Showing 81001 words to 84000 words out of 92896 words

Chapter 28 - HAMDAH part 1 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

11917

bari idan na koma nakuma fitowa da shirin zuwa naku gidan, maganan nu kawai".
hannunta da aka ɗaura mata ruwan narike ganin tana faɗan tana ɗagoshi gashi maganar ma da ka ganshi kasan cikin karfin hali take nace
"Inna kinga sun fita ma ki sai da hannunki kar ya goce"...
to kawai tace min bata kuma yin magana ba zama nayi a bakin gadon ina rike da hannunta a hankali tarufe idanunta nan bacci ya ɗauke ta,
ido na ɗan zuba mata sai naja wani dogon ajiyan zuciya jinsa kawai nayi batare da nasan da zuwan saba,sai na daɗa rike hannunta da kyau.
kaf ɗakin sai da suka juyo da kallon su gare ni Abbu yace
"Menene HAMDAH wani abun ne?".
kai na girgiza masa da sauri nace
"Ba komai".
sai kuma nayi hawaye yacika min ido har suna kokarin zuba cikin dabara na ɗago bakin gyalena nataro waɗan da suke son zubowa, ina ɗago kaina karaf muka haɗa ido da Ya SALEEM ida nunsa a kai na da fuskar tambaya, murmushi nayi ina gyara zama na yayin da naji wasu hawayen suna kokarin zubowa haka kawai narasa dalilin da yasa nake jin hawayen da kuma son yin kuka,
hannun ta na aje kan gadon naɗan gyara na tokare shi da mayafin ta ta in da zai zauna dai-dai ruwan yasa mi damar shiga yadda yakamata.
sai namike naɗan ja gyalen kaina yaɗan kare fuskata sai na nufi kofa.
Ina fita da sauri nayi ta bayan room ɗin in da wasu kananun bishiyoyi ke jere nashige cikin su da sauri ina toshe bakina jin kukan nason kwace min..

Ina shiga nasaki kuka mai tsuma zuciya cikin yin kasa da sauti..
ganin sa kawai nayi a gabana yanaɗe hanyayen sa a baya yazuba min ido,da sauri na ɗago ina duban sa hawaye naciga ba da zuba a idanuna.
"Me yasa ki kuka?".
yajefo min tan bayar idanunsa a kai na,
kai nashiga girgizawa sai nafaɗa jikin sa ina faɗin
"Nima ban sani ba ban sani ba bansani ba Ya SALEEM".
nafaɗa cikin muryar kuka sosai.
a sannu yazaro hannayen sa dake goye a bayan sa yazagaye ni da shi shiru yayi batare da yace komai ba yayin da zuciyar sa keta bijiro masa da yanayin ta na ƴan kwanakin nan, numfashi yasau ke yadaɗa rungume ni sosai kana a hankali yafurta
"Ya isa kiyi shiru haka duk san da kika ji tsoro ko wani abu maka mancin haka kirika furta innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kinji".
kai na gyaɗa masa tare da soma nanata karmar cikin zuciya ta da fatar bakina,
a hankali yatallafo kaina yasaka ƙwayar idanunsa cikin nawa dasuke siyayar da ƙwalla, sai ya girgiza min kai idanuna na ɗan lumshe hawayen da suke ciki suka zubo kana na buɗe su a kan sa a hankali yamaso da fuskar sa daf da nawa sai ya sauke kyawawan lips ɗin sa kan nawa, yazuro harshen sa yakamo lip ɗin na na kasa yaɗan tsosa sai ya zura harshen cikin baki na sai da ya tabbatar da yasai da kukan da hawayen kafin yazare harshen sa. gaba ɗayan mu fitar numfashi'n mu sai da yasau ya cikin ɗan lokacin.
tafin hannunsa yasaka kan fuskata yashare min hawayen da ke kwance kan fuskar kana yaruko
hannuna muka koma cikin room ɗin.
har lokacin Inna tana bacci Mamie da Ummi ne kawai muka tadda cikin ɗakin su Abba sun tafi masallaci,hannuna yasake shima yanufi masallacin...

Har dare muna asibitin sai bayan sallar isha muka koma gida badun naso ba dan cewa nayi ni a nan zan kwana Abbu yace mutafi ga goggo Hauwa da Mamie su zasu kwana,
har muka isa gida hankali na nacan asibiti gun Inna babu abun da yafi tada min hankali in da naga haka ta wuni a kwance bata kuma ci komai ba, da yammacin ma ɗan hirar da idan anayi tana ɗan amsawa shima ta daina tana dai kwance.
haka ranar nakwana da tunanin Inna.
Washegari da sassafe naje ni side ɗin Ya SALEEM da sallama natura kofar bedroom ɗin sa nashiga
yana zaune a bakin gado boxes ne kaɗai a jikin sa, Na'ima na kwance a gefen sa ta wani ware kafafu daga ita sai zani shima ɗin ba a ɗaure yake ba rufe jikin ta tayi da shi.
kallo ɗaya na musu daga su har gadon da suke kai wan da bedsheet ɗin sa ya yamutse, na kawar da kai na gefe sai kuma na juya da sauri na koma da baya,
wani dogun tsaki Na'ima taja tare da faɗin
"Ya zaki shigo wa mutane ɗaki kai tsaye haka ba sallama in da kin shigo kin sami mutum cikin wani yanayi kuma kice me da alla malama kidai na faɗo wa mutane ɗaki kai tsaye haka".
ban ko tankata ba sai handle da na kama nabuɗo kofar.
muryar sa najiyo yana faɗin
"Wani abun ne *HAMDAHHH*?".
"Dama gurin Inna zani".
nafaɗa ina ficewa daga cikin ɗakin.

Ina komawa part ɗina bayi nashiga nayi wanka nafito nasoma shiri yayin da nake jin wani bakon lamari can cikin kasan zuciya ta,tun ganin da nayiwa Ya SALEEM da Aunty Na'ima naji wannan abun a can kasan zuciya ta.
cigaba da shirina nayi ina gama sa kaya nayafa gyale na isa gaban mirror inda na aje wayata na ɗauka ina juyowa, yanaturo kofar yashigo,
kafe ni da ido yayi niko nayi saurin kawar da kaina daga kallon sa, a sannu yatako ya iso gabana yaruko hannuna yana ɗan murza shi yayin da idanunsa ke kaina ya kafe ni da su kamar maison gano wani abun a hankali yafurta
"Ina zaki na ganki da mayafi?".
da sauri na ɗago na dube shi sai kuma nakuma kawar da kai na, wato ma bai san ina zani ba ko ba ɗanzun nan naje nace masa zani gun Inna ba, sabo da yana tare da matar shi dole ya mance mema nace.
"Ke tambayar ki nake?".
baki na turo gaba nace
"Asibiti gun Inna".
nafaɗa a takaice ina kuma janye hannuna daya riƙe.
wannan kallon yaci gaba da bina da shi kana yace
"Baza kije ba kijira na dawo nakai ki yanzu Na'ima zan kai unguwa sai in mun dawo".
Wani irin waro ido nayi yayin da abun da nake jinsa can kasan zuciya ta yakaru, da sauri naɗa go kaina na sauke idanuna cikin nasa sai kuma na juya da sassarfa nafaɗa kan gado da ciki tare da sakin kuka.
da sauri ya nufoni yaɗa go ni yana faɗin
"Ke baki da hankali ne akan cikin zaki faɗi!!!!!".
fizge-fizge nashiga yi daga rukon da yayi min cikin muryar kuka nace
"Ni ka kyaleni ka sake ni kaje gurin Na'ima ka kai ta ni ko baka kai ni ba ni nasan hanya zanje"...
cigaba da kokarin kwace kaina nake,
yace
"Ke ki nutsu, kinutsu nace!!".
yakuma faɗa cikin tsawa
sai da fizge-fizge'n da nake nayi sai hawayen dake zuba a ido na,yaci gaba da magana cikin kakkausar murya
"Kiyi wasa da komai banda wannan".
yafaɗa yana nuna cikina. sai kuma ya sassauta muryarsa yasan ya idanunsa cikin nawa yana yi musu wani irin kallo kamar wani abun yake son gani cikin su, sai kuma yasaki wani murmushi'n gefen baki kana yakuma gimtse fuska.
sannan yace
"Cewa nayi kijira mu dawo ko baki gane abun da na faɗa ba ne?".
idanuna na lumshe hawaye suka zubo kana a hankali na zame jikina na kwan ta gefe batare da nace komai ba.
shiko mikewa yayi yafita...
ina jin tashin motar sa sai naji wani kuka yazo min sai dai ban bashi damar fitowa ba.
najima sosai a ƙwance jin wuyana ya hure na mike jiki a saɓule nanufi side ɗin sa nashiga kitchen natsiyaye suwan shana nasha kana nakuma tsiyayar wani a cikin cup nafito rike da shi dan nasan anjima zan buka ceshi,
ta babban parlour nabi dan yafi sauke shi ba zagaye bane ina shiga cikin parlour'n na hangi Na'ima zaune Rufa'ila na masa mata kafafun ta,
da mamaki nakalle ta ita da suka fita ya akayi kuma na ganta zaune anan.
dogun tsaki taja wan da yadawo dani daga tunanin da natafi,nazo daf zan gota su takuma jan wani tsakin tace
"Munga farkon sa zamuga karshen sa!".
ko in da take ban kuma kalla ba nawuce abina.
sai dai har nakoma cikin bedroom Ina nanata kalmar da tafaɗa
"Ko me take nufi"
nafaɗa a fili sai kuma na kawar da zan cen ma da faɗin
"Ko ma me ita tasani"...

Haka nayita jiran Ya SALEEM har yamma bai dawo ba sai daf magriba najiyo shigowar motar sa,
bai shiko side ɗina ba kuma sai bayan sallar isha.
koda naji knocking a hankali na mike dan yanzu bana barin kofata a buɗe har in ba yana waje na bane, in muna tare shine zaka sami kofar a buɗe yana fita kuma na kulle.
jin shine yasani buɗe kofar kafin ya shigo najuya nakoma bakin gado, yamai da kofar ya rufe yatako in da nake yazau na gefe na yaɗan sauke numfashi alamun gajiya kana yace
"Mun dawo dare kuma yayi yanzu sai dai gobe ke ma na kai ki in da zaki je ɗin".
kallon sa kawai nayi ban ce komai ba, janyoni yayi jikin sa kana yace
"Ko kin hakura da tafiyar ne?".
yafaɗa yana tura hannunsa cikin rigata ta yacaf ko ababen kirjina yashiga wasa da su.
nan ma shiru nayi tare da cuno baki gaba.
"To shike nan tun da goben ma kin hakura".
yafaɗa tare da curo hannunsa yayi sama da rigar baccin jikina sai ya kwantar dani da baya ya kafa bakin sa kan ababen kirjina yashiga tsotsar ko wannensu,yaɗau lokaci yana tsotsar su kana ya zare bakin sa yana mai da numfashi.
a sannu ya mike yafita yana fita naje na kulle kofar na dawo na kwanta....

Washegari da safe yashigo cikin shigar kananun kaya sai kyalle yake kamar tauraru. kamshin sa na shaka tare da lumshi idanuna
"Muje ko".
yafaɗa yana janyo ni jikin sa, fuskata na cusa cikin kirjinsa ina shakar kamshin sa.
leko fuskata yayi yace
"Ok na tuna ma kince yau ɗin ma kin haku ra ko".
da sauri na ɗago tare da make kafaɗa, sai na zame a jikisa na ɗau gyalena muka fita...

Koda muka iso cikin asibitin sai naga yabi tawani hanya ba ta inda shekaran jiya muka biba, da mamaki nake kallon kofar room ɗin da muka iso,ganin yashige ciki yasani bin bayan sa da sauri,can na hango Inna ƙwance da alama bacci take sai goggo Hauwa zaune akan kujera a gefen ta,
su biyu ne rak cikin room ɗin, da sauri nakaraso bakin gadon nace
"Goggo Hauwa ya jikin Inna yaushe kuka dawo nan ɗakin kuma??".
tace
"Yau kam jikin ta alhmdllh bakamar na jiya ba ai tun shekaran jiya bayan fitar ku jikin yafara birkice wa, jiya kuwa jikin yabir kice sosai amma yau gashi har ta sami bacci".
numfashi nasau ke tare da mai da kallona kan Inna tayi wani fayau da ita fuskar ta yayi wani haske hancinta yadaɗa fito wa yayi zarr da shi.
Ya SALEEM ya gaida goggo Hauwa da tan bayar ta ya mai jiki kana yajuya yanufi kofa tare da ɗaga kiran da yanzu yashigo wayar sa.
juyowa nayi nace
"Goggo Hauwa su Abba fa".
tace
"Suna can waje ai wannan room ɗin ba a barin mutane cikin sa sai mutum ɗaya kawai".
kai na girgiza jin hawaye yacika min ido nace
"Ayya goggo Hauwa shekaran jiya taci abincin kuwa?".
"Shayi kawai tasha garama jiya da yamma da jikin yaɗan lafa SALEEM ya kafe sai da ta ɗan ci wani abu".
da mamaki nace
"Jiya Ya SALEEM yazo nan ne?".
tace
"Ai tun safe da shi muka wuni anan shi yasa aka canza mana ɗaki ma".
numfashi na sauke kana na mai da kallona kan Inna datake ta baccin ta...
ban bar ɗakin ba har sai da naga farkawar ta har muka ɗan yi yira duk da muryar ta baya fita sosai...

Har yamma muna asibitin ina kuma room ɗin tare da Inna, yau nayi iya bakin kokari na wajen danne kukan da nake ji irin na shekaran jiya da zarar na ji kukan sai na shiga nanata kalmar da Ya SALEEM yace narika faɗa aduk san da naji kukan wato innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un. karshe dai ranar goggo Hauwa fita tayi tabar ni kasan cewar tsarin zama kan mai jiya nacikin room ɗin mutum ɗaya ne. sai daf magriba Ya SALEEM yashigo shi da su Abba yace mutafi,
sai a lokacin naji kukan na kokarin kwace min,kallon Inna nayi nace
"Inna zamu tafi sai da safe Allah yakara sauki".
amin tace tana bina da murmushi har nakai bakin kofa sai naku dawowa nace
"Inna sai yaushe ne zaki ci abincin kince sai anjima gashi har dare yayi tun ɗazu fa kika ci kikara yanzu".
tace
"Zanci anjima kafin nayi bacci yan zu bana jin yunwa".
kai na gyaɗa tare da faɗin
"Allah Inna kinga yanda kikayi wani haske kuwa yau".
murmushi tayi kana tace
"Ai dan baki sanni a kuruciya ta bace fara ce ni soll dai na ganin hasken da kike dashi ɗin nan nafiki haske da nake kuru ciya ta yo duniya ce kawai me mai da akawu kuku,
ai ko mai sunan malam ma kyan mai tunan nashi yaɗau ka, dan Malam kyakkyawan mutum ne gashi ya samma mai sunan shi".
dariya dukan mu mukayi abin mamaki har da Ya SALEEM da ban taɓa jin dariyar saba da sauri na ɗago na kalleshi fatabarakallah masha allah.
ajiyan zuciya na sau ke jin kukan yakuma taho min cikin dariyar da nake nan kuma hankalin su yadawo kaina da jin doguwar ajiyar zuciyar da na sauke wan da yafi na shekaran jiya tamkar wacce akayi wa dukan tsiya tagaji da kuka,
juyawa nayi ina kokarin barin gurin sai naji ta ruko hanuna a hankali najuyo gare ta,
murmushi takuma yimin kana tace
"Kiyi hakuri da rayuwa a duk in da tazo miki ki karɓi ƙaddara mai kyau ko mara kyau jiki a ranki Allah shi ya ɗaura miki kuma shi zai yaye miki,
duk inda rayuwa tazo miki kada ki mance da Allah kada kiyi ammafa ni da juyawar rayuwa ki jefa kanki cikin halaka duk musulmin kirki godiya yake wa Allah idan jarabawar rayuwa tazo mishi, mai kyau ko mara kyau,ki gode masa sai yayi miki zaɓi da sauyi nagari,a duk san da kika ji fargaba cikin ranki kirika nanata kalmar innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un zaki sami sassaucin lamuran ki".
tun da Inna tafara maganar hawaye ke wanke min fuska sai na rike hannunta da karfe ina kokarin fashewa da kuka
tayi saurin cewa
"Yoo kujimin yarin ya meye kuma abun kukan je kutafi sai da safe".
kai na gyaɗa mata hawaye nacigaba da zuba a ido na Ya SALEEM yaruko hannuna muka fita ina zama cikin mota sai na fashe da kukan yajuyo da sauri yace.......!★





*Free page saura kiris ya kare*




Mommyn twins ce


🌺 *HAMDAH*🌺




*Na*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



_BOOK_ _ONE_



Free page


My no 08034690723



🅿️31



_Sanarwa sanarwa sanarwa🗣️🗣️ ina ɗauke muku da wani daddaɗan albishir💃 wata baiwar Allah ta biya kuɗin karatun book ɗin nan wa mutane 25 tace na sanya mutane 25 a cikin group ɗin da zaku rika samin littafin batare da sisin kuba burin ta kawai kuyi mata addu'a fatan samin nasara ga abin da tasa gaba. dan haka nake yimuku albishir duk wan da Allah yasa da rabon sa ya biyo ni pc idan kuma ka makara shikenan barabon ka bane_😅






Yace "Menene na kukan daga anyi miki nasiha sai ki kama kuka ke baƙya gajiya da kuka ne?".
kai na haɗa da guiwa naci gaba kuka na wan da nake jin sa har cikin raina. tada motar yayi kana yajuyo ya dube ni tare da faɗin
"Ya isa". da sauri na ɗago kamar an zabure ni na kalleshi hawaye tap idanuna sai na juya da sauri na ɓalle marfin motar nafi ina faɗin "Ina zuwa dan Allah Ya SALEEM".
nafaɗa ina fita a motar da sauri nanufi cikin asibitin ina ji yana kira na ban ko juyo ba...
ina isa bakin kofar room ɗin da Inna take ciki na tura kofar da sauri nashiga,juyowa su Abbu sukayi da su Ummi da suma suka shigo yimata sallama zasu tafi, Inna ta ɗago idanunta tare da yafato ni da hannu da sauri na zo in da take sai ta riko hannuna tace
"Baku tafi ba kai mai sunan malam me kuke jira dare fa nayi".
juyawa nayi jin tana maganar tana kallon kofa, lokacin yake mai da kofar yarufe yakara so ciki,maganar tace tasani juyowa gare ta
"Wannan haske da kema kika kara bayamma ce kawai ai gashi ya bayyano kansa gasu a hannun ki sun fito raɗa-raɗa,bari cikin yayi wata 6 zan zo na ɗauke ki mutafi kisha magani har sai kin haihu,yoo ai ba'a wasa da wannan cutar faraɗ ɗaya yake kashe jariri dole kisha ganyayya ki".
tafaɗa tana jujjuya hannuna,
baki Ya SALEEM ya taɓe tare da faɗin
"Ku wai har yanzu bazaku dai na wannan al'adar takuba garin jinya a kwaso wata cutar".
sai kuma yayi kasa da murya
"Babu inda zata bare aje garin yin wani jinya akashe min ɗaya da wasu gangayya ki".
yayi maganar ne a iya laɓɓansa bai san yafito ba.
murmushi Ummi tayi dan tasan yayi maganar ne batare da sanin yafito ba,
Abbu kuwa dakuwa yayi masa yace
"Kaci gidan ku shine mu bamu mutu ba".
"Shi kanshi ma dai da bai mutun ba".
cewar Mamie,
Inna tace
"Rabu dashi yoo kai ɗin badun taima kon Allah da ganyen ba da kakai nan,kai akwai wan da yakai ka laulayi ma haka a ka haifo ka fari soll da kai jiki duk bayamma kayi ta wahalar da mutane, ai idan ɗan naka yayi gadon ka kam wannan ƴar tashiga uku,bari ma kaga a sallame ni in zan koma tare zamu koma da ita,a tare cutar da wuri tun kafin ɗan naka yazo duniya ya wahalar da mutane".
Mamie tace
"Ai kam dan ita tasha wuyar ka tun ranar da kazo duniya har kayi arba'in".
murmushi nayi dan natuna wani rana Inna tataɓa yimin hirrar har take faɗa min ma ita ta yayeshi.
shiko fuska ya gimtse ganin su Aunty Rafee'at suna dariya,
Inna ta dube ni da murmushi tana faɗin
"To kuje sai da safe,kai kuma mai sunan malam gobe kazo min da farin goro".
sai kuma ta kuma mai da duban ta kai na taci gaba da faɗin
"Idan rayuwa ya juyawa mutum baya kada ya mance da Allah shike yaye da muwa da kunci,duk abun da yasa mi bawa da sanin uban giji,ina daɗa faɗa miki kada juyawar rayuwa tasaki mance wa da Allah kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login