Showing 30001 words to 33000 words out of 110563 words

Chapter 11 - SANYI DA ZAFI BY M SHAKUR

M SHAKUR   

29 Jun 2024

21048

na isowa chak ya tsaya wajen kofan batare daya shigo ciki ba yana kallon su, jan Rashida Madam ta shigayi da karfi gaske ganin yanda take dukan Hussy, sauran yan aikin suna banbare hannunta daga jikin Hussy sunajan Hussy da bakinta yayi jina jina da jini harda hanci baya suka kwasheta da kyar daga hannun Rashida, Madam data rike Rashida cikin tsananin bacin rai tace  fighting awajen aiki are you too Mad? Rashida wat is this why did you beat her up like this? Itafa idan tana fushi bata gane kowa, kabar da hannun Madam tayi daga jikinta a haukace kaman ba Rashida ba cus ranta yabaci tace  dalla sakeni kekuma Malama tajuya zata closet nata cikeda taurin kai duka ma aikatan har Munir saida yakalli Rashida yasake kara kallonta jin abinda ta gayama Madam, Hussy dake haki an riketa tace  Ma kinga halinta ko saisa all worker ke cemata psycho, kolomental ce wlh, mahaukaciya ce very weird girl, shegiya yar shaye shaye, an gayamiki bamusan asalinki bane, uwarta nada HIV! Chak Rashida dake tafiya ta tsaya kaman kankara, ihu Hussy tayi ganin ta tsaya chak da tafiyan datakeyi that means maganan ya shigeta tace  ai duk munsan sirrin ta Ma, harnan akazo tundaga layinsu aka gayamana we should be careful with her tanada HIV Mamanta ma nadashi, bamu gayamiki ba Madam sabida karki koreta cus munsan she needs this job for her virus drugs da Mamanta, amman shine zata kama dukana ba ban mata komiba bayan tanada wacce tafi chanchanta adaka islamically agida, diyar fasika kawai! Wani irin juyowa da Rashida tayi zaka dauka zakanya ce ta taho da gudu tareta Madam tayi tace  where do you think you re going wani irin hankada Madam Rashida tayi saida Munir yatare Madan da sauri dan inda tafadi wlh saita karye, Hussy na ganin haka ta wuce da gudu tabi gefen Riyad ta gudu tafice da gudu Rashida ta taho itama tsabagen fushi ko ganin gabanta batayi ahankali Riyad yadaga kafanshi yashigo ya tare kofan yayi blocking nata, hakan yasa ta dago jajayen idanunta takalleshi adake cikin tsananin fushi da zuciya tace  ka tashin mini daga hanya Madam da Munir ya daga kyar tace  it seems da gaske yarinyar nan is mad, call security namu and call the police yana kallonta ta glass batare daya dauke idanunshi daga kallonta ba yace  don t call anybody cikin kumfan zuciya kaman zata fashe tai wani irin ihu tace  nace ka tashinmini daga hanya strictly yace  you re not going anywhere! Wlh ayanda zuciya ke daukanta kaman ta dagashi ta yar takeji kawai tasan batada karfin ne, yanda hannayenta ke rawa da jikinta yasa kawai ta juya fuuuu tawuce dan bence din dake wajen ta zauna tai folding hands dinta akirji duk yan dakin kallonta suke she s shaking, sai alokacin yakalli Munir yace  get first aid box go and attend to that girl, yakalli Madam da sauran yar aikin dake kallon Rashida da mamaki kaman yau suka fara ganinta yace  ku wuce kutafi cikeda mamaki Madam tana kallonta tace  this is your last day here duk wucewa sukayi suka fita yarage Riyad kadai dake tsaye awajen kofan dan kwalinta dake kasan dakin ya kalla ahankali ya shigo ya duka gently yadauka dusting nashi yayi sannan yataho inda take zaune kanta akasa tayi folding hands a kirji ahankali ya yafa gyalen akanta.



Dago kanta tayi tazubamai jajayen rinannun idanunta yanda yara masu taurin kan nan sukeyi tace  ina ruwanka dani? Wayace katabamin gyale na? Wat is your business with me? Nabar aikin naku dagayau nima, bazan kara aiki inda wata ta kira Mamana& & . Saita kasa karasa maganan sabida yanda abin ya tsayamata awuya saikawai tajuya mai baya da sauri takai hannunta ta sharce hawayen daya soma zubomata, data sharce da wani yasake zubowa sunki tsayawa yakai almost 1min yana kallonta sannan yajuya ahankali yafice tareda maida kofan yarufe kaman jira take fashewa tayi da kuka haryafara tafiya yajuyo sautin kukanta chak ya tsaya har shesheka takeyi yakai kusan 1min ahaka sannan yabar wajen, kusan 5min tayi tana kuka sannan ta goge fuskanta tass ta tashi tawuce drawer ta ta shiga kwashe yan small small tarakacen datake dashi awajen uniform nasu tabar musu sannan ta goya jakan abaya ta tsaya takara goge fuskanta tass bazaka gane tai kuka ba unless u look into her eyes tafito sai kallonta ake a reception amman ko kallonsu batayiba ta wuce tafita ta tafiyanta gida.


JOIN MY WATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/Ckm5Bo7CcqR1NYkgT0HEvR
=ث? SANYI DA ZAFI =ث?



'

EPISODE 1?? 4??

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ChfonTBUkdg8q2KIWCSk46 Assalamu alaikum. my name is Faredah Haruna Mamuda the founder of REEDAH'S EMPIRE, i base in kaduna state we are your number one home appliances no (SCAM ZONE) we are 100% legit all our items are from Lagos,Egypt,Turkey and cortonor we do delivery nationwide thanks u'll


Wuraren 3 Mama na zaune tsakar gida tana gyaran shinkafa ta kunna radio ta ijiye gefenta saman tabarma tana sauraro taji an turo kofa an shigo hakan yasa ta kafa ido taga wazai shigo bakuwa tayine saitaga Rashida sosai gabanta yafadi ganinta cus bata taba ganin Rashida ta shigo gida around this time ba, kallo daya ta mata tagane tai kuka dawuya ne Rashida tama wani abu tai kuka, ita kadai ke iyasa yarta kuka dasauri ta ijiye tray shinkafan tace  lafiya menene kika dawo dawuri haka? Murmushi ta kakalo tace  Mama kaina ke ciwo sosai saisa nadawo tai maganan tana zama kusada Mama kanta Mama ta taba tace  bari na kawo miki vitamin C kisha tashi ki cire jallabiyan kisha iska tashi tayi tawuce ciki Mama tabi jakanta dayay strange girma da kallo sai kawai ta jawo tabude ganin karikitan ta ne ciki yasa da sauri ta tashi tabita daki tana tsugunne gaban ganamasgo tana neman kaya Mama tace  an koreki wajen aiki ne ? Dago kanta tayi ta kalli Mama zatai magana Mama tace  karki kuskura kimin karya an koreki daga wajen aiki ne? Ahankali tace  Madam dina tace yau ne last day na aiki na a hotel dinsu waje Mama tasamu dasauri ta zauna jin jiri zai dibeta tace  Meya faru tell me everything Mama tariga ta ganota hakan yasa tafadima Mama komi ba karya, ba karamin baci ran Mama yayi ba tace  sau nawa zan gayamiki ki dinga hakuri arayuwa Rashida eh? Zagi na kari ne? Koko zagi na nunawa ajiki ne? Dan an zageni sai mene dasauri Rashida ta kalli Mama, Mama tace  yes dan wata ta zageni and so wat dazaki hau fada awajen aikin ki kina hankade Madam dinki har sau biyu mai hotel din gabaki dayama shima kinmai rashin kunya ahankali takai hannu ta goge hawaye tace  Mama bazan iya daurewa azageki agabana ba ko ace wani abu mara kyau wlh saikuma tarushe da kuka tace  narasa me nayima yan layin nan duk inda nake aiki sai sunsan yanda sukayi sukaje suka batani su fallasani, wlh kowaye meyi ban yafemai ba tabama Mama tausayi amman kawai saita wuce tabude drawer tadauko hijabinta har kasa ta saka da sauri Rashida ta mike tace  Mama ina zaki? Cikin dan masifa tace  ina zani? Ina kuwa zani inba wajen aikin naki ba naje nabada hakuri itama yarinyar a nunamin gidansu naje nabada hakuri, idan babu aikin nan tayaya zaki gama makarantan ki eh? Me zamuci? Dame zaki sami kudin siyan tufafi? Ga wayanki ta lalace baki dawo da itabama that means bata gyaruba duk ina zamu samu kudin nan kafin kisami aikin nan kin manta kalan wahalan dakikayi eh? To zuwa zanyi nabada hakuri dasauri ta taho takama bakin hijabinta tace  Mama dan Allah dan Allah karkije kinji Mama fizge hijabinta Mama tayi tace  inda bakiso kisani naje nabada hakuri ai da bakiyi abinda zai tursasani inje ba, yau ko basu karbeki ba dolena naje na bada hakurin abinda kikayi kinma mutanen dake gaba dake reni sannan kin fasama yar mutane hanci da baki baki Rashida tabude zatai magana Mama ta nunata da hannu tace  kimin shiru anan ta fizie hijabinta tajuya tafita fuu Rashida nada zuciya so tasan yarinyar didn t even realize how important this work is to them most especially towards karatun ta she will do everything ta tabbatar Rashida tagama karatun ta lafiya.

Kafa Mama tasa ahanya tana tafiya ahankali kanta na sarawa amman ta daure cus she knows what school din Rasheeda means to her, she will not allow her to sabotage mean na school fees payment nata ba, she just hopes darajanta zaisa sumata afuwa.
Tanakai junction ta tare keke da taso taje da kafa ne, amman taji jiri na dibanta bazata iyaba, har hotel din aka kaita ta sauko tabiya kudin tajuya ta kalli tamkeken hotel din almost duka inda Rashida take aiki ta sani musamman take binta dan tasan inda diyarta ke aiki incase wani abu yafaru she knows inda zataje neman diyarta amman bata taba shiga wajajen aikinta ba, ijiyan zuciya ta sauke jin yanda heart nata ke beating saita dan natsu kafin ta shiga building din motoci cike anyi parking, hotel din yahadu bana wasaba, karasawa tayi zuwa entrance door din zata shiga from yanda take looking security guard dake gadon kofan shiga reception din yace  Hajiya wakike nema? Idan zancen taimakone Oga yace jibi ranan juma a za ayi rabon abincin azumi you can come by 10AM ahankali Mama tanuna kanta tace  nine Maman Rashida sannunku da aiki, Rashida na aiki anan maybe kasanta, to tayi laifi ne shine nace bari nazo nabawa Oganta hakuri dan Allah akomar da ita sannan nabama yarinyar hakuri kallon Mama sukayi sannan suka kalli juna kafin daya ya nuna mata kujera dake chan gefe wani plastic chair yace  guest da ma aikata kadai ke shiga ciki jeki zauna achan Oga nada baki amman zai fito anjima kadan sai a gayamai Mama batai musu ba tace  toh wucewa tayi zuwa kujeran dasuka nuna mata ta zauna tabuga tagumi tai shiru burinta kawai karsu kori Rashida addu anta kenan, gabanta sai faduwa yake cikeda fargaba.





Tunda yaje office nashi yayi shiru bakin dasukayi ma yawanci Munir ke kulasu, agogon hannunshi kiran Rolex ya kalla 5 tayi na yamma kaman an tsikaresh ya mike duk kallonshi sukayi  excuse me yafadi tareda wucewa wajen kofa yafice Munir yabishi da kallo kafin yacigaba da abinda yake samin kanshi yayida shiga elevator ya sauka kasa, he doesn t even know why he s doing this but samun kanshi yayi da zuwa hanyar changing room din ganin kofan wangale abude yasa yadan leka ciki babu kowa wajen fuzar da iska yayi yajuyo yafito daidai Madam zata shigo hanyar chak ta tsaya ganinshi surprisingly tace  Yallabai wani abu kake bukata ? Kaman bazaiyi magana ba saikuma yace  where is she ? Kallon hanyan Madam tayi tace  wa she? Oh mahaukaciyan nan ? Dan lumshe idanu kadan yayi hakanan yaji kalman azuciyanshi yadai daure bai nuna wani abuba ya kalleta, dasauri tace  ta tatare kayanta ta kwashe komi na locker ta tatafi tabar aikin da kanta kafin mu mata official kora yanda taga yahade fuska yasa dasauri tace  sorr& . Ahankali yace  sack the other gurl Hus& . Cikeda Mamaki Madam tace  Hussyn Yallabai ? Babu wasa akan fuskarshi yace  I don t want her working for my company, just compensate for the injury, give the other gurl a call tadawo aiki yana maganan yawuce baki Madam yakasa kulluwa tana kallonshi, yarinyar data barar da ita yake cewa akirata back, wacce aka jibga yayi sacking, dan ijiyan zuciya tasauke aranta tace  his company his rule! Tawuce ta tafi office nata.
Wucewa kawai yayi yabar wajen yafito, security daya budema wani guest kofa dazai shigo ne ya hango yallabai hakan yasa yashigo ciki da gudu daidai zai shiga elevator yace  Yallabai barka da hutawa dama wata mata ke nemanka awaje wani kallo Riyad yamai irin wata wa? Shi kuwa? Dasauri security yace  tace wai itace Maman yarinyar da aka kora tazo tabada hakuri tana waje, she s Rashida s Mom Sir hakanan Riyad kawai yaji gabanshi yafadi but yadaure yace  why is she sitting outside? Dan sauke kanshi kasa Security yayi yace  uhmm Yallabai cewa akayi cutan kanj& &  fuuu Riyad yawuce zuwa entrance door din kafinma abudemai kofan dayake glass door ne yana iya hangota yanda tazauna kan kujera tayi tagumi tana kallon waje daya cikeda tsananin damuwa and kana kallon matan kasan she s really sick she looks so skinny and pale jiyayi zuciyanshi yamai ba dadi sosai yanda security sukai trashing nata awaje haka, dasauri yafice bayan an budemai kofan yayi wajenta direct yana zuwa kawai saiya duka cus bemasan mezaiyi ba, she s the mother of the girl that save his life kome yayi bai biyataba, cikeda girmamawa yace  Mama firgigit Mama tadawo daga dogon tunani datake tajuyo ta kalleshi, dasauri tace  Naam Bawan Allah kaina mai wajen nan nazo nabada hak& .. kafin takarasa maganan dasauri yace  Mama hakanan Mama taji yanda yakirata yataba zuciyanta, yanda yakira sunnan just touched so many things a zuciyanta kawai sai hawaye, life and sickness nata have made her so emotional, muryanta na rawa tace  dan Allah dan Allah kuya kuri nasan Rashida da zafin zuciya ga fada ga taurin kai, kome akace tama yarnyar nan nasan tayi dan Allah kuyakuri kurufamin asiri kada ku koreta daga aikin nan dan Allah ku taimakeni tai maganan tana jan kujeran baya zata duka dasauri Riyad yakama knees nata ahankali yace  Mama dan Allah karki rokeni, ban koreta ba zata iya cigaba da zuwa aiki da sauri Mama ta kalli fuskanshi tace  da gaske? Gyadamata kai yayi yace  eh ijiyan zuciya Mama ta sauke tace  to inane gidansu yarinyar naje na bada hakuri ahankali yana sakin knees nata yace  basai kin bada ba lafiyanta kalau Mama, is just normal misunderstanding da kananun maganan yara yajawo fadan kada ki damu kinji gyadamai kai tayi tace  Allah maka albarka murmushi yamata kadan baice komiba, Mama tace  bari natafi gida to Alhamdulillah nagode nagode nagode kaji daga yanda take maganan kasan hankalinta ya kwanta gyadamata kai yayi, Mama tace  to sai an jima  saida safe Mama yafadi ahankali, Mama ta wuce cike da farin ciki tafara tafiya kadan kadan sabida yanda kanta ke sarawa, tayi tafiya daya biyu uku ana hudu kawai ta yanke jiki tafadi, Riyad na tsaye yanama security magana sukaji karan fadin abu juyowa sukayi ganin Mama yasa dawani irin gudu Riyad yayi wajenta suma security din haka dago kanta yayi yana tapping hannunta yana kiranta.  Mama Mama Mama amman shiru dasauri yace  help me daukanta sukayi yabude bayan motanshi yasata yakoma yashiga gaba yatada motar sai wani babban private hospital dayake zuwa anytime yake Kano yana zuwa aka karbi Mama sai emergency yawuce office na Dr dinshi ya shiga Dr ya sallami patient dayake tareda shi yace  Ranka shi dade mai Martaba dan yatsine fuska yayi yace  don t call me that I have a patient tana Emergency I want you to be on her case fast tashi Dr yayi suka fito tare ya shiga emergency din, shi ya tsaya agaban wajen yarasa yanda zaiyi sai kuma yakoma office na Dr ya zauna, yana nan zaune yana jiranshi har aka kira magrib saiya tashi yafito yawuce mosque yana gani Munir na kiranshi yaki dauka salla yayi yafito yawuce ciki yakoma office na Dr yazauna sai gashi Dr yashigo dasauri Riyad yatashi yace  how is she ta farfado? Gyadamai kai Dr yayi yace  da kyar muka samu ta farfado amman tana bacci saikuma ya zauna ya kalli Riyad yace  kasan wacce ka kawo? Who is she to you? Batare daya amsashi ba yace  does that matter? Meke damunta? How can I help? Gyara zama Dr yayi yace  she s HIV patient! Yayi maganan yana kallon fuskan Riyad dayaga bai chanza ba saima yace  me da me take bukata yanzu ? Ahankali Dr yace  is like she s on medication so bahsine abinda ke damunta ba bashine kuma dalilin yankewan jikinta tafadi ba, abinda yafi komi damunta is BP, BP ta yayi raising sama sosai I don t think zan sallameta yau ko gobe ko jibi ma sef, sai ya sauko sannan zan sallameta, just get wanda zai zauna da ita and then drugs yashiga rubuce rubuce duk Riyad na kallonshi saida yagama komi sannan yanunamai takardan, tashi Riyad yayi yazaro wallet dinshi ya ijiye akan table din cikeda izza yace  take any amount kake bukata for drugs, bills, pin is 6648 yana maganan yawuce yafita akasaitance yasauka kasa dakin dayaga an shiga da ita yawuce shiga yayi ahankali ya tsaya bakin gadon an cire hijabinta daga ita sai riga da zani da hulan dake kanta an samata drip, shiru yayi yana kallonta sannan yajuya yafice daga dakin yawuce yaje motanshi yashiga yadau wayanshi yana shirin kiran Munir wayanshi yashiga ringing Munir dinne yana dagawa kafin yayi magana yace  Munir open file na employees dina a desktop get info na Rashida I need address nata ASAP kafin yayi magana ya katse wayan yayi shiru chan saiga Munir din yakira yace  suna Ranji, wajen tudun Murtala baimasan inane wajen ba but haka ya katse wayan ya kunna google map yashiga driving& .



Tunda tai magrib ta zauna tai shiru tana

18, August 2024
Suhaima

Gud

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login