Showing 1 words to 3000 words out of 66781 words

Chapter 1 - KWANKWASON JIMINA BOOK 1 hausa novel

24 Aug 2024

13596

[2/11, 5:10 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_NA_

_NANA HAFSATU_
_MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

*_arewabooks:mssxoxo_*


*_Free page :01_*


_wannan LITTAFI mai suna a sama kirkirarre ne, wasu sunayen, garuruwa, abinci, al'adu da sauran su duk kirkira ce. Idan hakan yayi dai dai da rayuwar wani ko wata... Toh akasi aka samu👌_

_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ_


________


_01_


*YANKIN BUNZA...*

Mutanen da suka fara zama a yankin bunza makera ne da suka tashi daga garin GAFA domin neman kasa mai arzikin zinare, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita mai ado..

Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin zinare, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta...

Wajen ya kuma kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari, Duwatsun su ne dutsen BUNZA da GAFA da FANNAU da SARBO da DENTEKA

Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Lawuna, da kuma kogin Nakare.
Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama...

Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin makeri da ya iya kera zinare ana cewa dashi BUNZA, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na BUNZA..

Dutsen BUNZA wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita 634,209, watau kwatankwacin kashi 52 cikin dari na girman jihar baki daya.

Yankin BUNZA ya hada da hamadar GAFA mai cike da tsaunika..

Mafi yawancin jama'ar yankin amce larabawa ne na Lebanon wanda ibtilai ya same su a daruruwan shekaru aka kwaso su zuwa kasar nijeriya. A ka kuma sauke su a yankin na BUNZA...Nan suka hayayyafa suka tara zuri'ah, akwai kuma barebari, Fulani da kuma Hausawa..

Yankuna da dama ne suka taru don shiryawa yadda zaa ci yankin BUNZA da hari. Domin yankin nada tarin arziki na zinare da suke hakowa. Kasashen da dama sun bukaci da yan usulin yankin su sayar musu da sansanin don mallakar wajen. Mutanen BUNZA suka ki amincewa da hakan...

Hakan yasanya yankuna dadama suka hada karfi da karfe suka kaiwa garin BUNZA hari. Suka kashe na kashewa suka farfasa duwatsun suka haqe suka kwashe zinaren. Sai babban uslin dutsen yankin na BUNZA shine bai karasa fasuwa ba daga gefe basu lura ba maharan. Suka ci garin da yaki suka kyale su.

Harin da aka kaiwa yankin BUNZA ba karamin rasa rayuka da arzikan tattalin yan garin sukai ba. Zuriya dadama sun mummutu. Wasu sun bar yankin sun gudu. Yayinda wasu da aka kwashe wa arzikin su nan take wasu suka futa hayyacin su. Wasu Suka samu tabin kwakwale da sauran su...

Bayan tafiyar lokaci mai tsawo....yankin BUNZA a yanzu babbar sana'ar yankin itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun 1970's harkar bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin...

Amman duk da hakan al'adar yankin ta na nan 'ya'ya mata basa karatun boko. Mazan ne keyi kawai... Suma da sum dan tasa za'a dakatar dasu sun daina sai su koma noma da sauran aiyukan karfi na gado.

Dan karatun da sukayi amfamin sa shine idan masu yawon buda idanu suka zo yankin. Kuma basa jin hausa ko fullanci ko larabci to sai yaran su mazan suyi mu'amala da su ta yaren turanci..

Haka zalika matan da sun dan tasa sun fara girma sai a aurar da su ga mazaje. Suma mazan ba Kuma masu shekaru bane. Dik Yara ne wadanda Suka dara matan da shekaru kadan.. Ba Kuma son ransu ake basu ba.

Al'adar itace namiji zai nome gona acikin kwanaki kadan. Ya yinda macen zata dinga zuwa bingi/tekun ruwa don debo ruwa a manyan bokitai ta kai gidan surukai. Har sawu goma duk kwana daya.

Kuma tsakanin tekun da inda gidajen yan yankin yake akwai tazara sosai a tsakani... Amman duk wannan uban wahalar da ake sha kowane yaro da yarinyar sai sun cikace hukuncin sannan a daura musu auren dole. Hakan Kuma zaka hakura... Domin KADDARA!! KOWA DA IRIN TAASA (Free book dina)👌

Mai karatu kada na isheka/ki da ratattako takaitaccen bayani game da yankin na jihar BUNZA... Bara mu tsunduma cikin labarin don jin yadda kowane bangare zai kasance...

Amman Kafin sannan bari na Kara maimaitawa Mutanen yankin BUNZA. Kyawawan asaline musanman zuri'ar:


*HAMIDNIYYA LEBANON*


*Zaune* Nawraah take akan yar katifar ta. Hannun ta rike da biro da paper tana rubuta ABCD da manyan baki.

Amnah ta shigaa dakin da sauri. Tana karkada mata hannu. Hakan yasa Nawraah daukar littafin da sauri ta cusa shi karkashin katifa biron Kuma ta boye shi acikin hular kanta.

Sai zare idanu takeyi. Kalo daya zakai mata kasan batada gaskia. Ta tsiri riko hannun Amnah tana ce mata.........




_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/13, 1:49 AM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_NA_

_NANA HAFSATU_
_MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

*_arewabooks:mssxoxo_*


*_Free page :02_*

__

  "Ba kiji ciwo ba ai ko?... Ki dai na tsalle tsalle Amna.." Ta karasa fada tana mai tambayar ta da hannu alamar menene?

Amna ta bude dan karamin bakin ta tana furta sunan yafendo a hankali. Ai kuwa bata karasa rufe bakin nata ba yafendo ta karasa dakin tana dogara yar sandar ta.

"Ah yafendo..." Cewar Nawra tana mai danne gefen katitar data zura littafin ta zauna akai.

"Amna tace baki da lafiya ko?"

Nawra ta kakaro murmushi tana kada kanta.

"Da sauki amma.."

"Tun dazu nake cewa kina ina ne duk su Layla suna nan.. Bake kwata kwata. Kwanakin nan na rasa gane kan ki. Na tambayi mahaifiyar ta ki tace zata miki magana. Sai Amna ce danasa Adam ya kirawo ki tace ai baki da lafiya "

Nawra dai kanta a kasa tana lankwasa yatsunta. Tace,

"Uhum... Amman da sauki ai. Nagode sosai"

"Sannu kinji?. Allah ya baki lafiya Nawrah. Kwanta ki huta"

"Tohm yafendo.. "
Nawra ta haye Kan katitar sosai ta kwanta tana mitsitsika idanu..

Yafendo ta mike dakyar tana dafe bango ta fice daga dakin

Nawra ta sauke katuwar bahaguwar zuciya ganin yafendo ta fita. Tadaga gefen katitar da saurin gaske ta zaro littafin, ta bankada kasan akwatin ta ta saka.

Amna na gefe tana kallon ta. Nawra ta riko hannun kanwar tata tace,

"Nagode sosai Amna tah.. Yau da yafendo taga Ina rubutun nan ai sai an kusa yankani. " Ta karasa fada tana kada Kai.

Amnah tayi murmushi kawai. Tana Wasa da zaren jikin rigar ta.

"Ungo biyar dinnan na baki jeki sayi wani abun"

"Nagode" Amna ta karba cike da farin ciki ta fice da sauri.

Nawra ta kwanta akan katifar ta ta lumshe idanun ta.... Fuskar ta ta gauraye da murmushi. A zuciya take karantowa. idanuwan ta na hasaso mata rubutun haruffan da zanen su. Ya yinda labbanta ke matsowa ahankali tana karanta su...

"Nawra.... Nawra .... Nawra" Layla ta kwada mata kira. Ta shiga dakin nasu.

Nawra ta mike da sauri tana duban ta tace,

"Kai Kib katse ni wallahi"

"Dalla aiken mu akayi..."

"Ina aka aike mu ?"

"Gidan bappah Auwalu."

"Tam. Bari nasaka hijabi"

"Dalla muje a haka kaman wasu manya zamu saka hijabi?" Cewar Layla ta fada tana yiwa Nawra nuni da kanta.

Nawra ta girgiza kai tache,

"Zan saka.. Ammi tace da hakan ake dorewa har girma. "

"Shikenan sai ki saka ai"

Nawra ta girgiza kai. Ta bude wardrobe din kayan su ta dakko hijabin ta ta zura... tana duban kanta a wani madubin su karami dake jikin dressing mirror dinsu..

Tsaf da ita kamar wata babbar budurwa ta dubi Layla dake nannade kasan zaren hannun rigar ta tace,

"Muje"

"Yauwa."

A tare suka futa daga cikin dakin sukayi hanyar fita daga gidan yafendo na daga can runfarta ta hango su tace,

"Nawra kinji sauki me? Layla ba ke kadai aka aika bane sai dakika taso ta?"

"Wai ba..." Bata karasa ba Nawra ta saka hannu ta gwabe wa Layla baki. Da Sauri tace,

"Na ji sauki yafendo yanzu..."

"Mashaa Allahu. To kuyi sauri ku dawo"

"Tohm" suka hada baki..

Fita sukayi daga cikin gidan. Layla ta dubi Nawra cike da mamaki tace,

"Ina tsoron ranar da su bappah zasu Kama ki..."

"Ba zasu Kama nI ba inshaa Allah.. "

"Toh Allah yasa... Ni kam Dadi nakeji bama yi, karatun nan ba fa wani Dadi ne dashi ba kinaji yan maza na fada"


"Ni dai inaso"

"To ai shikenan..."

Suna tafe suna hira hadi dawasa a hanya Suka karasa gidan bappan na su.

Basu dawani nisa sosai. Don hakan bazasuyi wata tafiya can ba Sika karasa.

Bakunan su dauke da sallama suka shigaa cikin gidan.

A zaure Suka ci Karo da shi Yana tafe Yana duban goro a hannun sa.

"Ahh.." Ya fada Yana kallon su

"Bappah Ina kwana?"

"Bappah Ina kwana?"

Suka shiga gayshe da shi. Ya amsa musu Yana duban su da Karin bayani.

"Bappah Wai Kai ake jira.." Layla ta fada tana duban sa.

"Ai gabi Nan dama candin zani ai. Muje ko?"

Ya nuna kofa.. suka matsa ya shige suka bi bayan sa suka futa .

"Zo mu biya dangaki.... (Dangaki shine sunan babbar gonar data mamaye rabin garin BUNZA. Gona ce data fi wani garin girma. Itace ake yankawa samarin garin idan zasuyi sure. Kowanne sai a shata masa wani yanki nadaga ciki ya nome. Shi daya ba dan tayi. Idan ya nome ita kuma amaryar dazaa hadasu sure. zata dinga ebo ruwa sawu goma daga Rafinrau (sunan babban rafi ne da wasu ke Kira da teku. Ance duk shekara ma ya kanci mutane sama da dari. To Nan amaren ke zuwa suna ebo ruwa daga rafin da take can bayan garin zuwa gidajen surukan su wato gidan iyayen mazajen. Su Kai su koma har sawu goma. Shikenan sai a daura musu aure. Gwarzon da gwarzuwa kenan. Amfamin noman da angob yayi shikenan sai suyita ci agidan auren nasu. Ruwan nan kuma haka za aita bawa amarya tana girki ko aikin abinci har adadin data evo Kafin aure. .. wannan wata babbar al'adace da Yan yankin BUNZA ke gudanarwa shekara da shekaru...


'Yau farisu ke nome gonar auren su da fiddau.. zo muje kinji?"

Nawra ta girgiza kanta ,

"Jeki ke kadai "

"Kinsan fada zaa mun agidaa idan ba ke. Idan mu biyu ne kuwa fadan kadan ne bama lalle ayi ba."

Nawra badan taso ba. Tabi bayan Layla suka nufi dangaki don ganewa idanun su noman karshe da farisu angon fiddau zai yi...

Bappah Muhammad sani ya karasa cikin gidan bakin sa dauke da sallama. Yayi hanyar sashen mahaifiyar su

Ya durkusa har kasa ya gayshe da ita. Ta amsa kanta a gefe cike da kunyar dan fari.

Duk yaran nata sun hallara. Bappah sani, Bappah Auwalu shine na biyu amman yaci sunan Auwalu Lawan, Bappah salisu da bappah Junaid sai kuma mace guda daya yakunbo aminatu. Wadda itace ta biyun karshe. Bappah Junaid ne autan Dadaa (yafendo)..


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/13, 5:49 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_NA_

_NANA HAFSATU_
_MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

*_arewabooks:mssxoxo_*


*_Free page :03_*



***Hajiya Fanta... Wato Dadaa mahaifiyar su Bappah Auwalu kuma kaka ga su Nawra dake kiran ta da yafendo...

Tana a zaune ne akan babbar kujerar parlorn.. parlor ne matsakaici dauke da saitin kujeru dai dai misali.

Yayinda yaran nata ke zazzaune daga kasa kowannen su yana fuskantar ta.

Dadaa tayi gyaran murya tace,

"Dalilin daya sa na kirawo ku nan gaba daya akan wannan taron abubuwa uku ne zuwa hudu... Kuma dukkanin ku nan babu wani dayasan dalilin hakan sai Allah mahaliccin mu. Sannan bana bukata wani acikin ku ya nemi bijerewa ko ince kawo wata shawara ta daban ga zantukan da zanyi. Ina fatan Kuna saurara?"

"Muna sauraron ki Dadaa" suka hada baki wajen amsa ta..

Dadaa ta kada kai ta cigaba da cewa,

"Allah ya muku albarka duka...Allah ya hade kawunan ku ya kauda fitnah a tsakani. Allah ya raya muku zuri'ah ya albarkace su.. Aamin"

"Aameen Dadaa"

"Aaameen"

"Yauwa ku saurari abunda Zan fada da kyau. Ku Kuma nazarci zantukana a kwakwalen ku. Kada wani yayiwa maganganu na fahimta a baibai ce. Sannan duk abunda na fada Ina fatan ya kasance mafi alkhairi agare mu baki daya"

"Aameen"

"Allah ya kara Miki lafiya Dadaa"

"Aameen... Maganar fitar da ni waje don gano menene gundarin wannan rashin lafiyar tawa ni Fanta na soke ta... Babu ita"

"Amma Dadaa...

"Ya isa karkace komai...sai da na ce muku da fari bana bukata wani acikin ku ya nemi bijerewa ko ince kawo wata shawara ta daban ga zantukan da zanyi. Ku ma kuka amince ko baa ayi hakan ba?"

"Anyi Dadaa."

"Tuba muke"

"Yauwa wannan magana ta futa na soketa. Dukkanin abunda Allah ya kadarta wa bawa na rashin lafiyar kai komai ma da sauran su. Allah ne kadai zai magance maka a duk sanda yaso.. sa'annan wannan lalurori nawa sunci kudaden da cikinmu basu ci ba. Garuruwa nesa dana kusa bawanda baa zaga da Ni asibutin sa ba don gano gundarin ciwo. Don hakan na hakura ni. Wannan ciwo bana warkewa bane .. Allah ne kadai zai mun maganin sa."

"Dadaa ki dai na cewa hakan"

"Me ake jira ne? Dukkanin munan kowa fa tasa yake jira... Mutuwarnan sai ta dauki kowa babba dayaro kowa ba Wanda zata Bari. Don hakan a kyale ni na zauna da ciwo na. Kankarar zunubai ce. Idan Kuma lokacin tafiyar ne yayi Allah yasa mu cika da Imani"

"Ki bar fadin hakan Dadaa"

"Magana ce ta gaskia... Allah ya sa mucika da Imani"

"Aamin Dadaa"

"Aamin"

Suka amsa mata dukkanin su. Dadaa ta Dan dubi fuskokin su.

Bappah Auwalu ita yake kallo, Bappah sani ma itan yake kalla data kalle shi sai ya sadda kansa kasa. Ya yinda bappah salisu kansa ke akan agogon dake daure a wutsiyar hannun sa yana saita lokaci. Bappah Junaid Kuma kansa a kasa.. Sai yakunbo Aminatu dake lankwasa yatsunta tana duban mahaifiyar tasu Dadaa.

Dadaa ta sauke katuwar ajiyar zuciya tace,

"Allah ya hade kawunan ku...ya kauda fitnah a tsakani. Amin"

"Aamin Dadaa"

"Aamin"

"Sai magana ta gaba akan yaran wajen ku mazan... Wadanda ke makarantar boko yanzu... Tun ba yau ba ahali da yawa na yankin bunza ke aibatar mu kancewa mu muna qafafa muna fatali da al'adar kaka da kakanni. Bama koyi da sauran mutanen gari... Ku dubi ibtila'in daya saukarwa yar wajen ku kalatacciyar al'adar jigilar ruwan Rafinrau zuwa ga gidan surukan ta akan hanyar ta rasu a sawu na bakwai... Wannan munanan al'adu naki jinin su bana kaunar su.. Don hakan tun kafin rasuwar mahaifin ku muka gama magana dashi muka yanke shawara.. Zamu tarkata komai namu mu bar musu yankin nan. Zaman mu acikin sa babban ibtilai ne musanman da zuriyar mu ce kadai ke da kadarorin zinarai ragowa na dutsen bunza..."

"Mashaa Allah Dadaa... Wannan zance naki haka"

"Hakan shike Dadaa.. Allah ya amince"

"Amma Dadaa kina ganin Mutanen Nan zasu kyale mu mu bar yankin nan? Kinsan mugayen alkadarin su akan zuriyar mu"

"Babu abunda suka Isa suyi Mana Wanda Allah bai rubuta ba. Mu mayarda komai gare shi sai ya buda Mana kofa masaukakiya. Don hakan Kar ku wani damu da su. Idan aka sauya yanki sai a kyale yarannan maza suci gaba da karatun su. Matan Kuma a kyale su har zuwa sanda zasu tasa a aurar da su... Duk dai yadda ta kasance din..Kar a tsaurara akan matan nan"

"Inshaa Allah hakan zaai Dadaa."

"Wannan zance naki haka shike Dadaa"

"Toh Allah ya Mana muwafaqa"

"Aamin Yaa Rabbi

"Sai magana ta karshe.... Dukkanin dukiyar data ragemun a duniya na hadeta waje daya na kasata kashi uku. Kashi daya zaa ajiyeta ayiwa Yara aure idan sun tasa... Su Sameer, Khaleed, Ashiir da ashfeef, Ahmad, Kashi daya zaa bawa miskinan yankin nan wajen mararrabar Ballo Mai sardii.. kashi daya na rabata tsakanin sani, salisu , Auwalu da Kuma ke Aminatu.....

Duk sukayi shiruu suna sauraron ta. Ta daga Kai ta dora akan autan ta Bappah Junaid da kansa ke a kasa tace,

"Kason daya rage na karshe kuma na barwa junaidu shi kadai.... A nan na kawo karshen maganganun da zanyi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login