Showing 51001 words to 54000 words out of 92896 words
min sallaya yasaka min hijabi,a zaune nayi sallan shima da kyar, ina idar wa nasulale a gun,ya ɗaga ni ya mai dani kan gado,
kana ya dubeni cike da kulawa tare da manna min kyakkyawar sumba a goshi kana yaɗa go yace
"Bari na ɗauko waya na nakira Dr yazo ya duba ki".
Ido kawai nabishi da shi har yafita...★
A can state locos gidan su Abbu kuwa
Zaune suke a parlour'n Inna Aunty Rafee'at da mijin ta Dr Faruq da yanzu suka kawo mata ziyara,
Goggo Hauwa na zaune a gefe tanata kare tsohuwar ta da suketa yi mata tsiya,
dariya Goggo Hauwa tayi da faɗin
"Allah ya shirya to ku kuzau na kada ku tsofa".
Dariya sukayi Aunty Rafee'at tace
"Allah goggo Hauwa kidai na kare wannan tsohuwar, iya nuna wariyar launin fata gare ta,wai tazo garin nan taki zuwa gida na da na Jaleela tayi zaman ta a gidan HAMDAH".
"To ai ku manya ne".
cewar goggo Hauwa
ta mike tana cigaba da faɗin
"Ni bari naje nafara shiri".
Aunty Rafee'at ta dubeta tare da cewa
"Shiri kuma goggo Hauwa ba sai an jima zaku tafin ba?".
tace
"Eh gobe idan Allah ya kai mu nake son koma ni Inna Kam tana nan tukun, yanzu gidan SALEEM zani na tarkaso kayana gobe sai tafi".
Inna ta dubi Dr Faruq tace
"Kai Umar baza ka tashi katafi gurin sana'ar kaba kasaya biye nata ko,kabar majin yata a can".
murmushi Dr Faruq yayi kana yace
"Yanzu ma kuwa".
sai kuma ya dubi goggo Hauwa
yaɗaura da faɗin
"Goggo to muje nasau keki sai na wuce daga gun".
tace
"Yauwa to bari nafito mutafi".
tanufi cikin ɗaki,
Inna taɗaga murya tana faɗin
"Ɗauko jakata kiyi min gaba da shi kafin na tawo an jima".
baki Aunty Rafee'at tabuɗe sai kuma ta kalli mijin ta tasaka dariya tana cewa
"Ai dama masani ɗazu da Abbu ke cewa tabari sai da daddare takoma gidan HAMDAH, nasan zaman kan kaya zatayi kafin daren,ba gashi ba wai ayi gaba da jakarta kafin tazo".
Shima dariyar yayi yana faɗin
"HAMDAH ƴar gidan Inna".
Ko da goggo Hauwa tafito sallama sukayi wa Inna suka tafi....★
Tun daga cikin
parlour najiyo Muryar Aunty Rafee'at da goggo Hauwa suna kwaɗa sallama,ido na rumtse tare da share ɗan guntun hawayen da yazubo min,da da lafiya ta da tun san da naji karar tsayuwar moton dasukazo ciki, da ni zan fara tarosu kafin sushigo, amma sai gashi har suka shigo suna sallama bani da ikon da zan iya amsa musu sallamar da karfi har suji.
Daga cikin parlour'n Aunty Rafee'at ta dubi goggo Hauwa
tare da faɗin
"Sai yanzu ma abin yadaɗa sumo ni kajimin Inna'n nan tun yaushe nasami labarin zuwan ta, Amma ko maganar zuwa gida jen mu batayi, amma ta iya cewa wai wani a taho mata da jakarta kafin tazo, Allah tsohuwar nan taci bashi sai ta rama mana kwanakin da tayi a nan muma dan bamu yafe ba".
dakuwa goggo Hauwa tayi mata tare da shigewa ɗakin da suka sauka ciki tana faɗin
"To kada ku yafen mana".
dariya Aunty Rafee'at tayi tajuya ta nufo bedroom ɗina,
"Wai matar gidan nan kam bacci ne bata tashi ba kokuma sammakom unguwa tayi".
tafaɗa tana tura kofar ɗakin da sallama,
Ido kawai na zuba mata har takaraso bakin gadon tana faɗin
"Ikon Allah yau kuma kiwuyan ce ta mosa a ka kwanta babu ko shin fiɗi kan gadon".
murmushin yake na bita dashi,
zama tayi saman bedside drower tadube ni kana tace
"Yaya dai HAMDAH bakida lafiya ne?".
kai na gyaɗa sai ga hawaye sharr
mikewa tsaye tayi tana faɗin
"Subhanallahi me ke damin ki taso maza bari na tsai da Abba'n Adil ya duba ki kafin ya tafi sannu kinji".
tafaɗa tana kokarin tai maka min namike tace gaba da faɗin
"Taso ki sa kaya a jikin ki sai muje parlour yashigo ya duba ki".
ta janyo hannuna na mike tsaye, da karfi na rumtse idanuna yayin da jiki na yasoma cirawa,
blanket ɗin da na ta shi da shi a jiki na tajashi tana cewa
"Sake wannan kije kisaka kaya kiyi maza kada ya tafi dan Allah..."
sauran ragowar maganar ta haɗiye ganin agogo da boxes sun faɗo daga cikin blanket ɗin,
da kyau ta zuba musu ido,
sai kuma ta mai da duban gare ni, da sauri na rike hannun ta da karfi tare da tashewa da kuka nace
"Aunty Rafee'at zan faɗi".
cikin hanzari ta tai makamin nakoma na zauna bakin godan,
cike da ɗinbin al'ajab taɗago agogo da boxes ɗin ta gyara musu zama a gefen gado, da kyau ta dubeni cike da tsananin farin cikin da ya gaza ɓoyuwa har sai da ya bayyana kan fuskar ta, tasaki wani kayataccen murmushi,kana tace
"Ina Ya SALEEM ɗin?".
Ido na matse cikin muryar kuka nace
"Wai yaje kiran Dr".
wani murmushi mai sauti tayi kana tace
"Ok". luuu haka naji ida nuna yayi
sai kuma na rike hannun ta da karfi murya na rawa nace
"Aunty Rafee'at jiri nake ji zan faɗi".
da sauri ta ce "Kwanta bari na sai da Abba'n Adil kada ya tafi".
tajuya da sauri ta fita fuskan ta ɗauke da zallar farin ciki,
tana fita kuwa lokacin Dr Faruq yake tada motar sa zai fita da sauri tanufo in da yake ta buɗe marfin gafen sa,tana faɗin
"Ashe da na ɓata lokaci da ka tafi".
kai ya jinjina kana yace
"Ai ma dan natsaya amsa waya ne da yanzu nayi nisa,
ya dai na ganki cikin farin ciki haka ko mu koma gida ne nabaki kyauta".
murmushi tayi tare da faɗin
"Rike kyautar ka banaso sai da daddare, HAMDAH ce ba lafiya muje ka duba ta".
takarashe maganar cikin masha huriyar farin cikin da ya gaza boyuwa gare ta,ko ba komai yanzu tasan Ya SALEEM ya karkato gun HAMDAH abin da tajima take fata da burin kasan tuwar hakan,
da ɗan mamaki Dr Faruq yake kallon ta kana yace
"Bata da lafiyan shine zan ganki cikin farin ciki haka".
baki ta buɗe da zummar bashi amsa sai ta hango Ya SALEEM,shiru tayi tana cigaba da murmushi har yakara so in da suke,gai sheshi tayi ya masa sai ta juya ta koma ciki,
Dr Faruq yafito daga cikin motar ya mika masa hannu suka gaisa,
Ya SALEEM yadube shi kana yace
"Yanzu nake da shirin niman ka a she dai kana tafe".
"Eh wlh offece zan wuce shine nabiyo na sauke goggo Hauwa,amma dai lafiya ko?".
Dr Faruq yafaɗa yana duban sa,
tsayuwar sa ya gyara kana yace
"HAMDAH ce ba lafiya zaka duba ta".
"Ok to ba damuwa muje sai na duba ta".
ya buɗe motar yaɗau jakar kayan ai kinsa,
suka nufi side ɗin HAMDAH.
Aunty Rafee'at tana shiga ta rungume goggo Hauwa da ke tsaye cikin parlour, da sauri goggo Hauwa tace
"Ke meye haka".
cikin da riya da tsantsar farin ciki ta saketa cikin kasa da murya tace
"Goggo albishirin ki yau ɗiyar ki ta girma".
Murmushi goggo Hauwa tayi kana tace "Wace wai HAMDAH kike faɗa?".
Kai ta gyaɗa tana faɗin
"Kwarai ita". murmushi mai yelwa ya bai yana kan fuskar goggo Hauwa tashiga faɗin "Masha Allah".
Ganin su Ya SALEEM sun shigo sai ta koma ɗaki zuciyar ta cike da farin ciki da tausaya wa HAMDAH,
Dr Faruq yazau na kan kuje ra Ya SALEEM kuma ya shige ɗakin HAMDAH,
Aunty Rafee'at na ganin shige warsa tamaso in da Dr Faruq yake ta rungume shi tana murmushi shima murmushin yayi,tace
"Allah Abba'n Adil taban sau sayi dan nasan taji wuya amma fa farin cikin yafi yawa".
Kai ya girgiza dan ya fahimci ko menene ciwon HAMDAH,hancin ta ya lakato yace
"Hm ai wata kila ma rakine kawai irin naki ta ɗauko, wani irin wuyane ban shaba a First night ɗin mu".
dariya tayi tana faɗin "Ai ku ɗin ne ba sauki bakusan kalar a zabar da mutum yake jiba a lokacin Allah sarki HAMDAH"...
Ko da Ya SALEEM yashigo gaban wardrobe ya yanufa yabuɗe yaciro wani doguwar riga mara nauyi da ɗankwali,
ido kawai na bishi da shi har ya zo in da nake,
Yaɗago ni ya tallafo ni jikin sa yana faɗin
"Sa rigar ga Dr Faruq zai shigo ya duba ki".
kai kawai na gyaɗa sai ga hawaye sharr,tafin hannun sa yasaka ya share min kana yasaka min rigar,
yajanyi pillow ya mannashi da jikin gado kana yagyara min zama na jingina da shi, sai ya mike yafita,
Zuwa can yashigo yana gaba Dr Faruq na biye da shi suka karaso.
Dr Faruq ya aje jakar kayan ai kinsa yadube ni yana faɗin
"Ya jikin dai HAMDAH?"
"Da sauki" nafaɗa can kasan makoshi,
Kuma dubana yayi kana yace
"Ya kike ji cikin jikin naki?"
narai-narai da ido nayi sai ga hawaye,
Ya SALEEM ya gyara tsayuwar sa yace
"Am tana cewa tana jin jiri idan ta mike kuma sai tace zata faɗi, so kawai batama iya tafiya".
Ɗan shiru Dr Faruq yayi yana sauraran sa kana yace
"Ok". jakar da yashigo da shi ya buɗe yafiddo dawasu kayakin goje-gojen sa,nan yashiga duddu bani da yimin ƴan wasu tambayoyi, ni dai bana iya cewa komai Ya SALEEM ne ke bashi amsa.
daga bisani yace
"Za'a saka mata drp sabo da taji karfin jikin ta, sannan kuma a sama mata abinci mai ɗan nauyi da kuma ruwa-ruwa,zai tai maka mata wajen daɗa samin karfin jikin,sai wasu magunguna da zan rubuta yanzu tana cin a bincin sai tasha,yanzu dai bari na saka mata ruwan tun da Allah yasa ina da shi a nan".
Batare da ɓata lokaci ba yasaka min ruwan tare da allurai a ciki,kana yana gama wa yaɗau jakar sa yana faɗin
"Allah ya kara sauki".
tare suka fita da Ya SALEEM yana yi masa godiya sai da suka fito waje Dr Faruq ya tsaya tare da duban sa yana ɗan sosa keyar sa yace
"Da alama jiya da yunwa a tattare da ita sai kuma ka bakwan ceta cikin jin yunwar gashi kuma sabuwar gamuwa ce, so shi yakawo duk wannan ɓarin jiki da kuma taji kamar zata faɗin,yana da kyau tarika cin a bin ci da daddare kafin kwan ciya".
Hannu Ya SALEEM ya mika masa tare da kuma yi masa godiya sukayi sallama Dr Faruq yashige matar sa yafi a gidan,
Shiko Ya SALEEM side ɗin sa ya shiga yayi wanka yashirya cikin shiga na alfarma yaɗau makullin mota yanufi parking space.
Acan cikin side ɗin HAMDAH kuwa
bayan fitar su Ya SALEEM, Aunty Rafee'at da goggo Hauwa suka shigo ɗakin ganin bacci yafara fizgar ta sai suka fita suka fita suka jamata kofar dan tasamu tayi baccin da kyau.
kitchen suka wuce,nan suka fara sama mata abin da zata ci idan ta farka daga baccin, cikin kankanin lokaci Aunty Rafee'at tagama kammala lafiyayyen ferfesun kaza wan da yaji kayan yaji da na kamshi,goggo Hauwa kuwa kunun alkama mai haɗin kayan yaji acikin sa ta dama,suka jujjuye komai cikin wurin da bazai yi sanyi ba koda wuni zai yi, goggo Hauwa tafita takoma ɗaki domin cigaba da shirin ta,
Aunty Rafee'at takimsa cikin kitchen ɗin kafin ta fito, takoma ɗakin HAMDAH ta duba ta har lokacin tana kan baccin ta cikin kwanciyar hankali, sabo da allurar baccin da aka zuba cikin ruwan,shima ruwan yana sauka yadda ya kamata har yayi rabi yanzu,fita tayi taja mata kofar taje ɗakin da goggo Hauwa take, nan suka zauna suna ɗan taɓa hira....
Motar Ya SALEEM ne da yanzu yashigo ya dai-dai ta parking a parking space, yafito rike da laidar magunguna da yasiyo yanufi part ɗin ta,
Ko da yashigo ya tarar tana bacci sai ya aje laidar kan bedside kana ya maso bakin godon yasun kuya ya manna mata kiss a goshi sannan yafita yakoma nashi side ɗin,yana shiga ya tadda Na'ima tsaye wani irin kallo tabishi da shi shiko wuce ta yayi yashige bedroom ɗin sa.
A ɓangaren su Aunty Rafee'at
agogo ta kalla tare da mike wa tana faɗin
"Goggo bari na duba HAMDAH".
to goggo Hauwa tace ita kuma tafita,
tana shiga ɗakin dai-dai lokacin na farka daga baccin da nake, da sauri ta karaso tananyi min sannu tare da faɗin
"Yauwa ruwan ma saura kaɗan ya kare".
Idanuna na juya na kalli laidar ruwan saura ɗan kankani.
"Bari ya karasa shiga sai kiyi wanka ki daɗa jin daɗin jikin".
tafaɗa tana zama kusa da kafafu na,zaman ta dakamar 10min ruwan ya karasa shiga,tamike ta cire, kana ta shiga bayi ta haɗa ruwan zafi cikin bathtub tafito, ta taimaka min namike tsaye ga mamaki na sai naji namike bana ji kamar zan faɗin sai dai ina jin zafin HQ ɗina har yanzu, a hankali narika ɗaga kafafuna tana rike da hannuna muka shiga bayin,
da kyar na yarda na shiga cikin ruwan ina matse ido,tana tsaye tana tanuna min yan da zanyi sai da ruwan ya rasa ni sosai kana tafita tana faɗin
"To kiyi wanka"...
Ɗakin ta dawo ta ciro wani bedsheet ta shin fita kana ta kimsa ɗakin tsaf takunna turare,nan da nan ɗakin ya kaure da sassanyan kamshi,koda na gama wankan da kaina nafito dan sosai naji daɗin jikina duk da dai har lokacin ina jina babu nauye, na tadda ta ciromin kayan da zan sa wasu riga da sket ne na atamfa, nazau na gaban mirror nashafa mai har na mike sai kuma naɗau kwalbar haɗeɗɗen Humra mai matukar daɗin kamshi haɗi ne na musamman haɗin, (★Asma'u Jos)
na shafa shi a jikina kana naje naɗau kayan na zauna bakin gado naso ma sawa.
Aunty Rafee'at tanufi kofa tana
cewa
"Yauwa yi maza ki saka bari na kawo miki abin ci"...
Tana fita ta dawo rike da tray Mai ɗauke da Foodflaks da ɗan madaidaicin flaks da plt cup spoon and fork. tadire shi kan table ɗin da ke gaban gadon,
nan ta zuba kunun nicin cup farfesun ma ta zuba shi cikin plt kana ta masomin da table ɗin gabana tace
"Maza cinye su duka".
Ido na waro "Duka". nafaɗa ina kallon kunun da ta cika shi cikin cup da ferfesun da ta loda cikin plt, tace
"To ci yadda zaki iya amma kici da yawa".
To nace tare da gyara zama na.
Da sallama ya turo kofar Aunty Rafee'at ta amsa tare da mikewa taraɓa ta gefen sa ta fita,ida nunsa a kai na,
a hankali ya tako in da nake ya zauna daf dani har jikin mu na gogar juna, hannuna yariko yana ɗan mammatsa shi cikin nuna kulawa yaɗan karkato fuskarsa yana kallon nawa fuskar yace
"Ya jikin dai da sauke ko?".
baki na turo tare da yin rau-rau da ido nace
"Har yanzu bai bar min zafi ba".
daɗa masoni yayi sosai yacusa fuskar sa a gefen wuya na ya manna hancin sa jikin kuwaya na yaɗan ja numfashi kana yazuro harshen sa ya laso fatar wuyan,a hankali cikin wani irin sassanyan murya yace
"Zai bari kin ji?".
kai nayi saurin gyaɗa wa jin yan da yake ta lashe wuyana yana ɗan gangarowa ta kirji na, da sauri na ɗan muskuta ina kokarin janye jikina.
Ɗago kansa yayi kana yace
"To ci abincin".
A hankali na ɗau fork nasoma cin ferfesun,
Naci daɗan yawa kuwa na kara da kunun duk da yajin da yake ciki kunun da ferfesun, idan na cire hannuna cikin a bincin sai yace naɗan kara kaɗan jin cikina yacika sosai sai na ture plt ɗin ina faɗin
"Cikina zai fashe fa".
yace "Ok". mika hannunsa yayi yaɗau laidar maganin da yashigo dashi ɗazu, yaciro maganin yaɓaɓɓare yaɗau gorar ruwa yabuɗe tare da mika min,
Tuni ida nuna yacika da ƙwalla tun ban shaba nafara jin zuciya na yafara tashi,
"Karɓa kisha". yafaɗa yana mika min tuni hawayen yafara zuba na karɓi maganin na rumtse idanuna tare da wasa shi cikin bakina nakora da ruwa da kyar yawuce, idanuna na daɗa matse shi da karfi jin yan da zuciya ta ke juyawa, ina zaman jiran naji ya miko min sweet ɗin da yake bani idan yabani magani nasha a wancan lokacin,
sai jin bakin sa nayi kan nawa yazura harshen sa cikin bakina,cikin tsananin tashin zuciyar da nake ji najuya harshe na cafko nashi nashiga yi masa tsotsar minti..........★
Mommyn Twins ce
*🌺HAMDAH🌺*
*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*
_(Book one)_
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*
*Free page*
My no 08034690723
🅿️21
Sosai na manna bakina cikin nashi narika sosa a hankali narika jin aman yana kwanciya sai narika sauke numfashi a hankali a hankali,
A sannu na buɗe idanuna sai na shiga kokarin zare bakina,tallafo kai na yadaɗa yi sosai tare da daɗa tura harshen sa cikin bakina, yayin da cikin ƴan mintunan idanunsa suka sauya, fitar numfashin sa ma yaɗan karu.
nayi saurin juya kaina,nazare bakina tare da yin kasa da kaina cike da sananin jin kunya yan da nayi ta tsotsar bakin sa cikin halin jin aman da nake, a madadin sweet dan bana da zaɓin da yawuce wannan in kuma ba haka ba to sai dai nayi aman abin da nace,sai nashiga wasa da ƴan yatsuna.
A hankali cikin muryar sa da taɗan sauya yace
"Aman ya koma?".
kai nagyaɗa cike da jin kunya,
A hankali ya mike tare da ɗaga kiran da yashigo wayar sa yanzu yanufi kofa,bayan sa nabi da ido har yafita, numfashi nasauke a hankali nagyara na kwan ta bakin gadon....
Da yamma Aunty Rafee'at tashigo takuma haɗa min ruwan zafi tace naje na kuma gasa jikina,a wunin ranar sosai naji daɗin jikina sai ɗan zafin da kasana yake shima ba sosai ba.
da misalin karfe 6 Dr Faruq yazo ya ɗauki Aunty Rafee'at kafin ta tafi sai da takuma sani nagasa jikina,
motar su na fita Iro direba nashi go wa shida Inna.
I najin muryar ta gaban kirjina ya yanke,shike nan nakaɗe Inna ta yankani ta gama..
Haya niyar su narika ji a parlour inason fita, Amma inajin tsoro dan ganin nake tana ganina zata gane abin da Ya SALEEM yamin,haka na zauna duk da inaso na ganta amma ina jiwa kai na tsoro.
bayi nashiga nayi al'wala nazo nagabatar da sallar magriba da yanzu a ka kira ina idarwa namike a hankali nafita nanufi ɗakin da Inna take, a zaune a kan sallaya na iske ta tana jan jarbi goggo Hauwa na zaune a bakin gado,a hankali nakaraso na zauna kusa da goggo Hauwa dubana tayi tana faɗin
"Ya jikin dai HAMDAH?".
da sauri naɗa go jin Inna na cewa
"Au bata da lafiya ne ". rass haka naji gaban kirjina ya buga "Eh zazzaɓi ne ke damun ta ai da sauki ma naga yanzu jikin nata".
wani numfashi na sauke tare da haɗiya miyau da kyar,
Inna tace
"Yo ba dole zazzaɓi ya kamata ba