Showing 78001 words to 81000 words out of 110563 words

Chapter 27 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21063

Rashida ta sauko tana sanye da rigan bacci iya guiwa tana goge idanu tazo dinning din, tabaya ta rungume Muji tace  morning Dad tasakeshi tawuce wajen Jummai ta rungumeta tace  good morning Mommy washe baki Jummai tayi tace  sai yanzu aka tashi sabida anzo hutu daga school ko, Allah kaimu next month ki koma Istanbul zamuga karyan iskanci Muji dake binta da kallo idanunshi suka sauka kan Nail polish dake kumbunan

ta shi dama yanada fada sosai cikeda fada yace  wat is that kikasa a nails naki? Da sauri ta kalli kumbunan saikuma ta boye hannun abayanta cikeda fada yace  Maryam kina yar musulma zaki dingasa nail polish? Ashagwabe tace  Dady is normal thing fa zabura Muji yayi zai tashi ganin haka yasa Jummai ta tashi da sauri kafin kace me ta kwashe yarinyar da mari tace  how dare you Babanki na magana kina bashi amsa are you Mad? Tarbiyan dana baki kenan Maryam? Ke tadaga hannu zata sake kwasa mata mari dasauri Muji yariketa yace  common it s okay! She s just a child cikin fushi Jummai tace  23yrs ne a child, noo babu wacce ta isa tai talking back at her Dad dan lumshe idanu Muji yayi yadaga mata hannu ahankali yace  it s okay koma ki zauna zama Jummai tayi ba musu shikuma yakama hannun Maryam dake kuka yace  don t mind Maman ki da saurin hannu rungume Baban yarinyar tayi da sauri ashagwbe tace  Dady I love you alot I don t love Mom she always hit me hararanta Jummai tayi dayasa Muji yayi dan dariya yace  ya isa to Mommy ki is just trying to correct you kinsan Maman ki mace ce datasan values na rayuwa ga ilimi ga hikima, ga dabara, I want you to grow up and be like her okay, dan haka kada ko kara shafa this abu on your nails kinji ? Gyadamai kai tayi tace  okay Dady sakinta yayi yace  bari naje wajen Mai Babban daki zauna ki break yayi maganan yana wucewa yafita Jummai tabishi da kallo yana karasa ficewa da sauri ta tashi tazo wajen Maryam tana duba fuskan ta tace  ohh my child na mareki sosai? Yakuri kinji? Tureta Maryam tayi da karfi saida ta dafa kujera kaman zata fadi, yarinyar ta nunata da hannu cikeda tsiwa tace  Momy idan kina act naki stop hiting me banso, haba zaki illatamin face ne kija Kamal yace I m looking ugly wat is wrong with you ? Cikeda lallabawa tazo kusa da ita takai hannunta tana shafa fuskan tace  yakuri my baby, bazan karaba i promise, haba Yamyam dina, sorry sorry, Mommy is sorry gayamin mezan miki kihakura Dasauri Maryam tace  to kibarni naje party Kamal in kinaso na hakura Dasauri Jummai tace  nabari but kidawo dawuri before your father notice baki gida .



EPISODE HABISMA IS A BUSINESS THAT DEAL WITH INNERWEARS BOTH NA MAZA DA MATA HARMA DANA YARA ME KUJE JIRA?? MAKESURE KUN SAYI NAKU BY SENDING THEM A DM 09034049623 08064643886 Around 5 yafito daga part nashi yana tafiya daidai kaman baiso yataka kasa yana zuba uban kamshi. "Bijimin Sarki, sadaukin Sarki, adalin Sarki, ci gari yaya ka kwana, ci gari yaya ka tashi, ka kwana lafiya ka tashi lafiya, da kai da mutanen gidanka, dogo da gajere, da mai tsawo da, mace da namiji, da babba da yaro? Ci gari yaya ka tashi. Sadaukin sarki adalin sarki, Kano garinka ne, Kanon dabo kasar ka ne, da anki da anso, Allah ka taya maka, Annabi ka taya maka, ci gari zauna daidai." Ahankali yake takawa harya shiga fadan yadan zauna yayi magana da mabiyansa dan an kwana biyu ba a gansa ba inda wasu kemai yajiki wasu namai an dawo lafiya yagaisa da Waziri daketa kallonshi yana murmushi bai wani dadeba ya sallami mutane yatashi yabar fadan zuwa side na Mom wanda yaga miss calls nata yafi a kirga this past few days yaki dagawa, shiga ciki yayi da sallama zaune yaga Mom kan kujera Haleema zaune kusada ita tadaga kafafun Mom din tadaura kan cinyanta tanama Mom tausa suna hira, kallo daya yama Mom bala in daya hango a fuskanta saida gabanshi yafadi sauke kanshi kasa yayi yamaida kofan yarufe yashigo cikin dakin waje yasamu yazauna akan kujera ahankali yace  Mom ina yini Haleema da tunda yashigo take kallonshi kaman tsohuwar mayya wani azaban sonshi na tashi azuciyanta tace  ina yi& &  hannu Mom tanuna ma Haleema ranta a bala in bace kaman zata yanka mata mari tace  karki kuskura ki gaida tambadadden yaron nan, wanda bai girmamani ba bazaki girmamasa ba Haleematu dan lumshe idanu Riyad yayi kafin yadaga kanshi yakalli Haleematu anatse yace  dan bamu wuri nai magana da Mom cikeda fada Mom tace  taje ina? Wani wuri zata bamu? Haleema is part of familyn mu babu wani sirri na jikinka dabata sani ba so she s not going anywhere dauke kanshi kasa yayi yarasa mesa tunda yazama Sarki shi da Mom ke having issues, baison abubuwan datakemai, and bai isa yayi magana ba tahau fushi da fada, daurewa yayi yadago kanshi yakalleta ahankali yace  I m sorry Mom for not answering calls naki I was in the middle of something sai& & .  Kana tare da karuwan dadiron ka ko! Dasauri ya kalli Mom hakan yasa ta karbe kafafunta da Haleema ke matsawa har lokacin ta sauke kasa tace  inace ita takiraka tsakar dare ka mike jiki narawa ka shiga saka kaya katafi ? Ahankali yakalli Haleema data sauke kanta kasa dasauri kaman munafuka ganin bazata taba chanxawa from telling Mom everything about them ba saikuma yasake daurewa yace  Mom ba abinda kike tunani bane  abin miye to eh stupid boy? Kana ganin kazama sarki an fara huremaka kunne ni zaka watsama kasa a idanu? Bayan I was the one that made you the king? Munir dinma dagayau na rabaka dashi wlh! Dasauri yakalli Mom tace  yes and duka mukaman daka bashi na company ka ka karbe yaje ya nemi nasa kudin ya bude nashi company atoh! Dagayau d ana bazai kara feeding nashi ba harma kayi sponsoring lavish lifestyle dinsa nan ko ba asan uban mamarsa malamin zaure bane anzo an mannema nawa yaron dakeda grandfather attorney na federal republic gabaki daya sauke kansa kasa yayi kasa ganin ran Mom abace yake yasa ahankali yace  Mom kiyakuri cikin fushi Mom tace  tun ranan hawan salla an rasa ina kake ni ni uwarka bankai matsayin ka dauki wayana ba ka zama gantalallen sarki Allah kadai yasan inda kake zuwa ka saki matarka kaman kaza baka iya gamsar da ita lusarin namiji dakai! Dan ijiyan zuciya Riyad ya sauke kadan saikawai ya mike tsaye yajuya yayi hanyar kofa kai yanda Mom taji jikinta kaman an kwara mata wuta ganin ita kemai magana agaban Haleema zai kunyatata haka yatashi zai tafi yasa batai wata wata ba ta tashi kawai Riyad jiyayi an kama bayan riganshi da sauri yajuyo, Mom batai watawata ba ta yankamai mari ganin yajuyo jikake tasssss!

Saida Haleema tai ihu taredakai hannunta da gudu tarufe bakinta ganin yanda Mom ta daurama Sarki gabaki daya Riyad mari tana huci, chak Riyad ya tsaya yanama Mom wani irin kallon dabata taba ganin yamata irinshi ba, tunda yataso Mom bata taba daga hannu tadakeshi ba tun yana dan kankani sai yau, cikeda hargowa tace  kake kallona haka daga hannu karama mana ko bazaka iya bane eh? Ai na dauka kakai karfin tunda kazama Sarki rama marin Riyad kasa daina kallon Mom yayi, Mom ta nunashi da yatsa tace  kai harka isa ni Mamanka ina maka magana ka mike and walk out of me? Who are you? Are you mad? Go back there and sit down! Tanunamai kujeran daya tashi dagakai har lokacin kallonta yake ihu tamai tace  Wlh Riyad bazan sake magana ba kuma ka wuce kaje ka zauna kona mummunar bata maka rai, zan maka abinda bantaba maka ba, I said go and sit! Tayi uban ihu, ijiyan zuciya ya sauke ahankali yakoma yaje ya zauna mamaki ya kashe Haleema yanzu biyayyan Riyad yakai haka dama? Wlh wlh Mamanta bata isa tamata irin marin da Mom tama Riyad ba har gefen idanunshi yadan tara jini sabida tasami wajen idanunshi dan yajuyo ne without knowing zai sha mari tasameshi awajen. Komawa Mom tayi ta zauna tana facing nashi tana dukan kirjinta tace  the slap is for walking out on me ina maka magana, for not answering calls dina for days, Riyad ba sarki ga ko president kazama zan hukunta ka sabida you re my Son! And you re a boy in my eyes, dagayau inhar bawani uziri bane katashi kafita kabar gidan nan wlh saina wulakanta ka saina cimaka mutunci, Haleema dasauri Haleema tace  na am Mom dina cikin iko da isa tace  duk randa yasake batamiki rai koyatashi kuna kwance yafita ki sanar dani ahankali Haleema tace  to Mom dina dan huci Riyad yayi ahankali, Mom takalleshi tace  if you like kazama 90yrs you are my baby and zan hukuntaka if you misbehave stupid boy kawai ta tashi tawuce sama abinta dasauri Haleema tabita sama gudun kar Riyad ya huce akanta tace  Mom don t be angry .
Yadade rabon da ranshi yayi irin bacin nan dayayi ahankali yatashi yafito kanshi namai zafi wucewa flat dinshi zaiyi daidai Munir na zuwa wajen yace  Ammi na kira baiso yajeba but sanin Rashida na wajen yasa yabishi yaki kallon Munir karya lura da fuskanshi shiga side din yayi da sallama ganin Ammi bata falo yasa yawuce sama ahankali yayi knocking gaban dakinta Ammi tace  come in bude kofan Ammi yayi ahankali yashiga ciki magana taso tamai kan Rashida amman fuskanshi datagani abinka da farin fata barin wajajen idanunshi yasa ta mikeda sauri duk yanda taso ta daure karta tambaya takasa hakan yasa tace  meya samekaa fuska? Dan dago idanu yayi yakalleta jin tambayan datamai hakan yasa taga dan jinin daya taru a idanunshi da kyau da sauri yadauke kai yace  fuska na? Meya sameshi ? Tashi Ammi tayi tazo dab dashi ta tsaya saikuma tace  Riyad! Ahankali yadago kanshi ya kalleta gefen fuskanshi tabi da kallo kafin tahade rai tace  who slapped you? Sauke kanshi yayi kasa dasauri baitaba sanin Ammi zata gane anyi slapping nashi ba bazai taba iya mata karyaba nor bata amsa Ammi jitayi zuciyanta yamata badadi ranta yabaci haryakai ga batasan sanda tace  ban haifeka sabida wata ta dakamin kai ba! Ahankali yakalli Ammi, jaa Ammi taga idanunshi sunyi dasauri tasa hannunta takama hannunshi takaishi gaban gadonta zaunar dashi tayi ya zauna tabude karamin fridge na dakinta taciro ice bag tawuce bayinta da sauri tai wrapping nashi cikin towel tafito tsayawa tayi agabanshi ahankali tasa hannu takama habanshi tadago da kanshi ta daura ice bag gefen idanunshi lumshe ido yayi yanajin saukan ni ima ajikinshi tunda yake baitaba jinshi this close to Ammi ba sai yau, ahankali kaman dan Baby ya rungumeta yadaura kanshi akan cikinta tareda kulle hannunshi tabayanta batare dayace komiba, mutuwan tsaye Ammi tayi cus bata tabajin dumin yaronta like this ba tunda yana jariri, murya chan kasa tace  this should be the first and the last time dazaka tsaya wani ya kaimaka duka kowaye kai koda nine! Riyad dudda nasan forcing naka akayi kazama sarki that doesn t change the fact that you are a king! Kafadi dole aji! Dole abi! Kowa na fadan nan abayan ka suke! Stand up for yourself and be a man! Idan you can t protect kanka how can you protect marainiyan yarinyar nan daka aura? Dago kanshi ahankali yayi yakalli Ammi ahankali Ammi taduko tai cupping face nashi tace  kai Gwarzo ne jarumin jarumai! Zaki dodon kowa! This incident should never repeat itself am I clear? Gyadamata kai yayi ahankali saikuma yakara hugging nata he s feeling wani irin strong love for mahaifiyarshi da bai tabaji da ba sai yau.
EPISODE 40
Sun dade ahaka batare daya saketa ba, bude kofan dakin da akayi yasa yasaki Ammi da sauri, Munir ne yashigo yana kallon fuskanshi yace "meya sameka?" Ammi bata tanka ba tawuce tafita daga dakin, dan lumshe idanu Riyad yayi yace
"I'm fine don't worry Munir" sosai abin yataba Munir cus yasan aikin Mom ne amman ya kyaleshi yace tashi muje mosque" tashi yayi Munir yabashi wani bakin glass karba yayi yasaka suka fice tare, har isha'i a mosque sukayi sannan suka fito tare suka koma side dinsu babu kowa a falo hakan yasa ya wuce sama hoping Ammi na salla adakinta.
Ahankali yabude dakin da Rasheeda keciki yashiga tana kwance kan dadduma ta cire hijabin ta ijiye a gefe gashin kanta abarbaje wanda har yanzu da danshi, idanunta a lumshe haryau fuskanta a kumbure suke, tundaga kan kafafunta yabi da kallo dake sanye da skirt din daya kama hips nata zuwa dan navel dinta daya leko sabida yanayin yanda ta kwanta yasa rigan yadan dage sama, kallo daya yama chest nata ta rigan yacire idanunshi da sauri kafin ahankali yadaura idanunshi kanta.
Bawai tayi bacci bane idanunta biyu yanzu kawai batajin dadin rayuwanta ne, batajin dadin zuciyanta batajin dadin komi she knows she's alive but noting makes sense again, kamshin turaren shi dataji yasa ahankali tadan bude idanunta, daga inda take take kallonshi kaman yanda Riyad ya tsaya yana kallonta daga kofa, akwai something about Riyad presence that gives mind nata peace, and that is just how she felt yanzu ma data ganshi sai kawai ta tsareshi da idanu tana kallonshi batako kyaftawa kaman yaune rana na farko data fara ganishi, ahankali yazo wajen kafin gently yazauna yana kallonta kaman yanda take kallonshi cikin tsantsan care yace "how are you? Are you okay?" Wani abu taji ya tsayamata awuya tana kallonshi baitaba expecting zatamai magana ba sai chan cikin muryanta da idan baka natsu ba bazaka tabaji ba tace "Mama left me l'm all alone yanzu" hannunshi yakai ahankali ya sharce hawayen daya gangaromata zuwa hanci saikuma ya tsareta da idanu murya chan kasa yace "you are not alone Rashidahh!" Lumshe idanunta tayi saikuma ta tashi ahankali tana dafa gado tajuya zata wuce bayi karaf yarike mata hannu hakan yasa ta tsaya kaman yabude mata fanfon kuka sai kawai tafashe da kuka, ahankali yatashi yajuyo yasha gabanta ya tsaya yana kallon yanda take kuka tana kallonshi kafin ahankali yabude hannuwanshi yace "I will always be here for you come" tadade tana kallonshi ganin taki motsi yasa gently yajawota jikinshi kankameshi tayi sosai tana kuka sun dade ahaka atsaye kafin yafara tafiya ahaka yazauna bakin gado tana jikinshi ta kankameshi shima haka, bayanta yake tapping ahankali yace "cry as much as you want too l will not leave you" she's just feeling maganganun shi da yanda yake lallashinta like a little girl yana patting bayanta, dago kanta tayi tana kallon idanunshi yasan abinda take kallo hakan yasa ahankali yace "it's just a little accident Ammi tabani magani, and bayamin zafi" yayi maganan looking cute da kwai saitaji kirjinta ya buga maida kanta kirjinshi tayi back tai Kano yana patting bayanta har lokacin, sun dade ahaka tai lamo ajikinshi tana lumlumshe idanu kafin bacci yayi nasaran awon gaba da ita.
Ahankali ya kwantar da ita agadon yana kallon fuskanta daurewa yayi kawai be nuna komiba but the way ta kankameshi yana feeling every bit na boobs nata da yaji ba bra ajikinsu yakusan loosing control lips nata ya tsare da idanu sannan yatashi ahankali yaja bargo yarufa mata yawuce kofa ya kashe mata wuta yafito yana tafita ahankali yanda baiga kowa a falon ba ba bakarakin dadi yajiba yawuce yafita.Rabon dayaje flat na Haleema da kansa harya manta but yau kawai yawuce wajen, kai tsaye ya shiga gidan, jakadiya da wasu bayi yagani a compound nata suna bawa shuka ruwan dare suna gainshi kowa yazube. "An gaida mai Martaba sarkinmu mai adalci...." kofa yabude yashiga ciki Haleema yagani a falo tana zaune ta daura kafa daya kan wasu bayi na matsa mata kafada suna ganinshi suka zube.
"An gaida sar....." sama yayi yace "meet me upstairs" faduwa gabanta yayi takalli bayin tace "kutafi bangaren ku" sannan tamike ahankali gabanta na faduwa saikuma ta dauki wayanta ta shiga kitchen dasauri tai dialing number Mom tana dagawa tace "Mom ga Riyad yazo flat dina yawuce sama yace na sameshi achan, Mom idan ya rama marin dakikamai akaina fa"? Dan murmushin keta Mom tayi tace
"shi ya isa! Yasanni ai! Jeki sameshi kiji dame yazo kome yace ki kirani ki sanar dani" ahankali aleema tace "tom Mom dina" ta katse wayan tafito tawuce sama, dayake yanada still dakinshi asama hakan yasa tawuce wajen tareda bude kofa ahankali ta shiga yana zaune kan couch dake dakin yaciro waya yana dannawa hakan yasa tawuce bakin gado tazauna gabanta na faduwa still, tabude wayanta dake hannunta da sauri ta danne recording sannan ta kifa wayan akan cinyanta murya kasa kasa tace "gani Mai Martaba" kusan one minute yabata sannan yadago tareda ijiye wayan nashi a gefensa yazubamata wani irin matsiyacin kalio da saida gabanta yafadi tasauke kanta kasa da sauri strictly yace "are you married to me to married to my Mother?" Kallonshi tayi dasauri cikin muryan nan kaman na munafukai tace "haba Baby wat are you implying......"Answer the question!" Riyad yayi maganan azafafe babu wasa kodaya a harshen sa dayasa Haleema taji kirjinta na bugawa dim dim dim ahankali tace "kai nake aure!" Yana kallonta yace "do you think is okay kidinga fadama Mom every bit of details na auren mu?" Kanta akasa dan tasan takalleshi bazata iya bashi amsaba tace "ai Maman ka ce, ba wata naje na samu na fadimawa ba, and Mom is a strong Mom strong

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login