Showing 87001 words to 90000 words out of 92896 words
shiga zubowa Mamie tace
"HAMDAH duk wani wan da kika gansa a duniyar nan tofa karshen sa kenan yanda mukazo da ɗai-ɗai haka zamu koma lokacin Inna ne yayi mutuwa akwai zafi amma hakuri shine maganin".
Zuwa yanzu bana gane mema take faɗa da sauri na nufi kofa ina ji tana kira na tuni nayi waje da gudu na nufi side ɗin Inna,
a guge nafaɗo cikin parlour'n har lokacin mutane na nan dam dan sai karuwa mutane suke daɗa yi,
ɗakin Inna nashige da gudu nafaɗa saman gadon ta sai a lokacin naji wani irin kuka sai kawai na fashe da wani irin kuka mai karfi cikin sananin tashin hankali.
Hankali tashe su Ummi da wasu daga cikin mutanen da suke zaune cikin parlour'n suka rufamin baya Ummi na kokarin hanani kukan,
wata ƴar baffan su Abba Aunty Halima tace
"A'a kada ki hanata kuka kibar ta tayi shine samin sassaucin zuciyar ta, ɗazu ai kasa yin kukan tayi barta tayi kukan zuciyar ta zai ɗan sami sassauci"...
kukan nake babu kakkau tawa har numfashi na nawani irin tafiya yana dawowa kamar zan shiɗe...
nakai tsawon awa guda ina kukan zuwa lokacin har muryata ta toshe bata fita da karfi. sai a lokacin suka shiga rarrashi na amma ina bana ko jin abun da suke fa....
A ɓangaren Ya SALEEM kuwa yanzu da muwar sa ta kasu kashi biyu,har suka isa makabarta yana tunanin yanzu wani hali take,ɗaya ɓarin zuciyar tasa kuwa ɗin bin damuwar rashin Inna ne aciki,
Kakar su abin alfaharin su yau sun rabu da ita rabuwa na har abada.
har aka kamla bisu suka juyo yana alla-alla ya'iso gida yaga awani hali take yanzu.
koda suka iso gida kan cewar har lokacin da mutane a kofar gidan ga waɗan da suka dawo daga makabarta sai ya faka motar a in da yafaka ɗazu yafito yashiga cikin gidan da sauri,
direct part ɗin Mamie yawuce ganin basa nan sai ya fito ya nufi part ɗin Inna,
haka yakusa cikin jama'ar yashige ɗakin inda yake jiyo sautin kukan ta,
nan ya iske su Ummi suna ta faman lallashin ta a sannu ya raɓa gefen su suka bashi hanya yakarasa bakin gadon,
" *HAMDAHHH*".
yakira sunana a hankali,ban amsa ba sai dai sautin kukan da naɗan rage dan zuwa lokacin wani irin masifaffen ciwon kai nake ji,
a sannu ya mika hannu yakamo nawa yaɗa go ni zaune, idanuna sunyi wani irin kunburi sabo da sabar kuka har bana iya buɗe su duka.
hannun nawa yarike da kyau yaɗan jawo ni na sauko a gadon, kana yanufi kofa yana rike da hannuna har lokacin kukan nake muka fice daga cikin side ɗin gaba ɗaya.
haka mukayi ta gilmawa cikin jama'a duk wan da ya kallene sai ya kuma kallona da fuskar tausaya wa,waɗan da suka sanni kuwa faɗi suke
"Dole kiyi kuka".
ɗakin shi nada dake ta nan farfajiyar gidan yanufa da ni a cikin makullan dake haɗe dana motar sa yazura ɗaya daga cikin su yabuɗe kofar,
muka shiga, ɗakin tsaftsaf kamar da mai kwana cikin sa sai tashi da daddaɗan kamshi yake.
a bakin gado ya zauna tare da zaunar dani a jikinsa ya..........!★
*Free page saura kaɗan yakare waɗan da basu biya ba su hanzar ta*
Mommyn twins ce
🌺 *HAMDAH*🌺
*Na*
*RASHEEDA S DIRECTOR*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
_BOOK_ _ONE_
Last Free page🙌🏻
My no 08034690723
_Wannan page ɗin ɗungurugum ɗin sa sadau karwa ne ga ƴan group ɗin HAMDAH Shalele Fans_🥰🤗 _walla bani da bakin yi muku godiya_
*_jinjina gare ki ta hannun daman Rabin jiki Khadijah🥰 Fans suna ta miki godiya fa dayi miki addu'a Allah yabiya miki bukatan ki da biya musu kuɗin karatu da kikayi_*😍
🅿️32
Ya gyara min zama sosai a jikin sa kana a hankali yasaka hannu ya rungumo ni yana ɗan jijjiga ni kamar wata jaririya,
kana a sannu ya tallafo fuskata ya sanya kwayar idanunsa cikin nawa da suke tsiyayar da kwalla,
kana a hankali ya furzar da iska mai zafi cikin bakin sa
a hankali ya furta
"Kiyi hakuri ki dai na kukan nan haka yau kwana na wa kullum acikin kukan nan kike kinsan fa ba ke ɗaya bace hakan zai iya janyo dake da abun cikin ki matsa kinaso asa mi matsalar ne?".
komai ban ceba bankuma fasa kukan ba,
"To kinaso nima nafita nayita kukan irin naki ne iye *HAMDAHHH*? Inna ta tafi addu'ar mu kaɗai yanzu take bukata haka zamu zauna madadin mubita da addu'a sai mu bita da kuka anya kuwa Inna zataso hakan,yakike gani zataji idan muka bita da addu'a madadin kukan namu? idan akayi kaɗan sai a kara da hakuri dole zamuji zafin rabuwa da mutum irin Inna, sai dai bamuda yan da zamuyi wan da yafimu sonta ne ya ɗauke ta acikin mu, kodun ya jarraba imanin mu, kinaso muzama daga cikin marasa imani da tawakkali da karɓar kaddara kowace iri ce?".
ido kawai na zuba masa jin yau karo na farko yayi doguwar magana irin haka.
yayin da nashi ga sauke ajiyar zuciya da son dai na kukan sai dai nasan ko da na iya daina kuka mai sauti abune mai wuya na iya dai na zubda kwalla,Inna uwace agare ni ba kaka ba.
Ya SALEEM yana da taurin zuciya a duk family'n mu babu wan da baiyi kuka ba hatta Abba da Abbu sai da suka zubda kwalla amma shi ko ɗigon hawaye ban gani a idanunsa ba sai dai yan da idanunsa suka sauya daga farare tass zuwa ja...
Tafin hannunsa ya sanya kan fuskata yashiga share min hawaye kana a hankali yafurta
"Ki dai na kukan haka ki huta tukun".
yafaɗa cikin muryar lallashi kana ya haɗe bakin mu sai da ya tabbatar da ya sai da kukan kafin ya zare bakin sa,
kana yashiga tuɓe min kayan jikina koda yazare min doguwar rigar jikina yarage daga ni sai pant dan ko bra babu ajikina, kasan cewar shi ɗazu yasaka min kayan.
mikar dani yayi kana shima yamike yaruko hannuna muka nufi bathroom dake nan cikin ɗakin,
ya tai maka min nayi wanka muka fito na mai da kayan da na tuɓe,kana ya zauna kan gado ya ɗan kishin gida yayin da ya kwantar dani a gefen jikin sa,
naji ɗan daɗin jikina kuwa danayi wankan.
dubana yayi da kyau ganin inata mammatsa idanuna yace
"Kukan zaki fara?".
kai na girgiza cikin disashshiyar muryar ta da ta dishe dan kuka nace
"Kai na ne ke min ciwo".
nafaɗa ina matse idon,
a hankali yashiga shafa kaina kana yace
"Zakisha magani?".
kai na girgiza da sauri, tare da faɗin
"Zai bari da kanshi".
numfashi ya sauke kana yace
"Idan baki kuma yin wani kukan ba shine zai dai na".
shiru nayi ina daɗa manna kaina da kirjin sa...
Har lokacin sallar la'asar tayi muna tare da shi acikin ɗakin a kuma cikin ki jikin sa, sai da a ka kira sallar kafin ya ciro ni a jikin sa kana yaruko hannuna muka fito a ɗakin.
side ɗin Ummi yanufa da ni,
a parlour muka taddata da wasu ƴan uwan mu, da alama sallah suka dawo yi,
akusa da Ummi na zauna
sai da yaga na zauna kafin yafita yanufi masallaci.
Mikewa tsaye nayi Ummi ta dube ni da sauri tana faɗin
"Ina zakije?".
nace
"Sallah zanje nayi".
tace "Ai ho" sai ta mike ta kamo hannuna muka shige cikin bedroom ɗin ta..
tana tsaye a kofar bathroom har na idar da al'wala nafito kana ta shin fiɗa min sallaya na haye kai na tada salla,ita kuma ta zauna gefe na a bakin gado.
ina tada sallar naji wani irin kuka yazo min,haka nayi sallar hawaye na wanke fuskata, na daɗe inayiwa Inna addu'a a cikin sallar ko da na idar ma naɗau lokaci ina yi mata addu'a kana daga bisani nashafa sai na jingina kaina jikin kafar Ummi.
kai na ta shafa alamun lallashi sai ta miko min wani littafin addu'oi tace
"Karɓi zai sama miki salama da yardar Allah".
na miko hannu na karɓa kana na buɗe nasoma karan ta addu'o'in sai naji hawayen yana raguwa...★
Da daddare Ya SALEEM yakawo min kaya na acikin ɗan ma dai-dai cin a kwati.
Ni dai tun da nashiga bedroom ɗin Ummi ban kuma leka ko da parlour ba,Ina zaune a cikin ɗakin,in Ummi ta fita to Aunty Jaleela zata shigo ko Aunty Rafee'at ko kuma wasu daga cikin dangin mu ba a taɓa barina na zauna Ni kaɗai,
ko bayi zan shiga to sai na sami mai rakiya ya tsaya a bakin kofar har sai na fito.
kullum Ya SALEEM zai shigo sau biyu da sassafe kafin mutane sufara zuwa sai kuma dare bayan sallar isha...
Yau gidan cike yake tam da jama'a kamar ranar da akayi rasuwar, yau kwanan Inna uku kenan da rasuwa.
Muna zaune da su Ummi jama'a sai shigowa suke dan dole Ummi tasa nafito parlour dan wasu da dama idan suka shigo sai sun tambaya ina nake.
jin ta aziyyar da mutane ke yimin nason fama min mikin dake cikin zuciya ta sai na mike na koma ɗaki ina share wasu zafafan hawaye da suka zubo min, Aunty Jaleela ce tashigo da sauri rike da wayata da tun ranar rasuwar ban ma san in da yake ba ta mika min tana faɗin
"Karɓi a na kiran ki Ya SALEEM ne naɗa ga yi magana".
tafaɗa tana samin wayar a kunne.
hawayen na share kana nayi sallama,
batare da ya amsa sallamar ba yace
"Kuka kike ko?".
kai na girgiza kamar yana gabana sai kuma nace
"A'a".
numfashi ya fesar kana yace
"To zo gani a waje".
a hankali na zare wayar na mike nashiga bayi na wanko fuskata nafito,Aunty Jaleela na tsaye ganin na nufi kofa sai ta bi bayana tana tan bayana ina zani nace mata Ya SALEEM ke kirana,jin haka yasata tsayuwa a parlour nikuma na wuce ina ɗan rike zundireriyar hijab ɗin da ke jikina.
a daf kofar shiga side ɗin na ganshi tsaye,ido ya zuba min har nakaraso in da yake,
ganin kallon da yake bina da shi yasani yin kasa da kaina a hankali ya furta
"Kinyi kuka mana".
ɗagowa nayi na ɗan kalle shi sai nakuma yin kasa da kai na,hannuna na ya ruko yana faɗin
"Fuskar ki ta nuna ai, baza ki sawa zuciyar ki hakuri bako?".
"Bana sanin san da hawayen yake sauka ne amma na dai na kukan".
janyo hannuna yayi yasoma tafiya kana yace
"To ki dage ki iya mai da hawayen idan zasu zubo,gobe zamuje asibiti a dubaki".
na buɗe baki zan yi magana sai nayi shiru lokacin muka karaso farfajiyar gidan ina ɗagowa mukayi ido huɗu da Na'ima tafito daga side ɗin Inna taɗau hanyar part ɗin Mamie,
kawar da kaina nayi ganin irin kallon da take binmu da shi har ta wuce sashin Mamie.
maganar sa najiyo a hankali
"Ta a ziyya za su miki".
ɗago kai na nayi jin abun da yafaɗa nan idanuna ya sauka kan wasu mutane guda biyu da ka gansu kaga manyan mutane,muka karaso in da suke,
gaishesu nayi suka amsa kana suka ɗaura da yi min ta'aziyya.
rau-rau nayi da ido sai ga hawaye ya cika ido na,Ya SALEEM yace
"Kukan zaki fara kenan".
kai na girgiza da sauri ina mai da hawayen.
muna tsaye muna gaisawa da mutanen Na'ima ta fito daga side ɗin Mamie ta nufi na Ummi.
ɗaya daga cikin mutanen yace
"Sai a hankali zata dai na rashi a kwai zafi sai hakuri".
Nan suka ɗan yi min nasihohi kana suka yi wa Ya SALEEM sallama suka shiga motar su suka tafi.
yace na koma ciki bari ya fita a kwai masu jiransa a waje,nace masa to.
na juya na nufi ciki shikuma yayi waje,
kafin na karaso kofar side ɗin Na'ima ke fitowa daga cikin sa ko minti 4 batayi da shiga ba tafito wai har tayi ta'aziyyar kenan,wani irin kallon sama da kasa tabini da shi kana ta taune laɓɓanta na kasa tare da girgiza kai
sannan tace
"Ya hakuri".
"Muna koyi".
nima na faɗa a takaice,
kai ta guma girgizawa tawuce ni.
ban ma san tanayi ba nawuce ciki abina....★
Ranar da Inna ta cika kwanan bakwai ƴan uwa na nesa da na kusa suka fara komawa ciki kuwa har da su Aunty Rafee'at da tun ranar rasuwar suna gida muna tare da su.
da daddare Ya SALEEM yazo yace mutafi, kuka nasaka mishi nace nidai bazan koma ba sai da su Abba suka yi da gaske wajen lallashi suka ce ga Aunty Halima ƴar baffan su Abbu'n mutafi tare zata ɗan rika ɗebe min kewa tun da bata da aure kuma ba yanzu zata koma ba ita ma mijin ta ya rasu watan sa huɗu da rasuwa kenan.
kafin na yar da na bishi muka koma har da Aunty Halima.
ranar da muka koma nayi kuka sosai dan ina shiga gidan Inna ta faɗo min arai ga kuma tsoron nan dake nan cikin raina,ranar sabon lallashi Ya SALEEM da Aunty Halima sukayi...
tun da muka dawo gidan kullum muna tare da shi in yafita kuwa zan koma gun Aunty da ta sauka cikin ɗakin da Inna take sauka idan tazo gidan...★
Haka rayuwa yacigaba da tafiya kamar sannin ku yanzu kwanaki basa da wuyan juyawa.
kwanta tashi asarar mai rai rayuwa sirri inji masu iya magana.
Yau kimanin kwanakin Inna arba'in da rasuwa hakan kuwa yayi dai-dai da lokacin fara tafiya ai kin hanjji ma niyyata sunata shiri domin tafiya ai kin hajji in da wasu garuruwan ma da dama jirginsu yafara tashi ciki kuwa har da garin Bauchi'n Yakubu.
Mamie da Abbu suna daga cikin maniyyatan wannan shekarar,kamar yadda suka tsara wa kansu duk bayan shekaru uku Abba da Ummi zasu tafi bayan wani shekaru uku kuma Abbu da Mamie.
a na saran gobe da karfe 8 na safe jirginsu zai ɗaga insha Allah.
yau tun da sassafe nayita masawa Ya SALEEM nace sai dai ya kai ni gida naje nayiwa su Mamie Sallama,yace na bari sai da daddare ko kuma da safe muhaɗu a airport.
nace nidai a'a.
yace to nahakura duka na kirata a waya nayi mata sallamar,kuka na saka mishi nace ni dai na yar da ya kai Ni da daddaren.
murmushi yayi kana yace
"Kin sau ko layi kenan"...
kamar yadda yafaɗa kuwa bayan sallar isha ya kwashe mu har da Aunty Halima ya kai mu gidan...
A farfajiyar gida muka dadda Abba da Abbu da alama dai tattaunawa suke irin na ƴan'uwan taka muka gaidasu kana muka wuce, Ya SALEEM kuma ya tsaya a gun.
koda muka shiga side ɗin Mamie nan muka taddasu gaba ɗayan su dasu Aunty Rafee'at suma ɗin sallamar suka yi musu har da Ummi duk suna cikin parlour,da goggo Hauwa da itama tazo ɗazu dan yi musu sallamar.
hira sosai ake cike da ɗebewa juna kewa kowa yana faɗin kalar tsarabar da za a kawo miki, Mamie ta dubeni kana tanisa tace
"Ni banji kince ga abun da kike so a kawo miki ba,ko wannan karo kin yafe ne akawo miki ɗankwale kawai".
tafaɗa tana dariya.
dariya duka a saka Aunty Jaleela har da buga cinya tace
"Allah Mamie kikawo mata ɗankwali mu kikara mana tsarabar tun da bata so".
baki na murguɗa mata tare da faɗin
"Ni nace miki bana so ai na barine kugama faɗan naku sai na faɗa mata nawa dan kar kusa ta mance da nawa".
a can kasan raina kuwa ba haka abin yake ba Inna ce kawai ta faɗo min shi yasa nayi shiru in da tana nan da har da ita acikin tafiyar bayan rasuwar tane Abbu yaje ya amso kuɗin kujerar ta,da kyar na dage na iya mai da hawayen da suka ciko idona.
maganar Mamie ne yasani dawo a hankali na kalle su
"To me kike so a kawo miki HAMDAH?".
murmushi nayi da faɗin
"Mamie dogayen riguna da gyale da warwaro da zobe".
tace
"To ba damuwa naki zan fara siya kafin nasu".
dariya Aunty Rafee'at tayi tace
"Mamie abun ma wariya ne to me za a siyo wa baby'n ciki".
ɗan kallon cikin nayi da yafara tasowa amma sai ka lura zaka gane sai dai inajin nauyin sa.
Mamie tace
"Ai kuwa dele na amma fa idan miji ne to akwatin sa ma daban ne, idan kuma kishiya ce ko ruwan zam-zam bazata gani ba, sai ta jira idan Ummi'n Fauzan taje tazo mata da shi dan nabar mata ita".
dariya aka saka gaba ɗaya cikin muryar dariya Ummi tace
"A'a dai Mamie'n Nusaiba in dai kishiya ce kikawo mata tsaraba in kuma miji ne to ki bari idan naje ni zan kawo masa".
dariya Abbu yayi da yanzu shigowar su shida Ya SALEEM da alama sunji muhawarar da ake, Ya SALEEM kuwa murmushi ne ɗauke a fuskarsa, na lura in dai ana magana kan cikin nan sai yayi ta murmushi.
Abbu yace
"To dayake magana ne kan kishiya kowa yanata kakkaɓewa a jikinsa to ni ina so in matace kuwa duk tsaraɓar da zanyi natane".
Aunty Rafee'at tace
"Yauwa Abbu ka siya mata irin kayan da Mamie da Ummi basu taɓa sa irin saba".
goggo Hauwa tace
"Ai kam a siya wa kawata tun da duk kishi ya ishe su"..
haka a kayi ta hira cikin raha da jin daɗi da ɗebewa juna kewa,
duk hirar da ake kuwa baka taɓa jin maganar Ya SALEEM sai dai wani sa'in yayi murmushi.
har wajen karfe 10 muna zaune anata hira sai a lokacin Ya SALEEM ya mike yace mutafi.
kafaɗa na make nace nidai kwana zanyi,zai kuma magana Abbu yace ya barni nakwanan haka yatafi badun yaso ba.
Washegari gaba ɗayan mu mun hallara a parking space har da su Aunty Rafee'at dan suma anan ɗin suka kwana.
motar Abba Ummi Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela Fauzan suka shiga, inda mukuma muka shige motar Abbu Iro direba shi zaija motar Abbu na gefen sa Ni da Mamie da goggo Hauwa da Nusaiba muna baya,
Aunty Halima Kuma barta ita ta zauna a gida.
a haka muka jera muka nufi airport
muna isha motar Ya SALEEM yana isowa
dai-dai kuma lokacin kuma ake ki ran sunan mahajjata dan haka batare da ɓata lokaci ba muka fito su Abbu suka nufi ciki muna ɗaga wa juna hannu.
Naso bin su Ummi mu koma gida Ya SALEEM ya hana haka ya ɗauke Ni a motar sa muka koma gida.
muna isa na kira Aunty Halima nace tahau napep ta dawo dan Allah tace min zata dawo amma sai jibi....
A ɓangaren Na'ima
zaune take a cikin parlour'n ta yayin da Rufa'ila ke gefe tana ta mata hidima. nan wayar ta dake gefen ta ya kama ringing koda ta ɗago wayar taga aminiyar ta Raliya ce ke kiran nata da sauri