Showing 90001 words to 92896 words out of 92896 words

Chapter 31 - HAMDAH part 1 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

11914

ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnen ta tare da faɗin
"Hello".
Daga cikin wayar Raliya tace
"Aminiya akai kyakkyawar albishir yanzu muka gama waya da malam na kan tudu yake cemin yadawo daga gurin ai kin da suka tafi".
da sauri Na'ima ta mike tana faɗin
"Ai kuwa wannan babban albishir ne kinci tukuicin yanzu kuwa zan je gurin sa wlh kar jiki yan da naji dama hakuri yana daf da karewa".
Raliya tace
"To muhaɗu a gurin sa dama nima akwai wani Alhaji'n da nake so yayi min ai ki a kansa yashigo hannu".
Na'ima tace
"Ai kuwa yanzu ma kuwa".
tafaɗa tare da kashe wayar tashige ɗaki da sauri tazari makullin mota da mayafin ta tafita,tashiga motar ta ta ɗau hanyar gidan bokan ta...

A kusan tare suka iso da aminiyar nata dan suna ta waya da junan su tun a hanya hakan yasa suka iso tare.
kamar koda yaushe suna fita acikin motocin su suka tuttuɓe takalmar su kana suka nufi bukkan malam na kan tudu.
suna zaune a gaban sa sun naɗe kafafun su kamar masu neman gafara shiko sai surkullen sa yake kana daga bisani ya ɗago ya dubesu yace
"Meke tafe daku yau nasan dai ai kin ku na wancan karo yaci".
Na'ima da tun ɗazu taketa alla-alla bakon yaɗa go ya saurari bukatar su, ta gyara zama tace
"Boka akwai babbar matsala ai ki yaciwu da farko sai kuma gata da ciki daga baya narasa ta yan da akayi hakan ya faru, ta daɗa kanainaye shi bakaga yanda yake rawar kafa a kantaba,daga shi har iyayen sa kamar basu taɓa ganin ciki ba sai a kan ta,
boka nikam na kaɗe ka tai make ni kamar yadda kasaba tai mako na".
Wani irin dariya ya kece dashi kana yace
"Ai dama nasan za ayi haka dan nagani tun ranar".
da mamaki suke kallon sa dajin abun da yafaɗa gusar musu da mamakin su yayi da cigaba da faɗin
"Ai tun ranar da nayi bincike nagano tana da ciki to abun da yasa ban sanar muku ba naga hankalin ki a tashe ne kinaso ayi-ayi miki ai kin shiyasa,
tun wancan lokacin tana da shigan ciki sai dai karami ne sosai lokacin satin sa biyu ne kacal,
Sai nayi amfani da hikimar mu nayi miki ai kin,
muka ɗaure cikin har sai ranar da kwai ɗin da na baki yafashe kafin muka sake shi,in da koda asibitin duk duniyar nan za'aje lissafin daga kan wannan ranar da kwan yafashi zai nuna musu wa'adin shigar cikin acikin ta".
wani dariyar yakuma kecewa kana
yasoma zane-zanen kan kasa da bubbuga shi sannan yace
"Sai ku lissafa kwanakin da kwan yafashe shine watannin cikin sai dai akwai ɗaurin saki biyu in da babu wan da yasan dashi sai mu, mun so mu ɗaure cikin ne ƙwata-ƙwata in da bazai tashiba sai dai hakan bai samu ba dan aljani durkus ya kauce a lokacin".
shiru sukayi kowa da kalar tunanin ta can Raliya ta nisa tace
"Tabbas kuwa lokacin da Sakeenat ta faɗa min tana da cikin cikin wata ɗaya ta cemin".
Na'ima kuwa wani numfashin ta sauke kana tace
"To yanzu malam wani tai mako za'ayi min?".
yace
"Faɗi me kike so ayi miki yanzu a aiwatar".
zaman ta ta gyara sosai kana tace
"A kasheta kawai dan nasan koda an zubar da cikin ma zata kuma yin wani tun da kullum yana like da ita, shine kawai samin kwanciyar hankali na".
tana faɗan haka wani irin bakin hayaki yafito fuuu daga cikin wani tukunyar kasa da ke gefe da bokon wani irin zabura sukayi dukan su sukayi baya.
da sauri bokan yace
"Maza janye wannan kudirin bama kisa yanzu munyi alkawari wa shugaba, sai dai duk abun da kike so a duniyar nan zaki samu ban da kisa".
yafaɗa da karfi yana zazzaro ido.
yana gama faɗan haka kuwa hayakin nan ya koma cikin tukunyar.
ɗan matsoww sukayi jiki na rawa
suka haɗa baki wajen cewa
"A gafarce mu". cikin ɗar-ɗar Na'ima tace
"To Malama ni dai ayi min duk abu da ya dace".
hannunsa ya mika baya yaɗau wani kullin magani kana ya jefa shi cikin wannan tukunyar da ta fidda hayaki yanzu nan tukunyar ta fara fidda wani sauti kamar ruwa akan wuta yana tafasa,zuwa can yasa hannu yaciro kullin maganin ya mika wa Na'ima yace
"Mun girke shi mun kuma yi masa mugun kulle babu mai iya karya wannan sihirin in duniya ce kinsa mu, Je ki saka masa a abinci ko sha da zaran yaci shike nan duk abun da kike so kin samu".
da sauri ta mika hannu takarɓa tana zuba masa godiya kamar zata sa goshin ta a kasa,
sai dunkule maganin take a hannunta sai kuma tasaki wani shu'umin murmushi mai kunshe da ma'anoni iri-iri.
bayan Raliya ta gabatar da bukatar ta itama nan ya haɗa mata kalar nata lakanin kana suka cikeshi da kuɗi suka haye motocin su suka fice a cikin dajin in da kowa ta kama gaban ta Na'ima tayi gida Raliya ma tayi gidan su....
Tun da Na'ima ta dawo gida take tunanin ta in da zayi tazubawa SALEEM maganin nan acikin abin ci harya ci,dan yanzu rabon da yaci abincin ta harta mance,ko da ɗin ma basosai yake ciba dan shi ba ma'abocin cin abinci da yawa bane yafi bukatar tea a koda yaushe kamar wan da yahaɗa jinsi da larabawa.
sai dai ta kudura wa ranta ko tawani irin hanya sai tabi wajen ganin ta zuba masa maganin yaci....



Tsaye nake gaban wardrobe fitowa ta daga wanka kenan ina kokarin ciro kayan da zan saka najiyo wayata dake kan mirror tana ringing,
a sannu na isa in da wayar yake na ɗau wayar ganin kiran na kokarin yan kewa da sauri na ɗaga na kai wayar kunnena tare da yin sallama.
daga cikin wayar ya amsa sallamar kana ya ɗaura da faɗin
"A kawo min tea yau fa ba'a bani ba tun da safe".
To nace ina sau ke wayar.
Na'ima da yanzu shigo warta side ɗin shi tazo zata shiga cikin bedroom ɗin sa taji wayar da yake da sauri ta juya ta koma side ɗin ta,cikin hanzari ta haɗa tea taje ta ɗau ko kullen maganin da bokanta ya bata har jikinta na ɓari ta kunce kullin hannunta na rawa taɗebo garin maganin tazuba cikin tea ɗin ta garwaya da sauri tafito rike da cup ɗin tea ɗin ta nufi ɗakinsa...
sai da nasaka kaya kafin na wuce kitchen naje na haɗo masa tea ɗin nanufi side ɗin shi.
sallama nayi a bakin kofar bedroom ɗin shi kana na tura kofar,
tsaye na ganta gaban shi tana mika masa cup,yayin da shiko system ne a gaban sa gaba ɗaya ya mai da hankalin sa kan sa.
narke murya tayi
cike da kirsa take faɗin
"Barka da hutawa my SALEEM Bismillah".
tafaɗa tana daɗa mika masa cup ɗin.
ganin haka sai naja na tsaya nan bakin kofa.
A hankali yaɗa go yaɗan kalleni sai ya mai da idanunsa kan abun da yake kana yace
"Cigaba da tsayuwar zakiyi har sai yayi sanyi?".
a hankali nasoma takowa na iso in da yake na mika masa cup ɗin, hannu ya miko zai karɓa ganin hannunsa bai iso ni ba kasan cewar Na'ima tana daf da shi sosai ne, sai na ɗago kafata zan kuma yin gaba sai naji nayi tuntuɓe da kafar mukum sai cup ɗin ya suɓuce a hannuna bai kai ga isa kasa ba nayi saurin taro shi akayi rashin sa'a ruwan tea ɗin yazube kasa har sai da ya fantsalu masa a jiki zuwa kan kafarsa.
ido na waro cike da fargaba,
dogon tsaki Na'ima taja tare da faɗin
"Ke makau niya ce jibi yadda kika ɓata min jiki".
tayi maganar tana yaguna fuska tare da zame jiki tayi gefe.
niko kasa nayi da kai na dan son ganin kafar da nayi tuntuɓen dashi.
ɗagowa yayi tare da bin ta da wani irin kallo kana ya jinjina kai
baki na buɗe da zummar bashi hakuri ganin shima tea ɗin ya taɓa shi sai ya katse min nawa maganar da faɗin
"Je ki kawo min wani".
wani dogon tsakin takuma ja kana tayi waje a hankali nima nafita na nufi part ɗina da sauri dan guri yayi duhu duk da kuwa hasken wuta daya zagaye ko ina na gidan.
da sauri na haɗo wani tea ɗin na kai masa koda na shigo bedroom ɗin sa baya ciki sai motsin ruwa danaji cikin bathroom da ya shaidar min da yana ciki,aje masa nayi kan bedside najuya nafita da sauri dan so nake naje na kira Aunty Halima yau mukayi da ita zata dawo gashi har dare ban ganta ba gashi ina jin tsoro...


Tun fitar HAMDAH har dawowar ta akan idon Na'ima ne tana ganin fitar ta ta saki wani murmushi kana ta bayyano cikin parlour'n a file ta furta
"Wan da yariga ka bacci dole ya rigaka tashi".
takuma sakin wani murmushin jin daɗi da gaskata kanta da shirin da tsara yanzu kuma take ganin yiwuwar sa.
cikin sanɗa ta tura kofar har lokacin yana cikin bayin a hankali tarika ɗaga kafar ta har ta isa in da cup ɗin yake kana da sauri ta kunce kullin maganin ta ɓarbaɗa shi cikin tea ɗin ta ɗan garwaya da karamin cokalin da ke ciki kana ta juya cikin sanɗa tafita ta ja kofar a hankali ta rufe da sauri takoma side ɗin ta tana shiga cikin bedroom ɗin ta ta tuma tsalle tafaɗa kan bed cikin sannin murna da farin cikin yau burin ta zai cika na daɗa mallakar SALEEM har abada...

A ɓangaren Ya SALEEM kuwa tea ɗin da ya ɗan zuba masa ajiki ne yasashi kuma yin wanka, yafito ɗaure da towel a kugunsa hango cup ɗin da ta aje masa can kan bedside sumar kansa yashafa afili yafurta
"Oh yarinyar nan ajiyewa tayi tayi tafiyar ta".
a sannu yatako ya zauna bakin gado,ya mika hannu yaɗau cup ɗin kana yakai bakin sa yashiga kurɓar tea ɗin a hankali har ya shanye..
a je cup ɗin yayi kana yamike tsaye wani irin sara da fizga kansa yayi masa har sai da yadafe jikin garu cikin hanzari jin wani masifaffen tsarawar da kansa yiyi kamar guduma ne aka narka masa a sakiyar kai sai kuma fizga yake kamar ana ƙoƙarin ciro kwakwalwar sa,
da sauri yakoma ya zauna tare da dafe kansa da kahon zuciyar sa dake faman harbawa da karfi-karfi. da gyar ya'iya mosa laɓɓansa ya furta "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un".
yajima sosai zaune yana dafe da kansa da kuma kirjinsa,kana zuwa can yamike da gyar yaje yasa kaya yahaura godo ya kwanta,har lokacin yana cikin wannan yanayin.
yakai a wa guda a haka sai a lokacin yaɗan fara jin sassaucin abun da yake jin a hankali yamike yasau ko a godan yafita...

Ina tsaye gaban mirror ina ta feshe jikina da turarukan sa kamar kullum in zan kwanta baya kuma kusa dani to kalar turarukan sa da ya sayo min su shinake mulke su a jikina har na samu nayi bacci,in kuwa bacci mai daɗi nake son yi to sai in kuwa ina cikin jikin sa ina shaƙar kamshin sa.
duk abun da nake cikin mutuwar jiki nake yayin da tsoro yadaɗa ninkuwa cikin zuciya ta fiye dana ko yaushe,sai kuma share wasu zafafan hawaye da nake tayi tun ɗazu wan da bana sanin fito warsu sai dai naji ɗumin su kan fuskata.
jin karar turo kofa yasani waigowa da sauri dan sai yanzu na tuna ban kulle kofar ba,
wani numfashi na sauke ganin shine,
da ɗan sauri ya karaso in da nake sai ji nayi ya rungume ni ta baya sosai yazuro hannunsa kan cikina da yaɗan turo kaɗan idan ba lura kayi bama bazaka gane hakan ba,sai dai ni inajin nauyin cikin,yana ɗaura hannunsa kan cikin sai ji nayi cikin yayi wani irin harbawa da karfi ya mosa motsin da bai taɓa yin irin saba sai yau,
idanun sa ya lumshe kana yarika shafa cikin ya ɗau lokaci yana shafa shi duk kanmu babu wan da yayi magana sai numfashi'n da ko wannen mu ke saukewa.
zuwa can yajuyo ni yasan ya idanunsa cikin nawa yarika kallona babu ko kiftawa.
a hankali nayi kasa da kaina yayin da wasu hawayen suka zubo min a hankali na furta
"Ya SALEEM inajin tsoro".
janyoni jikin sa yayi ya rungume ni sosai batare da yayi magana ba har lokacin.
a hankali yafara sassauta rukon da yayi min kana ya zame jikin sa yajuya yasoma tafiya ganin fita zai yi da gudu naje na rungumo shi ta baya sai na saki kuka cikin muryar kukan nake faɗin
"Ya SALEEM ina jin tsoro ka zauna dani ko katafi dani ko kace wa Aunty Halima ta dawo".
nan ma baiyi magana sai zame jikin sa da yakuma yi yafita a ɗakin da sauri hannunsa ɗaya yadafe kansa ɗaya hannunsa kuma yakai dai-dai saitin kahon zuciyar sa.
Kofar ɗakin na kulle na koma kan gado ina mai cigaba da kukan.....★


Washegari zaune yake a parlour yana ƴan wasu ayyuka cikin system Na'ima tashigo takaraso in da yake ta zauna kusa da shi tare da faɗin
"Barka da war haka yallaɓoi".
ɗagowa yayi ya kalleta kana yace
"Yauwa".
sai ya mai da idonanunsa kan abun da yake.
zaman ta ta gyara tana murmushi cikin narke murya tace
"Ai ki ake tayi haka?".
ɗagowa yakuma yi ya dubeta shima da murmushin kana yace
"Eh wasu ƴan ayyuka nake ɗan yi amma yanzu zan gama".
tun da yafara maganar taware idanunta a kansa cikin matukar jin daɗin ganin duk abun ta ta tambaye shi sai ya ɗago yabata amsa wani irin farin cikine ya lulluɓeta taji kamar ta mike tayi ta tika rawa a ranta take faɗin
"HAMDAH kin makara".
wani murmushin takuma sakewa kana tadube shi tace
"Da ma wata magana ke tafe dani sai dai kuma gashi kanata ai ki kada na katse maka ai kin ka".
a hankali yakuma ɗagowa yace
"Uhum ina jinajin ki".
numfashi ta sauke kana ta marairaice fuska cikin nuna tsantsar gaskiya ta soma magana.

"My SALEEM akwai wani abun da ke faruwa a gidan nan wanda ya daɗe yana dami na nayi ta zuba ido ko zaka ganewa idon ka sai dai ban sani ba ko kagidan,
SALEEM kai ne babba da koma waye dake cikin gidan nan idan kuma kasa kafa kafita to dole ragamar hakan tadawo kai na dole na tayaka sa ido da binciken al'amuran da ke gudana a cikin gidan nan,kama daga walwalar jama'ar gidan da kuma shige da ficen su dama wani wan da zai shigo daga waje".
ɗan numfashi ta sau ke kana yacigaba da magana ganin ya mika mata hankalin sa gaba ɗaya
"Na daɗe ina so na sanar maka amma bansan da wani fuska zaka kalleni ba wata kila ma kaki yar da da abun da zan faɗan sai dai yanzu ban damu ba ko ka yar da da abun da zan faɗa ko kaki yar da Allah yana gani nasau ke nauyin a kaina bazai hutume ni ranar gobe kiyama akan ɓoye gaskiya kan abun da nasani ba".
kuma gyara zama tayi ta dubeshi da kyau sannan taci gaba
"SALEEM lokacin da kayi tafiyar da kaje kayi kimanin wata guda, kabar gidan nan HAMDAH bata da sarki ma ana tana fashin sallah, ta ya akayi kuma bayan dawowar ka da kayi kimanin wata guda baka gida sannan ciki ya bayyana a jikin ta na wata ɗaya?".
binta da kallo kawai yake yayin da yake jin kansa cikin wani irin yanayi nan da nan zuciyar sa yatsanan ta bugu.
Ita kuwa kai ta shiga girgizawa da faɗin
"Hmm wannan abu zai bai wa duk mai hankali mamaki amma a guri na ba abun mamaki bane, SALEEM yau zan sanar maka abun da baka sani ba, tun ranar da kabar gidan nan wani yazamo madadin ka, ranar na fito zan shiga kasuwa wani yashigo da uniform irin na makarantar su HAMDAH har zan wuce ganin yana taɗan dube-dube sai natsaya nake tan bayar shi ko wani abun yake nima sai cemin yayi gun HAMDAH yazo shi ɗan makarantar su ne, tayi masa kwatance ne yazo sai dai bai gane side ɗin ta ba,da hannu na nuna masa side ɗin ta,
sai da nafita a gidan tunani daban-daban yarika zuwar min abun mamaki har nadawo gidan yana nan bai tafi ba haka nayi ta sa masa ido sai yanma ya fita ya tafi,
tun daga ranar kullum sai yazo wani sa'in yazo da uniform wani sa'in kuma da kayan gida,
har abun yafara da mina narar da yazo yashiga side ɗin ta ganin yaɗan jima bai fito ba sai nabi bayan sa ina shiga ka wai nayi mummunar gani".
shiru tayi tare da dafe kanta ta matse idanunta da karfe sai ga wasu guntayen kwalla sun fito ta kai hannu ta share kana tace
"Kayi hakuri da abun da zakaji daga bakina yanzu,
a kan gado na same su tamkar mata da miji ina nufin yana kan ta suna six".
idanunta ta saka cikin nashi kana cikin nuna tsantsar gaskiya tace
ko a gaban ta zan mai-maita sannan kuma ina da kwararan shaidu da zan iya gabatar da su ko a gaban alkali ne idan ta musa.........!★



🤗 *masha Allah alhmdllh alhmdllh to masu karatu anan nakawo karshen book one domin son ci gaban labarin sai ku tare ni a cikin littafi na 2 dan son jin yadda zata kaya*
*Kamar yadda na yi muku alkawari book one daga farkon sa har karshen sa kyauta ne to gashi yau na cika muku alkawari*
🤔 *shin asirin da Na'ima tayiwa*
*SALEEM zatayi tasiri a jikin sa?*. *shin ma ganganu da ɗaurin goro da tayiwa HAMDAH SALEEM zai yar da* *da batun nata*?.
*sannan kuma* *wanene shai dun nata datake ikirarin* *ko a gaban alkali zata gabatar da su*?.
*Menene makomar rayuwar HAMDAH nan gaba?.*
*duk wannan* *amsoshin sunan cikin littafin* *HAMDAH kashi na biyu domin samun ci gaban labarin sai ki-ka biya ɗari 200 kacal👌🏻ta wannan asusun bankin*👇🏻
*(3170524141 Rashida salihu first bank)*
*ko katin mtn ta wannan lambar👉🏻 08034690723*




*_ina son duk mai sona sonso fisabilillah_*🥰



😢🙌🏻




Mommyn twins ce


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login