Showing 39001 words to 42000 words out of 92896 words

Chapter 14 - HAMDAH part 1 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

11900

wajen garashi ba, ina gamawa nafito muka ƙwashi kayan da goggo Hauwa muka shiga da shi ciki.sai min tsiya take wai ni na ƙwashe musu uwa gashi tace bazata gidan ƴaƴan taba a guri na zata zauna,
Ni dai sai dariya nake dan yau ina jina cikin masanan ciyar farin cikin zuwan sun,
muna gama shiga da kayan muka dawo parlour'n, nan Inna ta cicciro min tsarabar da ta zomin da su, nata murna wan da zan iya ci naci a gun sauran nakwasa naje na aje.
sai da a ka kira sallar magriba kafin Inna tashige ɗakin da a ka buɗe mata,nima can nabita wanka da sallah ma duk a can nayi.

Ina makale da Inna mun raba dare muna hira, nan Inna ke faɗa min an sa auren Rabi wata mai kamawa za'a yi bikin,nace in Sha Allah zanje bikin,
Ranar kam a ɗakin nakwana, washe gari da sassafe nashiga kitchen nashirya mana breakfast muna zaune bayan mun yi breakfast, Ya SALEEM yashigo da sallama.

Yakaraso ya zauna kan ɗaya daga cikin kujeru 1-1str da ke cikin ɗakin, goggo Hauwa yafara gai sarwa sannan ya gai da Inna tare da saka hannun sa cikin aljuhu ya zaro goro da ke ɗaure cikin laida ya mika mata,ta amsa tana faɗin
"Ma dallah Allah yayi albarka".
hira Inna tashiga yi masa shi dai um yake bin ta da shi
kamar mai ciwon baki.

Tun shigo war sa Idanu na na kan waya ban ko ɗago ba, sai da naji an ɗan dungure kafata, naɗa go sai naga goggo Hauwa ce,
nuna min shi tayi da ido kasan cewar muna jere da ita.
"Baki ganshi bane ko kinje kin gaishe shi a ɗakin sa ne?". rausayar da kai nayi kana nace
"Ina ƙwana Ya SALEEM".
bai amsa ba sai ɗaga kiran da yashi go wayar sa yayi yamike yafita.
Baki na taɓe
Na mai da idanu na kan wayar nacigaba da a bin da nake.

ƙwanan su Inna uku da zuwa sai a ranar na ukun Na'ima ta zo ta gaishe su, shima ɗin sai da Inna ta tanbayi Ya SALEEM ko bata gidan ne, bayan fitar sa shi ne tazo.

Zaune muke a ɗaki yashigo kamar yan da yasa ba tun zuwan su Inna, zai shigo da safe kafin yatafi offece, bayan ya dawo daga offece ma zai kuma shigowa,sai dai yau ga dukkan alamu da shirin fita yashigo dan ko zama bai yiba yagai shesu yajuya yana kokarin fita, Inna tace
"Mai sunan malan kazo min da goro wan da ka kawo min ranar ya kare".
To kawai ya ce yayi waje.

Bayan sallar Isha muna zaune Inna ta dubeni tace
"Tashi maza kije ki karɓo min goro gun Mai sunan malam, ni na iya irin wannan zama babu a bun mosa baki".
mikewa nayi nafita.

Ina fita daga ɗakin yana turo kofar parlour'n,naɗan tsaya yakara so ciki ganin yana kokarin wucewa ɗakin da Inna take ciki nayi saurin cewa
"Ya SALEEM wai kabani goro in ji Inna".
ɗan gajeren tsaki yaja sai ya juya yasoma tafi har yakai bakin kofar parlour sai yace
"Zo ki karɓa mata".
yafaɗa tare da buɗe kofar yafita.

Bedroom nawuce na ɗau hijabi na zura kan doguwar rigar baccin da ke jikina nayi waje,ina fita na hango shi tsaye rike da waya a kunne Shi dai kullum da waya a kunne. In da yake na nufa lokacin shikuma ya sauke wayar daga kunnen shi yashige cikin side ɗin shi, nabi bayan shi da sauri ina shi yana shigewa cikin bedroom ɗin sa, sai naja natsaya a sakiyar parlour'n.

Ido nayi ta zubawa kofa dan ganin fitowar sa amma shiru,har nafara jin kafafuna sun gaji da tsayuwa,a sannu na taka na isa bakin kofar, na daura hannu na jikin kofar nasoma knocking a hankali har sau uku kafin na sau ke hannuna,shiru bai buɗe ba nakuma ɗago hannu zan kai jikin kofar, sai ya buɗo kofar da karfi tare da riko hannu na ya fizgo ni cikin bedroom ɗin,yamai da kofar yarufe sai ya tura Ni jikin kofar ya manna baya na da jikin kofar, yayin da hannunsa guda ke rike da nawa,ƙwayar ida nunsa yasanya cikin nawa yana yimin
Kallon cikin ido,
sai kuma ya furzar da iska daga cikin bakin sa kana yace
"Jiranne bazaki iyaba sai kin ƙwanƙwasa min kofa?".
Kai nashiga girgizawa dan narasa ma me zan ce dan tsoro.

Ida nunsa ya janye cikin nawa sai ya juyar da kansa gefe, tare da kuma furzar da iska, sai ya saki hannuna ya juya.
numfashi'n tsoro na sauke jin yasaki hannu na dan nagama ɗauke wuta kan cewa buguna zaiyi,
lai da ya ɗauka kan mirror yamika min da sauri na amsa na juya da sauri sai naji ya..............





Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*




My no 08034690723




🅿️15




Ya kuma rike min hannu tare da juyo ni,har sai da na ɗan garu da jikin sa, nayi saurin ja da baya sai naji kofa ta tare ni, gani na daf da shi ba karamin tsorata nayiba,
fuska ya suke tare da faɗin
"Abin banza ne Ba kuɗi a kasa a ka siye shiba".
jin a bin da ya faɗa sai nayi saurin ɗagowa na kalle sa, ba shiri nayi kasa da kai na ganin ni yazuba wa ido fuskar sa kuma a suke,
"Zaki ɗau ka ne ko tsayuwar zaki cigaba da yi".
Da sauri na kalli in da yayi nuni da yatsar sa goron ce kwara huɗu a kasa, saurin kallon lai dar da goron ke ciki nayi sai naga laidar taɓule ta kasa, bani raba ɗaya biyu garin saurin da nake ne handle yaɓula laidar, da sauri na zame kasa nashiga tsino su.

Hannun sa ya ɗago yacusa cikin sumar kansa yayin da ɗaya hannun sa ke rike da gungun sa, a hankali ya juya yasoma tafi wata kofa naga yashiga wacce nafi zaton bathroom ne,
ina ganin shige warsa nayi saurin mikewa na fice daga cikin ɗakin da sauri,
Ina fita naja wani irin wawan burki kaɗan yarage muyi karo da Na'ima da tasako kai tana kokarin shiga ɗakin,
Cikin wani irin masha huriyar tsananin tarin mamaki take bina da wani irin kallo wan da yafi kama da kollon tuhuma.
Gefen ta na raɓa nawuce da sauri nafice gaba ɗaya daga cikin side ɗin.


Bayan ta tabi da kallo har taɓace wa ganin ta,wani uban numfashi tasauke tare da furta
"Kutumar uban can uban me take a nan".
Da sauri ta bankaɗe kofar tashiga kamar wacce a ka wurgo,sai tashiga bin ɗakin da kallo yayin da takejin zuciyar ta yana wani irin tafarfasa,
HAMDAH har cikin maƙwancin minta lallai tayi mugun yin sake.
tawani taune baki tare da yin ƙwafa, jin saukar ruwa a bayi yasata nufar kofar bayin ta tura kofar da karfi tasako kanta ciki.


Dai-dai lokacin yakashe makunnin panpo dake sauka a kanshi, yazaro towel ya ɗaura a kugun sa, kana yatako yaraɓa gefen ta yafice daga bayin.
Sai a lokacin Na'ima tadawo daga mutuwar tsayen da tayi tana kallon shi, wani irin juyi tayi tarufa masa baya,
tasha gaban sa dai-dai lokacin da yake kokarin zama bakin gado,
da mamaki yaɗan kalleta ganin yan da ta wani sha gaban sa tana bin sa da kallon tuhuma.

"SALEEM me wannan yarin yar take a nan mekuma wannan wankan yake nufi".
Ta jefo masa tan bayar tana girgiza da cika da basewa.
ko mai bai ceba, sai mikewa da yayi yaje yaciro kaya yasoma sawa,
bin sa ta kuma yi cikin ɗaga murya take faɗin
"SALEEM nace menene dalilin shigowar yarin yarnan ɗakin nan ban gane bafa, kafa dai na rai namin hankalin wai...."
Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu batare da yabar ta ta karasa faɗar a bin da take son faɗa ba,dan surutun ta yasoma yi masa yawa, yayi mata a lama da hannu tafita,
Kugu ta rike tana faɗin
"Eh dole kace na fita, sabo da a sirin ka yana daf da tonuwa,na rantse baka isa ka rai namin wayo ba".

Wani uban tsawa ya buga mata da sai da ta taune harshen ta da ta buɗe baki zata kuma ci gaba da maga na.
yatsar sa ya kaɗa tare da nuna mata kofa cikin tsawa yakuma faɗin
*"get out!!"*
Kame-kame tashi ga yi sai kuma tajuya ganin babu a lamar wasa a kan fuskar sa, ta fice tana ciza baki tare da ban ko kafar da karfi.
tsaki yaja ya haye gado ya ƙwanta.


Yau tun da safe goggo Hauwa ta shirya ta tafi gidan su Abbu ganin Inna bata da niyar zuwa,
Da yamma ina ɗakin da Inna take in da nanne yanzu yazame min gurin wuni wani sa'in ma har da ƙwana,
Inna na zaune a bakin gado tana jan jarbi, Ni kuma ina
ƙwance a gefen ta rike da waya ina chatting da ƴan ajin mu,
ɗan gajeren tsaki naja ganin an ɗauke wuta nan da nan kuma zafi yaziyar ci ɗakin,mikewa nayi zaune ina faɗin
"Kai gaskiya yau a na zafi daga ɗau ke wuta ji yadda zafi ya cika ɗakin".
Inna da ta fara ɗan gyn-gyaɗi a zau ne ta buɗe ido tana faɗin
"Ai kam garin a tsaye yake cak sai dai da alama in Allah yaso zai bamu ruwa dan ga hadari na yawo a sama".

"Allah ya kawo shi bari nidai na wasa ruwa gas kiya ina jin zafin nan sosai".
nafaɗa ina zamowa bakin gadon,sam bana shiri da zafi kaɗan ne yake tada min hankali,
Doguwar rigar jikina na zare yarage daga ni sai sket ƴar ciki da bes. nanufi kofar bayi.
baki buɗe Inna ke kallona kana tace
"In ba kalen muraba
ina wani zafin da yan zunnan kikayi wanka kikuma yin wani, wato baki dai na wasan ruwan nan naki bako".
Shigewa cikin bayin nayi ina faɗin
"Kai Inna zafi a ke fa".
"Allah shi sawaka, da kan ka karika kalo cuta wa kan ka".
Ina jin ta tayi ta surutun ta.

Abin da Inna ta hasashon shi nayi dan kuwa shigewa cikin ruwan nayi na zauna, naɗau lokaci kafin na wanke jikina da zallar sabulo na fita a cikin ruwan na mai da sket da best ɗin da nacire nafito.

nakaraso bakin gado in da na a je rigata na mika hannu zan ɗau rigar, yaturo kofa da sallama,
Inna ta amsa tare da gyara zama tana faɗin
"An dawo ne mai sunan malan". da sauri na juyo karaf muka haɗa ido,
cikin hanzari na ɗau rigar nanufi kofar bayi, na zunɓuro baki ina kunkuni cikin wuya.
"Shi ya'iya cewa wani wai in mutum zai shigo yayi sallama ya tsaya kafin ya shigo amma ai gashi shi da ga yin sallamar ya shigo".
Baki na murguɗa
nashige cikin bayin na mai da kofar na rufe.
Ina saka rigar na fito sai na tadda shi zaune Inna na kan zuba masa hira shiko na ai kin latsa waya,
ɗan ƙwali da waya ta na ɗau ka na raɓa ta gefen sa nayi waje,
Bedroom ɗina na koma naci gaba da chatting ɗina....
Tun da nashiga ban kuma fitowa ba sai da naji da wowar goggo Hauwa...★


Yau farin ciki na ya daɗa karuwa dan kuwa ƴan gidan mune suka taho gaba ɗayan su,duk muna tare a ɗakin da Inna take.
Abbu Mamie Abba Ummi Fauzan Nusaiba,
Ina zaune a sakiyar ahalina yayin da zuciya ta ke cike tap da farin ciki.
Bakina yakasa rufuwa sabo da sabar murna, kusan wuni sukayi a gidan kasan cewar yau karshen mako ne,
Ko da zasu tafi sunyi-sunyi su tafi da Inna taki fir tace suje zatazo gada baya, in taga ma yimin ƙwanakin da ta yanke zata yi min kafin za tazo..

Ranar da Inna tacika sati ɗaya, tun da safe tasa goggo Hauwa tashirya mata kayan ta.
Ina zaune a gefen ta nayi shiru kamar ruwa yaci kai na,
kallon Inna nayi cikin marairaice murya kamar zanyi kuka nace
"Ayya Inna karki tafi yau kikara wani sati dan Allah".
dariya goggo Hauwa tayi tare da cewa
"To kece za a zau na a kare miki kwanakin a nan sannun ki fa".
Muskutawa Inna tayi tana faɗin
"Sati guda zan musu na dawo daga nan kuma nayi shirin koma wa gida".
Kamar an zabure ni na mike nace
"To shike nan ni bari na shirya kayana mutafi gidan to".
da sauri goggo Hauwa tace
"Ki shirya kayan ki kibi wa da izinin wa kuma?".

Baki na ɗan zunɓuro sai kuma nayi saurin cewa
"To ai rakaku zan yi".
"Ai ho to ai sai dai in rakiyar".
Waje nayi ina faɗin
"Ai dama rakaku zanyi na dawo".
A kasan rai na kuwa faɗi nake
"Ai idan natafi bazan dawo ba sai dai mu dawo tare".

Tun da a kayi sallar Isha nakasa zama alla-alla nake muyi mutafi, haushi na ɗaya da Inna tace Ya SALEEM ne zai kai mu gashi har yanzu bai zo ba.

da sauri nafito daga cikin bedroom, na tako bakin kofar da Inna take daga bakin kofar na tsaya ina faɗin
"Inna nikam fa na gama shiri na kuzo mutafi kawai tun da Ya SALEEM ɗin bai zoba".
Nafaɗa ina shiga cikin ɗakin,cak naja na tsaya daga bakin kofar ganin sa tsaye da alama fita zaiyi, goggo Hauwa narike da jakar Inna ita kuma Inna tana gyara zaman mayafin ta,baya nayi a han kali,
shiko yasako Kai yafita muka rufa masa baya.

Ko da muka zo gurin mota kokarin shiga baya nake, goggo Hauwa tace nashiga gaba ita zasu zauna da Inna a baya,babu musu na shiga dan ina alla-alla na ganni a gida,
jakata na da ɗa makale shi dan nasan goggo Hauwa tana gani zatayi magana.
A hankali yayi wa motar ki muka fita a gidan,ganin mun ɗau hanya farin cikina yagaza ɓoyuwa sai murmushi nake,
muna isa nariga kowa sauka nayi sashin Ummi na da sauri, su Inna Kuma sashin ta dake cikin gidan suka nufa ita da goggo Hauwa.

A parlour na tadda Ummi tana ganina tamike tana faɗin
"Har Inna'r ta iso kenan".
"Eh tana part ɗin ta".
nafaɗa ina karaso wa ciki, Ummi ko kofar fita ta nufa,
aje jakata nayi saman kujera, na bi bayan ta muka tafi part ɗin Inna,a nan muka tadda su Mamie,hira sosai a ke cike da jin daɗi da kaunar juna,
ko minti 5 ban yi da zama ba Fauzan yashigo da gudu yace
"Aunty HAMDAH wai kizo".
tun kan na am sa yajuya yayi waje da gudu.

Bayan sa nabi da sauri ina faɗin
"Kai wake kirana".
nafaɗa da karfi.
bai tsaya ba bai kuma amsa ni ba sai da ya isa jikin motar Ya SALEEM, in da shi ke jingine jikin motar,
ɗan nesa da su naja na tsaya.
A bu ya mikawa Fauzan daga in da nake tsaye bazan iya gane ko menene ba kasan cewar dare ne gurin kuma babu hasken wuta sosai,
ga yanayin yan da Fauzan ɗin yakarɓi a bun yajuya da murna yayi sashin Inna, nasan komai a kayi abun ƙwalama ne.

Ina tsaye ban koma ba ban kuma karaso ba duk da nasan cewa shine mai kira nan, gefen direver yazaga yabuɗe marfin sai yajuyo in da nake yaɗan kalle ni
"Naci gaba da jiran ki kenan".
ido na waro jin a bin da yafaɗa sai kuma naturo baki nace
"Nifa kwana zanyi"
wani kallo ya wurgamin
tare da shige wa cikin motar batare da ya kuma cewa komai ba.

Tuni idanuna suka ciko da ƙwalla, ganin yata da motar sai na karaso jikin motar nabuɗe nashiga, muna fita a gidan hawaye suka fara gangarowa kan fuska ta,
har muka isa hawayen bai tsaya ba,yana dai-dai ta parking nafito daga motar da sauri nanufi kofar side ɗina, ina ɗaura hannun na kan handle natuna nabar makullin side ɗin a cikin jaka a parlour'n Ummi,
dasauri najuyo dai-dai lokacin yafito daga cikin parking space yana kokarin wucewa side ɗin sa,daga in da nake tsayen na dubeshi tare da share hawayen da yazubo min nace
"Nabar key ɗin kofar a gida".
tafiya yasoma tare da faɗin
"To sai ki ƙwana a gurin".
baki buɗe nabi bayan sa da kallo har yashige side ɗin sa.
"Naƙwa na anan, ai na rantse gida zan koma".
Najuya da sauri da niyyar nufar get sai kuma na tsaya ganin karfe 10 tayi nasan ko na fita ma ba lallai bane na sami a bin hawa,wani hawaye naku maji na zubo min, baya nayi sai na zame na zauna kan step ɗin kofar,nacusa fuskata sakankanin cinyoyina,jin wani
kuka ya zo min sai kawai na fashe da kukan...★

A hankali narika jin kamshin sa na masoni,zuwa can sai naji motsi kusa da ni. duk da nasan shine dan kamshin sa ya sanar min da hakan,
ban ɗago ba sai ma sautin kuka na da nakara,
Jin karar buɗe kofar sai na ɗago da sauri dai-dai lokacin yake zare key ɗin da yabuɗe kofar da shi,
da sauri na mike na sako fata saman step ɗin da yake kai tare da jan guntun tsaki, nawuce shi nashige ciki da sauri.


Direct bedroom na shige cike da bakin cikin a bin da ya min, nayi niyyar kwana a gida amma yahana ni yaɗau koni yadawo da Ni sannan kuma yace wai na kwana a waje,
Ina shiga ɗaki nazube kan gado naci gaba da kuka na.

Da karfi a ka turo kofa jin kamshin sa yasanar min shine, yatako bakin gadon sai ji nayi ya zauna daf da ni kokarin, matsawa nake dan jin yan da yamannu da jikina sosai, sai jinayi ya yasako hannun sa ta kasan ciki na yaɗa go ni gaba ɗaya ya rungume ne tare da
matseni da karfi har sai da naɗan saki kara, cak na sai da kukan da nake sa bo da tsoro mai haɗe da mamaki, ban kaiga dawowa daga duniyar mamakin da natafi ba naji ya sauke hannun sa kan.......★




*Kuyi maneji bayawa*
*Gaskiya yanzu ina busy bana da time sosai ba lallai bane kurika jina kullum*





Mommun Twins ce



*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login