Showing 12001 words to 15000 words out of 110563 words

Chapter 5 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21054

zatamai magana yadaga hannu yace  inajinki ranki shi dade wucewa falo yayi yazauna Mama da Haleema suka biyoshi a speaker yasaka wayan dashi da Mom ke magana suna shirya komi kaman ba mutuwa aka musu ba, planning auren da yanda zasu sami kujeran suke hankali kwance.
**


Wuraren 10 yafito daga dakinshi yana sanye cikin wani farin yadi da akamai dinkin jumper yamai kyau sosai sai kamshi yake zubawa kaman zaije gasan turare, binshi da kallo Mom tayi tana murmushi tace  Son katashi? Munir yashigo yakai sau uku nacemai bai isa yatasheka ba, bayan kunyi sallan asuba tare a mosque karasowa yayi yazo kusadab da ita yazauna ahankali yace  morning Mom as usual pecking nashi tayi a goshi tareda shafa kumatunshi tace  morning Riyad, yaya jikin? Zakai breakfast yanzu ne ? Girgiza mata kai yayi alamun no, dasauri tace  to maza je Gwaggon ku ta aiko dazu akiraka kadawo saikai breakfast kafin kafita fada ko ? Dan gyadamata kai yayi yatashi ahankali yayi kofa haryasa hannu zai bude kofan tace  idan tamaka maganan auren Haleema kai naam dasauri yajuyo da kanshi ya kalli Mom dauke kai tayi kafinma yamata wani maganan, dan jim yayi sannan yabude kofa yafita ma aikata fada sun cika wajen yawanci Mom bata barinsu falo so anan waje suke yashe kaman kaya, gaishe gaishe da kirari sukahau mai ya wuce abinshi ko kadan baison zuwa wajen Gwaggo shi kadai hakan yasa yaciro wayanshi daga aljihu dailing number Munir yayi ringing daya yadaga yace  kana ina ? Daga dayan bangaren yace  ganinan daure da towel wanka zan shiga dan yatsine fuska yayi yace  be fast to ya katse wayan baiso ya koma ciki dan baiso Mom tasan baijeba kuma baison yayita tsayawa awajen hakan yasa yawuce flat din su Munir wanda da dan tafiya sai gaidashi ake bai amsa kowa har gaban flat din tsayawa yayi jimmm awajen sai chan yasa hannu yabude kofan da sallama ahankali hada idanu yayi dawata mata dake zaune a falon sanye da hijab da charbi a hannunta kaganta kaman ita tai kakinshi ta tofar sunyi kama sosai, itama tanada haske kaman shi, sauke kanshi yayi kasa da sauri sannan ahankali yashiga ciki tareda maida kofan yarufe yama kasa magana, tadade tana kallonshi sannan tasauke kanta kasa tace  Munir nasama kaje ka sameshi gyadamata kai yayi sai chan kaman me tsoron magana yace  ina kwana Mami batare data kalleshi ba tace  yajikinka dafatan basu maka komi ba ? Dan dago kanshi yayi yakalleta ganin kanta akasa yasa shima ya maida kanshi akasa yace  I m fine daidai lokacin Munir yaleko daga sama daure da towel yace  ina fitowa daga bayi naji kamshin turarenka wlh daukomana breakfast kataho dashi mugun kallo yamai saikuma kawai yawuce dinning din yazauna yana bude warmers din saman table din, ganin shayi dayaji kayan kamshi mai zafi dasauri ya zuba a cup ya debi waina da pepper soup yadade rabon dayaci traditional food kawai yahauci bini bini Mami na dago kanta tana kallonshi dudda yabama falon baya, sosai yakecin abincin dan yanada ci yana cikin ci wayanshi yahau ringing ganin Mom yasa yahadiye wainan bakinshi da sauri yakai wayan kunnenshi kafin yayi magana cikin kakkausan murya strictly Mom tace  kana ina Riyad? Kasa magana yayi yay shiru cikin masifa sosai Mom tace  okay sabida na barka tareda Munir shine yanzu gidansu kake zuwa kasan nida matan nan bamayin juna but you keep going there kana ganin gidan nan kowani yaro najin maganan uwarsa ni ban isa kaji nawaba ko ai shikenan kayi duk yanda kakeso& ..  Mommm! dip ta katse wayan dasauri yatashi yajuyo sauke kanshi kasa yayi cikeda girmamawa yace  Mami bari naje in Munir yafito yasameni awajen Gwaggo ahankali Mami tace  okay kofa yayi dasauri yabude yafita tabishi da kallo sai kawai ta sauke ijiyan zuciya, wajen Gwaggo yawuce, Babban flat ne uwa gari guda, ga hayaniya ana shiga da fita masu aiki sai gaidashi ake kaman anga sarki amman ko kallon mutum daya baiyiba harya shiga dankareren falon Gwaggo, dudda dakin yacika da mutane yana shiga Mai Babban daki ta sallami kowa falon yarage daga ita sai shi yawuce wajenta yazauna yayi shiru, fuskanshi Gwaggo ta taba sannan takama hannunshi tabi da kallo tana dube dube tace  yaro jiki uwa na baturai kai kenan baka isa kaga kazanta ba murmushi yayi ya fizge hannunshi yace  Gwaggo ni na warke kidena dubamin jiki dan Allah tsuki tayi tareda hankadeshi tace  kaga shashasha Hararanshi tayi tace  ni shiga dakina ka dauko huran dana dama maka daga babanka sai kai kap cikin jikokina keson furana jikinta yayi sanyi shima haka sai yayi shiru ganin yanda yayi yasa da sauri tai murmushi tace  bance kamin fuskan mara lafiya ba, Allah shiya bani babanku kuma shiya amsa Alhamdulillah d ana yayi abubuwan alkhairi da dama aduniya yayi shukoki daban daban, ya gina makarantu, rijiyoyi, gonaki dan haka banda nadama Allah ubangiji yakai haske kanarinsa jeka dauko tashi yayi ahankali yadauko kwaryan fura yazo yazauna yafarasha anatse tana kallonshi harga Allah itama zatazo Riyad yazama sarki cus yarone mai tausayi mara hayaniya ga kwarjini ga biyayya sannan ga kwazo, baida sa ido, shine yaro na farko kap yaran sarki daya fara neman nashi da kanshi, tun ana gulma ana cecekuce but marigayi yace abarshi yayi abinda yakeso dudda kalan kudi dayake dashi baitaba raina wani ko yadingaji yafi kowaba gashi da tausayi ya tsani yaga wani na fushi ko kunci sanadiyanshi dan haka itama Riyad ne zabinta daman tariga ta jefamai kuri a. Ahankali tace  zabinka ne diyar Waziri ko zabin Mamanka Maryama dan nasanta da tsinannen taurinkai, dason saka kabi ra ayinta sabida taba Allah ya yoka me biyayya, kaika zabi Haleematu ? Abu yaji ya tsayamai awuya but ya daure ya gyadama Gwaggo kai batare dayayi magana ba, Gwaggo tace  ai shikenan za ai magana idan anyi bakwai na babanka muji, zanma Baffan ka Muji magana nama kirashi daman daidai nan Munir yashigo yana zama akai sallama Mujitapha yashigo yana sanye da manyan kaya daya fito da katon teban daya ijiye sai kyalli shaddan jikinshi yake kana ganinshi kasan yasha kudi ya koshi waje ya samu ya zauna hakan yasa daga Munir har Riyad suka gaidashi atare.  Ina kwana Baffa binsu yayi da kallo shikebin mahaifinsu yanason yaran wanshi baida matsala dasu, yanason ya gaji sarautan but then again idan baisamu ba no big deal idan any of yaran wanshi suka samu, adai dauko wani sarki ne daga cousins nasu da sauransu shine bazai yarda ba, anatse yace  kai yajiki? Kasami lafiya? Gyadamai kai Riyad yayi Baffa yace  har yanzu ana kan investigation koma su waye sukai kokarin kasheka za a kamasu, so don t worry, it s good zakai aure koda bakai maganan ba ma yana cikin plan dina nace kafito da mata you need to settle down shi lokaci baya jiran kowa mutuwa ake kullum Munir ya kalla daketa sunnar dakai yace  kaikuma fa yaushe zaka fito da taka matar? Dasauri Munir yadago kanshi saikuma ya nuna kanshi foolishly yace  Baffa ni akufule Baffa yamai dakuwa yace  a a ni Gwaggo ta zubamai rankwashi tace  dan kaniyanka kaima kafito da mata akace kabar da hannun Gwaggo yayi yana turo baki yakalli Baffa yace  toh Baffa zan fara nema daga yanzu gyadamai kai Baffa yayi yace  kutashi kuje toh lemme speak to Mama tashi sukayi suka fice daga dakin.
Direct dakin Mom yayi yana bude kofa Mom tace  get out Riyad gaban kofan ya tsaya yace  sorry Mommy please Munir naje kirafa yarakani wajen Hajiya


Cikin fushi Mom tace  tell me Riyad akwai abinda kataba so daban maka ba? You showed me duk cikin yan uwanka Munir kakeso dudda ban shiri da mahaifiyarsa but nabarka dashi but na gayamaka kadena zuwa side dinsu banso banso yare nake maka daka kasa fahimtata eh? Ahankali yafara tafiya yakai inda take sai kawai ya rungumeta ashagwabe yace  I am sorry Mommyyyy bazan karaba kinga banda lafiya karki fushi dani please am missing Dad already abin zaimin yawa shiruu tayi saikuma ahankali tace  okay nahakura but baka ba ita that woman is the reason har Babanku ya rasu baya shiri dani she come between ni da shi, allow me to plan your wedding and coronation in peace kaji sakinta yayi sai kawai ya daura kanshi kan cinyanta ahankali yace  Mom kimin auren na yarda but please Mommy banson nazama sarki dan Allah I am too young to be Sarki, Mom I want to tour round the world with my wife in peace cikeda fada tace  kaje sama da 58 countries wani tour round the world ne yarage bakayi ba? Is time kayi taking responsibility naka Riyad, you are royalty Riyad, kai Royal blood ne ba normal samari out there ba, duk wanda aka haifa a royal family akwai high possibility zai iya zama king so accept your calling, and Babana zai turo bodyguards dazasu dinga binka anywhere and everything dasauri yatashi yace  Mom banso wlh banso wani kalan kallo tamai tace  did you even know su waye da waye ke kokarin kashe ka? Kallonta yayi yace  suwaye? Tana kallonshi tace  I don t know but my gut is telling me Yayanku from the way yake eye service dan he s everywhere, da yarinyar nan bata cecekaba I don t know what would ve happened dan ijiyan zuciya Mom tasauke cike da damuwa tace  kullum bana baccin dare sabida tunanin wasu out there are trying to kill my son dan lumshe idanu Riyad yayi ahankali yace  Mom lemme see the footage iPad dake gefenta agadon tadauka ta bashi daidai lokacin akai sallama yar aiki ta gayamata tai baki tashi tayi tawuce tafita shikuma ya kwanta ahankali kan gadon tareda playing footage din da aka samo daga airport din yana kallo kusan footage biyar ne daban daban tun na shigowan shi arrival hall dana elevator saina bayin wanda shine na ukun, tsare cleaner yarinyar da ido yayi, a lokacin da abin yafaru bai wani kalleta ba dan yana cikin tashin hankali sai yanzu yake kallonta on this footage dudda is not that clear video karkar dinnan but yanda ta turashi cikin sharan yakala da yanda tarufe da how she handled everything ahankali yace  who is this feisty gurl ? The way takebin music yake kallo, he was actually watching the footage to see kozai gane criminals din but yana fara kallo attention nashi kawai yadawo kan cleaner, har footage data kaishi wajen dumping shara yakala da yanda take tafiya sai kawai yayi pursing video tareda zooming face nata yace  who are you? You saved my life.
CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK

wa.me/+2347012181461

=ث? SANYI DA ZAFI =ث?




'

HAPPY JUMMA AT GIFT <؁?

EPISODE 7??
Zaune suke dukansu afada, dan kowa yanzu is at home babu wani maganan zuwa aiki ko wani abu zaman makoki suke, yawanci Kabir ke attending, Riyad na zaune inda yake hardly yake magana, wayanshi ne yahau ringing ganin Mom yasa yadauka yakai wayan kunne batare dayayi magana ba, Mom tace  come nayi arranging private outing dakai da Munir da 2 security personnel da Doddo (Baban Mom Attorney General na Nigeria) ya aiko maka dashi daga Abuja kuzo kuje kaga Haleema gobe zata wuce school jiyayi kawai ranshi yabaci amman yadaure ahankali yace  okay yazare wayan daga kunne, kallon yayinshi yayi yace  Mom nakirana bari naje gyadamai kai sukayi banda Kabeer dako kallonshi baiyiba, tashi yayi a tsanake yana gyara zaman milk jumper rigan dake jikinshi nawani attajirin yadi, fadawa sukahaumai kirari.  Takawanka lafiya Babban mutum! Yariman dashi kadai aka haifa agarin Riyad mai martaba yabashi suna Riyad, dan kwalisan zakaran da ya riga yayi cha& .. wucewa yayi dasauri yafice dan baiso yawuce side na Mom a falo yasameta ita kadai tai murmushi ta taso dasauri tana gyaramai gaban wuyan riganshi tace  Masha Allah, yarona akwai kyau wlh, bama saika chanza kaya ba ashagwabe kaman zaiyi kuka yace  Mommmm dan hararanshi tayi tace  shagwabanka will not work nabiye maka u will never get married ko Doddo yayi na am da decision din ahankali yarike hannun Mom din kaman dan yaro yace  but Mom I don t even know the girl balle na sota dan shiru tayi tana kallon yanda yake mata wanda halinshi ne duk girmanshi idan bayason abu haka yake mata shagwaba at this point so take ta lallabashi dan batason tasake fada da yaronta datakeso sama da komi aduniya cikeda so tace  Son you are from royal family yawanci haka ake aure, first wife din Baban ka Maman su Kabeer da 2second wife dinsa Maman su Munir duk auren hadine baya sonsu, mai Babban daki ta zabamai su ya aura dan bayaja da maganan mahaifiyarsa, daga kan Maman su Shuibu dakuma ni last wife dinsa ne matan da marigayi yaso yakumayi soyayya damu is a normal thing haka abun yake, gidan sarauta kenan with time zakaso Haleematu she s a good girl duk agaban mu nan ta taso and she really loves you kaman kamata asiri d ana badai farin jini ba Mom tai dan dariya dayasa kawai ya rungumeta tareda daura kanshi kan kafadanta wlh zaka dauka karamin yarone murya chan ciki yace  to Mom at least Baba yayi koda 7days ne kafin nafara zuwa neman wata, Mom I am still moaning my father I am not in the right state of mind to meet any girl ko talk to her cikeda lalama Mom ta shafa kanshi tace  I know but do it for me kaji ko akwai abinda bazaka iyamin ba ni Maman ka? Ahankali yace  babu murmushi tayi tace  yauwa dan albarka, Oya tafi jeka shiga mota suna jiranka abaya gyadama Mom kai yayi yasaketa ahankali wani kalan murmushi Mom take tabishi da kallo tana kara wani son yaron nata da alfahari dashi wucewa yayi yazaga baya budemai bayan wata mahaukaciyar tinted jeep akayi ya shige security yarufe kofa kallon yanayinshi Munir yayi ahankali yace  chill kawai being born from this family I guess comes with all this abubuwan fuzar da iska Riyad yayi yakalli gefe baice komiba aka tada motan fita daga gidan sukayi tawani secret gate basu da nisa nan da nan sukakai gidan Waziri lafiyayyen kayattacen iso aka musu aka kaisu wani lafiyayen falo suka zauna wayanshi yaciro yana dannawa kawai, Maman Haleema ce tafito cikeda farinciki tace  sannunku da zuwa Yarima Riyad da Munir sannu sannunku anatse Munir yace  ina yini Anty anatse shima Riyad kanshi na kasa muryanshi baya fita sosai yace  ina yini Anty washe baki tayi kaman ta yaga zuciyanta sabida farin ciki tace  aahhh Riyad call me Mama ai yanzu anzama daya sannunku da zuwa bari naje gatanan zuwa tashi tayi tabar falon bata wani dade da fitaba Haleema tafito tana sanye dawani ubansu exclusive atampa an mata dinki Riga da skirt daya kamata dam ajiki, ta yano karamin gyale tayi makeup tai matukar kyau da black beauty ce abinta mai kyau tana kamshi, kallo daya tama Riyad zuciyanta yakusan tarwatse, gogan yayi masifan kyau yayi wani zama kaman shugaban kasa yana danna waya abinshi batare daya nuna alamun yamasan an shigo falon ba, zama tayi kujeran dake facing nasu cikin murya mai laushe da dadi tace  barka da zuwa Yarima Riyad ina yini ganin Riyad wayanshi yake dannawa yasa da sauri cikin barkwanci kartaga kaman yamata wulakanci Munir yace  auu ni za a watsama kasa a ido ni hoto ne a falon nan ko Riyad kadai kika gani ? Dan murmushi tayi tace  ai kaima zan gaidaka kawai nafara gaida wanda zai kasance mijinane kuma uban y ay ana nan bada jimawa ba  uh uh uhmmmm Munir yayi gyaran murya yana kama baki sai kawai yamike cikeda wasa yace  bari naje waje abuna tunda abun hakane, nima Allah yabani tawa uwar y ayan yataba Riyad ganin yaki dena taba waya yace  ina waje gyadamai kai Riyad yayi yawuce yatafi zai cigaba da danna waya dasauri cikin murya mai sanyi Haleema tace  bismillah yallabai ga abinci da abunsha na ijiye maka a dinning dan dago idanu yayi ya zubamata su dasauri tasauke nata idanun kasa dan bazata iya jure kallonshi ba, idanunshi kaman an wanke da madara, tana wani irin jin dadi aranta kaman an gama biya mata bukatunta na duniya, daga sama zuwa kasa ya kalleta yaune rana na farko dayake kallonta baiga wani makusa ba she s fine, educated classy but shi baiji that feeling of love da akace anaji in his heart ba, his heart is not racing, daya ganta his heart didn t flutter, infact zuciyanshi is beating normal, breathing nashi bai chanza ba, ya kalleta and he don t feel like looking at her again, she s fine but batai making heart nashi fine ba, he s not having butterflies nor goosebumps acikinshi da jikinshi, he s not finding her intriguing dudda tai makeup etc, nothing about her is enticing his aura, he read alot barinma lokacin PHd nashi, he knows the signs of love and baiji ko daya game da itaba, he sees her just the way he sees kowace diya mace aduniya nothing special nothing different, all this look and assessment yayishi ne in secs na kallonta kawai ya dauke kai yacigaba da danna wayanshi ayangance batare dayace mata uppan ba

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login