Showing 18001 words to 21000 words out of 110563 words

Chapter 7 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21051

karasa maganan ba yawani kalan hankadata kan gado dasauri ta juyo ganin yana bude mazariyan wando wlh har cikin ranta taji kaman tai ihun dadi tadai daure tai shiru tana jiranshi, kafafunta yaja cikin fushi yace  you reported me sabida this I hope nabaki shikenan ya kwashe skirt nata sama yadage rigan sama addu a yayi yashiga ciki, runtse idanu Haleematu tayi tanaji kaman zata shide, wata daya babu abinda ya shiga tsakaninsu sai yau.

Almost 1 good hour yayi cur akanta not because of kanshi but her, ya sauke hakkinta daga kanshi tunda harta fara kai karanshi, saida yaji ta bushe ya tabbatar idan yacigaba zafi kawai zataji sannan ya kyaleta sannan yatashi zaune kafin chan yamike tsaye yawuce bayi ya barta kan gadon wani mugun bacci na daukanta tana numfashi haryau takasa gane kan Riyad, zai iya 2month bai nemeta ba yawanci saitasa Mom a case nasu yake nemanta and he s so damn good in bed Innalillahi! The way he s this quiet bazaka taba tunanin zai iyacin mace ba, but en anytime yayi having wani abu da ita jitake kaman she s the luckiest gurl on earth, Riyad is good on bed, she don t even know how to explain, yana wasa da jikinta wani kalan dirty play fa, yauma haushin abinda tayine yasa bai tattabata yanda ya sababa, wlh haryau takasa gane yanajin dadin ta ko bayajin dadinta oho ko gurnani bayayi bai tabayiba, he s just super wired guy data kasa fassara halinshi haryau, and wiredness dinshi ke kara mata sonshi sosai aranta wlh, ahaka tana lumlumshe idanu bacci yayi awon gaba da ita.
**


Around 5 Mama ta tadata daga bacci, da kyar ta tadunma Mama, Mama tace  ke yarinya sai nauyin bacci kaman wani kato, tashi kin manta yau zaku koma makaranta eh? Hope kin dauki permission wajen aiki an baki shift na yamma ? Gyadama Mama kai tayi cikin gajiyan bacci, hannu Mama tasa tadagota ta taro kafadanta hakan yasa Rashida tasauke kanta akan kafadar Mama tana kara lumshe idanu still cikin bacci, dan jijjigata Mama tayi tace  Rashida ahankali tabude idahunta tass takalli Mama dasu Mama tace  I think drop most of ayyukanki tunda kin koma school kinga yanzu year 5 kike you need to study well, nakosa naga diyata tazama likita, saura 1yr yanzu, Allah ya aramin rai, ranan super wax zan saka amin combination da super lace dan murmushi kadan Rashida tayi tanason taji Mama na maganganu haka it makes her happy, Mama tace  yanzu dai kinga kina bukatan lokacin hutawa da lokacin karatu bakiga yanda kike gajiya ba da kyar kike tashi, ki saki sauran ayyukan ki rike na hotel din nan kadai tunda anfi biya, su Maman Miwa da sauran wajajen nan ki sakesu dan murmushi tayi sai kawai tahau yunkurin tashi ahankali dan muryanta baya fita sosai sabida daga bacci ta tashi tace  Mama so kike na bar aiki sabida mudinga karban abincin sadakan da yan anguwan nan suke kawo mana out of pity? Tadanyi shiru daidai takarasa mikewa tsayen batare data kalli Mama ba tace  this year is clinicals, zamuyi aiki a pediatric da obstetrics&gynecology, I can manage everything Mama trust me, Alhamdulillah kome aka koyamin sau daya ya zauna akaina, sannan daga yanzu koda ranan Sunday ne zan dinga zuwa library duk sati sau daya nayi muraji an duka abinda aka koya mana na that week, I can study Mama, I can do my duties na kula dake da siyamana kayan abinci da kudin magunguna, I can manage my work also tana maganan tayaye labule tafita daga dakin tawuce waje saida tafara sa abinci awuta sannan tawuce bayi tayi wanka tafito lokacin har sanwan yayi tazuba taliya sannan takoma daki tashiga saka kaya Mama na zaune kan dadduma tana kallonta, tana kallon yanda taketa ciro kayan ghana masgon dasuke agoge daga gani kasan dan kaya mai kyau take nema na zuwa school abu Mama taji ya tsaya mata a wuya sai kuma ta daure kawai ta dauke kanta daga kallonta.
Wani doguwan rigan atampa maroon ta zaba ta maida gefe, taciro lab coat nata dayake a goge shima ta ijiye gefe sannan ta maida sauran kayan ta shirya tsaf tawuce tafita tasake juya taliyan sannan tadawo tasa hijabi ta kabbatar salla.

Tana idarwa bata tsaya yin azkar ba ta fita ta juyo taliyan a kula tasama Mama ruwan zafi na wanka sannan tadawo tasake zama kan dadduma tafara azkar tana gamawa ta kalli Mama dake kallonta tace  Good Morning Mama na nikadai, Mama naji dadi nikadai kika haifa nake moreki banda kanni dazaki dinga raba attention naki akanmu most time tana maganan ne idan taga abu na damun Mama dan tasata tai murmushi, ganin Mama batai murmushi ba yasa takama hannunta tarike dasauri ahankali tace  Mamaaaaaaa tai maganan ashagwabe tana lankwasa kai, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace  babban burina arayuwa shine ki zama likita Rashida, banson wani abu dazai hanaki zama, kina bukatan lokacin dazaki karatu, banson ki fadi, banson ki sami carry over, nasan kinada kokari but dudda haka karatu yanada amfani, kina all this ayyuka bazaki sami lokacin yi ba, ki manta da kula dani Allah daya tsaga mana baki bazai hanamu abinda zamusa abakin ba, after this year next year zaki gama, please Rashida kibar ayyukan nan and focus a karatu tunda Mama ke maganan take kallonta batason sata cikin damuwa hakan yasa tace  to naji Mama amman tunda kinga sat1n nan muka koma karatu da practicals bazasuyi serious ba kibari nayi aikin zuwa karshen wata abiyani kudina saina dena kinji, zancen night shift ai HOD mu tasan dani bata taba sani a night shift ba sabida ke Mama, so ko yanzu ma bazan bazanyi night shift ba, kinga na karbi albashina saimu ijiye, kuma Mama kidena damuwa yarki ta dauko brain dinki bazan fadiba In sha Allah bayan kinamin addu a, to yanzu kin hakura na karasa zuwa karshen watan nan duk sai na saki aikin nabar na hotel din? Shiru Mama tayi tana kallonta Rashida da taurin kai da kafiya hmm, ijiyan zuciya tasauke tace  okay! Yau sha uku ga wata, karshen wata zaki sallame kowa, next month banson ganinki kina zuwa ayyuka nan gyadama Mama kai tayi tace  naji tashi Mama tayi tace  ai shikenan tawuce sip wani akwati zata dauko dasauri Rashida ta tashi tace  Mama stop ki kirani na dauko miki dasauri tasa hannunta tadauki akwatin tasaukar dashi kasa Mama tazo wajen ta zauna itama Rashida ta zauna gaban box din tana jiran tadauki abinda zata dauka tasake daukan akwatin ta maida sama, wata yar jaka Mama tadauko ac1k1n box din tamika mata tace  gashi ungo dasauri Rashida ta kalli jakan data bata tace  na menene Mama ? Tasa hannu tana karba, zage zip din box din Mama tashigayi tace  naki ne kibude da sauri taciro bakin ledan data gani cikin jakan dayake a kulle tashiga budewa saiga crocs a ledansu pink color mai kyau ba asalin designers one dinba but irin normal wanda ake saidawa a market yan 5k-7k dakuma stethoscope pink shima mai kyau, da mamaki take kallon kayan dakuma murmushi akan fuskanta tama kasa cewa komi Mama ta kalleta tace  bakiso ne oya bani kayana, last month danaje clinic wata Hajiya tarabamana kudi a envelop naduba naga 20k ne shine na shiga kasuwa na siya miki crocs naga shi likitoshi kesawa a clinic dimu duka likitocin wajen shine akafansu shine na shiga kasuwa na sayomiki ashe haka takalmin keda tsada dubu takwas aka saidamin na hada miki da wannan abun gwajin nace nima y ata tai kaman yan gayun likitocin danake gani a clinic dinmu hawaye ne yacika idanun Rashida tana kallon Mama na bata labarin Mama takare da  nazo naboyesu nace bazan baki ba sai ranan dazakuyi resuming school daidai lokacin hawaye ya sauko daga idanunta Mama tace  ke mehaka kuka kikemin ? Kawai rungume Mama tayi da gudu ta kankameta ahankali tace  thank you Mama thank you shafa bayanta Mama tayi tace  gabaki dayan rayuwanki Rashida nine na cinye miki ita, bakida lokacin kanki, komi kika samu ni, kome kikeyi sabida nine, konace ki sayawa kanki abu bakiyi saisa na saya miki kema ki shiga sahun yan gayu aga y ata fess fess akara kallonta sabida yanda tai kyau, Allah yakawo miji na gari cikin shagwaba ta ture Mama tace  ni bazanyi aure ba Mama, bazan taba iya barinki ba baki Mama ta kama tace  ke kodai zan kaiki gidan zumane amiki rukiya kaman me aljanu bazaki aure ba gyadama Mama kai tayi tadauki takalminta tana budewa daga leda tace  inhar ban samu mijin dazai yarda na daukeki muje gidanshi tareba ina ganinki ina baki kulawa wlh gara na kare rayuwana ahaka da sauri Mama tamata dakuwa tace  kinci mai garinku Rashida dariya Rashida tayi sosai tace  wlh Mama da gaske nake bazan taba rabuwa dake ba Allah Mama ganin Mama zatai magana yasa ta tashi da sauri tace  bari nasa takalmina fararen kafanta ta zura cikin crocs din sun mata bala in kyau Mama tace  Masha Allah Tubarkallah komi kema yarinyana kyau wlh, kinga kafanki aciki kuwa dudda kafan fara ba lalli amman yayi kyau wani juyi tayi cikin takalmin tace  Mama inason takalmin thank you so much Mamaa, bari na tafi tawuce tasa doguwan rigan data fito dashi yakamata ya nuna her flat tummy sosai da very full chest nata cus she has boobs kaman Mama, itama Mama harda rama yasa ba a ganin nata yanzu, dan kwali ta daura tayafa gyalenta tai arranging lab coat nata a bag pack da books da stethoscope da Mama ta siyamata da komi ciki ta goya abaya tasa yar wayanta a aljihun riganta da earpiece tace  natafi Mama Mama tace  dan Allah kici abinci kinji kada ki manta dasauri tace  to Mama zanci, bye Mama Mama tace  ubangiji Allah bada za a Allah ya taimaka Allah ya tsareki Allah yakuma baki miji nagari .

Shagon Maman Miwa taje ta gayamata ta koma school da safe zata dinga zuwa aiki, nan da nan tayi wanke wanke ta share ko ina tai mopping after 8 tagama komi Maman Miwa tabata 2k saikuma ta bata 200 tace  kihau adaidaita kitafi makaranta baki takaba murmushi kadan tayi tace  nagode Maman Miwa sannan tawuce tafito MamanMiwa tabita da kallo tace yarinya ga kyau har kyau ba miji.

Adaidaita sahu ta tare ta shiga sai BUK direct department dinsu ta wuce staircase tahau tana tafiya daidai lokacin wani guy da wata young lady kaman mate na Rasheeda suna sanye da kayan gida lab coat a hannunsu na saukowa hada ido Rashida tayi da guy din da sauri ta dauke kai tacigaba da tafiya abinta tana hayowa su suna saukowa hade fuska yarinyar tayi tace  Bilal yaushe zaka fadamin inda kahadamin suprise birthday party ? Gabaki dayan hankalinshi nakan Rashida dake hayowa abinta batare data kara kallon inda suke ba, mintsilin shi yarinyar tayi abaya hakan yasa yakalleta da sauri yace  sorry Layla come again me kikace ? Abu taji ya tsaya mata awuya sai kawai tawuce da sauri tana sauka da sauri yabita da sauri yace  Layla wait common tuni tafice dan tsayawa yayi daidai Rashida tahau staircase din dayake kai yabita da kallo sabida kyau datamai doguwan atampan riganta yamata kyau over, dudda ko man baki babu a lips nata balle hoda ko kwalli ahankali yace  we re going to clinic you don t need to go up kasa zamu kaman bada ita yake magana ba kala bata cemai ba kawai ta juya tashiga sauka da sauri yabita yace  wai mesa bakimin magana Rashy? Chak ta tsaya saikuma tajuyo ta kalleshi tace  kada ka sake kuskuren kirana da sunan nan only those that are dear to me ke kirana dashi not you ta juya, dasauri yabita yace  I don t understand why exactly you re angry with me, I told you nace miki ina sonki ne banda knowledge na your mother s illness, agidanmu baza a taba barina na auri yar wacce takeda H& & .  Bilal!!!! Rashida takirashi da karfi ta daga hannu zata kaimai mari ranta abala in bace tace  the next time bakin nan naka zai ambato mahaifiyata wlh saina zubar da hakoranka! Nataba cemaka wani abu? Nace ka aureni dama? I don t even know kana existing so go to hell! Tana maganan tajuya fuuuu yabita da kallo kowa na department nasu yasan Rashida da masifa but shi he just said it badan rashin mutunci ba he was trying to tell her baza a bari ya aureta agidansu ba knowing Mamanta nada HIV, baza a taba bari ya auro diyar unholy mace ba, still he was trying to tell her su zama friends dan he was feeling guilty yanda yagama cewa yana sonta last year dan last year yayi joining nasu dan transfer ya karba daga former school dayake medicine a Sudan, sun fara soyayya sosai yan aji sukamai gulma Mamanta nada HiV bai yarda ba dan bata taba fadamai ba saida aka kirashi akace yazo ga Mamanta tazo clinic itama tana wajen Maman shine yaje ko yagani daga ranan yayi ghosting nata yaki kiranta yadaina daukan wayanda kotamai magana a class yayi banza da ita saima yazo yana kula yan matan class nasu sosai danya bakanta mata rai, saikuma during this 2weeks holiday saiyaji wani irin soyayya ta na tasomai yau daya ganta saiyaji tafi ko yaushe kyau sonyayyan yadawomai fresh azuciye kaman yahadiyeta dan wlh duk department nasu baiga me kyanta ba kawai dai no one can approach her ne sabida masifan ta da fitina.


Koda yafito yaga harta shige bus nasu ta zauna taciro yar wayanta ta makala earpiece tasa a kunne sabida yanda zuciya ta ke tafarfasa, ahankali yasauke ijiyan zuciya yawuce wajen motar shi inda Layla take a tsaye tana hararanshi yabude yana mata murmushi yace  wai ke lafiyanki common shiga mota muje yashiga mota yatada yaja motan Rashida ta kalla sannan tasake sauke ijiyan zuciya taso Bilal last session nasu sabida she thought shine mutum na farko daya sota for who she is dan ta dauka yasan waye ita kowa na department nasu ai yasani so tadauka yasani, tun bata kulashi tafara kulashi sabida yanda yake shige mata, she really liked him suna waya but rana daya kawai yadaina kulata yadaina amsa wayanta yana kula yan matan ajinsu agabanta yana cemusu yana sonsu just to hurt her, abin yamata ciwo sabida tanada kishi but bata taba nunawa ba, bata taba nuna tadamu ba saima daina kallonshi datayi da kallon inda suke cus she s even blaming herself data budemai zuciyanta bayan tasan duk wanda zatai soyayya dashi baya going anywhere, idan ba lectures gareta ba earpiece zatasa a kunne tana karatu tanabin everything da aka musu, she s a fast learner na ban mamaki, takoyama kanta rayuwan she s enough for herself, she doesn t need people cus gani take kowa yimata kallon yar mai HIV ake diyar fasuka, babu abinda ba a kiran Mama dashi har anan ajinsu su ana cewa Mama karuwa ce cus gata kyakkyawa daman, batason wata ko wani yashigo space nata and hurt her saisa she s always always protecting her space bawai batason tayi kawa bane ko kawance baya burgeta bane, no kawai she don t wanna get hurt, kawayenta na layinsu duk iyayensu sun raba yaransu da ita saisa ta maida kanta and centered her life to be just she and her mom.

Yan ajin always sees her as mafadaciya ko magana kama Rashida zai iya koma muku fada saisa suna avoiding nata suma but during group work ko wani abu zatai participating that is idan bamata daukin nauyin yin aikin gabaki dayaba dan tanada bala in kokari haka dai rayuwan ta yake.


Sunkai asibiti dudda sun saba da hospital din still saida akai orientation sannan aka nuna musu roaster gobe zasu fara taduba taba bata night, daga 8 ne shift nata zuwa 1 kullum banda asabar da lahadi all thanks to HOD nata! She s so happy da roaster sukai few abu by 11 suka tafi direct hotel din ta wuce takai wajajen 1 tawuce wajen changing room nasu tabude locker dinta taciro uniform nata tashiga chanzawa daidai tagama chanza kayan tana kokarin saka karamin farin hijabinta aka turo door aka shigo changing room din wata cleaner na ce Joy tai murmushi tana kallon gashinta dasauri Rashida takarasa saka hijabin Joy tace  Hi kinzo muje Madam zata mana magana kafin mufara aiki a seminar room maida locker Rashida tayi tarufe tadauki wayanta da earpiece tasaka a aljihun wando tawuce tafito Joy tabiyota abaya wani babban hall sukaje da kujeru ke cike su kusan 34 cleaners din na afternoon zama sukayi Madam dinsu dake tsaye gaban hall tace  I called for this meeting sabida na sanar daku Oga na gari he can come anytime, alot of you dakukai joining this hotel like 2yrs ago baku sanshi ba, he can come at any moment or day idan yaga dama, baya tolerating the slitest of dirt dan haka kuyi aiki dakyau, Rashida! Dago kanta Rashida tayi takalleta Madam tace  since kina afternoon duty yanzu anytime kika shigo before ki goge anywhere ki tabbata kinzo wajena kin amshi key kin goge office din Oga, for afternoon kene mai gyara office din da safe kuma Kola, abubuwan mop na gyaran office dinshi is different dana general gyara after the meeting you will follow me ki karba Gyadamata kai Rashida tayi tace  Yes Ma tunda take aiki yau ne rana na farko dataji anyi maganan mai hotel dinma kusan shekara biyu kenan bai

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login