Showing 96001 words to 99000 words out of 110563 words

Chapter 33 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21062

tasan diyarta is a strong girl! Tabata maganan Rashida yayi sosai Buba yace  nasan an cuceku, nasan so many things are not right but Rashida dubi sama kiga Buba yadaga hannu yanuna mata sama hakan yasa yace  shi Allah baya bacci kuma baya yafe hakkin wani akan wani, an kashe Mama amman an kwashe mata zunubi muna kyautata zato Mama yar aljanna ce, karshen ta yayi kyau Rashida meyafi haka? Buba yace  trust me Allah zai sakama Maman ki, zaki sha kallo nan gaba, Allah zai saka mata wallahi kuwa Buba yayi maganan kafin ahankali yace  Rashidah Mahaifiyarki ta rasu da buri aranta akanki na ganin kin zama likita ki ijiye komi a gefe a matsayinki na yar halak kiyi rayuwan cika burin mahaifiyarki become a Doctor, baki samu kin ceci mahaifiyarki ba but you can save other patients like Maman ki right? Gyadamai kai Rashida tayi tanajin wani karfi data dade bataji ba, Buba yace  become somebody in life da zaki bawa mahaifiyarki daraja jama a su kalleki ace ohh yanzu yarinyar diyar mai HIV dinnan ce tazama haka Allah kabani y a kamanta nima hawaye ne ya gangaro daga idanunta Buba yadaura hannunshi akan kirjinshi yace  Rashida ke jikana ne! Naji labarin abinda Riyad yamiki idan kinaso yanzu zan iya baki kudin ki biyashi ya sauwake mikin, kome kikeso I will support you and fight for you tun ranan namiki alkawarin nan kin tuna? Gyadamai kai Rashida tayi ahankali Buba yace  kinason nabaki kudin kibiyashi ya sakeki? Shiru tayi tana tunani, Riyad insult her pride and ego, he used kudi sabida yasan batada su, ita kuma she will prove to him cewa ita Rashida ce diyar Mama, she will work hard for that money and pay him duk randa tagama makaranta, ahankali ta kalli Buba girgixamai kai tayi har kasan ranshi yaji dadi amman azahirance yace  mesa? Cikin muryanta da baya fita tace  inaso nabiyashi with my hard earned money, zan gama school zan fara aiki zan biyashi Buba basaika tayani biya ba shiru yayi yana kallonta yace  naje dake kauyenmu toh? Girgixamai kai tayi ahankali tace  gobe zan resuming zan dinga latti na bika cikeda damuwa Buba yace  to me kikeso namiki tell me komenene zan miki, me kukeso ? Shiru tayi sai chan tace  yunwa nakeji Buba .
EPISODE Wani iri Buba yaji yanaji data gayamai yunwa takeji da sauri yatashi yace  bari inada abinci yawuce yana dan dingishi danya tsufa tabishi da kallo wlh tana sonshi sosai, mota yaje yadauko wani kula da ruwa da spoon bai damu da yanda ake kallonsu ba yadawo yamaida takalminsa ya zauna yashiga budewa yace  dambu kishiyarki ta dafamin yau nace mata ni wajen amaryana Rashida zani
kallonshi kawai take yanda yakeyi da sauri da sauri saiya debo Dambu a spoon yakai bakinta tsayawa tayi takalleshi ta kalli hannunshi da abinci da yanda yake kallonta sai taji zuciyanta ya tsinke ahankali tace  Buba kai kadai nakeda shi yanzu tunda Mama ta mutu ta banni Jaaaa idanun Buba sukayi da sauri cikin dauriya yace  imaza ci kisami karfi bance ki sakemin kuka ba kinaji
gyadamai kai tayi tabude baki hawaye na gangarowa ta karba taci haka yadinga bata abincin taci kusan rabin flask din yabata ruwa tasha tsaf Buba yace  tashi to muje na ijiyeki agidanki sai nawuce kauye biyar tayi batai musu ba ta mike tsaye suka wuce mota ta shiga baya ya shigo shima sannan driver shi yaja motan har GRA Buba yakaita akofar gidan sukai parking, wata kaka yadauka yaciro yan 500 bandir daya yakama hannunta yasa aciki yace  ki rike kudin nan ki boye kinji, kome kike bukata ki saya dasu ina wayanki ? Ahankali tabashi wayan number shi yasa mata yace  kome kikeso ki kirani kinji, kimin flashing yanzu nayi saving number ki, idan kunyi hutu a school kinaso kizo kauyenmu hutu ki gayamin zansa a kawoki okay?
Gyadamai kai tayi Buba yace  promise me bazaki kara kuka ba sabida hankalina ya kwanta kinga na tsufa dai ahankali tace  I promise murmushi yamata yace  sauka kitafi to Allah miki Albarka ahankali tace  Ameen Buba nagode sauka tayi Buba yasauke glass yana lekata yace  saida safe gyadamai kai tayi tana taba gate din aka bude mata security cikeda girmamawa yace  welcome Ma gyadamai kai tayi adan kunyace ya matsa mata ta shige tana kallon gidan daya hadu ta hango uban cefene Security yace  Ma Oga ya aiko da kayan abinci gasuchan idan kin shiga saimu shigar miki dashi Ma gyadamai kai kawai tayi awkwardly tawuce wajen kofan to ita ai bamata dauki key ba kayan abincin take kallo buhun sinkafa, semo, Irish, eggs, drinks, spices, yam, potatoes, beans, fruits da buhu na nama dana kaji dasuka fara tsiyaya sabida ba a saka a fridge ba batanan, key tagani jikin kofan ya makala mata hakan yasa tadauka ahankali tabude kofan kawai gabanta na fadi ta shiga cikin hadadden falon securities din sukace zamu shigo ma tsayawa kawai tayi cikin falon suka shigo sun daddauki abubuwa suka tsaya cikeda girmamawa sukace  ina zamukai ma ? Rasa abinda zatace tayi ganin duk kallonta suke yasa tace  ki& & kitchen wucewa kitchen sukayi suka shiga store suka ijiye, suka dauko naman suka jejjerea komi tsaf a freezer suka shigar da drinks sannan suka fito har lokacin tana tsaye a wajen sukace  mun gama Ma, good night gyadamusu kai tayi suka fita saida taga sun rufe kofan sannan ta sauke ijiyan zuciya ta kalli katon falon bata taba ganin gida mai kyau in her life like this ba, yanzu agidan nan zata zauna harsai ta biyashi? Tadade tsaye awajen kafin ahankali tawuce sama tana tafiya kafan kadan gaban dakinta na jiya ta tsaya tadade tsaye ahaka sannan tasa hannu tabude kofan, ahankali ta shiga, manya manyan jakunkuna tagani na shopping manya manyan ciki kayane ta hango ciki saikuma daya na su cream da kayan shafa daya kuma taga su chocholate da snacks daban daban.
Irinsu biscuits, Pringles da komi, shiru tayi saikuma ta zauna kasa tareda ijiye jakanta tai shiru tana kallon komi kuka takeso tayi but ta hana kanta, magrib dataji ana kira yasa ta tashi tawuce bayi kayan jikinta tacire sun gaji sunyi datti sai kallon washing machine dake bayin tayi kafin kawai ta matsa ta ijiye kayan cikin lundry basket tadaura towel tafito ganin babu sabulu abayin tafito tana kallon jakan data hango sabulai tai shiru tana tunani idan yace suma saita biya fa, saikuma ta tuna yace zai sauke hakkinshi na mijinta kudin daya kashe kafin auren ta dana Mama kawai yakeso, dudda haka takara shiru kafin ta daure kawai tasa hannu tashiga ciro abinda ke ciki taga akwai body wash face wash dakuma set na su shampoo da conditioner da cowash da body scrub tawuce bayi.
She wants to go back school gobe hakan yasa ta wanke kanta da shampoo da conditioner ta sannan tai wanka da ruwan zafi sosai bakaramin dadi taji ba tai brush sannan tai alwala tafito tasake dawowa ta tsaya tana kallon kayan wani farin rigan bacci data hango saman wani jaka tadauka takala spaghetti hand gareshi daurewa tayi tasaka tasa hijabi tai salla jin jikinta na mata kayau kayau yasa tasake dawowa wani cream ta shafa ta feffesa turare tacire na towel kanta ta maida bayi sabida gashinta yabushe tadawo jakan again dan duba ko akwai comb ganin babu yasa ta zauna saikuma ta kalli black bag nata da sauri tawuce tadauka tabude 200k na sadakinta tafara kwasa taja drawer gefen bed nata tasaka su ciki da 50k Buba sannan taciro lab coat dinta dataga duk yayi squeezing ga datti ta tafi bayi bataga omoba kawai ta kwara bath wash nata ta wanke dashi saikuma tafito tana tunanin yanda zata shanya kayan.
Akwatin dazu da safe tabude taciro wani pink hijab tasaka sannan tasauka kasa rikeda lab coat din nata adan karamin bowl tabude kofa tafito ta tsaya gaban flat nata tana kallon yanda har an wanke wajen jinin naman, securities din na chan dakinsu dake wajen gate tana jiyo muryansu suna hira abinsu bataga wajen shanya ba daidai lokacin taga sun fito suna kokarin bude gate ana sako kan motan ciki ta ijiye bowl din ta takoma ciki da sauri tawuce sama ta maida kofanta tarufe tasaka key.
Parking yayi dayake da kanshi yayi driving yakalli gaban dakin tareda yin murmushi intentionally yasa akabar kayan awajen cus yanaso tai engaging da activities na gidan ta tadan sake ta warware, yakalli bowl din lab coat din kafin ahankali yadauka ya zaga backyard da kanshi ya shanya mata yanaji yanda kayan ke kamshin shower bath that means bataga omo ba, dawowa yayi yabude falon ya shige ya maida kofan yayi locking yawuce kitchen, detergent ya dauka yasa a bowl din yahayo sama har gaban dakinta ya tsaya sannan yaduka ya ijiye bowl da omo yawuce ya kunna tv nan falon sama kafin yabude dakinshi ya shige.
Salla tayi na isha i tanajin karan tv matsar da komi tayi tafito da komi na jakanta tayi babu some books nata Allah sa bai saida gidansu da yan littafan ta da credentials nata suke cikiba, shiru tayi saikuma ta jingina kanta gaban gado tai shiru tana tunani daban daban hawaye ne ya gangaro mata a idanu kafin bacci yayi nasaran kwashata awahale ahaka tana zaune daga ita sai yar rigan iya cinyanta ga gashinta a sauke.
Mugun sanyin AC yasa tafara rawan sanyi ta tashi tahau gado dasauri taja bargo ta dukunkune wuraren 6 tabude idanunta da kyar ganin gari ya waye yasa ta tashi zaune da sauri tasauka daga gadon tafada bayi tayi brush da alwala tafito tasaka hijab tai salla tai karatun Al Qur ani tunawa da laboact nata yasa ta mike tsaye da pink hijabin ta bude kofan tafito tanadan lekawa ganin bakowa yasa tai staircase tashiga sauka kasa hartai wajen kofa tana kokarin budewa kaman ance ta kallo wajen saitaga labcoat nata akan kujera an goge, dan jim tayi tana kallon lab coat din kafin tawuce tasa hannu tadauka tawuce takoma sama ta maida kofanta tarufe ta ijiye kan gado kawai saita shiga kaye kayan abubuwan cus tasaba aiki dasafe gashi akwai time before 9 duka kayan ta cicciro ta jera a wardrobe sannan tadauki wani atampa mai red embellish lace yayi kyau tasaka, dinkin riga da skirt, tadauki red veil ta ijiye sannan tafada wanka tayi wankan tafito ta shirya tasaka kayan dasuka mata mugun kyau babu comb hakan yasa tai parking gashinta like that kuma yayi kyau saita sake zama tadauki waya taga yanzu ma 7:30 na safe yayi.
Tashi tayi ta tsaya ta kalli kanta a madubi har yanzu idanunta a kumbure but sun soma washewa and fuskanta ma jan dayayi yasoma washewa tayi wani irin shegen kyau, jikin aljihun lab coat nata ta kalla da aka rubuta Dr Rash tasake kallon madubi ahankali tace  Mama I will not give up on your dream kinji Mama, zan zama abinda kikeso na zama, zanyi karatu zan dage zan zama wani abu Mama in sha Allah hawaye ne suka ciko idanunta danne kukan tayi muryanta na dan rawa tace  Mama ina kewanki sosai but I promise I will be strong bazan kara bari makiyanmu suga kukana ba Mama Allah zai sakamana da ni da ke natafi school tasake goge idanunta tass ta gyara rolling datayi she looks so pretty Ya Allah, crocs din tasaka daidai kafanta kuma yamata kyau ta tsaya tana kallo mutuwan Mama yasa batamasan inda ta zubar da crocs din da Mama ta siya mata ba, goya jakan tayi tabude kofan dakinta tafito tafara tafiya daidai tahau kan staircase taji an bude kofa da sauri tashiga sauka daga stairs din dan bamataso ta ganshi wlh daidai tana zuwa wajen kofan falon tashiga bude kofan but a kulle ga duk kamshin sa yacika falon, jin takun tafiyanshi daidai yasa da sauri ta matsa gefen kofan tawani juyamai baya, binta da kallo yayi kafin yasa hannu ahankali yabude kofan yafice saida taji yafice sannan tajuyo ganin bashi awajen yasa itama tabude kofan ahankali tsaye taganshi jikin wani arniyan black bulletproof jeep yana sanye da babban kaya yadaura wani alkyabba dake walkiya yana haske yasaka hula akanshi but bai daura rawani ba tukunna, hada ido sukayi da mugun sauri tadauke kanta babu alamun any jokes a fuskanshi yabude mata bayan motan yace  gobe driver ki zai fara aiki zoki shiga i will drop you off haderai Rashida tayi batare data kalleshi ba tace  I can go da kaina babu abinda zanyi da motarka tai maganan tana saukowa daga matattakalan tazo zata wuce karaf Riyad yarike hannunta a zuciye tadago kanta ta kalleshi tace  don t to& & .. hakanan jitayi maganan ya makale a wuyanta sabida yanda yamata wani shegen kyau da kwarjini kayan sarakunan dake jikinshi yasa yawani cika mata idanu dasauri ta dauke kanta daga kallonshi tashiga kokarin kwace hannunta amman ko gezau babu wasa kan muryanshi yace  matan Riyad can never enter public abin hawa take note! .

EPISODE Dasauri Rashida takalleshi jin abinda yafadi saikuma ta dauke kai takasa magana, cikin dan kakkausan murya yace  nima bawai inayi bane cus i want to do nope, as long as igiyoyin auren mu are intact you re my responsibility and dole na cika hakkokina dake kanki you are too small kisa Allah yakamani dasauri tadago kanta ta kalleshi wani shu umin kallo ya zuba mata yace  get in cus I don t want to ever force you kiyi wani abu, this is hakki akaina! Abu tahadiye awuya kaman ta shakeshi ta fizge hannunta da karfi tanaji kaman ta kurma ihu cikeda taurinkai tashiga bayan motan ta zauna kaman bataso ta shiga, driver dake wajen gate yataso dasauri ganin ta shiga ga mamakinta gani tayi yashigo bayan shima dasauri ta kalleshi danta dauka agaba zai zauna, gyara zama yayi sai kamshi mai bala in dadi yake, matsawa tayi chan karshe da sauri driver na zuwa ya duka yace  Barka da fitowa Ranka shi dade, Allah ya taimakeka, Allah ya karamaka daraja! Gyadamai kai Riyad yayi ahankali, driver yasake dukawa yace  barka da fitowa ranki shi dade uwar dakina juyo da kanta Rashida tayi haushin Riyad yasa tawani ballamai harara, da hannu Riyad yamai alamu ya rufo musu kofan, rufowa yayi yakoma ya shiga gaba yatada motan sukabar gidan sundan shiga hanya chan Riyad yace  what time zaku gama? Kaman bada ita yake magana ba tai banza dashi, anatse yace  ban baki izinin hawa any form na abin hawaba, I asked you wat time zaki gama? Yayi maganan yana zubamata idanu kaman bazatai magana ba chan tace  nima bansani ba authoritatively yace  mukaje zaki shiga ciki ki duba roaster and call me ki sanar dani, i will send my driver ya dauko ki cikin fushi tace  ko an tashi inada wajen zuwa? Ahankali yace  where? Shiru tayi tai banza dashi unexpectedly kawai taji ya fizgota ta taho jikinshi lokaci daya hannunshi yasa kan waist nata yarike gam, arude ta kalleshi jin yanda yakama mata kwankwaso hada idanu sukayi kawai taji gabanta na mugun faduwa sabida yanda yake mata wani shu umin kallo takasa magana sai kokarin kwace kanta datakeyi takasa tana numfashi da sauri da sauri, hannunshi akan waist nata kaman shock, strictly yace  next time idan namiki magana open mouth ki bani amsa yadanyi shiru kadan yana kallon fuskanta kaman yau yafara ganinta kafin yakara pressing waist nata dayaga tawani zabura yace  ina zakije after school ? Wlh she s breathing way to fast sabida yanda take kan jikinshi ga wani irin abu da hannunshi kema waist nata, ga driver na tukasu kuma babba ne driver ba yaro ba, kunya ma taji tanaji kaman ta shige kasa batasan sanda tace  saloon zani nai kitso 4 zamu gama yana kallonta yace  bazaki je ba! Da sauri ta kalleshi dudda gabanta na faduwa saida ta turomai baki cikeda stubbornness, lips dinta yabida mayen kallo yana tuna randa yayi kissing nata dasauri yazare hannunshi daga waist nata hakan yasa tasauka daga jikinshi da sauri takoma waje ta zauna har lokacin kirjinta bugawa yake har sukakai school babu wanda yasake magana Riyad yace  ina zamu ijiyeki ? ahankali tace  gynae har gaban department din sukaje sukai parking dasauri tashiga kiciniyar bude kofan saikuma ta tsaya chak takasa magana duk yana kallonta ahankali yataho wajen mannewa tayi jikin kujera kallonta yayi suka hada idanu dasauri yadauke
Tadauke kanta cikeda jin haushin shi tarasa mesa gabanta ke faduwa ahankali yasauke hannunshi daya kan cinyanta da sauri ta kalleshi hada ido sukayi hannun nakan cinyanta yana kallonta bayama kiciniyar bude kofan ture hannunshi tayi da sauri hakan yasa yakoma ya zauna wajenshi chan yace  open door for her Dasauri driver yace  to Yallabai haushi Rashida taji yakamata wat?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? o da gangan yahana abude mata bude mata akayi tajuya da sauri zata fita karaf taji yarike hannunta da sauri tajuyo ta kalleshi yana kallon cikin idanunta yace  today should be the last day dazaki bar gidana bakiyi breakfast ba haderai tayi hannu yasa a aljihunshi yaciro kudade dabaisan yawansu ba zai samata a hannu azuciye tace  ni banson kudin ka karike kayanka, Allah kyauta hannunta yabude da karfi yasa kudin a tsakiya yace  hakki nane na ciyar da matata! U can trash them kika fita idan kinga dama but dai use it eat yana maganan yasaki hannunta zata ijiye kudin kan kujeran azuciye yace  kika ijiye kudin nan bazaki school din nan ba saikin deba kin tafi dasu sosai taji ranta na baci ganin zai samata bakin ciki yasa kawai tajuya fuuuu

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login