Showing 18001 words to 21000 words out of 92896 words

Chapter 7 - HAMDAH part 1 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

11896

zuwa gobe in Sha Allah, Kai Ya SALEEM ya girgiza tare da tab'e Baki Wai ace babba kamar Abbu Wai shine Inna zata aika wannan ƴar tsohuwa da fitina.

Cikin hanzari yakarasa in da Abbu yake tsaye suna gaisawa da ma ai katan gidan, ritsinawa yy cikeda girmamawa yashiga gai dashi tareda yimasa barka da zuwa,kana yamike tsaye ya ce "Bismillah Abbu".
Yafad'a tare da nuna Masa hanya,Yana gaba Abbu na biye dashi suka nufi Side in HAMDAH, suna Isa bakin kofar part in yad'aura hannunsa Kan handle ya murd'a tare da tura kofar.

Da sauri nad'ago nazubawa kofar Ido Jin karar bud'e kofar dai-dai lokacin yasanya kafarsa yashigo,
baya yaɗanyi sai Yakuma jawo kofar yadaɗa bud'eshi sosai yakuma ja da baya cikin girmamawa yace
"Bismillah shigo Abbu".
daallama Abbu yasanyo kansa cikin parlour'n, da sauri namike tsaye ganin
Wanda suke tare da shi Baki nawashe na ce "laa Abbu sannu da zuwa".
Murmushi yy suka karaso cikin parlour'n yazauna saman kujera,shiko Ya SALEEM kasa yazauna gefen Daman shi,cike da Jin dad'in ganin sa namaso nazauna kasa gefen hagunsa.

D'an matsowa na kumayi tare da gyara Zama nace

"Ina kawana Abbu ya su Mamie da Ummi'na".

Murmushi Mai fad'i yy ya ce "duk suna lfy sunce nagaidaki".

Kai na gyad'a nace "to su Nusaiba da Fauzan su basuce a gaida niba?". Nakareshe maganar tare da d'an langwab'ar da kana gefe.
Yace "na mance ne su suka Fara cewa nagaida ki kafin su Ummin ku".
Murmushi nayi cike da Jin dad'i da kewar ƴan kannena.

Kallon a kwatin dake a je tsakiyar parlour'n Abbu sai kuma ya jinjina kai akasan zuciyar sa kuwa yakefad'in
"Ƴar gidan Inna kenan yarinta a kwai dad'i in ban da yarinta waza a Kai gidan aure yace sati
guda zaiyi yakoma gida".
Afile Yakuma murmushi yayi kana yamai da kallon sa kaina ya ce "HAMDAH wannan jakar Kuma meyasa a ka fito dashi Nan ki kaishi d'aki Mana".

Muskutawa nayi na ɗan kalli a kwatin turo baki gaba nayi nace " Abbu Dass zan tafifa".
Gyara zama yy cikin dabara da hikima irin tasu ta manya yace
"To yanzu tafiyar zakiyi kenan?".
Kai nagyaɗa alamar Eh kana na ɗaura dafaɗin "Amma sai katafi kafin natafi".
ɗan shiru yayi tare da ɗan tsuramin ido sannan
Yace "to meyasa zaki tafin?".
da sauri nace "Abbu ni kawai tafiya zanyi gun Inna, ni ɗaya kawai kamar mayya ni dai tsoro nakeji, da daddare sai na rufe idona da karfi kafin nayi bacci, kuma ma ai sati ɗaya nace wa Inna zanyi kuma yaune satina ɗayan".

Kallonsa ya maida kan Ya SALEEM da yayi kicin-kicin da fuska yana ai kamin harara kamar zai kai min bugu na tabbata in badun Abbu na gunba bb abin da zai sa bai kai min hannun ba.
"Meye ke in ba mayyar ba".
Yayi maganar a kasan zuciyarsa,tare da ɗan jan guntun tsaki a file.
Niko baki naturo tare da ɗan murguɗa shi ganin yan da yawani murtuke fuska.

Gyaran murya Abbu yy kana yazura hannunsa cikin aljuhun rigarsa yazaro waya yami kamin yana faɗin "Ungo karɓi nakine duk san da kkson jin muryar Inna sai ki kirata duk Number'n ƴan uwan ki yana ciki, wayar ita zata rika tayaki hira basai kin tafi ba kin jiko? Inna'r ma tana zuwa kuzauna a nan tare".
Da sauri na karɓi wayar cike da tsananin jin daɗi narika juya wayar a hannuna cikin muryar dariya nace
"Ngd Abbu".
Wata ƴar karamar laida yamikomin mai ɗauke da kwalin wayar da i'giyar cj, na amsa.
Yace "to tashi ki ɗau jakarnan kimai dashi ciki".
Tun kafin yakarasa namike da sauri yayin da ida nuna ke kan wayar ina ta lallatsa shi bakina kuwa yakasa rufuwa naja a kwatin nanufi bedroom cike da farin ciki.

Numfashi Abbu yasauke kana ya maida hankalinsa kan Ya SALEEM yace
"Shi yaro ɗan lallamine idan kace zaka tan ƙwasashi da karfi sai yakarye batare da yayi yan da kakeso ɗin ba, idan kabishi cikin dabara da lallami to fa bazaka taɓa shan wuya wajen sai tashi kan hanya ba".
Shidai Ya SALEEM kan sa yaɗan dukar kasa batare da yace komai ba.
Abbu yaci gaba da faɗin
"Gidan dai lfy babu komai ko ya ita ɗayan iyalin taka?".
"Lfy lau tana ciki batasan kashigo ba".
Yafaɗa yana mikewa tsaye
Abbu yace "ƙyaleta in bacci take ka gai data in tatashi."
Kofar babban parlour da ke nan cikin parlour'n yanufa yana faɗin
"Ba bacci takeba".

Ina aje akwatin najuya nakoma parlour'n ina jin wani irin daɗi a raina bakaramin daɗi naji da Abbu yabani wayar nan ba har na mance da batun tafiya Dass can gefe nazauna saman 1str ina cigaba da latsa wayar,
Zamana baifi da 4min ba su Ya SALEEM suka shigo yana gaba Na'ima na biye da shi sai wani yamusa fuska take da kaga yanayin yan da take tafiyar da yamusa fuskar da take zaka san dole a kayi mata,a kasa gefen Abbu in da ɗazu ya zauna nan yakuma zama,itama ta zauna gefen sa.

Ɗan sun kuyar da kai tayi cikin yamusa fuskar da take tace
"Ina kwana". tafaɗa a gajarce.

Abbu da bai ma fahimci yanayin taba ya amsa cikin sakin fuska kana ya ɗaura da faɗin
"Kuna lfy ya gidan da bakuwar taku?". "Lfy lau". tafaɗa can kasa.

gyara zama Abbu yy kana yace
"Masha Allah".
sai kuma ya ɗan yi gyaran murya yaci gaba da faɗin
"To madalla acigaba da hakuri dai dan yanzu kece babba ga HAMDAH nan kanwar kuce sai kunyi hakuri da wasu lamuran ta,
mu samman ke da kullum kuna tare da ita a gida dole wasu
a bubuwan ke zaki rika ɗaurata kan hanya,
ki ɗau keta tamkar kanwarki idan kinga tayi wani a bin da ba dai-dai ba ki nuna mata rashin dacewar shi, ita bakuwace a wannan ɓangare dole sai an nuna mata wasu abubuwan, sannan HAMDAH yarin yace sai kunyi hakuri da ita,
Allah yabaku zaman lafiya da hakuri da juna".

"Amin". Ya SALEEM yace.

Itako wani irin kallon shekeke tabi Abbu da shi sai kuma tayi wani irin shu'umin murmushi.

akasan ranta kuwa faɗi take
"Uhum dole kace yarin yace ita naga yarin yarce kaɗauko ta ka kawo ta gidan nan a matsayin mata, wai ni za'a kife bai-bai kuma ai kanwata bazata taɓa shigowa gidan nan a matsayin da nake ba, kishiya-kishiya ce Allah yasa wake tazamo kanwata".

Shiru tayi da zan cen zucin da take ganin Abbu ya mike yana faɗin

"To nabarku lfy a kula a daɗa yin hakuri da juna".

Murmushin yake tayi tace
"To Abbu mungode Allah yatsare a gai da gi da".
tafaɗa tare da mikewa tsaye tanufi kofa.

Ni duk a bin da suke ma sama-sama nake jinsu gaba ɗaya hankalina nakan game in da nake bugawa a wayar, ganin Abbu yamike ne yasani mikewa da sauri na a je wayar nace
"Abbu tafiya zakayi?"
Nayi maganar a marairaice.

Murmushi yy kana yace
"Eh zan tafi daga nan office zan wuce".
Nace "to kagai da su Ummi dasu Fauzan".
Yace "zasuji, ranar juma'a su Fauzan in zasuzo suyi miki kwana biyu ranar Lahadi su koma sabo da makaranta".
To. nace cike da jin daɗi, yayimin sallama suka fita.

Suna fita na koma nazauna na ɗau wayar Game in da naketa bugawa tun ɗazu nakashe, nashiga contact numbers in ciki nafara bi ina dubawa duk lambobin mutanen gidan mu yana ciki Number'n Inna nashiga laluɓowa cike da zakuwar jin muryarta na dannawa Number'n nata kira.
Bugu ɗaya a nabi taɗaga da tare da yin sallama
ko sallamar da take ban amsaba cikin zakuwa da ɗonkin jin muryarta nace
"Inna nice Abbu ya siyamin waya".
Nafaɗa cike da zallar jin daɗi.

Washe Baki Inna tayi tana dariya tace
"Kai to madalla gaskiya Abbu ya ƙyauta kuwa, yauwa kinga yanzu zan rika jin muryar ki batare da na kira wancan mai bakar zuciyar ba, dama nima nace yau zan zo to yanzu kam hankalina ya ƙwanta yanzu dai sai nakuma sa rana zan zo".

Da sauri nace
"Inna kizofa".tace
"Zan zo"
Hira muka buɗe sosai.

A can waje
har jikin mota Ya SALEEM yaraka Abbu,
Abbu ya buɗe marfin motar yashiga yana dai-dai ta zaman sa yakalli gefen sa, numfashi yasauke tare da mika hannu yaɗau wata laida dake kan sit ɗin gefensa yamikowa SALEEM yace
"Ungo kaiwa HAMDAH Mamei'n kuce tabani na bata kaga na mance sai yanzu da nagani". To yace tare da
Karɓar laidar, Abbu yatada motar yy masa sallama mai gadi yabuɗe masa get yafita,har sai da motar Abbu yafice a gidan kafin yajuya
part in sa ya nufa rike da laidar yana shiga bedroom ya aje laidar saman bedside drowar yashiga bayi wan ka yayi a ɗan gaggauce kana yafito ya shiriya cikin wani danda tsatstsiyar yadi kalar lemon grind wan da tasha ai ki da farin zare da ɗan ratsin red a jiki kaɗan.

Yasaka hula kalar kayan yaɗaura wata tsadaddiyar a gogo a hannunsa, sai bakar takallimi feshe jikinsa yy da turaruka masu daɗin kamshi da kasha,
wayo yinsa yaɗiba dasuke kan mirror yazura ɗaya cikin aljuhu ɗaya kuma yarike a hannunsa,
Ya ɗau jakar system ɗin sa yarataye a kafaɗar sa kana yaɗau makullin mota yafita,

Direct parking lot yanufa da ɗan sauri kasan cewar yaɗan makara da zuwa offece ɗin, yashige motar yafice a gidan.

Bayan mun gama waya da Inna
Number'n Aunty Jalela dake kusa da nata na dannawa kira sai da yakusa katsewa kafin ta ɗaga.

Jin ta ɗaga yasani faɗin
"Hello Aunty Jalela nice HAMDAH ce".
tace "nasani ai ya akayi ya rashin jin magana?".
Baki na turo gaba cikin murguɗa bakin nace
"Nidai inajin magana dan nakiraki na faɗa miki abbu yasiya min waya shine zakice min haka, ko Ummi na ban kira ba ina gama waya da Inna naga Number'n ki kusa da nata shinefa na kira".
Nakarasa cikin ɗan ɗaga murya da gatsali kamar dai yanda kullum idan muka haɗu sai munyi faɗa.

Tace "To an ji ƴar masu baki ko yaushe ne zaki nutsu? Allah yasa ma kina tare da wan da zai gyara miki maza Allah yasa kiyi masa halin ya nakaɗa miki duka".
Baki nakuma turowa nace
"Daga kiran ki sai ki kama yimin sururu toma bazan sake Kiran kiba".
nakatse kiran ina ci gaba da mitar.


Cikin tsananin zakuwa da begen Aunty Rafee'at na danna Number'n ta
bai daɗe yana ringing ba ta ɗaga
sinkayo muryarta nayi daga cikin wayar tana faɗin
"Ah ƴargidan Inna kice dai har wayar tashi hannunki".
Dariya nayi nace
"La Aunty Rafee'at dama kinsan nice?".
Aunty Rafee'at tayi murmushi mai sauti kana tace
"Nasani mana ai ɗazu Abbu yakirani da layin yace min nakine".
dariya nakuma yi dafaɗin
"Ai ɗan ɗazu kaɗan Abbu yakawomin wayar".
tace "Kinji daɗi kenan?" nace "Naji daɗi sosai Aunty Rafee'at".
tace "Ah to madalla lallai yaukam kice waya zatasha danne-danne".
dariya mukayi gaba ɗayanmu.
Cikin dariyar nace
"Aunty Rafee'at kince zakizo kuma bakizoba".
"Zanzo a cikin satin nan, ina fata dai duk abin da nace kirika yin nan kinayi".
ɗan shiru nayi tace
"Iye HAMDAH kinayi kuwa?".
nace "Eh". tace "An ya kuwa?". nace "Allah da gaske"
tace "To har da girkawa Ya SALEEM tea in da nace".
ɗan shiru na kuma yi sai kuma nace
"To zan yi idan yazo zan girka masa".
"Yauwa ko kefa ko bai zobama ki girka ki kai masa ɗakinsa kuma ɗan abin makulashe idan kika girka shima kiɗan rika kai masa ko bai cibama watarana zai ci".

Nace
"Kai Aunty Rafee'at Aunty Na'ima cefa ke yimasa girki"
Tace "Ina ruwan ki da Na'ima ai bata isa ta hanaki girka masa ba kafin ya santa ai ke yafara sani kin fita kusan ci da shi ke dai kiyi abin da nace miki".
To nace.

nan muka ɗan taɓa hira daga bisani mukayi sallama jin an tada salla a masallaci yasani mikewa nanufi bedroom.

Ina shiga na a je wayar saman mirror sannan na nashige bayi ruwa na kunna yafara sauka cikin bath kana nasoma tuɓe kayan jikina ina gamawa nashige cikin bath ɗin da sauri dan na zaku najini cikin wuwan wan da yacika cikin bath ɗin tam.
zama nayi cikin ruwan naɗan ƙwantar da bayana na ɗago kaina nayi pillow da bakin bath ɗin ruwan yakawo min har haɓana.

Lamo nayi a cikin ruwan inajin daɗin yan da ruwan yake ratsa ko ina na jikina wutsilwutsil haka narika yi kamar mai yin iyo cikin kogi, nakai minti 30 a cikin ruwan kana namike na ɗau soso da sabulu wanke jikina koda nagama wanke lungu da sako najikina ruwa na sakarwa kai na daga tsayen da nake ya wanke kunfar sabulun, kana nafito daga cikin ruwan bawai dan nagaji da ruwan ba sai dun ganin lokacin salla natafiya,
nazaro towel naɗaura a kirjina al'wala nayi kana nafita a cikin bayin.

Gaban wardrobe na isa na buɗe naciro zani na kunce towel ɗin naɗaura zanin sannan na mai da towel ɗin bayi nashanya na dawo ɗakin nazura hijabi na shin fiɗa sallaya na tada sallah.

Koda na idar nacire hijabin tare da naɗe sallayar na ajesu ma ajin su,
gaban mirror na isa nazauna,
mai na shafa naɗan murza pauda a fuskata tare da ɗan goga man baki kan lip ina kana namike naje naciro wata doguwar riga robal material mara nauyi nazura bayan nasaka pan da bra,
gaban mirror'n na dawo na feshe jikina da turare kana naɗau wayata wan da duk abin da nake ida nuna na kansa naje bakin gado nazauna naja pillow nakwan ta,
nan nafara latsa wayar.

Number'n Ya Masa'ud na laluɓo nakai wayar kunne na gyara ƙwanciya ta lokacin da naji layin tashiga,
har kiran ta katse ba'a ɗaga ba, kuma mai da kiran nayi harna cire rai da ɗaukar wayar nasa jin wannan kiran ma na kokarin katsewa.

Acan kasar India
Masa'ud ne zaune cikin ɗan ma dai-dai ciyar parlour'n wan da yake masau kinsa,
littattafai ne a gaban sa ya mai da hankalin sa kansu sai dubasu yake,daga can cikin bedroom yarika jiyo sautin ringing ɗin wayar sa,
ture littafan yy gefe yamike tsaye yanufi bedroom
yatako gaban bedside drowar in da wayoyin sa ke ɗaure a kai,
ɗau kar wayar yy tare da zama saman bedside ɗin yy saurin ɗaga kiran yaka wayar a kunne.
fuska ɗauke da murmushi yace
"Kaji manya ƴar gidan Inna".
Baki nawashe jin abin da yafaɗa cike da mamakin yan da akayi yagane nice na kirasa tun banyi magana ba.
nace
"La Ya Masa'ud kai ma kasan nice?".
ya ce "Eh ai Abbu faɗamin wannan layin nakine".

Baki nakuma washewa kana nace
"To ykk ya India da mutanen garin".
Dariya yaɗanyi mai sauti kana yace
"Suna lfy zance kina gai dasu".
Yafaɗa da yanayin zulaya
"To". nace cike da jin daɗi tare da cewa
"Ya Masa'ud har yanzu baka kusa da wowa ba?".
Yace
"Nakusa in Allah ya yarda".
Nace to kakawo min tsaraba".
"Bakida matsala jaka guda zan ciko miki na tsaraba amarya to ya Yayan namu yake?".
Baki natura nace
"Nidai kabar cemin a marya ba kai ne kaki da wowa ba ai da ma Inna tace da kai za'a mana aure gashi kaki zuwa ammana da Ya SALEEM".

Dariya yy kana yace
"to ai dani da Ya SALEEM ɗin duk ɗaya ne"

Da sauri nace
"A'a kam ai kai kana dariya shikuma bayayi kullum yayita ɗaure fuska kamar dodo nidai idan ka dawo zancewa Inna amana auren da kai kawai".

Kai ya jinjina tare da mikewa yazo bakin gado yazauna
yana mai cigaba da dariya haɗe da zallar shauki da jin-jina shiririta irin na HAMDAH kodaga maganar ta zaka gane ɗin bin yarin ta tattare da ita,
yace
"To ai mace bata auren maza biyu a lokaci guda kuma nan gaba zakiga yana miki dariyar, ina dai baya dukan ki?".

Kai na gyaɗa kamar ina gaban shi kana nace
"Eh ai Inna tace duk ran da yabigeni sai tasa Abbu yabigeshi shima".

Yace "to kin ga bazai ma faraba tun da yasan idan yabigeki shima dukan shi za'ayi".

Dariya nayi har da buga cinya sai kuma na rike haɓa naɗan waro ido ina ɗan girgiza kai nace
"Cab Kato dashi ai sai dai Abbu yaɗau katon bulala in ba haka ba bazai ji zafi ba ko Ya Masa'ud?".

Yace "ai dama babban bulala zai ɗauka yan da zaiji zafi sosai".

Kai na jinjina alamar gamsuwa
Hira sosai mukayi da Ya Masa'ud sai dariya muke dan shi Ya Masa'ud bashida ɗaurewa.
Nan yace min yana karatu ne idan yagama zai kirana mukayi sallama na sauke wayar.

Yau kowa sai da yasan an siyamin waya dan ina katse kiran Ya Masa'ud Ummi na kira muka gaisa har da Fauzan.
Sannan na kira Mamei ita ma muka gaisa nasa tabawa Nusaiba.
Abba ne kiran karshe daganan na aje wayar gefe na gyara ƙwanciya ba jimawa bacci ya ɗaukeni.

Ban far kaba sai wajen karfe 5 alawala nayi nazo nayi sallar la'asar koda na idar nafito parlour na nufi kitchen, abinci mai saukin dahuwa na girka taliya ce miyar jajjage
ina gamawa nazuba wan da zan iya ci cikin plt sannan nafito parlour, TV na kunna kana nazauna nan tsakiyar parlour'n Ina cikin cin a bincin a ka kira sallar magriba, bayan na gama naɗau plt ɗin na kai kitchen nawan keshi kana na Mai dashi mazau ninsa sannan nafita na koma ɗaki.
Wanka nashiga ban wani jima cikin bayin ba nafito dan ban tsaya wasan ruwa ba yanzu, wata riga da wandon bacci na ciro nasaka rigar takai min har guiwa wandon kuwa dogone har kasa, sai hula mai raga dana murza a kaina.

Kasan cewar nayi alawala sai na shinfiɗa sallaya nazura hijabi nagabatar da sallar magriba ban tashi kan sallayar ba har sai da nagabatar da sallar Isha.

A ɓangaren Ya SALEEM karfe 6 yadawo daga offece koda yashiga bedroom in sa rage kayan jikin sa yy yafaɗa bathroom wan ka saosai yy da ɗan ruwa mai zafi dan son cire gajiyar daya ƙwaso.
Na'ima ta turo kofar tashigo jin motsintsa a bayi sai tafi takoma ɗakin ta dan dama waya take da wata a miniyarta jin da wowarsa ne yasa akatse wayar nan suka ci gaba da wayar su.

Shiko SALEEM ko da yafito wata farar tattausar jallabi yazura yanufi masallaci da sauri jin an tada salla,
da misalin karfe 8 yashigo gidan ta kofar side in sa ta baya yashiga batare da yabi ta babban parlour ba, yana shiga ɗaki ida nunsa suka sauka kan laidar da Abbu yabasa ɗazu zuwan sa yace yabawa HAMDAH,
ɗan guntun tsaki yaje har ya juya zai haye gado sai kuma yakuma juyowa ya isa in da ya aje laidar yaɗauka tare da kuma jan wani tsakin yanufi kofa,
takofar da yashigo tanan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login