Showing 6001 words to 9000 words out of 92896 words
tashigo cikin d'akin Nan a haka ta same Ka?".
tsaki yaja Ya ce "a haka mana".
Da fe kirji tayi ta ce "what tashigo cikin d'akin Nan takan ka zaune haka!
Wata ta ganka bayan ni!".
Rai b'ace yad'ago yazuba mata ido watoma ita ba ma da muwar ta bakin cikin da 'yarnan ta cusa Masa bane ita da muwar ta da ban na kishin ta take,
Ganin kallon da yake yimata yasa ta saurin suke bakin ta,
Yamike tsaye tareda d'aukar jallabiyar sa yazura ganin na kokarin fita yasa ta masowa da sauri kusa da shi tariko hannun sa cikin muryar buka tuwa ta ce "My love Ina Kuma zakaje Amma fa kasan mun Riga da mun shirya komai yanzu kawai fa Kai nake jira."
Juyowa yy yakalle ta saikuma ya janye hannun sa yajuya yaci gaba da tafi yafita a d'akin parlour yaje yazare igiyar caji,
Bin bayan sa tayi tana fad'in
"Haba Saleem katsaya Mana Amma fa idan kayimin haka baka kyauta min ba yakamata a ce ka ban lokaci na ba kafita ba" .
Ko sau raran ta baiyi ba yy waje a bin sa.
A parlour ya iske Inna zaune tana Jan carbi ya wuce ta da sauri yashige d'akin Hamdah.
Zunbur namike na zauna ganin yadda yafad'o cikin d'akin
Kokarin durowa nake a gadon Dan nagudu yy saurin ruko hannun na yashiga zubamin igiyar caji ihu nashiga zab gawa da iya karfi na Ina tsalle,
Shiko da gewa yy yarika zubamin igiyar cj.
Da sauri Inna ta shigo d'akin har tana had'awa da gudu hannu na da ke rike a hannun sa tashiga ja tana fad'in
"Kai Mai sunan Malan kanka d'aya kuwa saketa me tamaka kk Mata irin wanna duka ha".
Ko sau raran Inna baiyiba yarika shin fid'a min bulalar,
Inna ta dadda ge tashiga saka nin mu ta ce "had'amu ka buga duka"
Tajanyo igiyar cj tad'aura jikin ta ta ce "duke mu Mana Mara kunya gadon Lantai"
Fizge cazar yy Yana huce yanuna ni da hannu ya ce "wlh ban barki ba Allah ya kaimu gobe sai nayi Miki dukar sa'a".
Rab'ewa nayi a gefen Inna Ina rusar kuka idan nakalli hannuna da shatin bulalar yakwan ta sai na da d'a fasa kara.
Inna ta ce "yo ai yanzu ma kamar sa'ar naka kasamu duba kaga yan da ka da ge kk dukar ta kamar kasami sa'ar naka, wlh Mai sunan Malan saidai kahad'a da ni da ita dukan mu kabuga baka'isa kakuma dukan taba mara kunyar banza Mara kunyar hofi Mai zuciya kamar fad'a wuta".
Kwafa yy ya ce "wlh duk san da tasake shiga min cikin d'aki batare da sallama ko niman izini ba saina b'ab'b'alla ta Kuma daga yauma nasa Miki doka har idan nazo ban yarda nasake ganin kafarki a bokar d'akina ba".
"Inna ta ce "kaji Mata ciwo uban ka yy jinya, ko yy dai sai kun nuna halin Lantai a tare da ku kud'inama da taci sai Allah kawai".
Ya ce "wannan Kuma ke kk Sani ni Ina ruwana".
Yajuya yafita fuuu.
Inna tariko hannu na tazaunar da ni bakin gado ta ce
"Yihakuri kinji ai su sun iya karfin hali ba Lantai suka gado ba....."
Lantana wacce Inna take Kira da Lantai kakar su Ya Saleem ce tagurin uwa tun shekaru talatin da d'ori taci bashin daddawar Inna na d'ari da a shirin Bata biya taba har tarasu kullum idan 'ya'yan Mamie suka tab'ota saita goranta musu Mamie Tasha biyan kud'in ba a dadi haka Abbu hatta Abba da Ummi ma a duk san da tatashi maganar idan suna gurin suna bata kud'in da ya ninka kud'in daddawar ta, Amma bashi zaisa gobe tace tana bin Lantai kud'iba,
Tun Mamie tana da muwa har tacire a bun a ranta.
tun bayan rasuwar Lantai da kwana biyu a ke biyan Inna kud'in har Kuma yanzu sai dai idan 'Ya'yan Mamie basu tab'ota ba.
D'akin sa yakoma yahaye gado yakwan ta duk ransa a jagule Na'ima dake zaune tun d'azu a bakin gado ta haura gadon takwanta a bayan sa tasa hannu tana kokarin tab'ashi yabige hannun ta tareda buga Mata tsawa ya ce "matsamin anan!".
Mamaki yakamata Nan take wani muguwar tsanar Hamdah yadirar Mata a zuciya
Tabbas wanna yarin yar itace silar ruguje Mata burin samun Saleem na wannan Rana,
A ranta take fad'in "ni haka kawai nakejin yarinyar Bata kwan tamin a raiba lallai zan d'au mataki a kan ki!".
Washe gari su Ya Saleem suka bar garin ko sallama basuyi wa Inna ba.
Menene a salin wannan family?
Malan Abdullahi Turaki mazaunin cikin garin Dass ne dake jahar Bauchi'n Yakubu,
yanada matarsa d'aya Mai sunan Aisha da yaransu uku Idris Shu'aibu sai Hauwa'u
Idris wato Abbu shine babba sai me bimasa Su'aibu Abba kenan sai kanwar su gogga Hauwa,
Sun taso cikin so da
kaunar junan su
Sun Sami ilimi in gan tacciya wacce yakaisu ga samun ai
kin gamnati Mai tsoka a yanzu Abba da Abbu suna zaune a cikin garin
Bauchi da nasu iyalan ko wannen su na da mata d'ai-d'ai
Abbu da matarsa Hajiya Maryam wato Mamie suna da yara hud'u Abdallah wanda yaci sunan mahaifin
su Abbu a nakiran sa da Saleem shine babba sai Rafee'at Masa'ud sai autarsu
Nusaiba.
Abba da matarsa Hajiya Fatima 'ya'yansu uku sai da ta haifi biyu suka rasu kafin sauran ukun a yanzu dai
Jaleela itace babba sai Hamdah sai Fauzan.
Family'n suna zaune cikin kwan ciyar hankali da lumana, duk da tarin dukiyar
da suka Tara a cikin gi da d'aya suke rayuwa sabo da kauna da a mincin da ke sakanin su.
Bayan wani lokaci Malan Abdullahi Turaki Allah yakarb'i rayuwar sa family ta girgiza ba kad'an ba
bayan ar ba'in su Abbu sukaso d'auko Inna su mai da ta cikin gari fir taki ta ce subarta a in da tasaba cikin 'yan uwan ta,
Haka suka hakura badun sun soba lokacin da su Abba zasu koma gida sai ya yanke hukuncin bariwa Inna Hamdah Dan tad'ebe Mata kewa tareda nema Mata wacce zata Rika yimata ai yukan gida,
Duk karshen wata suke zuwa duba ta harda Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela da suke gidan maza jensu.
Wanna shine takai taccen labarin family'n.
★★★★★★★★★★★★★
Da sauri nafito da ga cikin kicking rikeda kofin kunun da na da mawa Inna nanufi d'akin ta cikin hanzari Jin tana laf tamin Kira,
a kwance na sameta tanata numfarfashi na iso in da take na ce "Inna ga kunun".
Ta ce "um..uhum yarnan wannan ciwo naga a lama bana kare bane kiramin Idris da Shu'aibu"
kiramun su marmaza".
Tafad'a tana turomin 'yar karamar wayar ta kirar TECNO,
D'aukar wayar nayi najuya baya Ina d'an dariya kasa-kasa Yan da takeyin ne yabani dariya saiwani Nishi take nikuma banga wani ciwon kirki ba.
Lanbar Abbu na danna ringing d'a biyu yad'aga tareda yin sallama na ce "inayini Abbu".
Ya ce "lfy lau Hamdah Ina Inna'r take?".
"Gatanan batada lfy ne tace wai nakira ku".
"Subhanallahi meke da munta?".
"Zazzab'i ne" nafad'a Ina Mika Mata wayar kafin ta karb'a ma tuni Abbu yakashi wayar,namika Mata kunu "inna gashi kitashi Kisha".
Tamike ta karb'i kunun tad'an tab'a.
A b'angaren Abbu Yana kashe wayar numbern family Dr su dake cikin Dass yakira batareda b'ata lokaciba yazo wa Inna da magani.
A wa biyu sakani
saiga su Abbu sun iso,
nafito da shirina nazuwa islamiya naji muryarsu a d'akin Inna na nufi d'akin da sauri ina washe baki
"La Abbu Abba kunzone?".
Nafad'a Ina kuma murmushi Abbu yy "mun iso 'yar Inna yau kina inane Baki taromu tun da ga wajeba"
"Ai Abbu ina Shirin makaranta ne Kuma banji shigowar ku ba".
Ya ce "to maza a je makaran ta ka da ki makara".
Na ce "tom".
Najuya nafita Abba dai komai baice ba sai dariyar da ya bini da shi.
Inna tamike zaune da kyar tana Nishi Abba ya ce "sannu Inna jikin neko?".
Gyara zama tayi tanafad'in "hum Shu'aibu jiki Kam haka za'ayi tafama dashi har Allah yakawo wa'a di yanzu ni babban da muwa ta a rayu wa bai wuce Hamdah ba
Itace kad'ai da muwa ta inata fata kafin Allah yad'au rayuwa ta naga auren ta da idanuna".
Sai tashiga Jan hanci tacigaba da fad'in "ina tunanin wanni hannun namiji Hamdah zata fad'a mazajen yanzu basa da rikon a Mana inasowa
Hamdah wan da zai
riketa da gaskiya da a Mana wan da zaiyi hakuri da Jin bakin ta, a Yan zu kuwa samun hakan
sai wan da yasan zafin maishi".
Gefen zanin ta ta Kama tasharb'e hanci sannan ta kalli su Abba ta ce "kuhad'a Hamdah aure da d'an uwan ta Masa'udu inada tabbacin shi zai riketa da a Mana tunda shi yasan zafin ta".
Abbu ya ce "to shikenan Inna insha Allah kamar Yan da kk fad'a za'a had'asu idan suka kammala karatun su".
"Wani karatun? Idris harsai namutu kenan ni ban yar da ba idan Kuma baso kuke ku nunamin kun fini iko da 'ya'yanku bane".
Abba ya ce "a'a Inna ai damu da 'ya'yan mu duk mallakin kine baki dai fahimci abin da yake nufi bane".
"yo wani irin famimta kuke so nayi ai na famim ceku baso kuke saina mutu tukun kuyi ba".
tafad'a tana kokarin mikewa,
Da sauri Abbu ya ce
"Yihakuri Inna ko gobe kika ce a d'aura auren sai a d'aura Amma gawani shawara".
Jin haka yasa Inna gyara zaman ta
Abbu ya ce "kinga yanzu Masa'ud Yana India sai Nan da shekaru uku zai kammala karatunsa ya da wo idan ya da wo sai a d'aura auren ko ya kk ce Inna?"
Shiru Inna tayi zuwacan ta ce "to shikenan in da rabon nagani da numfashi na to................
Mommyn Twins ce
*🌺HAMDAH🌺*
*NA*
*RASHEEDA S DIRECTOR*
_(Book one)_
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*AL'FARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*
🅿️4
Tun da Inna tafara ciwon Nan kullum Nike da ma Mata kunu da safe duk da kuwa yanzu tasami lfy Amma Bata fasa ta da ni da sassafe wai na da mamata tunun ba,
ko bacci nake saita sa Fatu ta ta dani haka Ina mita zanje na da ma mata,
Ko yanzu ma motsin Fatu naji tana kokarin shigowa d'akina nayi saurin rufe Ido na.
Ta turo kofa da ga bakin kofar tatsaya ta ce " Hamdah wai kitashi inji Inna ki.."
Huf namike batare da nabari ta tarasa fad'ar a binda zata fad'an ba Fatu naganin haka tayi ficewar ta, nasau ko a gadon da sauri nafito d'akin Inna na nafad'a tana zaune a kan kujera tana Jan jarbi
Hannu nayarfe tare da fad'in
"Inna nifa bani da lfy to tun da ga Fatu basai ta da ma Miki ba ni kenan kullun-kullun da safe sai kin d'agani ni Kam bacci nakeji Yan zu".
Nafad'a Ina tura Baki gaba,
"Yo Mara lfyr haka yake duba fa kiga Yan da kk shigomin d'aki kamar Zaki fad'o min a ka,
To Ina am fanin baccin safen ma in ban da ya kara miki muguwar lalacin Nan naki shiyasa nace a had'aki da d'an uwan ki in ba shid'in ba wazai iya da halinnan naki na son jiki".
Turo Baki nakuma yi najuya Ina buga kafa nafita kicking naje na tad da Fatu harta d'aura ruwa har Yana tafasa,
Kunun na da ma Mata nakai Mata.
Ina gama karyawa wanka nayi nashirya da sauri nad'au mayafi na nafita Dan nasan har idan ina gidan tofa sai Inna ta ce muyi ai ki tare da Fatu,
Gidan su Rabi nanufa a gindin bishiyar kofar gi dan su na isketa zaune
Rike da waya a hannun ta tana kallo Baki na washe
"La Rabi wayan waye a hannun ki?".
Nayi tan bayar Ina zama kusa da ita
Ta ce "wayar Ya Maheer ne".
Kuma washe Baki nayi na ce "la laushe yazu?".
Ta ce "jiya da daddare yanzu yabani nakai masa caji".
Kuma gyara zama ta nayi na da d'a sauke ida nuna a cikin wayar sosai
Yayin da na Mai da han kalina gaba d'aya kan Shirin da a ke a cikin wayar duk da kuwa ba hausa (film) bane
Mace ce da na miji
Suketa ai kin shafa junan su yayin da bakin su ke had'e da juna,
Ido na waro sai na Mai da dubana kan Rabi na ce "Rabi Yan iska nefa".
Dariya Rabi tayi ta ce "hum soyayya sukeyi dai".
"Soyayya".
Na nanata kalmar ta ce "E mana". Nabud'i Baki da zummar Kuma yin magana muka jiyo muryar Ya Maheer wato Yayan Rabi da sauri tamike tayi hanyar shagon caji,
Nikuma nayi hanyar gida.
Tafiya nake yayin da (film)in da na kalla ketayimin yawo a Ido can Kuma cikin kwakwalwa ta kalmar da Rabi ta am Bata na soyya ita keta zirga-zirga cikin ta.
Ina shiga gi da d'aki nawuce nafad'a saman gado har a lokacin kwakwalwa ta da idanuna basu fasa baiyanomin wad'an Nan mace da namijin da na gani da a binda sukeyi da Kuma kalmar soyayyar da
Rabi ta am batamin ba
Juyi nayi a fili na furta
"Wannan shine soyayyar?".
Nayiwa kaina tan bayar Ina maikuma juyi a kan gado.
Ranar haka nawuni cikin tunanin wani a bin da ni kaina ban sanshiba....
Bauchi
Abba ne da Abbu zaune a parlour'n Abbu Kamar Yan da suka Saba a duk San da suka dawo daga gurin ai ki a parlour'n Abbu suke fara ya da zangon su kafin su shiga ciki gun iyalan su.
A cikin hirar da suke ne Abbu ya gyara zaman sa ya dad'a fuskan tar d'an uwan nasa da kyau ya nisa ya ce "Shu'aibu nifa wani a bu na da mina
Tun ranar da Inna tayi Mana magana a kan auren yaran Nan han kalina yakasa kwan ciya,
Idan baka man taba kwatan kwacin haka yatab'a faruwa lokacin daf da rasuwar Baffa kwatan kwacin maganar Inna shi Baffa yayi ya ce mu aurar da Rafee'at da Jaleela tun Yana da numfashin sa bamu d'au maganar da wata girmaba sai bayan rasuwar sa muke ciza yatsa,
To gashi Inna ma nakan maimaita kalmar kada muzamo 'ya'ya marasa biyayya ni nagama yanke hukun ci za'a d'aura wa yarannan aure juma'ar da zatazo Nan da kwana biyar idan shi Masa'ud in ya kammala karatunsa ya da wo sai a yi biki ta tare ko yakagani?".
Abba ya ce "wlh Nima a bunnan Yana Raina wanna hukun cin da kayan ke shine dai-dai Allah yanuna Mana ranar".
Nan suka tsara duk Yan da d'aurin auren zai kasan ce.
Cikin kwanaki uku a ka gama turawa 'yan uwa da a bokan ar ziki katunan gayysta da a ka buga.
Tun da nasami labarin za'a d'aura Mana aure da Ya Masa'ud a cikin satin da muke narika zan Dara ihu sai da natara makota ca
Inna tad'au bulala tabini da shi tana fad'in
"Ina ga halin naki idan ba d'an uwan nakiba wazai iyamiki".
nafita a guje nayi gidan su Rabi har na isa gidan ban fasa ihun danake ba Maman Rabi da ke tsakar gida tana aiki tad'ago cikin han zari tazo inda nake tariko hannuna ta ce "me yafaru *HAMDAH* wayarasu!?".
Tayimin tan bayar hankalin ta a tashi
tsaida ihun da nake nayi naturo Baki gaha na ce "wai ba aure za'ayimin da Ya Masa'ud ba".
Numfashi Maman Rabi tasauke ta ce "wlh harkin tsoratani nad'auka rasuwa akayi to inban da abinki Dan za'ayi Miki aure sai kibi layi kina ihu bakison auren kenan?".
Shiru nayi Dan nikaina bansan dalilin uhu naba bazan iya tantance shin son auren nake ko kinsa ba kawai ihun zuwarmin tayi nakama yinta.
Ganin nayi shiru sai tasaki hannuna tana fad'in "jimin yarinya da tsiya salon d'agawa mutane hankali ca nake mutuwa akai idanun ta babu ko kwalla wai tana ihu".
Ban Kuma bi takantaba nayi gun Rabi dake tsaye bakin kofar d'aki itama Jin ihu nane yafito da ita nawuceta nashige d'akin tabiyo bayana zama nayi bakin katifa itama tazauna
Dad'a gyara zamata nayi tareda washe Baki Kamar banice nagama ihu yanzu ba, cike da zumud'i na ce "yauwa Rabi ina wayar Nan kunnan Mana muga soyayyar Nan wan da ranar muka kalla a can gindin bishiyar kofar gidan ku".
Rabi ta ce "ai wayar Ya Maheer ne ai jiya yakoma birni".
Na ce "ayya yanzu yakoma wlh inso nasake gani
Nima inaso nayi irin soyayyar da naga sukeyi".
Ta ce "ke ance masu aurene kad'ai sukeyi wan da Basu da aure Kuma 'yan iskane".
Shiru nayi Ina nazarin maganar ta "wato masu aurene kad'ai sukeyin hakan?".
Nayi maganar a cikin zuciyata,
Sai Kuma nasheke da dariya harda tafa hannu na ce "la to ai shikenan idan a ka Mana aure da Ya Masa'ud sai muje munayi"
Dariya Rabi tayi ta ce "da gaske zakuje kunayin soyayyan".
Na ce "Eh Mana".
Sai yamma nabaro gidan su Rabi a kofar gida na had'u da Inna da hijabi a kanta Ina ganin ta nasan biyoni tayi hannuna tariko tajanyoni muka shiga cikin gida
tana surfemin masifa wai zaman me nake da almuru a waje.
duk da kuwa cewa aure kawai za'a d'aura banda biki hakan Bai Hana 'yan'uwa zuwaba su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela tun ranar laraba sukazo kan ranar Alhamis gida yacika Tam da 'yan'uwa washe gari Juma'a bayan an sauka daga sallar juma'a da misalin karfe 2 jama'a ne tam kofar gidan Malan Abdallah Turaki,
tuni aka fara gudanar da aurin aure yayin da hankalin al'umma gabad'aya ya koma kan shaidar d'aurin auren da suke
"Alhamdulillah² munshai da aurin auren *ABDALLAH* Idris Abdallah da *HAMDAH* Shu'aibu Abdallah uban giji Allah yabada zaman lfy".
Wanna kalmar ne ke fita daga bakin manyan limaman dasuka ziyarci d'aurin auren,
A razane yaciro wayar dake kare a kunnen tun isowarsa gurin yaketa amsa Kiran abokan sa wad'an da Basu Sami halartar d'aurin auren ba suna tayasa murnar auren kannensa dazai gudana ayau.
Kamar a mafarki yaji an Dan gantashi da auren da yanzu a ka d'aura cikin hanzari yashiga kusawa cikin jama'ar hankalinsa a matukar tashe ta'in da sautin kefita yanufa hannun wani mutun yarike dake kokarin fita daga gun,
Mutumin yajuyo Yana Masa kallon mamaki ganin yarike Masa hannu
Dad'a rike hannun nasa da kyau yy ya ce "Dan Allah wa akace an d'aura auren sa yanzu?".
Mutumin ya ce "kai da kazo shaidar aure baka ba da hankalin ka wajen karb'ar shaidar ba to *ABDALLAH*