Showing 27001 words to 30000 words out of 110563 words

Chapter 10 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21052

ta tara wani ruwa ta taho da sauri jikinta duk rawa yake zata fara mopping ruwan kunfan kasan jikinta duk yana tsiyaya kaman daga sama taji sassanyar muryanshi yace  stop! Dasauri tadago manyan fararen idanunta ta kalleshi, hada ido tasakeyi dashi for the second time da sauri ta dauke kai aranta tace  sai shegen kallon mata mtsww fitowa daga dakin yayi ahankali, cikeda tsantsan kulawa yace  step aside dasauri ta matsa gefe ga mamakinta sai kawai taga ya tsugunna yadauki bucket na mop din ya matsar gefe da vacuum cleaner, yashiga nannade carpet din na tsakiyan office din yadaga yadauka yawuce wajen kofa yabude yafitar dashi ya ijiye bakin kofan nan yashigo yasameta tana kokari fara mopping wajen cikin kwantacciyan murya yace  go and change dan kallon daga kasan riganta har zuwa crocs na kafanta tayi dake tsiyaya tace  karka damu I can do it banda wani uniform, zai bushe ai yanda take kallon jikinta tana maganan yake kallo with her voice dake piercing kunnuwa sabida dadinsu, calmly yace  go take them off kisa kayan gida kawai dan tasan office din mai hotel dinnan ne, sannan shita gani cikin offive din so dole tai assuming shine mai hotel din banda haka data gayamai me ruwanshi da yanda zatai aikinta yabarta tayi abinta tagama mana ha a, sai gwadamata yanda zatayi yake, sai kawai tawuce kofa batare datace komiba tana zare handglove din, tabude kofa tafita yabita da kallo kafin kawai yazaga yazauna kan kujeranshi na office yayi shiru.



Changing room dinsu tawuce ta chanza kayan tasaka doguwan rigan atampanta brown ne da milk just straight gown babu wani ado ajiki, dan kwalin kayan ta daura aka sannan ta zari gyalenta brown ta yafa daya kara haskata hasken fatanta yayi bau aciki, ta kwashi kayan bayinsu na staff ta shiga ta dauraye kayan ta wanke cinyanta da kafanta da takalmin tama wanke fuskanta kawai gaba daya hakan yasa tai wani haske mai kyau dinnan na bayan ka wanke fuska, tawuce baya ta shanya kayan sannan tafito tana tafiya da sauri sauri sabida tasamu tai sauran ayyukanta tabar office dinshi, tashiga elevator zuwa 5th floor tawuce office din kofan office din ta bude ahankali tashigo tunda ta bude office din ya kafamata ido, the first time daya ganta uniform ne jikinta, yauma haka yanzu ne yafara ganinta da kayan gida, kasa dauke idanunshi yayi akanta, ta taho direct cikin office din batare data kalli wajen dayake bama, zubamata idanu yayi yana kara tantancewa itace dai wannan mara kunyan ta airport, bai cika manta face ba idan yasan mutum, hade fuska tayi batacemai komiba dan jikinta yabata kallonta ake, tadauki moping stick din tafara moping wajen ahankali tana gamawa tadan juyo ta kalleshi karaf suka dake hada ido dauke kai tayi tace  zan iya shiga dakin na gyara ?  Yes ya amsa calmly hakan yasa kwai ta shiga ta sharo tai arranging bed din dataga ba a gyare ba, ta wanke bathroom din, kusan 5min tayi sannan tafito tawuce bayin nan office ta gyara shi in 3min sannan tafito tai arranging abubuwan datai amfani dasu tafita dasu waje sannan tadawo tazo gaban table dinshi tasa hannunta tana kwasan wayanta na wajen yanabin white long fingers dinta da kallo that looks so feminine, ahankali yace  wat is your name? Batare data kalleshi ba tace  Rashida Almustapha tana maganan tajuya dasauri zata wuce kaman daga sama yace  is your back hurting you naga kin fadi tabaya ?  No it s not tabashi amsa atakaice tacigaba da tafiya da sauri bataso yayi wani maganan kuma, hartakai kofa tasa hannu zata bude yace  Rasheedahhh! Wlh batasan meya faru ba hakanan gabanta yafadi chak ta tsaya takasa motsi sabida yanda yakira sunanta, kawai she felt something strange in her dayasa dasauri tajuyo ta kalleshi sake hada ido tayi dashi saikuma ta dauke kai tace  na am kusan 30secs yayi shiru saichan ahankali yace  Thank You Da sauri ta kalleshi zatace thank you for wat saikuma ta tuna maybe na gyaran ne hakan yasa ta gyadamai kai kawai tama kasa magana sabida yanda heart nata yafara racing tajuya tafito dasauri ta kwashi komi tawuce kasa ta maida komi store tawuce taje dakunan dazata chanza duvet nasu takai washing machine takai sannan tahau gyara Allah yasota bata hadu da Madam ba balle ta tambayeta ya akayi tasa kayan gida ba.



Wuraren 6 tafito daga hotel din sai fama take da wayanta dayaki kunnuwa sai cire battery tana maidawa take sabida ya kunnu yaki kunnuwa, ga jakanta goye abayanta.  Hi Rashy Aisha receptionist dake night zuwanta kenan tai waving nata tana murmushi awkwardly tadaga hannunta saikuma ta maida ta gyada mata kai kawai tawuce tafito waje tana hure huren waya, Munir da Riyad na tsaye awaje wannan karan ya chanza kaya zuwa jumper na milk yadi suna magan kaman daga sama ya hangota tafito tana hura wayanta, yanda hankalinshi da attention nashi yatafi wajenta saida Munir yajuya dasauri dan yaga meyake kallo haka ganin wacce yake kallo wacce kallo daya yamata she looks like worker nasu not guest yasa yace  who is she? Batare daya dauke kanshi daga kallonta ba yace  my savior dasauri Munir yadauke kanshi daga kallonta ya kalleshi dasauri yace  kaman ya your savior? Yana kallonta yace  the girl that saved me from those goons a airport dasauri Munir yajuya ya kalleta yace  wow the clearner damuka dade muna nema wat a small world ashe anan hotel namu take aiki, but did you tell her ? Girgixamai kai yayi daidai tasha kwanan layin yadauke kanshi yace  No bangayamata Munir yace  why? mota yashiga yace  bata ganeni ba tada motan Munir yayi yace  ai da saika gayamata, How will you reward her yanzu? Kai tsaye yace  I will ask her kome takeso arayuwa i will grant her any wish take da shi she s part of the reason I m alive today murmushi Munir yayi yace  wat got you so angry today? Yatsine fuska yayi yace  I don t wanna talk about it ahankali Munir yace  to mutafi gida? Mom tasa an sanar bakada lafiya just to manage situation din harda kiran Dr, tace na tabbatar mun dawo gida tare hannunshi yasa yasauke glass na window ya lumshe idanu bai sake cewa komi ba, ganin baison magana yasa yace  azumi saura 7days fa bakai approving fund na kayan abincin daza a rabama al umma da ma aikatan ka ba dan ijiyan zuciya yayi yace  i forgot bani file din da pen lemme sign ahankali Munir yace  bari mukai i will give u yana file dake back seat.
JOIN GROUP DANAKE POSTING

https://chat.whatsapp.com/Ckm5Bo7CcqR1NYkgT0HEvR

=ث? SANYI DA ZAFI =ث?




'

EPISODE 1?? 3??

Gida tashiga around magrib agurguje tai alwala tashigo ciki Mama nakan dadduma hakan yasa ta tsaya kusada ita ta kabbatar sallan.

Tana idarwa cikeda damuwa tace  Mama ruwa yashiga wayana taki aiki wlh tai maganan tana jawo jakanta taciro wayan cikeda damuwa itama Mama tace  garin yaya meya sameta? Cikin damuwa tana kara huhhure wayan tace  faduwa nayi ruwa ya kwaromin shine ruwan yataba har wayan dasauri Mama tasa hannu ta karbi wayan itama tana huhhura duk wani huji na wayan ta maida battery din kozata kunnu amman bata kunnu ba hakan yasa ta tashi tawuce chan wajen yan kayan abincinsu tabude ledan shinkafa tasa wayan ta zuba shinkafa akai tace  bari mugani kozata kunnu idan bata kunnu ba saina tattara kudin dake wajena kije ki sayo wata wayan dashi, kina bukatan waya kodan school, Allah kiyaye bakiji ciwo bako ? Gyadama Mama kai tayi tace  banji ciwo ba Mama tace  to ai mun gode Allah tashi kiyo wanka kici abinci dasauri tace  Mama girki kikayi ? Gyadamata kai tayi tace  eh nayi shinkafa da wake da mai sa yaji murmushi tayi tace  Mama banace ki dena girki ba ture mata hanci Mama tayi tace  to banji maganan ki ba Anty Rashida kwashewa da dariya tayi hakan bakaramin dadi yama Mama ba ganinta duk cikin damuwa sabida wayan tasan lissafi take ta yanda zata taba kudin saving dinsu tasai waya dashi kafin takara samin wani kudin fa, rashin lafiyan Mama fa, abinci fa, kudin wuta fa, tasan duk abinda take tunani kenan ganin tayi dariya yasa hankali ta ya kwanta, cikin shagwaba tace  kai Mama nine Anty Rashida Mama ta kama haba tace  yooo ai hakane, Mama karki kaza, karki kaza, kullum command kike bani yarnan kinga ai kinzama Anty Rashidan sake bushewa da dariya tayi kawai saita kwanto jikin Mama tace  Mama stoppp wlh ni ba Anty Rashida bane, Mama ina hanaki ne fa sabida karki fadi, kinga kinada yawan ganin jiri, k1nada migraine kuma, Mama I have to take care of you gwara namiki komi ko ruwan dazakisha na ijiye kusa dake sabida karki wahala wajen daukowa tabe baki Mama tayi tadagata daga jikinta tace  jeki wanka kizo kici abinci tashi tayi ba musu ta rage kayan jikinta tadaura zani ta kwashe kayan da lab coat da kayan Mama data cire yau dasafe tafito saida ta fara wankesu tsaf ta shanya sannan tawuce bayi tai wanka tadawo Mama tabata abincin ci tayi bawani sosai ba batawani cin abinci abin yabi jikinta sannan takai kwanon waje ta kuskure baki ta dawo tahau salla kusa da Mama tana idarwa ta kwanta awajen ko 2min ba ayiba tafara minshari Mama tai shiru tana kallonta sai kawai tasa hannu tadauki feet dinta ta daura kan cinyanta dudda uban tafiya akasa datakeyi bata da kaushi kafanta still looks very fine ga nails dinta farare kal masu kyau, ahankali take massaging kafafun ayanda ta gyara kwanciya kasan tanajin dadin tausan Mama is just looking at her babu salloli biyar dazatayi arana da zatakai goshinta kasa dabazatama Rashida addu a ba, banda kiyamun Layli datakeyi kullum, kullum addu an ta shine Allah yakawo ma diyarta karshen wahalan nan Rashida ita ke ciyar da ita, itace cinta shanta suturanta magungunanta da komi na rayuwan su Rashida ke nema, babu yanda zatayi ne dan batama da karfin aikin ne da itace zata fita ta nemawa diyarta abinci da komi ba diyarta tayi ba, kullum addu an ta is Allah ya tsare yarinyar ya tsare imaninta kar wata rana tagaji da aikin wahalan nan tace zata shiga duniya tabi maza dan shine hanya mafi sauki da akebi asami kudi, addu anta koda yaushe shine Allah yabata ikon kammala wannan karatun likitan, kowani shekara da hayya hayya take tara kudin school fees nata na last year bai musu wani wahala ba sabida tasami aikin hotel din nan ana biyan ta dubu 50k duk wata a nan ta tattara tabiya, fatanta shine Allah sa wannan shekaran na biyar kar kudin makarantan yayi yawa dubada yanda aka kakkara kudin makarantu, hawaye ta share ahankali daya zubo mata bata taba sanin dan Uwanta na jini zai iya juya mata bayaba sabida wannan cutan dudda da ranshi da lafiyanshi, bata da kowa sai Rashida, yau shekaru ashirin da uku kenan tana wannan wahalan tun Rashida na cikinta, ta haifo yarinya cikin wahala ta tashi cikin wahala sannan itama tana rayuwan wahala, batabama yarta komiba sai wahala, babu wanda ya yarda ya auri Rashida, ga yanda yar karaman yarinya ke aiki kaman namiji wata kalan uwace ita, hawaye ne suka kara zubo mata sai kawai ta jinginar da kanyon a bango takalli sama murya chan kasa that is very weak tace  Ya Allah idan mutuwata shine mafi alkhairi agareni dakuma y ata, idan mutuwata zai cireta daga cikin wahalan nan datake ciki Allah ka kasheni, ka aurar da Rashida gidan dazata huta, karufama Rashida asiri, ka lullubeta cikin nimarka Ya Allah.
Tadade ahaka yawanci tana boyema Rashida damuwanta da dama sabida kar yarinyar takasa karatu idan kanaso kaga Rashida ta birkice tarasa sukuni to Mama tace kaza namata ciwo tuni yarinyar zata rude, damuwa, tunani ga constant ciwon kai koda yaushe shiyafi damunta, saisa kullum tane asibiti BP ta is high, magungunan BP nema ke cinye musu kudi cus maganin HIV free ake bata a clinic?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? dinsu.



Ganin yanda bacci ya shigeta yasa bata tadataba tabarta tai baccin anan kan dadduma.



Wuraren 5 Mama ta tadata da kyar ta tashi wanda hakan daman is daily battle nasu, gyaran gidan tay1 tasa takai Mama tai wanka tai salla tazo ta dumama shinkafa da waken sannan tama Mama tuwo sunada miya daman kafin ta shirya cikin bakin abaya da stones nashi yagama fita tass but dudda haka ya mugun mata kyau abunka da fara tazo taje wajen wayanta taciro daga shinkafan tasa battery ta kunna amman still yaki kawowa Mama tace  bai kawo ba? Gyadama Mama Kai tayi ahankali, dasauri Mama tazo karban wayan tayi tace  kodai ba chaji ne tawuce wajen chazanta dake bango ta makala kusan 3min bai dauka ba, ahankali Mama ta tashi tace  bari nabaki dubu talatin din nan saiki sayo wata wayan kawai dasauri tace  a a Mama ki adana talatin din nan, bari zan kaita wajen yan waya a gyaramin zasu iya gyaramin badan Mama taso ba dan wayan tariga tagama tsufa dukta farfashe tace  to shikenan bari na baki kudin gyaran sip tabude taciro wani leda ta kirgo 5k tabata karba tayi sannan tayafa gyalenta tace  bye Mama har zaure Mama tarakota tace  adawo lpy dayake 9 ake fara clinic dinsu hakan yasa taje shagon Maman kuwa tayi aiki ta karbi 2k dinta sannan tawuce shan wajen gyara takai wayan ganin zai dauki lokaci tace  zata dawo da yamma tashiga keke sai hospital nasu.

she s not really doing much a consulting room take zama attached to consultant din da aka assigning nata to him yana duba yara marasa lafiya yana tambayanta me aganinta take tunanin is diagnosis din tafadi, kokuma yace wani investigation yakamata ayima yaron tafado sunayen series of test da za ayi ganin how brilliant d girl is tsohon likitan yace  i will comfortably leave the office for you tommorow gyadamai kai tayi dan she hardly smile outside, haka dai tagama by 1 tawuce mosque tai salla ta linke labcoat tasa a bag sannan tafito tashiga keke sai hotel.





Yau tadanyi latti sabida traffic sai around 2:30 tashigo hotel din ko kallon mutanen dake reception da lobby gabaki daya batayi ba da sauri sauri tawuce changing room nasu kofa tabude ahankali, ma aikatan su tagani gudu uku a lobby suna chanza kaya da kallo suka bita batace musu kala ba tawuce locker dinta tasa password dinta tabude, daya daga cikinsu ne taja tsaki tace  mutum sai fadin dai, nagadai da mutum dan wani ne dabaizo hotel neman aikin shara da wanke bayi ba, tundadai duk ansan juna menene na jijji dakai kaman diyar wasu ? Sauran biyun ne suka kwashe da dariya daya tace  dadine dake Hussy baki hadiye abu aciki parking gashinta tashiga yi da ribbon tace  eh mana kullum fuskan mutum amurtuke ana fadin rai ana daga shoulder kaman yar shugaban kasa amman shine akazo aikin wanke bayi a hotel wani irin buga marfin locker Rashida tayi saida yayi kara pammm!Tajuyo tai facing Hussy direct cikin zafin rai tace  dani kike maganganun nan? Wani banzan shakiyin kallo Hussy tamata dan tadade tanajin haushin Rashida wai ace ma aikata nawa a hotel din nan yarinya bata kula kowa, kuma kai kasauke kanka ka kulata taki kulaka back, bama wannan yafi bata mata rai ba yanda take nuna bamatasan anyi hallita irinsu a wajen ba ko ka kulata ita bazata kulakaba sai bakin taurin kai, jibidai yanzu datazo tasamesu ko Hi bazata iya gayamusu ba? Amman basu isheta kallo ba, cikeda tsana tace  naga dai ban kira suna ba, amman duk wanda ya tsargu dashi nake wani irin kallo Rashida tamata kaman taci ubanta saikuma ta tuna nan wajen aikin tane, da kudin aikin wajen nan zata biya school fees and other things bari kawai ta barta today is her lucky day, sai kawai tajuya tasa hannu zata dauki uniform nata batare data kara magana ba, cikeda neman fada Hussy tai wani shewa tace  jakan ta tsorata juyowa Rashida tayi da mugun zafin rai batai wata wata ba ta fizgo gaban rigan Hussy ta kifa mata mari a fuska ihu jikake tasss! Hussy tayi ihu ta chakume gaban rigan Rashida tace ni kika mara ? Sai dambe, dukanta Rashida take bana wasaba har gyalenta na fadi kasa bakin gashinta datai parking donut mai bala in kyau ya bayyana, sauran yammatan biyu na kallo sunajin dadi ganin suna dakan juna dudda Rashida nacin uban Hussy amman kallon fada da dadi yake sukaki rabasu, ganin jini Rashida tafasa bakin Hussy yasa daya cikinsu ta tsorata tace  baruwana kar ayi kisan kai agabana dasauri tabude kofa tafita da gudu dayan ma tabiyota hango Madam sukayi a lobby tana magana da receptionist kafin sukai wajen ma sukai ihu.  Madam ana fada daidai lokacin Munir da Riyad na shigowa yana shaye da brown jumper yasa brown shade a idanunshi na CK dayamai kyau sosai, arude dayan tace  Ma come oo harda blood everywhere! ganin Riyad yasa Madam tace  Sir welcome wai ana fada I don t even know with who lemme handle it tawuce jin yasa Munir yace  let s intervene Munir yayi gaba Riyad yabiyosu abaya yana tafiya one one a kasaitance, da gudu Madam ta shiga dakin tai ihu  what is this ? Ganin blood har wuyan Hussy, Rashida bama tasan an shigo bama Munir yashigo dakin daidai Riyad

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login