Showing 42001 words to 45000 words out of 110563 words

Chapter 15 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21040

yakawomin har yanzu da zafinsu a kula shi zanci, kizo kije school daganan ki wuce aiki, Riyad yace kidawo dasauri tafito daga dakin ta kalli Mama tace  Mama nifa yau na dauki permission bazanje school ba saikuma ta taho ta zauna wajen Mama tace  Mama wai kinsan mutumin chan ne ? Mama na kallon kwayar idanunta tace  wani mutumin ? Cikeda mugun hali tace  shi wannan mutumin daya kawomu naga kunatayi kaman daman kunsan juna ne tun chan dan murmushi kadan Mama tayi tace  a a amman kawai zuciyata ya natsu dashi kaman na sanshi daga wani wuri, kema kinsan dawuya nake natsuwa da mutane amman shi kawai yayi fuce araina, mutumin arziki ne mutunci da dattaku, yanada halaye da dama nagari, bantaba gani a idanunshi yamin kallon mai wata cuta ba, gakuma yanda yabiya kudin asibiti akamin komi, wanda yamaka Akhairi kasoshi ranta adan bace tace  Mama ni na tsaneshi baki Mama tasaki tana kallonta ganin da gaske take, yunkurawa tayi tace  kuma konawa ya kashe miki a asibiti saina biyashi alkawari ne ko zanyi shekara dari ina neman kudin dan dariya Mama tayi tace  zo ki juye abinciccikan ki wanke kulolin nidai fitina u wucewa tayi ta kwasa batai musu ba haka dai tai aikin komi Baba Liman ma yashigo gaida Mama wuraren 1 ta shirya ta tafi aikin sabida yanda Mama tace  saitaje ga mamakinta ko kallon banza Madam bata mata ba hakama sauran ma aikatan dudda bataga Hussy ba, kin zuwa office na Riyad tayi tadaiyi duka ayyukanta idan tana gaban desk aka kira ana neman cleaner a so so room ta taje, harta tashi by 6 bata ganshi ba bakaramin dadi tajiba ta tafi gida.

Washegari da sassafe ta tafi hospital nasu yau pediatric surgery departmant zasu to watch not to do itada team dinta zasu, direct tawuce inda suke ijiye bags nasu ta ijiye aka dan musu lectures kadan sannan tawuce tashiga shirye shiryen shiga surgery tsayawa tayi tana wanke hannunta wata tazo itama ta tsaya kusada ita tai murmushi tace  Hi saikuma ta kalli Labcoat nata tace  Rashida I m Maimuna but Maimoon ake cemin, tun ranan monday nake noticing naki, can we be friends pls ? Dan tsayawa Rashida tayi tana kallonta like a weirdo dasauri Maimoon tace  please dan lumshe ido Rashida tayi yarinyar seems very cool and calm ahankali tace  I don t know yanda ake friendship gaskiya murmushi sosai Maimoon tamata tace  I know and I will teach you, let s go shiga cikin operation room din sukayi duk hannayensu a sama aka sassaka musu handglove ga yaron da za ama operation din da baifi shekara biyar ba anyi sedating nashi shigowa surgeon din yayi wanda Babba ne bawai yaro ba aka samai nashi handglove din yawuce surgical table din student Doctors din dasuke su bakwai duk suka tsaya a gefe, Dr yace  yaron nan dake kan table din nan nada hydrocele wazai gayamin procedure da zanbi in this surgery, and ya sunan surgery din ? Maimoon ce tafara daga hannu tabata amsa yace  wrong almost dukansu saida suka bada amsa yace  wrong yakalli Rashida dabatai magana ba dan ita bata show off ko a aji, yace  make attempt miss dan ijiyan zuciya ta sauke Rashida confidently cikin turencinta that is good muryanta kuma makes it sweet a kunne tace  zamuyi Hydrocelectomy surgery to remove the hydrocele daga scrotum din, zamuyi making incision anan& .. tafara bayanin procedure din da sai kawai Dr ya tsaya yana kallonta exactly abinda zaiyi tafadi kaman ta tabayi, hannu yamikama head nurse yace  scalpel samai wuka akayi a hannu yarike yadauki marker yamikama Rashida yace  come close ahankali ta matso kusada surgeon din gabanta nadan faduwa yabata marker yace  draw the line karba tayi ahankali taja, to her biggest shock yace  make the cut dasauri ta kalleshi, confidently yace  I m here you won t make a mistake so go ahead dan tsayawa tayi Dr yace  we all start ahaka, go for it, I m right here ina kallonki bismillah tayi ahankali ta karba tana kokarin kallon fuskan yaron yace  don t look at his face ijiyan zuciya ta sauke tareda rufe ido what is her biggest motivation da inspiration na son zama likita? Ahankali tace  Mama! I want to become the best Doctor for Mama! I want to make research nagano yanda ake curing HIV for Mama! I want to make Mama better, I want to be the best Dr in Nigeria da kewaye da al umma zasuyi alfahari dasun samu daidainan tabude idanunta kawai tashiga cutting Dr na tsaye kusa da ita yace  suction aka kwashe jinin, wasa wasa da shi da Rashida sukai surgery din nan tass yasake barinta tai stitching yaron up, her stitching style kadai saida ya kalleta almost 10yrs yana aiki in this surgery student Doctors daban daban interns but baitaba ganin skilled yar baiwan Dr like this girl ba ita kanta for now bama tasan wacece itaba imagine abinda take iyayi in year5, sallaman su yayi yakalli Rashida yace  makesure you become a surgeon Doctor R dan sunnar da kanta tayi batare datai murnushi ba cus she hardly smile outside tawuce tafita Maimoon tabiyota tace  wowwww you are amazing Rash kai! I can never do that ahankali tace  thanks dasauri Maimoon tace  let s go grab some drinks wayanta Rash taciro daga jaka taga 2:30 tace  ohh no I have to go to work taciro log book dinta da sauri tawuce taje aka mata signing tajuyo takalli Maimoon tace  gobe bata jira amsanta ba tajuya dasauri Maimoon ta tsaya awajen tai shiru tana kallonta, tace  she s unique, Bilal you loose a rare gem . Wajajen 3 takai hotel din dan saida ta tsaya tai salla tana shiga tawuce changing room tafito kenan saiga Madam tace  yanzu ne lokacin zuwa aiki i will deduct 5k from salary naki sauke kanta tayi kasa tawuce tashiga aiki thank God yau Friday gobe ba aikin, tass tagama aikace aikacen ta wuraren 5 Madam ta kirasu hall duk suka wuce, abinci tagani an kakkasa buhun shinkafa, jarkan mai, indomie, madara da milo sugar sai gero da taliya tace  kowa ya tafi da abincin azuminshi gida courtesy of Oga sai murna ake, tunda tafara aiki dasu da Ramadan ana basu abinci last year an bata is not new thing amman saitakeji yanzu kaman karta dauka sabida Riyad but kuma idan bata dauka ba za ayita surutu daman ance tanada girman kai, Madam tace  zansa security su taya kowa fita da nashi sai kuje ku kira keke, Happy Ramadan to everyone ihu duk sukayi ana shouting thank you Ma sannan ta sallamesu wucewa tayi ta chanza kaya ta goya jakanta tafito taje ta taho da keke tana zuwa security suka tayata lodawa abayan keken ta tafi.

Yau sunday tana so taje kasuwa tadan yo musu yan kananun cefenen azumi tunda batada aiki yau, atampa tasaka green shima ya kwana biyu tadau wani black hijabi ta daura asama mai hula ya tsaya mata a knee aiko yamata kyau tafito falo inda Mama ke zaune tana kirga kudinsu, zuwa tayi kusada Mama ta zauna Mama tace  yauwa kin shirya ? Gyadama Mama kai tayi, kudin da Mama takasa agabanta kashi biyu ta dauki me yawan tabata tace  ga wannan kudin dubu talatin ne nakine kisai dan atampa da takalmi da yan kayan kwalliya da turare kema kiyi kyau da salla kuka dawo sai akai dinki ko dasauri ta maidama Mama kudin tace  Mama bana bukatan kayan salla, kayan danake dasu zan iya sawa da salla, Mama we have important things to do, drugs dinki, abinci, school fees dina dakuma kudin da mutumin chan ya kashe na asibiti ni sai na biyashi kallonta Mama take tace  shiyace miki kibiyashi  ? Girgizama Mama kai tayi tace  Mama you re my responsibility ni kadai don t others, banson wani ya taimakeni wajen kula da mahaifiyata, inda bekaiki asibitin masu kudin nan nasu ba dana iya biya amman yakama kaman an sashi ya kaiki asibitin kudi tai maganan tana batarai tsayawa kawai Mama tayi tana kallonta tun Rashida na yarinya tanada wani irin kishi dasai ka san halinta ne zakasan kishine itafa batason kowa na raban Maman ta, yana daga cikin abinda yasa takejin haushin Riyad dakuma so tabiyashi kudinshi sabida yanda taga yana nan nan da ita bataso taga Mama na kula wasu with a smile, maida kudin kawai Mama tayi hannunta ta danne tace  listen to me umarni nabaki kisai kayan salla inaso nima naga yarinyana tayi kyau takuma fito da salla kinji shiru tayi tana kallon Mama taki magana hade fuska Mama tayi tace  bazaki amsaba? Ahankali tace  naji toh dan murmushi tayi tabata 20k tace  wannan sai kiyo su cefene su maggi da nama da kayan miya tunda mun sami kayan abinci gyadama Mama kai tayi ahankali ta tashi Mama tace  adawo lpy ki duba titi kafin ki tsallaka kinji toh ta amsa tawuce tasa takalminta tafita abinta Mama tai murmushi.

Kusan 3hrs tabata a kasuwa, tasayo atampa mai kyau da gyale da takalmi tadansai bra da pant guda biyu sai pad dan tanaji cikinta na ciwo sannan tayo cefene tashigo keke tabar kasuwan.
Abakin titi aka saukesu hakan yasa ta dandaro cikin anguwansu da kafa, tun kafin takai gidansu ta hango wata arniyan karaman mota baka pake a kofar gidansu motan waye wannan? Hakan yasa ta kara sauri tana zuwa tabude kofar gidansu da sauri ta shiga saura kadan tayi karo da Riyad azaure yadan koma baya kadan tsayawa itama tayi gabanta kawai yafadi ta zubamai ido, yana sanye da wani milk soft yard dake kyalli yabi jikinshi kaman magic, kafanshi kafanshi sanye da Jordaan leather loafers brown, hannunshi daure da agogon Audemars Piguet, dayan hannunshi rike da waya samsung galaxy fold, ba hula gashin kanshi ya kwanta yana sheki sai kamshi yake zubawa, dauke kai tayi da sauri daga kallonshi dan he s so clean wlh ko datti ko stain ko tabo guda daya babu ajikin kayanshi, haka kayan a goge babu squeezing ko daya, shima tundaga kan kafafunta dake sanye dawani black takalmi flat da duk an dinke ya kalla dudda fararen kafanta are shinning ga long fararen nails na kafanta da babu lalli ko daya akai zuwa ataman dake jikinta da hijabin da ledoji biyun dake hannunta bakake data rike sannan yazubama fuskanta idanu she looks tired, she s even sweating a goshi dan duk gashi ya kwanta a goshin nata, ga lips dinta sun bushe kaman she s a bit sick.  Kallon fa ? Tai maganan cikeda rashin kunya dayasa ya daidaita kwayar idanunshi cikin nata dasauri ta janye idanunta hakanan taji takasa kallonshi but tsabagen karfin hali tace  kadena zuwa gidanmu banso cikeda isa kaman anyi forcing nashi yayi maganan awulakance yace  are you angry ba wajenki nake zuwa ba ? Wani dum! Taji saukan maganan da sauri ta kalleshi tsaf shima yake kallonta mene mutumin nan yace? Mema ya dauketa? Taji haushi dan ba wajenta yake zuwa ba on wat ground? Kokarin hado martanin dazata bashi take dan she was a bit speechless but yarigata wani kallon raini yamata calmly yace  bakida matsayin dazan zo nemanki yana maganan yabi ta gefenta yafice wlh takai 1 good minute fassara maganan shi take akanta taji ranta na kumfa dasauri tajuyo tafito kofar gida daidai yaja motanshi tabishi da kallo yana wani saka bakin glass a idanunshi ko inda take bai kallo ba yawuce abinshi kaman zata hadiye zuciya tamutu tace  nima ka isa kazo wajena ne aka gayamaka? Sai ji dakai kaman wani dan shugaban kasa sabida yana takama da dan hotel din dayake dashi I will leave your company soon zan nemi wani hotel din wlh kuwa tana maganan tajuya tana saisaita bacin ranta takoma cikin gidan kaya tagani cikin gidansu harda su indomie da kwalin kwai kudan 5 crete gasu manta manyan roban madara Milo oat, wlh shopping data gani zube a compound yakai na 300k ga bandir na kudi kuma ijiye kasa na yan 1k guda biyu dasauri ta shiga ta tsaya gaban kayan ranta abace tace  Mama waya kawo mana abubuwan nan ?

Ahankali Mama tace  Riyad yakawo kaman zata fashe sabida bacin rai tace  Mama shine zaki karba? Kallonta Mama tayi tace  babu yanda banyi dashi ba amman yaki yarda wai ni mahaifiyar sa ce kodan darajan azumi na amsa, kinga uban kudin daya ijiye dane naki amsa da kyar na zari yasake daura daya, haka ya ijiye komi anan dan ni naki karba cikeda bakin ciki harda abinda yamata a zaure tace  Mama shine baki kira yara kinsa sun maidamai da kayan mota ba ? Kaman wacce aka daka kawai saita fashe da kuka sosai ta ijiye kayan data shigo dasu daga kasuwa nan kasa ta tsallaka tashiga daki kawai tahau kuka idanunta sunyi jajir tashi Mama tayi tabiyota ciki cikeda damuwa tace  Rashida mekuma haka da kuka? Duk mai imani yadaga ido yaga rayuwanmu dole yaji tausayinmu, na karba badan komi ba saidai naga yaron kirki ne hakanan zuciyana ya natsu dashi kuma bawai saurayi bane ya gayamin yanada mata so mutum ne mai hankali ba yaro ba, saikuma dalili nabiyu shine karbansu zai saukaka miki kema at least daganan zuwa 2month zamu manta da siyan Kayan abinci albashin dazaki samu saimu hada da wayan nan kudin ki biya kudin school fees ragowan mu rike na asibiti, you think I m happy da rayuwan wahalan dakikeyi? Understand me it s Ramadan kyaututuka haka is normal ko na yan anguwan man sabida baki karba ne da yanzu an kawo mana, it s okay ya isa stop crying Mama tajawota cikeda lallashi rabon datai kuka haka tun ranan da aka kwantar da ita a asibiti cikin kuka tace  Mama stop collecting abu daga hannun kowa, I m enough for you, Mama bazan taba bari ki kwana da yunwa ba, I will never hawaye taji yaciko idanunta saikuma tai murmushi ta danne takai hannunta ta share mata fuska tace  I know y ata will never allow me to go hungry, natuba to bazan kara karban komi daga hannun kowa ba, Rashida na is enough for me, the best daughter aduk duniyan nan, come here Mama kawai ta rungumeta tana murmushi she s lucky Allah ya azurtata da y a dake sonta haka, sun dade ahaka sannan Mama ta dagota takai hannu ta yaye hijabin jikinta ta tana taba wuyanta tace  jikinki da zafi baki da lafiya ne ? Ahankali tace  cikina ke ciwo kadan gobe naje asibiti zan karbi magani cikeda so Mama tace  sannu kinji, zauna kihuta ni zan miki girki dasauri tace  zanyi Mama tashi zatayi Mama takama hannunta bawasa kan fuskanta tace  zauna kihuta zama tayi Mama ta tashi atampanta tafara dubawa ta yaba sannan tashiga daura musu abinci itakuma anan bacci yayi awon gaba da ita.


Da kyar Mama ta tadata around 4 na asuba sabida suyi sahur, tariga tasan bata azumi wucewa tayi tama Mama abincin sahur sannan tawuce bayi yau da hot water tai wanka dan zazzabi takeji da ciwon mara but she feels she can manage dan is not that serious tana dawowa takaima Mama itama nata ruwan zafin tashigo daki tace  muje Mama idanunta Mama ta kalla tace  dan Allah kina zuwa clinic kisha magana kar zazzabin nan yarufeki da kyau kinji gyadamata kai tayi Mama tace  barshi zan iya zuwa bayin da kaina jeki kimtsa batai musu ba ciki tawuce tashiga kimtsawa tasa black abaya tahada jakanta na baya saikuma ta kara kwanciya yawanci a rashin karfi ne kafi gane Rashida is sick dan baka ganewa a baki da fuska sabida masifa da fada, shigowa Mama tayi ganinta a kwance yasa Mama tace  namiki shayi ? Girgizama Mama kai tace  idan naje school zanci abinci Mama karki damu da dan damuwa Mama tadauko mai tana shafawa hartai salla tana kwance wajen saima lumshe ido data farayi sai kawai Mama ta barta zuwa 7 ta tabata tace  tashi kitafi school tashi tayi ganin Mama tafara damuwa yasa tace  laaaa Mama kinga najini garau maybe dama baccin danake ji yakara karamin zazzabi 200k na jiya Mama takawo da 100k nasu tasa asama tabata tace  gashi ki biya kudin makaranta kisai yan littafan da baza a rasa ba kallon kudin tayi zatai magana Mama tace  ni Maman ki aka bama kudin nan, nikuma nabaki, kaman yanda Hajiyan nan taraba mana 20k a clinic naje na siyamiki crocs consider wannan kudin haka, go and pay school fees naki and buy textbooks dakike bukata ayanda fuskanta kadai yayi kasan bataso ba but ganin yanda Mama tayi yasa tasa hannu ta karba kawai tasa kudin ajaka ta goya, taja black gyale tashiga rolling tai kyau kaman balarabiya dudda bakomi akan fuskanta sannan tace  Mama natafi 5k takara cirowa cikin kudinsu dabaifi 50k ba Mama tabata tace  dan Allah kihau keke yau, kici abinci mai kyau a school kinji gyadama Mama kai tayi tace  natafi Mama thank you  adawo lpy Allah bada sa a fita tayi tana kaiwa junction ta shiga cafe tai printing ramita, sannan tafito tashiga keke sai bank taje tafara biyan school fees nata sannan tafito tashiga keke again sai asibitin su, sauka tayi wuraren 9:30 taga student nasu Maimoon na hangota ta taho wajenta dagudu tace

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login