zuwa ranar Lahadi kafin mugama so sai ranar Monday zakujini inai ma kowa fatan alkhairi*👏🏻


*Sai a hankali banyi editing ba*👌🏻




Mommyn Twins ce







*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*


My no 08034690723



*Sadau karwa gare ki My sisi ƴar'uwa rabin jiki Aunty na na kai na ZAINAB S DIRECTOR*🥰🤗



🅿️11



Tabigi cokalin da naɗibo a binci zan kai bakina,da sauri na mike tsaye naɗan ja da baya. cikin masifa tanunani da hannu ta ce
"Ke har kin isa nace kizo kice baza kizo ba. yau ƙwana biyu ina turawa a kira ki kiki zuwa, bayan kin san ai kin kine. tukun na yau zan tura kizo kice wai baza kizoba, ke har kin isa nasa doka cikin gida na, ki ketare?.
Oya wuce kije kiyimin shara ke bari ma jiki har bedroom ina yau sai kin gyare".

She ke-ke nake kallon ta sai kuma nasaki wata ƴar karamar dariya ganin yan da take maganar tana wani girgiza wane mai shirin yin rawa.
sai kuma na gimtse dariyar na ce
"Nifa ba ƴar ai ki bace, gacan ƴar ai kin ki Rufa'ila jeki sata tayi miki dan ni daga yau bazan sake yiba,
Kuma dai gidan nan a iya sanina bai zamo nakiba ban san dalilin da yasa kike son dan gan ta kanki da abin da ba naki ba,
Idan can dakike zaune a cikin sa an am bace sa da naki, tofa ba shi zai sa yazamo nakin ba,
gida na Ya SALEEM ne kuma nasan kinsan meye matsa yin sa a gurina,
Idan can yazamo naki to nan nawane".
Ina kai wa nan najuya da sauri nashige bedroom na Mai da kofa na rufe.

Ina jinta tarika zazzaga buhun a shar da wasu irin muggan kalaimai wan da a karancin shekaru na nagaza iya fassara su.
da fari magan-ganun nata sunata yimin yawo cikin ƙwaƙwalwa daga bisani na watsar da su.

Fuuu tafice cikin parlour'n takoma part ɗin ta da bakin ciki da tarin takai ci,
A parlour tarika zarya takasa zaune takasa tsaye, tayi mamakin jin waɗannan magan ganun a bakin HAMDAH.


Zuwa can kuma tanimi guri tazau na tana girgiza kafa
Abin da bata taɓa zoto da tunani a rayuwar taba
shine zuwan wata mace cikin gidan SALEEM a matsayin matar sa, amma sai gashi yau har HAMDAH na kokarin dan ganta kanta da wani sashi na gidan a matsayin nata, bayan nan kuma har take faɗa mata tasan matsayin sa a gurin shi.
Wannan batu yagirgiza Na'ima ba kaɗan ba sai dai a bin da take tunani kan maganar HAMDAH ko kaɗan a gunta ita a bun ba haka yake ba,salon maganar HAMDAH ce dai bata fahimtaba, dan ita dan gan takar ƴan uwan taka take nufi bana aure ba.

Tunani daban-daban suka rika zuwar mata
har tafara tunanin to ko SALEEM yafara saurarar tane bata saniba tana nan ta buɗe baki a na can a na cin a manan ta,
Saurin kawar da wannan tunanin tayi tamaye gurbin hakan da tabbacin cewa SALEEM bazai taɓa sau rarar taba sai dai zata daɗa sa ido sosai,
zata kuma ɗau mataki bazata taɓa bari wata mace ta rabi mijin taba,
duk da yau karon farko HAMDAH ta dirar mata da wani a bu a cikin zuciyar ta mai suna fargaba......



Tun daga ranar bata sake turowa a kirani ba, sai dai cikin zullumin gamuwar mu da shi nake dan nasan iyanzu ta sanar masa, nayita zuba ido dan jin kiran uban gayyar wato Ya SALEEM ɗin jin shiru sai na sake a bina......
tun daga lokacin harkar karatu na nasa a gaba baji ba gani.

Haka rayuwa taciga ba da tafi, kamar yanda Abbu yayimin alkawari su Fauzan suna samin hutu a ka kawo min su,har sai da hutun su yakare kafin suka koma, duk kuma karshen sati suna zuwa min wato Saturday and Sunday.


Haka dai ƙwanaki suka taja suna juyawa izuwa maƙwanni maƙwanni izuwa watanni.

★★★

*Bayan wata 6*


Zaune suke gaban wani kasurgumin boka sun naɗe kafa sunyi tsit wani masu ɗaukar darasi, sun zuba wa wata faranti da ƙwarya dake gabansa ido.
shiko bokan sai zane-zane yake kan kasan dake cikin farantin idan ya zana sai ya goge yasake zana wani, yayin da hannun sa ɗaya kuma ke rike da wani gashi yana bubbuga ƙwaryar,
Lolaci zuwa lokaci sai ya zaro ido tare da sakin dariya.
Raliya da Na'ima kuwa sai su kalli yuna su girgiza kai sukuma gyara zama, dan sun yar da da ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login